Yini Na Ashirin Da Biyu
Da gari ya waye, sai dabbobi da yawa suka yi sammakon zuwa fada. Haka kuma aka yi katari manyan mukarraban Sarkin su Dila da Kahuhu suka hallara da wuri. Da ganin yadda fadar ta fara daukar harami kafin zuwan nasu kuma suka yi zargin makasudin. Dila ya ce, “Na yi zargin kun bugu wannan sammakon ne don ku ji yadda kashen labarin Sarkin Ungulu zai kasanace?”
Sai kafataninsu suka fashe da dariya. Kahuhu ya ce, “Wato su ji ko da gaske ne za a iya samun labarin, kuma in an samu ya zai kasance ko?”
Wasu daga ciki suka ce, “Eh Gafarta Malam.” Tare da yin dariya.
Suka zauna aka ci gaba da tattauna irin wannan maganganu har zuwa sa’in da Basaraken ya fito daga gida. Fadar ta yi kawai yayin da yake kokarin zama a kan karaga. Har sai bayan ya daidaitu a kantan ne kuma suka ci gaba da gaisuwa daki-daki. Gama karbar gaiuwar kuma ke da wuya, sai ya juya ya dubi Kahuhu ya ce. “Alaramma, jiya muna cikin tattaunawa mun isa wata gaba da muka ce sauraren tarihi zai fi amfanar da mu fiye da gama-garin labaru da muka saba ji”
Malam Kahuhu ya ce, “Kwarai an yi haka Rankashidade.”
Sai ya ce da shi, “Ta ina za mu fara ne?”
Malam Kahuhu ya risina tare da cewa, “Sai inda ka ce ai, Yallabai.”
A daidai wannan lokaci kuma sai Sarkin Ungulu ya karaso fadar cikin sauri, ya gurfana gaban Zakin: “Ran Sarki ya dade. Ka dade ka yi karko!”
Haunawa suka ce masa, “An gaishe ka Sarkin Ungulu.”
Zaki ya ce da shi, “Yaya, an aika jakadun ko?”
Sarkin Ungulu ya ce, “Ai har ma an samu labarin da karun Rankayadade!”
Haunawan Sarki suka kara cewa, “An gaishe ka Sarkin Ungulu.”
Zaki ya turo kai gaba cikin alamta zakuwa da jin ta bakin Sarkin Ungulu. “Wane hali suke ciki”
Sarkin Ungulu ya ce, “Duk suna cikin koshin lafiya Rankashidade.”
“Madallah,” In ji Zaki, “amma me ne ainishin abin da yake faruwa ne?”
Sarkin Ungulu ya ce, “Ai dukkan rundunoni biyun suna can makarantar Malam Kunkuru.”
Zaki ya yi mamaki: “Wa ne ne kuma haka?”
Sarkin Ungulu ya ce. “Wani katafaren Malami ne da ya hada wata babbar tsangaya yana karantarwa, wadda babu wani mahaluki da zai gifta ta tsangayar kuma ya tsaya ya saurare shi ba tare da ya yi kwadayin zaman dirshen a wurin ba.”
Zakin ya kai matuka wurin daure fuska, ya ce. “Kana so ka ce min zama suka yi suna sauraren wani Kunkuru, suka manta da nasu sakon kenan?”
Sarkin Ungulu ya ce. “Ubangiji Ya huce zuciyarka Rankayadade. Tabbas wadannan dakaru suna can suna sauraren wannan Malami, ba kuma su da niyyar barin wurin.”
Zaki ya daga kai sama ya yi wata kururuwa har sai da kafatanin dabbobin da ke wurin suka shiga razani. Sannan ya sauke ya kara duban Sarkin Ungulu: “Yini nawa ne zai kai mu tsangayar daga nan?”
Ya ce, “A kalla idan tafiya ce gama-garin tafiya irin ta manyan dabbobi za a yi yini uku sunkur kafin a isa. Amma idan za a samu dabbobi masu sauri suna iya zuwa a kasa da wannan lokacin.”
Zaki ya dubi Dila ya ce. “Wadanne dabbobi ne za su yi mana sauri a wannan sakon?”
Dila ya ce. “Akwai kananan kwari da za su iya wannan tafiyar a ciki yini guda, sai dai kuma ina gani ya kamata a samu wasu manya wadanda idan an gan su za a fi girmama sakon.”
Cikin bacin rai Zakin ya mike tsaye sannan ya ce. “A zabi wadanda za su je cikin gaggawa a taho min da su har Kunkurun, ko ta halin kaka.” Ya juya ya nufi kofar gidansa. Dila da Kahuhu ba su bar wurin ba sai da suka zabi runduna biyu da za su tafi isar da wannan sako. Runduna ta farko wanda ta kunshi kananan kwari, karkashin Kudan Zuma. Sai kuma ta biyu wanda ta kunhi manyan dabbobi masu karfi da gudu, karkshin jagorancin Damisa.
Rundunar ta farko ana sa ran za su yi gagarumar gaggawa ne, su isa tsangayar cikin wannan yinin. Su sanar da Kunkurun da kafatanin tawagarsa cewa Sarkin yana nemansu cikin gaggawa. Yayin da runduna ta biyu kuma za su riske su a cikin yini na biyu. Wadanda idan Malamin da mabiyan nasa ba su yi biyayya sun taho ba, su za su tursasa su da karfin tuwo su azo keyarsu.
Bayan kammala wannan shirin da kuma tafiyar dakarun ne fadar ta tashi, mazauna gida suka koma gidaddajin nasu.