Misalin ƙarfe 8:00pm na dare Usman na tsakiyar karuwai a Abedi, ana ta sheƙe aya, masu busa sigari na yi, masu daga kwalla na yi, masu casu na yi, kowa dai da irin holewar da yake. Zuwa can sai ya tuna da Humaira, kiran ta ya yi a waya tana ɗagawa ya ce, “Ina fatan dai kin isa gida lafiya ya su mummy, yanzu haka kina gida ko kuwa?”
“Hmm! Lafiya lau, su mummy ma lafiyarsu lau. E, ina cikin gida yanzu.”
“Okay, da ma ina son mu yi wata magana ne, kin ga dazu ko sallama ba mu yi ba.”
Humaira ta ɗan yi murmushinta mai sauti kana ta ce, “Ba komai wace magana ce za mu yi?”
“Ko za ki iya fitowa waje ƙofar gida?”
“Okay to ɗan kashe wayar sai ka sake kira kamar bayan minti biyar.”
Kashe wayar ya yi, bayan kamar mintuna bakwai sai ya sake kiran ta, ta amsa da cewa, “Yawwa to ina jin ka.”
Cikin yanayin kashe murya da sigar murmushi ya ce, “Idan babu damuwa ina son mu haɗu gobe zan ba ki tukwicinki da na yi alƙawari.”
“Hmm! Ba komai wallahi ka bar shi na gode ba sai mun haɗu ba.”
“Ni fa na yi niyya ba tambaya ta kika yi ba, kawai ki faɗa mini inda za mu haɗu na ba ki.”
“Allah kuwa na ce ka bar shi kawai na gode Allah ya saka da alkairi.”
“Ya zama dole tilas na ba ki tukwicinki, ba na son musu, ki fada mini kawai.”
“To shi ke nan, amma ni ban san inda zamu haɗu ba shi yasa na ce kawai ka bar shi na gode.”
“Okay wannan ba matsala ba ce in dai wajen haɗuwa ne, kin ga mu haɗu a titin Malam Aminu Kano, daidai WRECA. Misalin ƙarfe 10:00am na safe gobe, zan jira ki idan kin iso ki yi mini waya kawai kin ji.”
Haka ya kalamunce ta har ta sake yarda za su haɗun, bayan ya gama wayar ya koma cikin karuwan nasa suka ci gaba da sha’aninsu. Bai koma gida ba sai kusan karfe ɗaya na dare (1:00am). Sabansa ke nan da ma kullun idan ya fito ba ya komawa gida sai a daidai irin wannan lokaci. Satin farko na amarcinsu ne kawai ya zauna a gida. Anti Sakina ta nuna ɓacin ranta matuka game da wannan bakar dabi’a ta mijin nata har ta gaji ta zura masa idanu.
Washegari tun da safe da Usman ya tashi daga barci bai sake komawa barcin hantsin da ya saba yi ba dalilin raba daren da yake a waje. Misalin ƙarfe 9:30am na safe ya yi shirinsa, da yake a yanayin ɓacin rai suke shi da Anty Sakina din, daga gaisuwa babu abin da ya sake hada su. Har lokacin da ya gama kintsawa ya fice daga gidan ba ta tanka masa ba shi ma sai ya share ta bai faɗi inda za shi ba. Ta kuma san ba wajen aiki zai je ba, domin aikin rana yake sannan kuma yau bashi ma da aiki, yana hutu har tsawon kwanaki uku, bugu da kari ma gashi bai saka uniform dinsa ba kuma bai tafi dasu a jaka ba kamar yadda ya saba idan baya bukatar sakawa daga gidanm. Idanu kawai ta bi shi dasu.
Yana fitowa bakin titi ya tsayar da mai Adaidaita Sahu drop ko ciniki ba su yi ba, ya ce ya kai shi titin Malam Aminu Kano kusa da WRECA, Mai Adaidaita Sahun ya ja suka tafi.
To, ita ma Humaira a nata ɓangaren ta shirya ɗin, ba wata kwalliya ta yi ba gudun kada mummy ta yi mata tambayar ina za ta je, gabanta na faɗuwa. A falo ta iske mummyn zaune, “Shin wai wace ƙarya kuma zan yi wa mummy ta bar ni na fita yanzu?” A zuciyarta ta yi wannan tunani.
Ƙarya ta haɗa lafiyayya ta jingina da makaranta cewa, “Umma yanzu Shamsiyya ƙawata ta turo mini saƙo wai in je makaranta na duba registration ɗin jarabawarmu, idan akwai gyara ko a wajen suna ko wani bayanin sai na gyara kafin a fitar da slip.”
Mummy ta ce “To yaushe za ki je?”
“Yanzu nake son na je, ta ce mini da sauri ake buƙatar kowa ya je kafin a rufe shafin hukumar jarabawar.”
“To shi ke nan ba komai sai kin dawo ki kula fa kin ji.”
“Hmm! Mummy ba ni da kuɗin mota fa.”
Humaira ta faɗa cikin sigar shagwaɓa, mummyn ta ce, “Duba wajen mudubi ki ɗauki naira ɗari biyu.”
Kuɗin Humaira ta ɗauka ta zura hijabi ta fito, Adaidaita Sahu ita ma ta tsayar da ta ce a kai ta can wajen da suka yi za su haɗu. Shigar ta cikin Adaidaitar ke nan, sai ga kiran wayar Usman ɗin, tana ɗagawa ya ce, “Ya ya kin fito dai ko?”
“E, na fito ga ni nan a hanya ina zuwa yanzu.” Ta faɗa tare da kashe wayar. Babu jimawa mai Adaidaita Sahu ya isa da ita wajen, tuni Usman na can yana jiran ta a cikin Adaidaitan da ya kai shi, da ma bai sallame shi ba. Cewa masa ya yi ya jira shi zai kara masa kuɗi sosai.
Humaira na isa ta kira shi ta ce, “Ga mu a daidai kwanar WRECA.”
“Okay na gan ku kada ki fito, ina zuwa ki ce da mai Adaidaita Sahu ya yi parking minti biyu.” Yana kashe wayar ya mayar da hankalinsa kan mai Adaidaita Sahun da ya ɗauko shi ya ce, “Nawa zan ba ka abokina?”
Mai Adaidaita Sahu ya ce, “Yallaɓai ka bayar kawai?”
“Ka dai faɗa don Allah, ku haka halinku yake sai ku ce mutum ya bayar kawai. Hakan kamar kuna daure mutane ne da jijiyar jikinsu ne.”
Murmushi mai Adaidaitar ya yi sannan ya ce, “Ba matsala yallabai kawai ka kimanta ka bayar.”
“Idan na baka dari biyar (500) ya yi?”
“Eh ya yi ba damuwa na gode.”
Dari biyar din ya zaro ya mikawa mai Adaidaita Sahu, ya karba tare da godiya. Usman ya fito ya nufi Adaidaitar da ta kawo Humaira, kai tsaye ya shiga ya zauna kusa da ita sosai, har nanukarta yake. Fuskarsa cike murmushi ya ce, “Nayi zaton ba za ki zo ba ai da naga kina ta dodging. So ya kike ya mutanen gidan?”
Kunya ce ta kama Huamira, janye jikinta ta yi daga na sa cikin hikima, ta dan matsa kadan sannan ta ce, “Gida suna nan lafiya, ya Anty Sakina din? ”
“Lafiya lau take. Mu dan karasa nan gaba Dage-dage Supermarket ko Al-Amir Restaurant, ko tea ne mu sha ko?”
“Wallahi sauri nake fa.”
“No kin ga ba wani dadewa za mu yi ba ai, kai mai mashin kai mu Al -Amir, na Tal’udu.”
Mai Adaidaita ya ja ya kai su, suna zuwa Usman ya tambayi Humaira, “Nawa kuka yi ciniki za ki bashi?”
Humaira ta ce, “Dari biyu ne amma ban ce zai jira ni ba.”
Usman ya zaro dubu daya ya mikawa mai Adaidaita, ya karba ya ce “Na gode sosai.”
Cike da jin kunya Humaira ta fito suka shiga cikin restaurant din, can wani waje da babu kowa suka samu samu suka zauna. Ya yi oda aka kawo musu farfesu. Abin da ya dan ragewa Humaira jin kunya shine ta saka nikabi ta rufe fuskarta, shima kansa Usman din ya ji dadin hakan domin idan ba haka ba, za’a iya gane ta.
Kafin a kawo musu farfesun ya dube ta ya ce, “Humaira ki kwantar da hankalinki, babu wanda zai san me yake faruwa tsakaninmu, ki bani dama kin ji.”
“Gaskiya yaya Usman ina jin tsoro, ka ga ranar nan Anty Sakina ta binciken da ta rika tana min tambayoyi lokacin da ta raka ni titi, sai da na rantse da Allah sannan ta hakura ta kyale ni. Kuma kaima na san ta tuhume ka, gaskiya fa matsala ka yi hakuri.”
“Haba Humaira wace magana kike haka, wace matsala ce wannan da za ta gagare ni? Kin ga zan tsara komai kawai ki bani hadin kai. Ko mene ne kike bukata kawai ki fada min.”
“Ni dai gaskiya ina jin tsoro wallahi.”
“Hmmm! Humaira kenan, wane irin tsoro kike ji? Irin abin da muka yi waccan ranar shi zamu rika yi duk lokacin da na neme ki.”
Shiru ta yi ba ta sake cewa komai ba, ba ta son ta rika yi masa musu. Zuwa aka kawo musu farfesun aka aje gabansu, wani dan gajeren tunani Humaira ta fara.“Ga abinci nan bisimillah ko.” Usman ya fada yayin da yake bude plate din da aka aje gabansa.
Numfashi Humaira ta ja sannan ta ce, “Na koshi wallahi.”
Usman ya dan bata rai kadan tare da cewa, “Gaskiya sai kin ci koda kadan ne, bana son ina yi miki abu kina cewa bakya so ko kin koshi.”
Sama-sama ta dan yatsina ta ci farfesun, bayan sun gama ta ce, “Zan koma gida kada na dade, yanzu ma dakyar mummy ta barni na fito.”
“To shike nan babu damuwa, bari mu fita sai na saka ki a Adaidaita Sahu ya kai ki gida. Amma kafin nan ya kamata na san matsayata, idan na kira ki za ki zo?”
Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba, ya cigaba da cewa, “To shike nan na gane, kuma na gode sosai.”
Ya zaro kudi ya kirgo dubu biyar (5000) ya mika mata tare da cewa, “Ga wannan ba yawa ki yi hakuri zuwa karshen wata zamu sake haduwa. Kuma indai kika saki jikinki to ni wannan ba komai bane a wajena.”
Murmushi dai ta yi kana ta karba tare da cewa, “To na gode.”
Mikewa suka yi tare suka fito, ya tare mata Adaidaita drop ya biya ta shiga. Shima gidan ya komo daga nan din. To da yake weekend ne Anty Sakina na gida bata fita ba. Yadda ya sa kafa ya fice ba tare da ya yi mata magana ba, haka ma yanzu da ya dawo, shigewarsa ya yi ya tube kaya ya kwanta. Zuciyarsa cike da farin ciki, a ransa yake cewa, “Wallahi yarinyar ashe zazzafa ce, ta fi yarta komai. Sannu a hankali sai na cimma burina, Allah dai ya kai damo ga harawa…”
Yana tsaka da wannan daddadan tunani, Anty Sakina ta shigo dakin ta mika masa wata ‘yar guntuwar takarda dauke da rubutu kamar haka, Malam babu man girki, Maggi duka sun kare, taliya saura guda daya kawai, shinkafa ta kare tun wancan satin, Gas ma ya kare, semon vita rabin satchet ne ya rage. Tun wancan satin na fara sanar da kai, don haka ka kawo su.
Tana mika masa takarda ta juyo ta komo falo ta cigaba da rubuce-rubucenta na aikin makaranta. Shi kuwa yana gama karantawa ya taso a fusace ya nufo falon, “Ke Sakina, wane irin rashin mutunci ne kike son bullo min dashi. Ba za ki iya fada min da baki ba sai dai ki rubuta a takarda, me kike nufi ne?”
“Ni babu abin da nake nufi, kai ne naga kana bukatar hakan, lokacin da za ka fita ka yi min magana ne? Koda kana ganin ban kai matsayin da za ka fada min wajen da za ka je ba, to amma yana zan za ka fita sai ka dawo. Kawai sai ka saka kafa ka yi yafiyarki.”
“To shike nan na ji, yanzu batun kayan abinci dai kin san ba haka muke yi ba ai. Kema kin san yadda abin yake, shinkafar nan ke ce kike karbo mana loan a wajen aikinku kuma har man girkin duka ke kike sayowa. A takaice dai idan aka samu in-payment (tsaiko wajen biyan albashi) ke ce kike taimakawa da komai, kada ki bar shedan ya yi miki hudubar banza.”
“Gaskiya ba zan iya ba wallahi, wanda nayi a baya Allah ya bani lada. Ba hakkina bane samar da abinci, kada ka mai dani wacce bata san abin da take ba. Shike nan kai duk wata in-payment din ake samu a ma’aikatarku. Idan za ka tashi ka je ka nemo mana abinci ka tashi, ni dai na daina, ehe.”
Ganin yadda take maganar babu alamun fara’a ko wasa, ya tabbatar masa fa lallai da gaske take, risinawa ya yi tare da sassauta muryarsa ya ce, “Wai Sakina duk mene ne ya kawo wannan abin, duk kin bi kin canja halinki lokaci daya.”
“Ni babu wani canja halina da nayi, abin da ya zama dole ka yi ne nake fada maka, to kuma meye abin canja hali a nan.”
“To shike nan na ji duk abin da kike fada kuma haka ne, amma ina son ki cigaba da karbo mana kayan abincin a wajen aikinku idan anyi salary zan baki.”
“Wa? hahaha! Abin dariya, ba da ni ba, ka bari idan anyi albashin ka je kasuwa ka sayo kawai, wallahi ni dai na daina karba ehe.”
“Okay haka kika ce ko, ina lallaba ki sai wani sututai kike yi mararsa amfani.”
“E haka na ce kuma na yi surutan.”
“To shike nan tunda hakane sai ki bari sai lokacin da na samu albashi na sayo na kawo.”
“Ban gane na bari ba, yanzu taliya daya ce ta rage fa, Idy ta kare ya za’ayi kenan, Malam kawai ka fita ka nemo mana abinci.”
“Ba zan fita din ba kin ji ko.”
“To shike nan kada ka fita din ka yi ta zama.”
Shiru suka yi kamar mintuna biyar babu wanda ya sake cewa komai, zuwa can wayar Usman ta fara ruri, ya dauka tare da dagawa ya ce, “How far blessing, how you dey naw?”
Daga cikin wayar muryar mace ce kabila ta bayyana da cewa, “I dey ooo Usman, two days I no dey see you, where you hide?
“I dey, na work den de hide me.”
“Ok ooo, so how na your madam?”
“She dey okay”
Ya fada tare da duban Anty Sakina, wacce take ta aika masa da zazzafar harara. Kauda kansa ya yi suka cigaba da wayar shi da blessing, ya ce, “Any problem?”
Blessing ta sauya murya cikin yanayin shagwaba ta ce, “Pls Usman can we meet today in the night?”
“Yes naw, no wahala, but for which place?”
“I dey for BIG APPLES HOTEL as usual.”
Okay no wahala I dey come in the night, bye bye.”
Ya fada tare da kashe wayar. Wani dogon tsaki Anty Sakina ta ja hade da mikewa ta bar masa falon.
Wannan yarinya da suka gama waya da Usman mai suna Blessing, daya ce daga cikin ‘yan matansa da yake zaman daduro dasu ,abin nasa bai tsaya ga karuwan Hausawa ba, har kan kabilu. Babban abin da ke dagawa Anty Sakina hankali kenan, sannan idan rashin mutuncinsa ya motsa a gabanta yake yin da kowacce mace kuma ya fadi duk abin da ransa ya yi masa dadi kamar yadda mu ka ji yanzu.
Ta yi iyakacin bakin kokarina wajen ta nuna masa hanya ta gari mai bullewa, amma ya runtse idanunsa ya toshe kunnuwansa. Usman ya yi matukar yin nisa don haka ba zai ji kiranta ba, sai dai kiran duniya.
Cikin daki ta shige ta fada kan gado tana kukan zuci da na sarari, tana addu’ar Allah ya kawo mata dangane da wannan zaman kaddamar da take ciki.