Anty Sakina da Usman sun jima sosai suna ta hira abin gwanin ban sha’awa tamkar ba su ba ne ke rikici. Koda yake da ma duk lokacin da Usman ɗin yake son ya karɓi wani abu ko kuma ya ranci kuɗi haka yake mata. Sai ya zama mutumin kirki ya kwnatar da kansa kamar ɗa da uwa.
Ita kuwa Anty Sakina ba ta nuna masa ta gane manufarsa ko kaɗan, kawai ita burinta a duk lokacin da ta ga yana nuna halin kirki shi ne da ma ya ɗore da wannan hali, ya ci gaba da kasancewa mai halin kirkin.
Abin duk da take yi tana sane, ta yi ne don Allah. Amma duk lokacin da rashin mutuncinsa ya motsa ba ya ji ba ya gani, rufe idonsa yake ya yi duk abin da ransa yake so. Babbar damuwarta ita ce neman matan da yake, da zai ƙaro aure zai fi mata alkairi sau dubu a kan neman matan banzan da yake. Ba ta san wace cuta zai ya yo ya goga mata ba.
Har misalin ƙarfe 9:30pm na dare Usman na nan zaune suna ta hira ba ta ga ya miƙe ya yi shirin fita ba, tambaya ta jefa masa da cewa, “Yau babu fitar ne, ko an fara ba da hutun zuwa club ne?”
“Ban gane wannan tambayar ba, so kike na fita ɗin ke nan, kora ta ma kike daga gidan?”
“Hmm! Ni ba korar ka nake ba, da can ɗin da kake fita so nake? Kawai dai tambaya ce na yi. Na ga yadda masu zuwa club ɗin suke ba da himma wanda ko wajen ibada ba sa bawa muhimmanci kamar haka.”
“To ni ban sani ba, ba ni da amsar wannan tambayar.”
Dariya Anty Sakina ta yi tare da cewa, “To Allah Ya ba ka hakuri, daga tambaya sai cibi ya zama ƙari.”
“Ke kin san idan ba ma zuwa irin wannan wajen tashin hankalin da za a yi na kaɗan ne? Allah kaɗai ya san yawan mutanen da za su hallaka, za a riƙa kashe mutane kullum ta Allah. Don haka ki sani mu aiki ne ke kai mu ba wani abu ba.”
Cikin sigar mamakin ya raina mata wayo da hankali ta yi wani ɗan guntun murmushi tare da cewa, “Lallai kam dole a kashe mutane a wajen idan ba kwa nan, ai ya kamata ku ci gaba da zuwa kare rayuwar jama’ar.”
“Kin ga ni tashi ki yi kawo mini ruwa na sha idan kin gama tuhuma ta din. Ke wallahi da ma aikin namu kika koma kawai domin kin iya tuhuma sosai, babu shakka idan kika saka mutum a gaba ko bai yi laifi ba, za ki yi masa gadar zare ya taka ta burma da shi.”
To a wannan daren dai Usman bai fita ko’ina ba, a gida ya kwana. Washegari da safe Litinin da azumi Anty Sakina ta tashi, don haka abincin breakfast kaɗan ta yi masa. Bayan ta kammala, ta yi shiri ta fice wajen aiki ta bar shi a gidan kamar yadda suka saba a duk lokacin da yake aikin rana. Fitarta ke da wuya ya miƙe ya shiga bayi, wanka ya yi ya fito. Singlet da short nicker ne a jikinsa ya zauna a falo.
Misalin ƙarfe 9:00am na safe ya dauki wayarsa ya lalubi layin Humaira domin ya ji ko ta taho, ko kuma ta fara shirin tahowar. To da ma tun jiyan da suka yi waya, Humaira ta shirya wata ƙarya da za ta fada wa mummy domin ta samu damar fita. Ta faɗa mata cewa gobe za ta sake komawa makaranta ta duba ko an kafe musu admission. Saboda haka lokacin da kiran wayar Usman ya shigo daf take da shiryawa, ɗaga wayar ta yi tare da cewa, “Ga ni nan a hanya.”
Tana faɗa ta kashe sannan ta dubi mummy ta ce, “Mummy zan tafi da wuri domin na je na dawo a kan lokaci.”
Ta saka kafa za ta fita mummy ta ce, “Kuɗin mota fa ba za ki karɓa ba, ko kina da shi?”
“E ina da wani canji a wajena ki bar shi kawai.”
“To shike nan sai kin dawo Allah ya sa a dace.”
“Amin mummy, na tafi.”
Fitowa ta yi nan da nan ta isa bakin titi ta tsayar da mai Adaidaita Sahu ta hau kai tsaye babu ciniki ko kuma ina zai ka ita. Sai da suka fara tafiya ta ce, “Sallari za ka kai ni, nawa zan ba ka?”
Ya ce, “Ki bada dari uku (₦300).”
“Ka ga malam dari biyu da hamsin (₦250) zan ba ka, mene abin ɗari uku a nan? Ɗari biyu ne ma don dai ina sauri ne zan ba ka hakan.”
“To shike nan ba komai Allah ya kaimu lafiya.”
Nan da nan ya isa da ita unguwar Sallari, ta ce ya tsaya kamar kimanin taku ashirin kafin a karasa kofar gidan, ta ba shi kuɗinsa kamar yadda suka yi ciniki sannan ta fito ta taka a ƙasa zuwa gidan. Kiran layin Usman ta yi kafin ta kai ga gidan. Kwance yake kan kujera a falo, ransa cike da farinciki. Tunani yake yadda zai shawo kanta ta amince da shi ta ba shi haɗin kai ya cim ma baƙar niyyarsa ta raba ta da budurcinta.
‘Ko magani zan ba ta ta sha ta yi barci idan ya so sai na yi sha’anina kawai? A’a idan kuma ta sha maganin barcin ya ƙi sakin ta har lokacin da wannan shashashar za ta dawo fa? Gaskiya da matsala. Tunda dai ta amince har ta sake dawowa wataƙila za ta ba ni haɗin kai. Maganin hana daukar ciki kawai zan ba ta, na san duk tsoron da take ji bai wuce na daukar ciki ba, za ta amince da ni idan na fada mata haka.’ Wannan ne tunanin da Usman yake lokacin da kiran wayarta ya shigo masa.
Ɗaga wayar ya yi, ta ce, “Ga ni fa a ƙofar gida fa.”
“Okay to kawai ki shigo babu komai.”
A yanayin ɗar-ɗar ta jefa kafa cikin gidan, kallo ɗaya za ka mata ka gane tana cikin firgici, ƙara kaɗan na iya razana ta ta fita da gudu, domin gani take kamar Anty Sakina na gidan. Sallama ta yi da ƙarfi ta shiga falon, a kwance yake yana ganin ta ya miƙe zaune. Murmushi ya sakar mata tare da harbo mata wani irin kallo da ‘yan iskan idanun nan nasa jajaye sannan ya ce, “Barka da isowa ranki ya dade, bisimillah zauna mana.”
Zaman ta yi bisa two seater da ke duban wacce yake zaune, ya ci gaba da cewa, “Ya garin ya kike, gaskiya kin cika alkawari kin zo da wuri.”
Murmushi kawai take ba tare da cewa komai ba, ya mike ya ce, “Bari na kawo miki wani abu ko?”
Shayi da kwai da abincin da Anty Sakina ta haɗa masa na breakfast din ya dauko ya kawo ya aje gabanta sannan ya ce, “Ki fara da wannan ko?”
“Alhamdulillah! A ƙoshe nake.
Murmushi ya yi tare da cewa, “Ke dai haka kike kullum sai an yi fama da ke a kan abinci. Kin ga ni ma ɗin ban karya ba da ma, bari na rufe gidan na zo mu ci tare.”
Yana faɗa ya mike ya je ya garƙame gidan da sakatar ciki sannan ya dawo, kusa da ita ya zauna sosai. Ya ɗauki wainar ƙwan nan ya kai mata baki, sunkuyar da kanta ta yi, kunya ta kama ta. Ya ce, “Haba meye kuma abin jin kunyar don Allah ki karɓa.”
Ya faɗa tare da dago da kan nata ya saka mata a bakin ta ci, ya sake daukowa ya saka mata ta rika ci. Shi ma ya buɗe bakinsa ta dauko ta saka masa yana ci. Haka suka rika yi tamkar ango da amarya a daren farko. Bayan sun gama cin wainar, ya buɗe plate din abincin ya debo ya kai mata baki, ta ce, “Wallahi na koshi fa, cikina ya cika sosai.”
“To shike nan ba komai, ni bari na ɗan ci kadan.”
Bayan ya gama cin abincin ya yi mika tare da sakin wani irin dogon nishi. Humaira ta yi tsuru-tsuru, hannunta ya kama yana shafa tsakiyarsa yana kewaye ɗan yatsansa a tsakiyar tafin hannun. Ido ta fara lumshewa, jikinta ya fara saki hankalinta ya fara gushewa.
Zuwa can ya saɓa ta a bayansa ya goya ya nufi cikin uwar daki ya sauke ta a kan gado. Ya yi murmushi haɗe da dariya, ya haye sama, ya jima a kanta nishi da ihu kawai take. Zuwa can ya ji ta ƙanƙame shi, gabaɗaya jikinta ya yi collapse. Shi ma nan take ya ji gamsuwa, ya sauka daga kanta ya koma falo. Gumi ne kawai yake ta karyo masa.
Bayan mintuna kamar biyar ya sake komawa ɗakin ya ce da Humaira, “Dawo falo ki huta kada ki yi barci fa.”
Mikewa ta yi ta koma falon ta mayar da kayanta jikinta kamar babu abin da ya faru, zama ta yi amma ta gaza magana jikinta a mace yake, a zahiri da zai bar ta da ta kwanta ta huta. Sai dai ita ma tana jin tsoron kada barcin ya ɗauke ta, a sake kwata abin da ya faru a baya. Mintuna kamar goma suna zaune, zuwa can ta nisa sannan ta ce, “Bari na tafi.”
“Okay za ki iya tafiya yanzu, ko za ki ƙara hutawa na ga da sauran lokaci ko.”
“A’a bari na wuce din kawai.”
Ta fada tare da mikewa, shima mikewar ya yi sannan ya ce, “Ina zuwa ɗan jira ni.”
Ɗaki ya shiga ya dauko kudi masu ɗan yawa sosai, sun ɗara wanda ya ba ta a baya, ya fito ya mika mata tare da cewa, “To ga wannan ki yi kuɗin mota sai dai ba yawa.”
Murmushi ta yi sannan ta ce, “Kai dai ba ka gajiya da hidima haka.”
Shi ma murmushin ya yi tare da cewa, “Ke ma ai ba kya gajiya da yi mini hidimar, yaba kyauta tukwici. Duk abin da kike bukata ki fada mini kin ji.”
Ta karbi kudin tare da cewa, “To na gode Allah ya saka da alkairi.”
Ta saka hijabinta da takalmanta ta fice daga gidan.
Barci Usman ya koma ya dan kara matsewa har zuwa karfe 12:00pm na rana sannan ya tashi ya shirya, har lokacin fitarsa ya yi Anty Sakina ba ta dawo ba, da yake dama wani lokacin takan daɗe a makarantar, kowannensu akwai mukullin gidan a wajensa. Saboda haka yana kammala shirinsa sai ya fice ya kulle gidan.
To babu jimawa da fitarsa, sai Anty Sakina ta dawo daga makaranta. Shigowarta keda wuya bayan ta shiga dakin gado (bedroom) dinta, ta sake ganin wani abin zargin da ya jefa mata ayar tambaya a ranta. Ba komai ba ne illa yadda ta ga an tumurmusa shimfidar zanen gadonta, an birkice yanayin gadon an hargitsa shi, wanda da zarar mutum ya haska idanuwansa a kai dole ya yi tunanin cewa akwai abin da ya gudana. Komai rashin iya kwanciyar mutum shi kadai bai isa ya yamutsa shimfidar nan ba, kai koda a ce yara ne suka hau gadon zanen gadon ba zai tuje haka ba.
“To me ya faru kuma a wannan dakin haka? Indai gari ya waye muka tashi daga barci Usman ba ya komawa kwanciya a kan gadon nan, a falo yake kwanciyarsa kan kujera. Sannan ban taɓa fita ba face na gyara ko’ina, abin akwai daure kai.”
Tunanin da Anty Sakina take ta yi ke nan lokacin da ta shiga ta tsaya daga kofar dakin, abin ma har tsoro ya fara ba ta. Haka ta yi karfin hali ta karasa kusa da gadon, abubuwan da ta gani suka kara tabbatar mata da zargin da take, alamomin dattin kafafuwa da ‘yar ƙura ta gani a kan gadon. Matsawa ta yi sosai ta dauki zanen gadon tana kare masa kallo, a nan ta ga abin da ya tabbatar mata da zarginta gaskiya ne dari bisa dari. Sperm ta gani ya fantsala a jikin zanen gadon har ya ma bushe.
“Babu shakka an yi kwanciyar zina a kan gadon nan.” a zuciyarta ta faɗi wannan magana.
Ita dai ta san yaushe rabon da Usman ya kusance ta da kwanciyar aure har ta manta, sannan kuma koda sun kwanta ɗin shimfidar ba ta tujewa kamar haka. Kanta ne ya fara sara mata, wani duhu-duhu ta fara gani lokaci guda zuciyarta ta fara mata wani irin azababben radadi. Zanen gadon ta mayar yadda ta gan shi sannan ta dawo falo, kafafuwanta sun gaza daukar ta, zubewa ta yi kan kujera tana sauke wani nannauyan numfashi wani na korar wani. A hannu guda kuma zuciyarta na cigaba da tuƙuƙi tamkar wani abu na son faso kirjin nata ya fito waje.