Skip to content

Ƙauna Ta Yi Nisa | Fasaha Haimaniyya 1

4.7
(3)

<< Previous

Bismillah Allah sarkina gwanina

Kai ke da ikon dukkanin lammurana

Yau gani da ƙoƙo na ɗaga hannuwana

Roƙon da na yo ka cika burikana

Kai ne ke biya mana dukkan buƙatu

Hakane!

*****

So ya yi nisa zuciya ta yi kewa

Ina mararinta ruhi na ta ƙwawa

Burin idanu fuska su yi ganowa

Su kuma kunnuwa murya su yi jiyowa

Rashi na ganinta yasa na sha wuya

Hakane!

*****

Ita sahibata sam-sam bata da muni

Kyawun idon ta ya wuce kyan furanni

Tana da kyan diri, sura har da kamanni

Takan yi kwalliya da ado dukka don ni

Yau rashin ta yasa zuciya ta yi muni

Hakane!

*****

Muna son juna duk da dai ba ni da komai

Aka ce ba a ban domin ba ni da komai

Ita ko ɗiyarsu dukka tana da komai

Sun manta cewa Allah ke da komai

Shi ke da ikon yin komai ga kowa

Hakane!

*****

Yau na ga ta kaina na rasa yadda zan yi

Na kasa rabewa zafi ko kuma sanyi

Saboda tunani kaina ya yi nauyi

Na kasa komai sai dai yin bulayi

Da ma za na ganta zuciya ta ji sanyi

Hakane!

*****

Ku sani ‘yan uwa rayuwa bata da tabbas

Me raƙuma ɗari jiya yau ba shi da ko as!

Me taka kowa jiya yau sai silifas

Me yin mugunta wataran zai ga tabbas

In ka kyautata niyya wataran za ka fito fes

Hakane!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×