Skip to content
Part 1 of 6 in the Series Danyar Guba by Rukayya Ibrahim Lawal

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Maƙunshi

Wata irin cukurkudaddiyar rayuwa mai cike da datti ce take faruwa a cikin wani Ahali da suka kasance suna sabunta wankansu da ƙazantaccen soso. Salis da Nu’aymah ba su taba tunanin cewa ranar shanye daudadden damun da suka yi za ta zo ba. Ranar da yabanyar kazantaccen irin da suka shuka ta yi tsiro ta fitar da rassan munanan sirrukan su a duniya, har ta zamo silar ba ta su a idon duniya ta cusa musu nadamar ɗurawa cikinsu Ɗanyar Guba.

Tafe suke a babur yana faman karanta mata huɗubar tsiya, ya shiga ya fita ya lalubo manyan ayoyi a cikin littafin ƙaryar da ya rubuta yake ƙoƙarin saka wa ta amince da su. “Ki yi duk mai yiwuwa don ki yago mana wani abu a hannunsa, ki sani wannan ba komai ba ne yayin da aka shiga matsin rayuwa an yarda da yin komai don nemo wa rayuwa mafita.”

Matashiyar da ke zaune a bayan babur ɗin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kana ta ce “Amma Salis ba ka ganin cewa zunubi muke aikatawa? Haram ce fa…”

Bai jira ta sauke furucinta ba ya katse ta hanyar sanyayar da murya ya ce “Haba ke kuwa! Ba fa komai a ciki tun da da amincewa ta ne ba yaudara ta kika yi ba, kuma ma kin ji an ce amfanin zunubi romo.” Ya numfasa kana ya ɗora da faɗar “Ni dai ina mai roƙar ki don Allah kada ki yi abin da za mu rasa damar nan, ko me ya buƙata kawai ki amince in dai zai cake masu gidan ranar.”

A tare ya kashe saƙar zaren zancensa da kuma babur ɗinsa yana ƙoƙarin daidaita tsayuwar babur ɗin ya ce “Mun zo wurin, maza ki je na san yana jiranki a ciki, fatan nasara.” Ya ƙarasa zancen da murmushi tare da neman wata inuwa a can gefe ya zauna ƙarƙashinta alamar zai jira ta ne.

Jiki a sanyaye Nu’aymah ta ke kallon shi daga sama zuwa ƙasa tana ƙara mamakin al’amarinsa. A haka dai kamar mai hankali daga waje amma ta ciki da gyara. ‘To wai shi ba shi da kishi ne ko kuma shashancin nasa ne ya yi yawa?’ tambayar da ta ziyarto zuciyarta kenan.

Can kuma ta ɗaga kafaɗa alamar ko a jikinta, ta gyara zaman ƙaramin mayafinta a kafaɗarta tare da buɗe jaka ta ɗauki cingam mai daɗin ƙamshi ta jefa a baki sannan ta nausa cikin filin shaƙatawar tana kwarkwasa da karairayar da suka saje da yanayinta tana faman tauna cingam ɗin da yake bakinta yana ba da wani sauti ƙasƙas!

Ba ta yi wani nisa a ciki ba ta ja turus ta tsaya tare da ciro falleliyar wayarta ƙirar iPhone X, wayar ya yi ta wannan zamanin ta shiga daddannawa a yangance, bayan wani gajeren lokaci ta yi katari da samun layin da take nema.

Daga ɗaya ɓangaren aka ce “Hello Baby! Kin ƙaraso ne?”

Ta ƙara yin ƙasa da muryarta tare da gayyato salo na musamman ta yi masa mazauni a cikin muryarta “Eh, na ƙaraso Prince, wani hanzari ba gudu ba, ta ya zan gane ka?”

“Okay, ki matso gaba idan kika zo dai-dai filin wasanni na wurin za ki ganni zaune a kan wani Swing tare da yara muna nishaɗi.” Diriricewa ta yi na wucin gadi kasancewar ita ba ta yi wani zurfi a boko ba, asali ma sakandaren ma ba ta gama ba aka yi mata aure ina ita ina sanin wannan kalmar?

“Hello dear! Kina kusa kuwa?” Sai da ta ja dogon numfashi ta sauke kafin ta fara magana “Am! Ina jin ka na gane wurin, yanzu za ka ganni.” Tana gama faɗa ta danne malatsin wayar gudun kada ya sake danno mata wata kalmar da za ta ƙara hargitsa ta, har ta yi silar da zai kwaɓo jirginta, don ba ta so ɗan sauran mutunci da ƙimar da yake gani a tare da ita su zube.

Hakan nan ta miƙa har ta wuce wuraren lilukan tana ‘yan waige-waige tare da danna waya don riƙe tako, ba ta son a ankara da cewar wani abu take neman tantancewa. Masroor yana tsaka da nishaɗi da ƙananun yara ya hango wucewar ta ta gabansu, yana nan yana nazarin kamar ita kamar ba ita ba, ya ga ta tsaya tana waige-waige tare da zare makeken gilashin da ke manne a fuskarta.

‘Waccan uwar iyayin kamar ita ce wacce nake jira? Amma ta yaya za ta kasance ita? Ko dai yanayi ne suka yi?’ zuciyarsa ta raya masa. Ya girgiza kai! Alamun a’a yana ƙaryata zancen zuciyarsa da faɗar “ba zai yiwu ba, princess Nu’aymah ta fi wannan hasken fata.” Sai dai da ya tuna sharrin filtocin zamani da yadda suke sauya asalin kalar fatar mutum da ma halittarsa gabaɗaya sai ya ji ya dace ya gamsu da zancen zuciyarsa. Wannan dalilin ne ya sa ya fara tunkarar wurinta sai kuma ya ɗan dakata tare da ciro wayarsa daga aljihu ya danna mata kira, amma idanunsa suna kan matashiyar budurwa da yake hasashen ita ce ko ba ita ba ce.

Ganin ta ɗago wayar hannunta tare da dannawa ta kanga a kunne a daidai lokacin da ya ji an amsa kiransa, sai ya tabbatar cewa ba ƙarya idanunsa suka faɗa masa ba.

Ya yi wani shaƙiyin murmushi a zahiri ya ce “Filter duniya ce Alaji.” Sa’annan ya zaro nashi gilashin daga aljihun gaban riga ya sanya kana ya gyara zaman hularsa ya tunkare ta yana dabsa murmushi.

“Barka dai gimbiya!” Wannan sautin ne ya dawo da hankalinta zuwa duban inda ta ji sautin ya fito. Kawai sai ta ga bayyanar mutum a gabanta don kuwa ko da wasa ba ta ga tahowar shi ba. A take ta samar murmushi matsugunni a fuskarta yi ƙasa da muryar cikin kwarkwasa ta ce “barka dai Prince! Shi ne ka ɓuya don na sha wahala ko?

Shi ma martanin murmushin ya maida mata kafin ya ce “Ke kin san ba zan yi abin da zai wahalar da ke ba gimbiya, a gabana fa kika wuce kawai dai ki ce ba ki gane ni ba ne, ko kuma kina so ki azabtar da zuciyata shi ya sa kika wuce da gangan.”

Ya ɗan matsa nesa kaɗan da ita yana kallon cikin ƙwayar idonta ya ce “Shi kenan mu je can mu zauna.” Ya nuna mata wata ‘yar bukkar zamani da ke nesa da su kaɗan. Ba ta yi magana ba ta ci gaba da tauna cingam ɗinta tare da bin bayansa.

Wuri suka nema a kan kujerin robar da aka jera a ciki suka zauna, hankali kwance suka fara hira ransa fayau ba fargabar komai. Ita ma hankalinta kwance kamar tsumma a randa suna tsaka da nishaɗin su suna kwashewa da dariya har da tafawa ta jiyo a bayanta ana faɗa cikin ɗaga murya “Mrs Salis!” Da farko yi ta yi kamar ba ta ji ba, amma a ta ciki hankalinta a tashe yake ainun ‘wace banza ce za ta rusa mini shiri?’ Ta faɗa a ranta tana ƙara dakewa da ƙaƙalo murmushi “My prince kasan yadda nake matuƙar ƙaunarka kuwa? A ɗan ƙanƙanin lokacin da na sanka ka…” Ba ta yi nasarar ƙarasa zancen ba don jin muryar da ta ambace ta dab da ita tana maimaita faɗar “Mrs Salis” sannan ta ɗora da “Wai ba ki gane ni ba ne?”

A hargitse ta juyo da dubanta zuwa inda take jiyo sautin don ganin mai ƙoƙarin karya mata alkadari. Tabbas ta shaida fuskar matar aminin Salis ce Safna, suna ɗasawa sosai amma a wannan lokacin dole ta yi wani abin da zai kuɓutar da ita daga zargin Prince, ta lashi takobin ba za ta taɓa bari wani daga cikin manemanta ya san ita matar aure ba ce, don haka ta zuba idanunta a cikin na Safna tana ƙoƙarin yin magana ganin yadda Prince ya kafe ta da ido kamar mai ƙoƙarin nazarartar yanayinta.

“Ko ba Nu’aymah matar Salis ba ce?” Safnan ta sake faɗa tana bin ta da kallon mamaki.

Saurin bugun zuciyarta ne ya ƙaru ta janye idanunta daga cikin na Safna tana sunkuyar da kai ƙasa “Waye Salis? Yi haƙuri sis sai dai in kama ce.” Ta sauke tana rarraba ido kamar wacce ta yi gulmar sarki a kunnen fadawa.

Kodayake masu azanci na cewa mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi.
Safna ta girgiza kai da alamun mamaki fuska ba yabo ba fallasa ta bar wurin, shi kuwa wanda take kira da Prince ya kafe ta da abin taƙamar mujiyarsa yana ci gaba da nazartar ta. Ita ko sai ta yi wani tsamo-tsamo kamar kazar da ta faɗa ruwan zafi.

Gyaran murya ya yi kaɗan, hakan ya sa ta ɗago kanta tana ƙoƙarin saita nutsuwarta da ƙyar ta buɗi baki cikin sanyin murya ta ce “Yi haƙuri, wannan matar ta zo ta ɓata mana hira, kama ce fa kawai, wataƙila ma tana da matsalar ido amma kasan halin mutane da yanke hukunci kai tsaye.”

Riƙo tafin hannunta ya yi tare da sarƙe shi cikin nasa ya ce “kar ki wani damu, gaskiya dokin ƙarfe ce wanda yake kai ba shi da fargaba.” Ta sake sunkuyar da kai tana ji kamar magana ya yada mata, duk da a halin firgicin da take ciki ba ta iya tantance farar magana da baƙa.

Zahiri kuma ba tana damuwa ba ne a kan wai tana aikata fasiƙanci da aurenta, damuwar ta ita ce kada manemanta su fahimci hakan su gudu ba tare da ta gama morar su ba.
A hakan dai da yake ta iya barikanci sai ta saki jiki kamar komai bai faru ba suka ci gaba da hirarsu kafin suka tashi suka zazzaga cikin park ɗin ya nemo musu abin taɓawa. Mintuna ashirin kawai suka ƙara daga lokacin ya dube ta “Ina ga yanzu za mu yi sallama zan koma gida akwai wata dinner da za ni anjima. Mu je na raka ki gun motarki.”

Ɗif wuta ta ɗauke mata tana maimaita kalmar mota can cikin maƙogwaronta, da a ce a lokacin ya mayar da hankalinsa a kan laɓɓanta zai ga yadda suka furta kalmar mota da mamaki. Ya sake yin gyaran murya sannan ta dawo hayacinta tana ƙoƙarin waskewa “Kar ka damu wurin nan ya yi mini daɗin zama zan ɗan ƙara koda mintuna talatin ne kafin na tafi.”

Ganin ta ƙi tayinsa sai ya ƙara faɗaɗa murmushinsa tare da sanya hannu a aljihu ya ciro damin ‘yan dubu ɗaɗɗaya guda ya miƙa mata yana faɗar “ki sa mai a motarki zan faɗa miki inda za mu haɗu a gaba sai ki same ni can, yau ba sarari ga shi ban ƙoshi da ganinki ba amma zan tafi.”

Ba ko musu ta karɓe tana jujjuya su a hannunta tana wani shu’umin murmushi. A maimakon ta yi masa godiya sai ta tara hannunta ta busa sumba a jiki ta yi amfani da leɓunanta wurin hura masa iskar ga fuskarsa. Shi ma da yake ɗan duniyan ne irin ta, sai ya ranƙwasa kai tare da lumshe ido ya buɗe hannunsa na hagu kamar zai karɓo abu a gun ta ya dunƙule ya buga a kafaɗarsa yana sunkuyar da kai alamun ya karɓe sumbar kuma yana godiya.

Daga haka ya juya ya nufi baƙar dalleliyar motarsa ya shige tare da tada ta ya fice daga wurin shakatawar.

Tana ganin tafiyarsa ta ƙara kallon kuɗin hannunta tana zabga murmushi. Kafin ka ce me iska ta fara karkaɗa takardun kuɗin, da hanzari ta buɗe jakar hannunta ta tura kuɗin tare da kallon sararin samaniya.

Ta yi mamakin ganin yadda lokaci ɗaya sama ta sha toka, duk da ba a mamakin al’amarin ubangiji da yadda yake gudanar da shi cikin ikonSa. Hadarin da a da yake ƙasa ya taso ka’in da na’in, gajimare ya mamaye ilahirin sararin samaniya sai walƙiya da iska mai ƙarfi ke kaɗawa kamar za ta ƙwace mata mayafi. Cikin hanzari ta fara gudu-gudu sauri sauri tana ƙoƙarin fita daga cikin filin shakatawar, sau uku tana auna arziƙi na rashin faɗuwa don ko ƙafafuwanta sai harɗewa suke, takalmi mai tsinin da ke sanye a ƙafarta ya taka rawar gani wurin ƙoƙarin saka ta cin ƙasa, amma sai Allah ya yi mata gyaɗar dogo ba ta kifa ba.

Kira ne ya shigo wayarta ko duba mai kira ba ta tsaya yi ba don ta tabbatar da cewa mijinta ne yake kiranta. Ɗagawa ta yi tare da ɗorawa a kan kunnenta ba tare da ta jira jin abin da zai ce ba ba kuma sallama kawai ta ce “Yanzun nan za ka gan ni.” Daga haka kuma ta katse wayar ta rufe ta ta jefa a jaka tana ƙara hanzari. A haka ta fito titin iska na ƙara manne ɗamammun riga da siket ɗin da ke jikinta a fatarta, waɗanda tsabar matse tan da suka yi kamar ma a jikinta aka ɗinka su.
Yana hango fitowar ta ya miƙe sai dai yana ƙoƙarin hawan babur ɗinsa ya hango ta tana leƙe a jikin wata ƙerarriyar mota da yana kallon lokacin da mai motar ya yi mata siginal ta je, da alama lambar wayarta take ba shi. Lallausan murmushi ya saki yana faɗar “Shegiya tawan ba dai farinjini da iya kwarkwasa ba! Haka nake so.” Ya ƙarasa faɗa yana shafa dokin wuyansa cikin jin daɗi. Sai da ya ga ɓacewar mai motar sannan ya hawo babur ɗinsa ya yo inda take yana faɗar “Sauri ki hau mu je, kada ruwa ya rutsa mu.”

Yanzun ma irin zaman ɗazu ta yi wato zaman gefe, don ba yadda za a yi ta iya ware ƙafafunta ta hau babur ɗin sosai kamar yadda aka saba saboda suturar jikinta. Sauri kawai yake zubawa kamar zai tashi sama, iskar daminar da ke kaɗawa da kara-kainar ababen hawa ba su hana masa yin abin da ya saba ba “Allah ya sa dai kin samo mana da yawa, kuma ba na son rinto kin sani, ki faɗan gaskiya nawa ya ba ki?”

Ta murguɗa masa baki daga bayan babur ɗin kamar yana kallon ta “Matsalata da kai kenan, azarɓaɓi! Me ma kake ci na baka na zuba? Ai dai ka bari mu je gida sai a yi wacca za a yi…” Kafin ta rufe bakinta suka ji saukar ruwan sama shaaa!

Ta ja doguwar ajiyar zuciya ta sauke a firgice ta bubbuga kafaɗarsa tana faɗar “Na shiga uku Habibie ka ƙara sauri don Allah! Don Allah ka yi sauri!”
Ɗan murmushi ya yi wanda ya fi kama da na mugunta yana ci gaba da tuƙinsa kamar ba da shi take zancen ba, duk da ya sani sarai cewa jikinta ko kaɗan ba ya son dukan ruwa, kamar akuya take da masifar tsoron ruwan sama sai dai shi saukar ruwan a wannan lokacin ya yi masa dai dai tun da ya kashe bakin tsiwar.

“Habibie! Wai ba ka ji na ne? Don Allah! Ba don ni ba…” Ta faɗa da rawar murya tana sharce ruwan fuskarta da tafin hannunta tana nishi kaɗan-kaɗan.

“Ina jinki kuwa Habibtie! Ai mun kusa ƙarasawa, fatana mu isa gida kafin ruwan su yi ƙarfin da za su hana mana tafiya.” Ya faɗa da wata iriyar murya.
Ba su fi mintuna bakwai ba a hanyar ya iso daidai kwararon da zai sada su da ƙofar gidansu, kasancewar gidan nasu ya ɗan shiga lungu ba a fuskar titi yake ba.

Tun daga nesa Nu’aymah take hango ‘yan matan gidan su guda huɗu tsaye a ƙofar gidan nata a tsattsaye sun yi cirko-cirko kowaccen su ta jiƙe sharkaf sai ƙanƙame jiki wasu daga cikinsu ke faman yi.

Ɗan bubbuga kafaɗarsa ta yi tare da faɗar “Lah! Ka ga ‘yanmatan gidanmu ko daga ina suka fito cikin ruwan nan?” Ba ta jira ya amsa ba ganin sun matso daf da gidan ta matsar da bakinta saitin kunnensa ta raɗa masa magana kamar haka, “muna sauka ka karɓe jakar hannuna ka shiga da ita ciki, ka san halin Inan tsaf za ta yi mini cajen jaka, tana ganin kuɗin nan kuma mun shiga uku.”

Murmushin jin daɗi ya yi, lokuta da dama Nu’aymah tana burge shi saboda basirarta ta iya tsara abubuwa yadda za su tafi dai-dai, haka nan yana ƙaunar matar tasa kasancewar tana ba shi haɗin kai sosai a wurin tallafawa burinsa. Shi ya sa shi ma ba ya wasa fagen yin duk abin da zai bunƙasa wannan harkar da suka mayar tamkar kasuwanci. Sara kawai suke faman yi ba sa duba bakin gatari, kuma ba sa hasashen zuwan ranar da kwabarsu za ta caɓalɓale da ruwa.

Suna isa ƙofar gidan ya take birki a gefe ɗaya cikin ƙatuwar rumfar maƙwaftansu da ‘yanmatan suka fake a ciki. Nu’aymah ta miƙa masa jakar da sunan riƙo kana ta duro daga kan babur ɗin ta nufi wurin ‘yan’uwan nata tana faɗar “Ahalin Mai’Alewa daga ina haka?” Ta watsa musu tambayar cike da murmushi a fuskarta.

“Daga gida zuwa gidan ‘yar’uwa sai dai rashin sa’ar ‘yar’uwar ba ta nan.” Nusrat ta faɗa tana ƙoƙarin matse leɓɓan hannun rigarta da ta haɗe wuri ɗaya.

“Ayyah! Ku yi haƙuri, wata fita ce mai muhimmanci ta kama mu.” Kafin ɗayar su ta buɗe baki ta ce wani abu Salis ya bayyana a gaban ƙyauren gidan yana ƙoƙarin zura ɗan makulli a cikin ramin ƙwadon ƙofar da har ya fara tsatsa, bai kalle su ba ya ce,

“Sannunku ‘yanmata!” Har suna haɗa baki wurin faɗar “Sannu ɗan’uwa” A dai-dai lokacin ne ya gama buɗe ƙofar gidan don haka gaba ɗayansu suka hau rige-rigen kutsa kai cikin gidan.
Shi ma ya bi su ciki tare da zuge babban ƙyauren gidan (Gate) sannan ya koma daga waje ya shigo da babur ɗinsa cikin gida tare da maida ƙyauren ya rufe.

Za a iya cewa wannan al’ada ce ta mafi yawan unguwanni da suka kasance marasa hayaniya, ko kuma a ce magidantan da ba su tara iyali da yawa ba.

Kafin ya shiga daga cikin falon sai da ya laɓe ya buɗe jakar tare da leƙawa. Zazzaro ido ya yi a waje yana zuro harshe kamar kwaɗayayyen karen da ya ga ƙashi.

Nan wurin ya tsaya yana shawara da zuciyarsa shin ya rage kuɗin ko kuma ya bari su raba kamar yadda suka saba? Wata zuciyar tana zuga shi da faɗar ‘ka zari ko guda goma ne ka ɓoye, ai ita ma rinto take yi maka.’ Wata zuciyar kuma tana lallasar shi da nuna masa ya yi haƙuri tun da har za ta raba ta ba shi haƙƙinsa.’

Da ƙyar ya iya jurewa ya lallashi zuciyarsa ta haƙura da ragewar sannan ya sa kansa a cikin falon yana sallama.

Ba wanda ya tarar a ƙaramin falon nasu sai dai yana iya jiyo hayaniyarsu a uwarɗakan Nu’aymah da alama suna kiciniyar sauya kaya ne saboda ya jiyo muryar ɗaya daga cikin su tana faɗar “Sanyi ya fara kama ƙashina, don Allah taya ni na cire wannan ɗinkin zamanin.” Kafin ya ƙarasa shigewa ɗakinsa da yake hannun riga da nata ya jiyo muryarta tana faɗar “Na san yau ba zan kwana lafiya ba, yi sauri Ashna ki taya ni na cire wannan mugun siket ɗin.”

Don haka sai ya wuce kai tsaye zuwa ɗakinsa zuciyarsa na ta yi masa saƙe-saƙe a kan kuɗin. Can bayan kamar mintuna goma ya ji an turo ƙofar ɗakin nasa an shigo. Bai juyo ba don ya riga ya san wacce za ta iya yin hakan kai tsaye.

Ƙarasawa ciki ta yi tana kallonsa cikin shigar da ya sauya daga yadi zuwa jallabiya shuɗiya. Zuwa lokacin tuni ta fara jin alamar zazzaɓi a jikinta amma da yake hankalinta na kan jakarta da ta ba shi riƙo sai ba ta wani damu da hakan ba, ta yi wurin jakarta da ke ajiye a kan gadonsa ta janyo ta tare da zama tana ƙoƙarin buɗe zip ɗin.


“Dubu ɗari ne cas! Bari ka gan su” ta zaro tana nuna masa, ya ja dogon tsaki tare da kawar da kai gefe ya ce “Yau dawa ba ta yi nama ba kenan, amma wannan mutumin matsiyaci ne ko?” Ta ɗago tana bin sa da kallon hadarin kaji ta ce “Au! Ka raina wannan ne?””Ina abin yake wai maye ya ga jariri?” Ya faɗa yana ƙara haɗe fuska tare da taɓe baki kamar wanda ya ga ɗanyen kashi, a lokacin da ita kuma ta fara ƙoƙarin mayar da kuɗin jaka tana faɗar “Yi haƙuri ɗan Ƙaruna! Na manta ka fi ƙarfin wannan kuɗin tun da kake yin matashi da dala.” Sarai ya san magana ta faɗa masa ya kuma santa ta ƙware a rinto tsaf za ta iya wawushe kuɗin ta hana masa a kan ‘yar wannan maganar. Saboda haka sai ya matso yana kwantar da murya da faɗar

wasa fa nake, ai ya ma yi ƙoƙari duka fa ba ku fi awa ɗaya da rabi ba a tare ya ba ki wannan, ciro ki ban kasona.”

Ta zuge zip ɗin jakar tare da miƙewa ta nufi wurin wadurof ta buɗe ta sanya a ciki ta rufe tare da cire ɗan makullin.

“Ban gane ba me kike nufi Habibtie?” Ta juya tana nufar hanyar fita tana faɗar “Ai dai ka bari baƙin su tafi sai mu raba ko?”

Ya sauke ajiyar zuciya tare da komawa kan gado ya zauna, ita kuma ta fice zuwa falon. Har zuwa lokacin ruwan ake kamar da bakin ƙwarya don haka sai ya zamana duk da riga mai nauyin da ta jibga a jikinta sanyin yana ci gaba da ratsa ƙasusuwanta.

Isowar ta falon kedawuya Inan ta ce “Yaya Nu’aymah haka ake baƙi a bar su ba abin taɓawa duk sanyin nan da muka sha?” Isa ta yi wurin kujerar zaman mutum uku ta zauna kusa da Nusrat tare da kishingiɗawa tana dafe kai ta ce “ban da neman magana ai ku ba baƙi ba ne a gidan, sannan ba na tunanin mun bar wani abin kirki da za a iya ci lokacin da za mu fita, sai dai ku dafa mana baƙin shayi ba za a rasa biredi da ƙwai a madafar ba.”

Daga haka ta rufe ido tana jin ciwon kai sama-sama. Inan ta gyara kwanciyarta a kan kujera mai cin mutum biyu da take kai tana rufe idanunta wai don ma kar a ga damar ta a ce ta tashi a more ta.

Ashna da ta kasance ƙarama a cikin su ta miƙe da ma ita ba ta da son jiki kwata-kwata, ta nufi kitchen ɗin don ta agaji cikinta da yake mata ƙugi.

Inan ce ta juyo dubanta ga Nu’aymah tana faɗar “Sister wai ina kuka je ne cikin ruwan nan?” Ba tare da ta buɗe idonta da yake rufe ba ta amsa ta da cewa “wata matar Abokinsa ce ta haihu muka je barka ruwa ya rutsa mu a hanyar dawowa.” Tana gama faɗa kamar wacce ta tuna wani abu ta buɗe idanunta tare da ɗaukar wayarta ta cire security tana danne-danne. Tana cikin haka ne ta jiyo muryar Ashna daga kitchen tana tambayar ta inda ta ajiye kanumfari. Sanin cewa ko ta yi wa Ashna bayani ba lallai ta fahimta ba sai ta miƙe tare da ajiye wayar da ke hannunta ta je kitchen ɗin don ta ɗauko mata.

A cikin madafar bayan ta buɗe loka ta janyo ƙullin kayan yajin kawai sai ta tuna wayarta da ta ajiye a buɗe. Da ƙarfi ƙirjinta ya buga sanin cewa tana da tarin ɓoyayyin sirruka da ba ta so a gani. sarai kuma ta san halin yaran gidansu da karambani tabbas wata za ta iya ɗauka ta ɓallo mata ruwan da ya fi ƙarfinta don haka da hanzari ta nufi hanyar fita ba tare da ta juyo ba ta ce da Ashna “ki duba cikin ƙulle-ƙullen za ki samu.”

A ƙofar kitchen ɗin ta ja ta tsaya bugun zuciyarta na ƙaruwa ba don komai ba sai don ganin wayarta a hannun Nusrat tana dannawa, kuma ta tabbatar da cewa bincike take yi mata a wayar don ta san halinta ba tun yau ba. Kafin ta samu kuzarin motsawa ta ga Nusrat ta ɗago idanunta ta kalli ɓangaren da take tsaye. Suna haɗa ido ta watso mata tambaya cikin saurin baki “waye wannan Zazzafan saurayin da kuke tare a hoton nan?”

Jin wannan tambayar ya saka numfashinta ya yi barazanar ɗaukewa kafin ta ce wani abu duka ‘yan matan da ke falon suka nufi Nusrat suna rige-rigen amsar wayar da ta juyo fuskarta tana fuskantar inda ta ke tsaye har suna haɗa baki wurin faɗar “mu gani! Don Allah mu gani.”

Danyar Guba 2 >>

1 thought on “Danyar Guba 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×