Da ƙyar wani bacci ɓarawo ya yi nasarar sace ta bayan ta kwashe dogon lokaci har zuwa ƙarfe ukun dare tana jiran dawowar sahibin nata amma shiru kamar maye ya ci shirwa. Haka ta kwana ta tashi da zazzaɓi mai zafi a jikinta. Tun ƙarfe biyar da rabi na asuba ta farka da tsananin damuwa lokacin da ta buɗe ido ta tabbatar Salis bai kwana a gidan ba, sai ta ji hankalinta yana ruɓanya tashi. Wayarta ta ɗauka ta sake gwada kiran shi amma shiru dai ba wani canji daga yanayin farko. Wani irin kuka ta ji yana zuwa mata da ba ta san dalilin zuwan shi ba, sai kawai ta dungure wayar ta miƙe ta ɗoro alwala ta zo ta gabatar da sallar asubar da har ta manta rabon ta da ta yi ta a kan kari idan ma za ta yi sallar kenan. Galibi bayan isha’i idan ta gama yawace-yawacen ta a gari take haɗewa dukan su ta yi a lokaci ɗaya. Amma yau da ta riski kanta cikin baƙon yanayi sai ta tuna da Allah, ta tuna cewa shi kaɗai ne zai iya ba ta mafita a wannan taƙin. Bayan ta kammala sallar ne ta ɗaga hannu sama ta shiga jero masa addu’o’i cikin sautin kuka faɗar ta ke
“Ya ubangijina ka fi ni sanin abin da ke faruwa da bawanka, kai ne masanin ilimin ɓoye da na sarari Allah ka kuɓutar mini da shi ka dawo mini da shi lafiya.” Ta shafa addu’ar sa’annan ta kifa kanta a gefen gado tana zubar da hawaye.
Zancen karyawa bai ma faɗo ranta ba balle ta tashi ta yi. Tana nan kishingiɗe a wurin ƙarar buga ƙofar da ake ya farkar da ita daga baccin da ya fara ɗiban ta. Ta ƙara kasa kunne da kyau, da dai ta tabbatar ƙofar ake bugawa ta miƙe cike da farinciki da fatan yin tozali da shi. Da ɗan guntun gudunta ta ƙarasa ƙofar tana faɗar “Ga ni nan.”
Sai dai gama zare sakatar ƙofar kedawuya ta ja ta yi turus yanayin fuskarta ya rikiɗe daga farinciki zuwa mamakin abin da ta gani da ya saɓa da abin da take tunani.
Wasu mutane ne guda uku tsaye sanye da fararen kaya, tana bayyana a gaban su suka haɗa baki wurin tambayar ta “Ina mijinki?”
Allah ya sa tana sanye da hijabin da ta gama sallah ba ta cire ba don haka ta saki jikinta tana amsa musu da “Ba ya nan, su waye ku?”
“Jami’ai daga hukumar ‘Yansanda kar ki yi mana ƙarya ina yake?” Ɗaya daga cikin su ya faɗa tare da nuna mata i.d card ɗinsa sannan suka kutso kai cikin gate ɗin ba jiran izini.
Da hanzari ta matsa gefe fuskarta na bayyanar da maɗaukakin mamaki ta maimaita kalmar ” Yan sanda?” Sannan ta ƙara da faɗar “Mu ba ɓarayi ba ba ‘yanfashi ba me ya haɗa mu da hukumarku?”
“Za ki sani idan muka kama macucin mijinki.” Babban cikin su ya faɗa yana ƙoƙarin shige wa falonta. Ta bi shi a baya a hanzarce a ranta tana faɗar ‘Ikon Allah! Na kwance ya faɗi.’ A zahiri kuwa cewa ta yi “Yallaɓai meye haka? Ya za ka shigar mini ɗaki ba izini? Ko ba ka san ɗaki sirrin masu gida ba ne.”
Bai ko kalle ta ba ya yi shigewar shi yana dube-dube a cikin ɗakin, shi ne har uwar ɗakanta yana leƙa ƙarƙashin gado. Ita kuma tana biye da shi a baya sake da baki kamar sakarya.
“Wai don Allah me mijina ya yi muku ne? Ko ku ne kuka ɓoye mini shi tun jiya nake neman shi?”
Jami’in ya ci gaba da dube-duben shi yana faɗar “Amsar tambayarki ta farko ba za ta samu a yanzu ba, amsarki ta biyu kuwa ita ce ba mu muka ɓoye shi ba muna neman shi ne don aikata hakan.”
Daga haka bai sake cewa komai ba sai da ya gama binciken shi tsaf bai ga komai ba kuma bai samu wanda yake nema ba sannan ya kalle ta, “Idan ya dawo kar ki sanar da shi mun zo.”
Yana gama faɗa ya fice tare da yi wa abokan aikin nasa umurni suka bar gidan.
Bayan ficewar jami’an Nu’aymah ta yasu a falo tare da fashewa da kuka abu ga mai rarraunar zuciya. Kodayake da ma mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Don haka sai da ta yi mai isar ta kafin ta gaji ta rarrashi zuciyarta ta wanko fuskarta ta sake dawowa mazauninta cike da ƙarfin hali da samun yaƙini a zuciyarta cewa Salis ya je ɓoyo ne, ta shiga kitchen tana dudduba abin da za ta saka wa cikinta. Sai dai dai-dai da guntun biredin da ta yi tsammanin samu babu, balle kuma ƙwai. Haka nan ta duba ma’ajiyar abincinsu shi ma tas, taliya ɗayar da ta rage ma da alama ya cinye ko ya sadakar.
Sai kawai ta je ta buɗe firiza inda ta samo rabin shawarmar da ya ci lokacin da za ta fita makaranta. Ta ɗauko ta tana ƙare mata kallo a rene.
Ita ta samu ta ci da sanyin ta ma ko ɗumamawa ba ta yi tunanin yi ba, ta kora da ragowar furar Rufaida da ta gani a roba.
Barin wurin firizar ta yi ta nufi ɗakinsa ta hau lalabe ko za ta samu ragowar kuɗi a ma’ajiyarsa ta samu ta sayi abinci ta adana kafin ya dawo. Sai dai can ma ba haske kasancewar a cikin wannan satin fatara duk ta yi musu yawa, ba kasuwar. haka yake dawowa daga buge-bugensa hannu fayau, ranar da aka yi sa’a ya riƙo abin da za su ci a lokacin to ita ce babbar rana a gare su. Daga ɓangaren ta ma kamar wacce aka yi wa farraƙu da samarinta duk ba wanda ya kula ta a wannan satin. Koda ta kira su kowa da uzurin da yake kawo mata wanda a bisa tilas take ƙyale su.
Daga can ɗakin nasa ta taho a guje tana kakarin aman da yake ta yunƙuro ta tun bayan da ta gama cinye shawarmar.
Kafin ma ta ƙarasa waje tuni aman ya yi mata tahowar gaba ɗaya, don haka a nan falon ta durƙushe tana fesawa. Sai da ta mayar da duk abin da ta ci kafin ta samu abin ya faɗa mata.
Jiki ba ƙwari ta je ta wanko fuskarta a banɗaki sannan ta kwashe ƙazantar da ta yi ta gyara wurin ta koma ɗakinta jiki a mace. Sa’ilin ne ta tarar da kiran da ta rasa (misscall) na sabuwar lamba a wayarta.
Kamar kada ta bi kiran don tunanin ko manemanta na waje ne za su dame ta a cikin wannan lokacin da duniyar ke juya mata. Tana nan tana tunani kiran ya sake shigowa ta ɗaga a sanyaye.
“Habibie! Ina ka shiga ne tun jiya.” Ta faɗa da muryar damuwa lokacin da ta ji muryarsa. A can ɓangaren shi murmushin takaici ya yi yana faɗar “Wasu sun zo nema na?” “Eh sun zo, wai me ka yi musu ne?” Ta amsa masa a gajarce kafin ta rufe zancenta da tambaya.
“Zan faɗa miki daga baya yanzu ya jikin naki?” “Da sauki.” ta amsa kamar mai ciwon baki.
“Kina ji na Habibtie? Yanzu ki shirya ki je gida, nan da kwana biyu idan na saita komai zan neme ki don ina da yaƙinin mutanen nan za su dawo, ba na son su ci gaba da ɗaga miki hankali. Kuma kar ki sake kirawo layin nan aron wayar na yi, zan sake kiran ki idan na samu sarari.”
Yana gama faɗa ya kashe wayar. Ko sakan goma na kirki ba a rufa ba ta bi kiran ta ji switch off alamar an zage layin daga gwangwanin wayar.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un” Take ta maimaitawa, don gabaki ɗaya kalmomin bakinta sun yi hijira wannan kalmar ce kawai ta samu damar yin kyakkyawar tsayuwa a tudun harshenta har ta iya furta ta. Ta fi mintuna talatin zaune a wurin tana laluben mafita sai dai ba ta hango wata manufar da ta fi wacce ya faɗa mata ba.
A gaggauce ta miƙe ta hau kimtsa kayan ta a ɗan ƙaramin akwati a ranta tana saƙe-saƙen inda za ta bar motar, sai abin ya zame mata ɗaki zufa waje sanyi.
Don kuwa ba zai yiwu ta bar motarta a gidan da ba kowa a irin wannan unguwar ba, haka ba za ta iya tafiya da ita gidan su ba don ko ta ce Salis ne ya saya mata za a tuhume ta a kan inda Salis ya samo kuɗin silayan mota a matsayinsa na cima-zaune da dalilin da ya sa bai sayawa kansa ba sai ita. Ta kuwa san halin baffa sarai zai ce sai an sayar da motar don ba dalilin da za a bar ƙaramar yarinya irin ta ta yi tuƙi a gari.
Wata dabara ce ta faɗo mata a rai ba tunanin komai ta yanke shawarar aiwatar da ita. Bayan ta kukkule ko’ina a gidan ta ja motarta ta kai ta gareji ajiya da alƙawarin idan ta zo ɗauka za ta biya balance. Daga can ta tare adaidaita ta wuce gida. Allah ya taimake ta da ragowar ɗari biyar a cikin jakarta da ta dawo da ita daga makaranta, su ta samu ta biya mai adaidaita ya sauke ta a Rikkos.
*****
A ɓangaren Salis kuwa, bayan da ya bar gida kai tsaye wurin ɗaurin auren abokinsa ya wuce. Ana tsaka da ɗaurin auren wani abokin harƙallarsu ya kira shi. Bai samu ɗagawa a karon farko ba saboda hayaniyar da ta hana masa damar jin ƙarar kiran. Sai a karo na biyu da ya ji alamar motsin wayar a jikinsa, ya saka hannu ya zaro ta daga aljihun wandonsa sannan ya ɗaga kiran yana ƙoƙarin zame jikinsa daga cikin mutane don ya samu damar sauraren abin da za a sanar da shi. Gefe ya koma inda hayaniyar jama’a ta yi ƙaranci sannan ya ce “Hello Sala money ka yi haƙuri ina cikin jama’a ne, amma yanzu ina jinka.”
Cikin wata iriyar murya mai bayyanar da tashin hankali wanda ya kira da Sala ya ce “Ka yi gaggawar cire layinka daga kan wayar don ba tsaro a tattare da ita, sannan ka nemi wurin ɓuya, don kuwa ɓalli ya tashi. Sa’id ya shiga hannun Jami’an farin kaya shi ne ma ya ambaci sunayenmu, yanzu haka daga mafakata nake kiran ka, kar ka sake ka ce za ka koma gida can ma ba tsaro. Ka fi kowa sanin hatsarin abin da muka aikata dai.”
Tun lokacin da Salis ya fara sauraren abokin nasa tashin hankali ya bayyana ƙarara a taswirar fuskarsa sai rarraba ido yake yana muzurai, duk ya firgice kamar ka ce masa kyaat ya zuba a guje.
“Na…na gode Sala.” Ya faɗa a gajartaccen sauti mai fitar da amon in-ina bai jira Sala ya katse wayar ba ya fitar da batirin ƙaramar wayar da layinsa ke ciki ya ciro shi yana sakawa a aljihu sannan ya bar wurin ɗaurin auren ba tare da ya waiwaya ba. A ransa yana faɗar ‘Tofa! Yau ake yin ta, ko’ina uban gayyar?’ haka ya ci gaba da saƙe-saƙen shin za su sha a wannan karon ma ko kuma dubu ce ta cika?
Bai zame ko’ina ba sai a gidansu Rose wacce ba a taɓa tsammanin za ta ba shi mafaka ba duba da banbancin addini da ƙabila da suke da shi. Uwa-uba sanannen abu ne cewa ba jituwa tsakanin kirista da musulman da suke rayuwa a jihar ta plateau suna yawan samun rikicin addini a tsakanin su.
A ƙasa layinsa ya kwana duk yadda ya kai da tunanin Nu’aymah da ke kwance a ƙasan ransa da son ya kira ta don ya ji halin da take ciki amma haka ya haƙura a dalilin abu biyu.
Na farko ba ya son ya ɓata wa Rose rai, na biyu tsoron abin da ka biyo bayan kunna wayar tasa. Ya sani ba iya rayuwarsa ba har ta matarsa zai saka a haɗari muddin aka bi diddigin jadawalin kiran shi. Hakan ya sa ko a lokacin da ya yi shahadar kiran ta bai yi amfani da tsohon layinsa ba sai ya yi da sabon da ya sa Rose ta siyo masa a ranar da ya zo gidansu, ya fita waje in da ba za ta jiyo shi ba ya yi wayar.
Har zuwa lokacin bai bar kowa ya san inda yake ba har iyayensa da ‘yan’uwansa.
Nu’aymah tana isa gidan nasu ta tarar da abin da ta ke fargabar riskar shi. Ko ƙarashe sallamar ba ta yi ba baffa ya tare ta da zancen dalilin fitowar ta a irin wannan lokacin kuma da akwati a hannunta.
“Ba dai auren kika kaso ba ‘yar nan?” Ya faɗa yana kafe ta da ido. Rissinawa ta yi har ƙasa tana gaishe shi, ganin bai amsa mata gaisuwar ba sai tsare ta da ido da ya yi, ya saka ta sunkuyar da kai ta fara magana “A’a Baffa tafiyar gaggawa ce ta same shi shi ne ya ce na zo gida na zauna har Allah ya yi masa dawowa.”
Baffa bai sake cewa komai ba sai bin ta da ya yi da kallon uku saura kwata da alama a ransa bai gama gamsuwa da zancen nata ba. Tana ganin haka sai ta miƙe jiki a saluɓe ta ƙarasa shigewa sashen mama ta ajiye akwatinta a ɗakin Ashna sannan ta je ɗakin mama suka gaisa.
Mamar ta kafe ta da ido tana faɗar “Amma na gan ki a dame, ga shi duk kin yi wani zuru-zuru, ko dai tuhumar da malam yake miki gaskiya ce?”
“Ko ɗaya mama, yadda kika ji na faɗa masan nan dai shi ne gaskiya. Ina fama da jinya ne shi ya sa kika ganni a haka.” Ta faɗa tana gyara zamanta a kan carpet.
“Kuma shi ne ya san ba ki da lafiya ya saka ƙafa ya tsallake ya bar ki?” Maman ta faɗa cikin muryar da ke bayyanar da mamaki da takaici.
Nu’aymah ta yi narai-narai da ido ta shiga yunƙurin kare shi, “Tafiyar ujila ce fa ta kama shi mama.”
“Shi kenan, Allah ya dawo mana da shi lafiya, ta shi ki tafi ɗakinku ki kwanta ki huta, ni ma nan kin same ni ina shirin in ɗan taɓa ƙailula.” Mama ta faɗa tana gyara kishingiɗarta don har a lokacin goman safe ba ta buga ba.
Ita ma sai ta miƙe ta je ta kwanta ta so ta samu yin ramakon baccin da ta rasa daren yau sai dai fargaba, tsoro da ciwon ciki duk sun hana mata sakat.
Haka ta ci gaba da birgima riƙe da ciki tana jin yadda yake murɗa mata kamar zai kar ta sai juye-juye take tana gunji ba kowa a ɗakin sai ita kaɗai.
Tana cikin wannan halin ne wayarta ta ɗau ɓurari, sai dai a yanayin da take ciki ba za ta ko iya ɗaukar wayar ba balle ta ga mai kiran.
A lokacin ne sautin ƙarar wayar ya janyo hankalin Amir autan mama da ya shigo gidan ba jimawa. Har zai wuce ya ji ƙarar wayar ya faɗa ɗakin da sauri don ganin wayar wa ke ƙara. Ganin halin da take ciki ya sanya shi yin tunanin ɗaukar wayar ya sanar da na kan layin. Don a iya tunaninsa mijinta ne yake kiran ta kuma a yadda ya same ta da alama ko magana ba za ta iya yi ba.
M.S ya gani a rubuce kafin ya ɗaga kiran ya tsinke, har zai ajiye wayar idanunsa ya kai kan saƙon da fiye da layi uku na cikinsa ya bayyana a kan fuskar wayar. Sai kawai ya ji yana sha’awar karantawa.
Nu’aymah da ke kwance cikin tsananin ciwo tana yunƙurin dakatar da shi daga zuciyarta amma harshenta ya yi nauyi wurin furta saƙon, ga shi ko motsawa daga inda ta ke ta kasa yi don haka ta dangana ta ci gaba da karanto addu’o’i a ranta tana fatar kar idonsa ya faɗa kan wani sirri nata.
Shi kuma Amir bai jira komai ba ya fara karanta saƙon kamar haka “Queen har yanzu fa ba ki cika alƙawarinki ba, kin ce zamu haɗu a otel amma shiru, kamar akwai abin da kike ɓoye mini amma…”
Iya nan rubutun da yake iya karantawar ya ƙare, ya yi turus yana ƙoƙarin nazartar kalaman da inda suka dosa. Duka-duka shekarunsa 14 ne amma yana da fahimtar cewa miji ba zai taɓa kiran matarsa zuwa otel ba da sunan za su haɗu can. Meye amfanin kwanan da suke a gida ɗaya kenan? A iya saninsa dai otel ba wurin mutanen arziƙi ba ne. Dalilin da ya sanya ya ɗago idanunsa ya zuba mata su, ya sake kallar fuskar wayar sannan ya maida idanunsa kanta.
“Waye M.S yaya? Me ya sa ya ce ku je otel?”