Shi kuwa Usman barcinsa ya shara sosai hankalinsa kwance, da gari ya waye misalin karfe tara na safe 9:00am, ya tashi ya shirya. Bayan sun gama duk abin da zan su yi shi da Blessing, ya kawo wasu kuɗaɗe ya ba ta ya ce ta riƙe a hannunta, idan dare ya yi ma zai sake dawowa, da yake kuɗin sati guda ya biya ya kama ɗakin.
Kafin ya baro hotel ɗin sai ya buɗe wayarsa, da ma Anty Sakina sai jarraba kiran lambar take ko Allah zai sa a dace, ai ko cikin sa’a tana yin kiran sai wayar ta shiga ta fara ruri, amsawa ya yi, cikin tsananin damuwa ta ce, “Lafiya kuwa, kana ina ne haka wayarka a kashe tun jiya?”
Babu wani alamun damuwa tattare da shi, walau a fuskarsa ko kuma a lafazinsa, don haka nan take sai ya ƙirƙiri wata karyar rainin wayo yake faɗa mata cewa, “Aikin gaggawa ne ya taso aka kira ni daga ofis shi yasa ban dawo ba.”
Anty Sakina ta ce, “To amma shi ne ba ka kira ni ba ka sanar dani cewa ba za ka samu damar komowa gida ba, ai sai na sani. Na kwana hankalina a tashe ban runtsa ba.”
“Kin ga malama dakata kin ji, ba ki yarda da abin da na fada miki bane kike tsara min yadda zan yi? Ko ni ɗanki ne da dole sai na faɗa miki abin da zan yi?”
“Hmm! To ka yi hakuri, ni na wuce makaranta sai ka dawo.”
Tana fada tare da kashe wayar sannan ta dauki jakarta ta fice ta nufi makaranta. Yanayinta babu wani kuzari, sam babu walwala, ta fahimci karya ya fada mata kawai don ya kare kansa. Babu wani aikin gaggawa da ya taso, ina jami’an dake aikin dare? Kawai dai abin nasa ne yake neman wuce gona da iri.
Kallon daya za ka yi mata ka tabbatar tana cikin damuwa, akwai abin da ke damunta koda bata bayyana ba. Haka ta isa makarantar zuciyarta babu dadi, kwata-kwata bata iya yin wani aiki ba, zama kawai ta yi a staff room ta fake da kanta na ciwo.
To shi kuwa Usman bai shigo gidan ba sai misalin karfe 10:00am, da yake ta fada masa ta tafi makaranta, bai yi tsammanin samunta a gida ba. Saboda haka sai ya taho da abinci take away, yana isowa ya wuce toilet ya watsa ruwa sannan ya yi sallar asuba a wannan lokaci da rana tsage-tsage. Bayan ya idar da sallar ya ci abincin sannan ya shimfide a gado nan take bacci ya dauke shi.
Karfe sha biyu 12:00pm Anty Sakina ta baro makaranta kafin a kai ga tashi. Ganin gidan a bude ya tabbatar mata lallai Usman yana ciki, tana shiga ta iske shi ya tashi daga baccin yana shirin tafiya wajen aiki. Sallama ta yi ya amsa ta zube a kan kujera. Dubansa take ranta cike da bakin cikinsa, sun jima babu wanda ya yiwa wani magana, ita ce dai ta nisa bayan ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya ta ce, “Usman ya kamata ka san cewa lallai Annabi ya faku, kai yanzu ba yaro bane, ka manyanta fa. Abubuwan da yawa ya dace ace tuni ka hakura dasu, hatta wannan fitar daren da kake bai kamata ba. Ka tuna kai fa mai tsawatarwa ne na musamman gwamnati ta dauka domin dakile Ire-iren wadannan miyagun ayyuka dake haddasa tabarbarewa da lalacewa gami da talauci a cikin al’umma. Amma kuma sai ga shi mai dokar bacci ya bige da gyangyadi, don Allah ka daina.”
“Wato nine ma nake yawon banza ko, shin wai ke a me kika dauke ni? A matsayin dan iska ko? To bari ki ji haka kika ganni, haka nake gudanar da rayuwata. Ni ba zan iya takurawa kaina ba saboda ke, idan kin ga za ki iya, to bisimillah ki zauna, idan kuma ba za ki iya ba sai ki san yadda za ki yi. Aikin banza aikin wofi, babu abin da kika aje kullum sai zargina. To duk ma abin da zuciyarki take fada miki a kaina haka ne, ni dan iskan ne mata nake nema, idan akwai abin da za ki yi, to ki yi din, shashahsa kawai.”
Hawaye ne mai tsananin dumi ya fara sauka bisa kuncin Anty Sakina, cikin rarraunar murya ta ce, “Allah ya ba ka hakuri, Allah ya huci zuciyarka, indai saboda na fada maka gaskiya ne to daga yau na daina ba zan sake ba. Duk abin da zan ka yi ka je ka yi duniya ce ta ishi bagaruwa jima, kuma akwai Allah sannan akwai sakayya.”
“To ya isheki haka idan kuma rashin kunya za ki min to bisimillah.”
Shiru ta yi ta rabu dashi kasancewar tana azumi, yawan cacar bakin bashi da wani amfani domin ba ji zai yi ba, sannan kuma a zahiri kan nata ya fara mata wani irin azababben ciwo. Bayan ya gama shiri ya ce, “Ni zan tafi.”
Ba tare da ta daga kai ta dube shi ba ta ce, “Ka san na fada maka babu komai fa a gidan nan kuma azumi nake ka sani.”
“Hakuri za ki yi sai lokacin da aka samu kudi, yanzu dai bani dasu.”
“Allah ya ba ka, a dawo lafiya.”
Haka nan ya fice daga gidan ba tare da ya bata koda abin da za ta yi buda-baki ba.
*****
Humairan na aikace-aikacen gida da rana, Najib ya kira ta, da yake ya danyi rashin lafiya kwana biyu. Tana daga wayar bayan sun gaisa ta ce, “Ya jikin da fatan dai kana samun sauki.”
“Alhamdulillah! Jiki ya yi sauki, amma ni fishi nake dake, ina kwance babu ba ki kira ni a waya ba, ba ki zo dubiya ba kuma babu kayan dubiya.
“Hmm! Lallai kam kayan dubiya.”
“E mana ko ba zan samu ba ne?”
“Hmm! To ai ka ce‘ka warke ko ba shike nan ba.”
“Haka ne na warke amma da kin yi niyyar kawowa ai kin san lokacin da na kwanta din.”
“Hmm! To shike nan ka yi hakuri nan gaba idan ka sake yin rashin lafiyar zan kawo maka ka ji.”
Dariya ya yi sosai sannan ya ce, “Subhanallah! Fatan cutar ma kike mini?”
“Ah to ba kayan dubiya kake son a kawo maka ba.”
“A’a gaskiya indai hakane bana bukatar kayan dubiyar, sai anyi min fatan ciwo, na yafe.”
Murmushi ta yi ba ta ce komai ba, ya dora da cewa, “Anjima idan mun tashi daga kasuwa zan zo.”
“To shike nan sai Allah ya kawo ka.”
“Amin ya Allah, ki gaida min da mummy.”
To a bangaren Anty Sakina kuwa, misalin karfe 4:00pm na yammaci bayan la’asar ta fita ta yo cefanenta ta zo ta hada kayan shan ruwanta, da magariba bayan an kira sallah ta yi buda-baki. Gamawarta keda wuya Usman ya shigo, sallama ya yi ta amsa masa, daga nan kuma babu wata magana da ta sake hada su. Bai nemi abinci ba, sannan bai tambaye ta ya ya tayi ba domin ya san tana da kudi. Ita ma din ba ta sake yi masa magana ba dangane da karewar kayan abincin nasu.
Kamar kullum dai bayan sallar isha ya fice yawonsa babu fashi tamkar mai halartar wata makaranta ko kuma wajen daukar darasi.
To kamar yadda Najib ya alkawartawa Humaira cewa zai zo da marece bayan ya tashi daga kasuwa, hakan ce ta kasance. Kai tsaye gidan ya nufo bayan ya rufe shagon kasuwa, yana isowa wayarta ya kira ya sanar mata cewa yana kofar gida. Ta jima sosai bata fito ba yana nan tsaye kamar kimanin mintuna 15-20. Zuwa can sai ga ta ta fito, ba wata kwalliya arziki ta yi ba, babu yabo babu fallasa. Haka take masa, indai da sabo to ya riga ya saba.
“Salama alaikum barka da isowa.”
Ta fada cikin yanayin kadaran kadahan (ita ba farin ciki ba kuma ba bakin ciki ba).
Najib ya masa da cewa, “Yawwa barkanki dai, yau kuma ina shimfidar da zamu zauna, ko kin yi training din tsayuwa ne.”
“Hmm! Babu wani training kaima za ka iya tsayuwar ai.”
Dariya ya yi tare da cewa,“Haba dai gaskiya ni dai ba zan iya ba, ki koma ki ɗauko mana shimfiɗa kawai.”
“Wallahi kana matsala ,kamar ba namiji ba.”
Tana fada ta juya ta koma ta dauko darduma ta shimfida musu a barandar kofar gidan, suka zauna.
Najib ya ce, “Har yanzu dai kina nan a kan bakanki ko? Idan kika duba karatun nan sheda ce kawai mutum zai ajiye, secondary ta wadatar da mutum ya yi rayuwa. Ke mace ce aure shine abin da ya fi dacewa dake Humaira. Ki bar maganar karatun nan kawai mu yi aure, ki duba shekarunki da yanayin jikinki.”
“Gaskiya kai dai akwai ka da maida hannun agogo baya, mun riga mun gama wannan maganar da kai kace ka ji ka gani za ka jira ni, to ba shike nan ba sai ka jira lokacin ba. Ka ce baka yarda na rika zuwa makaranta ba bayan mun yi auren. To ka saurare ni, nan da makonni biyu za’a kafe mana admission, saboda mu bar maganar hakuri da karatu, ina son na yi karatu.”
Najib ya nisa yana dubanta cike da mamakin taurin kan da take nuna masa, shi kam bai ga wani dalilin da zai sa ace dole sai mace ta yi karatun gaba da secondary ba. A tunaninsa koda mace ta yi karatu mai zurfi ba lallai bane ta amfane shi ba ko kuma al’umma su amfana da ilimin nata duba da cewa akwai hidimomi na aikace-aikacen gida a kanta. Murmushin takaici ya sauke tare da cewa, “To shike nan babu komai Allah ya taimaka.”
“Yawwa ko kaifa ,abin da ya dace ka yi min kenan. Sannan kuma ka sani karatun ba wani mai tsayi bane, shekara biyu ne fa kacal, Diploma ce zan yi. Kaine ma zaka rika kai ni makarantar idan ya zo sai na rika dawowa da kaina bayan an tashi.”
“Hmm! Ba ki da dama wallahi, kin san yadda za ki yi ki saka mutum farin ciki idan kin bata masa rai. Ni ba zan rika kai ki ba tunda ke kika saka kanki yin karatun sai ki je. Domin idan ana yanayin sanyi ko damina kin san ba zan fita ba ko.”
“Hmm! Wannan ma zance ne, ai dole ne ka fito ka kai ni, ba don kada Abba ya yi magana ba, da kai din ne kuma za ka rika komawa kana dauko ni.”
“Ai ko da ba ki dawo ba wallahi, sai dai idan ki yi ta zama a can.”
“Haka ma ka ce ko, to shike nan sai na zauna a can din ma na tare, dama akwai sauran dalibai maza da mata dake kwana a makarantar wadanda ba ‘yan gari ba.”
“Cabdijan! Lallai da kin sa na tashi dan karamin yaki a makarantar kuwa, ki kwana a makaranta? Ai da shike nan an gama da rayuwata, na san babu abin da zai yi saura kuma.”
“Hmm! Kai dai ko baka rabuwa da abin dariya, dama na san abin da kake tunani kenan shiyasa ka dage a kan ba sai na cigaba da karatu. Kawai ka kwantar da hankalinka.”
Sun jima ba laifi suna hira sosai, tana zolayarsa shima yana zolayarta, daga karshe suka yi sallama ta koma gida.
*****
Waye Najib
Shi dai Najib matashin saurayi ne dan kimanin shekaru ashirin da takwas (28 years). Da ne ga aminin Abban Humaira, wanda ya kasance makwabci a gida da kuma kasuwa. Mahaifinsa sunansa Alhaji Mukhtar Mai goro, ya rasu kamar shekaru biyu da suka gabata.
Abban Huamira ya cigaba da kula dashi a kasuwa tare da bashi shawarwari, ya dauke shi tamkar dansa na cikinsa. Duk wata kulawa da da ke bukata, ba wacce Najib ya rasa a wajen Abban Humaira. Shi kadai iyayensa suka haifa, yanzu yana tare da mahaifiyarsa ne. Shi ma ya yi karatunsa daga matakin primary har zuwa jami’a, amma baya sha’awar aikin gwamnati ko makamancinsa. Ya fi sha’awar kasuwanci kamar yadda ya tashi ya ga mahaifinsa na yi.
Tun Humaira na karama sosai yake sonta har kawo yanzu da ta girma sosai, kullum kaunarta karuwa take a zuciyarsa. Samari da dama suna yunkurin zuwa wajen Humaira, da masu zuwa don Allah, da masu zuwa don yaudara, amma tuni Abbanta ya hana ta kula kowanne sauri, Najib kawai ya amincewa.