Skip to content
Part 13 of 15 in the Series Zuciya by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Gudu sosai Ɗansahun ke yi da Nafi. Lokacin da ta Ankare da ta yarda Wayar da Tala ta ba ta sai ta dafe kai cike da Takaici. Ta maida hankalinta kan Hanyar da suke bi, kamar za a bar garin, hanyar wajen gari ya ɗauka samɓal, ita dai sai zare idanuwa take yi jikinta a sanyaye, Ga manyan gidaje masu kyau da suke ta wucewa amma ko ina tsit. Bakin wani ƙaton gida ya yi Parking, Ya ce, “Yawwa Baiwar Allah, nan ne inda aka ce na kawo ki, za ki sauka.” Ta zaro idanuwa ta ce “Nan kuma??” Ya kashe Napep ɗin ya sake faɗin, “E nan, dan Allah ki yi da ni, akwai waɗanda ke jira na”. Yanda ya ƙarasa maganar cikin faɗa-faɗa ya sa ta saurin fitowa jikinta har kyarma yake, Ya ja Napep ɗin sa da gudu ya bar ta nan tsaye. Wata irin faɗuwa gabanta ya shiga yi zuciyarta na bugawa jin ko ina Tsit. Ta ƙanƙame jikinta, tana ta kalle-kalle ta rasa ina za ta saboda tsananin tsoro. Tana nan tsaye ta ga wata mota na tafowa ƙatuwa saitin gate ɗin gidan amma ba ta matsa ba, Mai motar ta yi horn amma still bata matsa ba, wacce ke tuƙa motar ta ja ƙaramin tsaki dan ma ba mai tsanani ba ce, ta zuge glass tana ɗan ɗaga murya ta ce “Baiwar Allah ina son shiga gida kin tare min hanya”.

Tsoro ya kama Nafi cike da ƙauyanci ta sake dunƙulewa nan inda take, Matar ta dafe kanta tana jan guntun tsaki ba ta so ba ta buɗe motar ta fito, Ganin Nafin da ta yi sosai ne ya sa ta ɗan tsorata ta ware idanuwanta kan Nafi, tana kallon ta. Sai kuma ta yi jim kafin ta ƙarasa inda take, ta ce “Lafiya na miki magana ba ki kauce ba?” Ganin matar kamar ta taɓa ganin fuskarta ya sa ta matsa da sauri don tunaninta mutanen Hajiya Safee ne. Matar ta ɗan Nisa ta ce, “Me ya kawo ki nan, ko wani kike jira ne??” Ba ta yi magana ba dan mugun tsoron mutanen birni take ji, sai idanuwanta da suka cicciko. Murya na rawa Nafi ta ce “Dan Allah ka kai ni Rugarmu wajen Baffana”. Sai da ta yi magana sannan matar ta ɗan zaro idanuwa dan ba ta yi tunanin ‘yar Ƙauye ba ce. Ta ce mata “Ya sunanki da na rugarku?” Ta girgiza kai ta ce “Nafi” Matar ta sake maimaita sunan sai kuma ta yi murmushi ta ce “Kamar na taɓa ganinki a kasuwar rugarku har na tambaye ki mazaunin Maigarinku, ko ba ke ba ce na gani ba kina talla??” Ta yi ɗan murmushi tana jinjina mata kai alamun ita ce. Matar ta yi ɗan murmushi ta ce, “Okay to mu shiga gidana sai ki min bayani” Cike da rashin wadataccen wayau Nafi ta amsa Matar ta ƙwanƙwasa gate, Maigadi ya taso da sauri daga ciki ya buɗe yana ba ta haƙuri yana banɗaki yanzu ya fito, Ta amsa masa sannan ta ce Key ɗin motarta na ciki Driver ya shigo da ita. Ta ja hannun Nafi suka shiga cikin Main Parlourn gidan, ita dai Nafi duk a tsorace take shi yasa ba ta samu damar yin ‘yan Kalle-kalle ba. Tana gani matar ta yi Knocking, wata matshiyar budurwa wacce ba za ta wuce 14-15 ba ta buɗe tana rungume matar, sai ga wani ɗan yaro shi ma ya rungume ta, ‘‘Good Afternoon Mom”. Sai kuma suka kalli Nafi da ke rakuɓe, suka haɗa baki wajen faɗin, “Mom Kin samo mana Deedi ne??” Ta bakin Nafi ba su tsaya ji ba suka hau tsalle-tsalle Su ka ringume ta, Mom ce ta ture Anisa ta ce “So kike ki karya min baƙuwa ko, Baku bari ko hutawa ta yi ba.” Sultan ma yana nan naniƙe da Nafi har suka shiga cikin katafaren Parlourn ta zaunar da Nafi, sannan Mai aikinta Gwaggo ta kawo mata abinci.

Shiru-shiru Hajiye Safee ta ji Nafi daga gwada kaya, har ta bada nata uwayen kayan da ta lodo ta biya kuɗi Nafi kawai take jira ta fito. Cike da Salon Duniyanci ta nufi ɗakin da ake gwada kayan, ta murɗa ƙofar, Kasancewa turawa kawai Nafin ta yi ba ta san yanda ake rufewa ba ya sa ƙofar buɗewa kawai ba a jira wani abu ba ta faɗa har da rufe Door ɗin. Kunna fitila ta yi tana murmushi. Fara’arta ce ta koma sakamakon ganin ba Nafi ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta Murɗa ƙofar toilet ta duba ko ina babu Nafi babu dalilinta. Ta dafe kai tana jan ƙaramin tsaki, ta fito tana tunanin ko Nafin ta yi wani layin saboda ta san ba wayayyiya ba ce ba. Ta zazzagaye ko ina duk girman Shopping mall ɗin amma ba ta ha Nafi ba, Ta ƙarasa wajen ma’aikatan tana tambayarsu, Duk an duba ciki da waje babu Nafi, Time ɗin har ran Hajiya Safee ya fara ɓaci sosai,Ta fara surfa masifa to “Me ye amfanin cttv cameras ɗinku a duba mini mana”. Wasu har sun fara jin haushinta dan me zata musu faɗa su riƙe Yarinyar za su yi, kuma ai babu wanda ya ga fitarta, an duba ta Cameras duk babu inda ta fita, sai dai shigarta ɗakin gwada kaya, matsalar babu Camera a ɗakin, sun dudduba basu gan ta ba. Tsabar ɓacin rai duka kayan da Hajiya Safee ta siya nan ta bar su, Managernsu na ce mata ta bari a duba Cameras ɗin waje amma ta fice fu, ta shiga mota ta yi gida. Ko nutsattsen Parking ba ta tsaya yi ba ta afko Parlournta Tana ƙwala ma Hajjaju kira “Kina ina Zahida Nafeesa ta gudu yau ɗin nan!!” Cikin Rashin Fahimta Hajjaju da ke zaune ta miƙe tsaye ta ce “Saurara Safeena! Ki yi min bayanin da zan fahimce ki, ba tare kuka tafi ba ne??” “Tare muka tafi daga shiga ta gwada kaya babu ita babu dalilinta an duba ko ina wallahi ba zan yarda ba, na kashe kuɗaɗena a banza a wofi ba.” Wani irin kallo ta watsa mata ta ce “To me kike nufi Safeena?” Ta ja tsaki ta ce, “Kin fi kowa sani ai” Hajjaju ta bushe da dariya ta ce, “Oh really, Hum Safee ke nan, wallahi za ki sha mamaki idan ba ki nutsu kika fahimtar da ni komai ba..” A fusace ita ma ta ce, “Na natsu fa kika ce, Wallahi ba zan taɓa ɗaukar Asara ba, Baturiya ku fito kuma!!” Hajiya baturiya da sauran matan su huɗu suka sauka daga kan benen saboda ƙaajin Hajiya Safee. Hajiya Baturiya ba ta ɗaukar raini kuma ba ta da mutunci ko kaɗan, ta riƙe ƙugu tana Kallon Hajiya Safee ta ce, “Lafiya irin wannan kira haka??”. “Ita ta kawo haka” ta faɗa a zafafe don ranta a ɓace yake sosai ta saka rai da samun Nafi, domin an tabbatar mata za ta samu arziƙi sosai ta dalilinta linkin ma wanda take da shi, za ta juya abin duniya son ranta. Ta kalli Hajjaju kawai ta faahe da dariya ta ce “Hajja Ko ƙarawa gaba muke yi?” Hajjaju ta murmusa ita ma ta ce “Da alama kam.” Ta ce ‘Kin ga gwara mu ƙara gaba yanda muke hakan nan tun kafin ta kai ga an yi Bura’u, dan da alama ita ake so, tun daga sama na ji hayaniyarku kaɗan” Tana ji tana gani suka sa kai su biyun suka fice, Sai zazzafan huci take saukewa, Ta riga ta kwafsa ta san ba a ɗaga musu murya, Amma in sun san wata Ba su san wata ba ta faɗi cikin Ranta kawai ta haye samanta. Ganin ta haye sama ta rufo ƙofa yasa sauran matan sakin shewa suna dariyar mugunta irinta ‘yan bariki.

Hannun Ammi na kyarma ta yi ma Abdul Pointing Photon Maimartaba da Ahmaad tana son yin magana ta kasa saboda jirin da ta fara gani duk da a zaune take, Ta dafe kanta tana karanto sunayen Allah, zuciyarta sai bugawa take yi da sauri da sauri, Fargaba ta cika ta da tsoron abin da zai faru. Ta ce “Abdul’aziz ko mu tafi tare gudun wata matsala?” Yay saurin girgiza kansa cike da damuwa ya ce “Ammi bari in tafi ko me ke nan ma yi waya.’ Ya miƙe ya fara tafiya, tana ta mishi addu’a. Tun da ya ɗauki hanyar gidan Akarsh ɗin gabansa ke faɗuwa sam hankalinsa ya gaza kwanciya. Har ya shigo unguwar bai ga alamun ‘yansanda ba ko wani abu, Gabansa ya tsananta faɗuwa sosai, Ya yi Parking ƙofar gidan ya tura ƙaramar ƙofa ya shiga don gate ɗin a rufe yake, Tun a ƙofar gidan da ya ga babu motar ‘Yansanda gabanasa ha ya faɗi, har ya shigo gidan yana ta wuwwurga idanuwa bai ga wata mota ba, Gidan tsit. A hankali jikinsa kuma a matuƙar sanyaye, ya tura Main door ɗin bakinsa ɗauke da sallama..

Wata irin bugawa zuciyarsa ta yi, har sai da ya dafa bango sakamakon abin da Idanuwansa suka gani. Gabaɗaya gani yake mafarki ne abin da ya gani, Akarsh kwance ciki jini, Dr Daniel kuma da alama ma ya daɗe da mutuwa babu alamun rai a tattare da shi, an harbe shi a kai da ciki. Akarsh Kuma ga ciki harbi har biyu.

Hannunsa na kyarma ya zaro waya, yana dubawa ya ma rasa mai zai aikata. Irfaan ya faɗo masa a rai, kawai ya danna numbernsa, yana ɗagawa yay masa bayani cikin kyarmar murya, ya girgiza sosai amma ya maze ya ce yana zuwa. Mintuna goma da faruwar hakan ya fara jin jiniyar motocin ‘Yansanda suka shigo cikin gidan, da bindigogi, sai kuma Irfaan shi ma ya shigo daga baya suka fara Ma Abdul tambayoyi, ya kwashe duk abin da ya zo ya gani ya faɗa musu. Wani Ɗansanda ya masa kallon Banza ya ce “Kai ɗan saurayi kar ka raina mana wayau, in ban da abinka mu muka kira ka, kai ku saka masa ankwa kawai yana son basarwa ne, bayan abokinsa ya faɗa mana gaskiya.” Yana ji yana gani aka saka masa Ankwa, yana gani suka bincike ko ina ba su samu komai ba, aka kira Ambulance ta zo a ɗauke su, shi kuma aka tasa shi cikin mota zuwa Police station. Suna isa aka saka shi cikin Kanta suka kwashe komai suka faɗa wa DPO ya fito yana kallon Abdul ya saki fara’a ya ce “A’a wai dama Abdul’aziz ne! Maza ku cire masa ankwa, ko kun samu tabbacin shi ya aikata laifin ba a haka.” Ya daga kai yana Dan murmushi ya ce “E ni ne, Yalla’bai ya aiki?” Alhamdulillah ya ce sannan ya dubi Inspector Sada ya ce, “Ku zo kai da shi office ɗina yanzu” Ya amsa cikin girmamawa “Yes sir!” DPO ya fasa tafiya ya koma Office ɗin sa don dama wani muhimmin abu ne ya tsaida shi har yay dare. Suka Nufi office ɗin Inspectorn Ya yi Knocking daga ciki DPO ya ba su izinin shigowa, Ya nuna ma Abdul kujera ya zauna, sanna ya fara jera mishi tambayoyi, “Abdul’aziz garin ya haka ta faru kar ka ɓoye mini koami ka faɗa min gaskiya?” ya jinjina kansa ya ce,“Ina zaune aka kira wayata a ka ce, jami’an tsaro ne na zo gidan Akarsh an kashe su, na ɗauki hanya na je, sai da na isa na ga saɓanin yanda aka faɗa mini ba jami’ai ba ne, sai na kira Abokina Irfaan na faɗa masa.” Ya fesar da numfashi ya ce,“Ka tabbata?” ya jijjiga kansa alamun tabbatarwa, DPOn ya juya ga Inspectorn ya ce “Ku ya aka yi kuka je gidan?” “Yallaɓai abokinsa ne ya kira mu, ai nan ne inda za mu lokacin kana waya da Cp shi ne mu ka fita” DPO ya sake cewa “Shi ne Kuke zagin shi ne ya kashe su?” Cike da nuna girmamawa ya ce “Sir ai bayanin da abokinsa ya mana ya sha banban, shi ya ce ya kira sa ne ya ce masa yana cikin mawuyacin hali ya zo gidan Akarsh ya tarar da An kashe shi ya zo da Police, shi kuma ya ce Kiran abokinsan kawai yay, ka ga ko nan Akwai alamar tambaya Yallaɓai” Dpo ya gyara zama ya ce, “Kai Abdul’aziz ka ji” Cikin ɓacin rai Abdul ya ce, “Raka ya daɗe ba gaskiya ya faɗa ba wallahi” Dpo ya ce “Good! idan haka ne Sada shi ma Abokin suspect ne, a kira shi ya zo nan ko kuma ku tafo da shi” “To An gama Yallaɓai” ya faɗa yana sara masa ga fice daga Ofishin nasa, Ya maida hankalinsa kan Abdul ya ce, “Ka kwantar da hankalinka Abdul’aziz In sha Allahu ba za a samu wata matsala ba, tun da har ka tabbatar abin da ka sani ke nan” Ya murmushi ya ce “To na gode ƙwarai Sir zan iya yin kira?” Ya ɗaga masa kai ya ce “Yeah of course you can” Ya zaro wayarsa ya fara tunani wa ya kamata ya fara kira, sai kawai tunanin Ahmaad ya kutso cikin ƙwa-ƙwalwarsa, Ya ji a ransa da yana da rai shi ne wanda zai riga kowa sanin condition ɗin da yake ciki, ya yanke shawarar Kiran Ammi, Bugu biyu ta ɗaga, dama jira ta ke yi, “Ya Abdul’aziz ina fatan dai komai lafiya?” ya gyaɗa kansa kamar tana ganin sa ya ce, “Ammi Daniel ya mutu, nd i’m not sured Akarsh too will live, nd I’m in Police station now” Ta wani zaro idanuwa kamar tana gabanshi ta ce “Police Station fa. How could this happen tell me..?” Ya numfasa sannan ya fara mata bayanin duk abin da ya faru,, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” “Wace Police station ce?” Yay saurin girgiza kai ya ce, “Please Ammi…” ta katse shi da faɗin “No don’t say anything” Ya ce “Sabon gari” Ta kashe wayar, Ya dafe kansa da ke masa ciwo kaɗan-kaɗan Sunan Allah kawai ya ke ta kira a zuciyarsa, DPO ya kalle shi ya ce, “Duba numbern da aka kira ka da ita mu gani” Knocking aka yi ya ce “Yes” Wani Ɗansanda ya shigo cikin girmamawa ya ce, “Sir ga wayoyin da muka samu nan, Ɗaya ya mutu ɗayan kuma yana AAI sun yi nasarar cire bullets ɗin duk da sun tabbatar mana ba lallai ba ne ya rayu, amma yana Emergency room yanzu haka sai Zuwa anjima za a kai shi ɗakin hutu.” Ya jinjina masa kai ya ce, “Good job! ajiye wayoyin a nan” Ya ajiye Wayoyin ya fice.

Bayan Nafi ta ce Abinci ta huta Mom ta fito daga ɗakinta ta dawo Parlour inda ta bar Nafi tana Kallo Anisa da Ƙanenta Sultan su ma suna zaune a Parlourn suna buga game. Ta ƙaraso kusa da Nafi Ta zauna ta ce, “Nafeesa sannu da hutawa.” Nafin ta amsa tana sunne kanta mom ta ce, “Yawwa, yanzu za ki iya faɗa min wanda ya kawo ki nan garin Katsina?” Sai kawai ta ga Ƙwalla sun cika idanuwanta, ta fara ba ta labarin tun ranar da ta ganta da tallar har Kawo ta Birni da Hinde ta yi, sai dai kuma ba ta san yanda aka yi ta zo gidan Hajiya Safee ba. Matar ta jinjina Rashin imani irin na Hure da Hinden da ta kawo ta, ta ce, “Share hawayenki Nafeesa in sha Allahu zan taimake ki, zan kuma taya ki bincika babarki, ba zan maida ke ba har sai kin zama wata aba, Amma ko da wasa kar ki fita daga Gidan nan ni a gane Hajiya Safeen da kika zauna gidanta mijinta shi ya fito takarar Governor shekaru huɗu da suka wuce bai ci ba, yanzu kuma zaɓen da za a sake yi ya fito”. Ita dai Nafi iyakarta gyaɗa kai dan ba ta san wani zaɓe da ta ke magana a kai ba. Ta ce, “Nafeesa daga yau ki ɗauka ni ɗin kamar mahaifiyarki ce, waɗannan kuma ‘Yan’uwanki, Maigidana ya yi tafiya, idan ya dawo zan mishi bayani, Ki saki jikinki sosai, Ina kika tsaya da karatu?” Haka nan Nafi ta ji Hankalinta ya kwanta da matar, ta ce “Ba ma yin karatu” Ta gyaɗa kai kawai ba ta sake magana ba.

Hajjaju na isa Ta sa aka kira mata Hinde. Ta dube ta a yatsine ta ce, “Ke Hinde ko kin san inda Nafi take?” Cikin mamaki ta ce, “Nafi kuma Hajjaju ba tana gidan Hajiya ba” Ta taɓe baki kaɗan ta ce, ‘Wai sun fita Shoping ita da Hajiyar sun dawo ta ce ba ta gan ta ba wai ta gudu” Hinde ta zaro idanuwa cike da mamaki ta ce, ‘Ta gudu kuma, ai gaskiya ba ta san ko ina ba a nan garin” Ta taɓe baki ta ce “I think so, Anyway if she want her, she can find out where’s her, i can’t stress myself for no reason, nd can’t she take care of her very well so that she’ll not be able to run anywhere is her fault, she don’t have the right to blame anybody, Yuh you can go” Ta faɗa ta nuna ma Hinden ƙofa. Duk da ba ta fahimci turancin ba ta nuna mata ƙofa ta san Tana nufin ta kama gabanta. Ta miƙe tana faɗin, “Hajjaju dama yau zan wuce Ƙauye da Rugarmu, Idan an samu wasu ‘Yan’matan zan taho da su.” Ba ta baa amsa ba Ta lumshe idanuwanta dan Ranta a ɓace yake, Har Hinde ta sa Hannu za ta buɗe ƙofa Ta ji muryarta ƙasa-ƙasa ta ce, ‘‘Ki kira min Leesha’’ Ta amsa tana ficewa. Jim kaɗan sai ga Leesha ta shigo ɗakin tana wata irin rangwaɗa, ta ce ma Hajjaju ga ta, Kawai ta miƙo mata hannu, tana jin haka ta fara rage After Dress ɗin jikinta, ta rage daga ita sai riga da wando ta cire rigar gabaɗayanta ta ƙaraso gaban hajjaju ta Zuge Zip ɗin rigarta, daga nan Ta kashe wutar ɗakin, ta fara Shafo sassan jikinta cike da tsantsar ƙwarewa, gabaɗaya sun fice daga hayyacinsu sai nishi suke yi kaɗan-kaɗan.

(Allah ka raba mu da Muguwar Ƙaddara, Allah ka shirya mana zuri’a da Khullihin musulmai.🤲🏾)

<< Zuciya 12Zuciya 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×