Skip to content
Part 6 of 6 in the Series Danyar Guba by Rukayya Ibrahim Lawal

Waɗannan tambayoyin ne a ransa yake son ya jefa mata su to amma ko kaɗan ba shi da ƙarfin gwuiwar yin hakan saboda haka ya ajiye mata wayar ya fice da hanzari zuwa ɗakin mama ya sanar da ita halin da Nu’ayman ke ciki.

A hanzarce maman ta shigo ɗaki tana ta sallallami, bayan ta gane wa idonta yanayin Nu’aymah sai ta fice zuwa ɗaya daga cikin sashunan gidan ta nemo kanwa da sauran itace da ake jiƙe-jiƙen gargajiya don maganin mirɗar ciki ta jiƙa ta ba wa Nu’aymah. Ba don Nu’aymar ta so ba ta karɓa ta shanye tas tana yamutsa fuska ba wai don tana don sha ba sai don ba ta da bakin yin musu da mama. Mama irin mutanan nan ce na da da suka yarda da gargajiya da canfi shi ya sa komai idan ba a gargajiyancen ba ba ta cika yarda da shi ba.

*****

A kwana huɗu da Nu’aymah ta yi a gida duk ta zabge ta rame, saboda jinya da take sha, haka nan gaba ɗaya a takure take don ba halin ta yi wayoyi da samarukanta ballatana kuma ta fice zuwa yawo, haka tana son zuwa makaranta amma ba ko sisi a jikinta, uwa uba kowanne motsi da za ta yi a gidan idanu na kanta hakan ya haifar mata zaƙuwa da son komawa gidan mijinta. Sai a sa’in ta yarda da azancin da ake cewa komai daɗin gidan uba gidan miji ya fi shi.

A ranar wuni na huɗun ne tana fama da tunanin mafita sai ga kiran Salis ya shigo wayarta.

Cikin zumuɗi ta ɗaga, bai tsaya gaisuwa ba a gaggauce ya ce “Ki shirya yanzu zan zo na ɗauko ki mu dawo gida.”

Har da ɗan ihun murnar ta kafin ta ce “To, yanzu ma kuwa, na yi kewarka da yawa Habibie.”

“Ni ma haka Habibtie, wuya ce ta ɓoye ni.”

Daga haka suka ci gaba da magana sai dai ba su wani jima kan layin ba ya katse wayar don ya ba ta dama ta kimtsa. Ko mintuna talatin ba a rufa ba sai ga sallamar shi a ƙofar sashin. Aka amsa ya shiga suka gaisa da mama sa’ar shi ɗaya bai tarar da baffa ba da ya sha tambayoyin da wataƙil da ƙyar ya iya amsa su. Tana ganin shi ta janyo akwatinta tare da yi musu sallama ta bi bayan shi suka fice.

Tun a hanya suka ɓalle da hirar yaushe gamo tana ta ba shi labarin damuwar rashin shi da ta shiga har suka isa gida. A daren ta titsiye shi da tambayar wanne laifi ya yi hukuma suka zo neman shi.

Nan da nan ya ɓata rai ya juya mata ƙeya daga kwancen da suke suna fuskantar juna. Ta miƙe zaune sannan ta yi ƙasa da murya sosai tana faɗar “Habibie ka yi haƙuri idan na ɓata maka rai, amma ka sani ba a ɓoye wa abokin cin mushe wuƙa, shekaru biyu kenan da muka fara sana’ar da muke kai amma ba wanda ya taɓa jin kanmu ko yasan sirrinmu, to ka sani wannan sirrin ma idan ka faɗan haka zai zauna kamar yacce matacce ke kwance a cikin ƙabari.”

Bai juyo ya kalle ta ba sai ajiyar zuciya mai ƙarfi da ya sauke kafin ya ce “Yan buge-bugen da muke kai ne aka samu damuwa kayan wasu ƙusoshin gwamnati ya faɗa hannun mai gidanmu aka samu matsala daga ɓangaren shi shi kenan?”

“Uhm! Na gamsu, amma ina son sanin a’ina ka ɓuya kwana biyar ba labarinka? Wane irin abu ne kuka je yi aka samu matsalar?” Sai da zuciyarsa ta yi tsalle har ya ji a ransa ko ta samu labarin mafakarsa, amma a haka ya daure ya fatattaki fargabar da ta ziyarce shi ya ce da ita “Wani masoyina ne na haƙiƙa ya suturta miki ni da ga masu farauta ta, godiya ya kamata ki yi masa ba wai ki tsaya tuhuma a kansa ba. Tambayarki ta biyu kuma ba ta samu gurbi ba a wurina, bana son ƙara jin ta.”

Tun daga nan ba ta sake cewa komai ba, ba wai don ta yarda da maganganunsa ba kawai ba ta son ta ja zancen da tsawo ne a ranta ta ce ‘Idan ta yi wari ma ji.’ ta juya ta gyara kwanciyarta.

*****

Washegari ta je ta ƙarbo motarta daga gareji ta mayar gida. Sati ɗaya ta ɓata ba ta je makaranta ba ga shi ana ta fama da test hakan ya saka Fatima ta dinga jero mata kira, sai dai ta kasa ɗagawa ta yi mata bayani, to me za ta ce ya riƙe ta? Ita dai ta san ba za ta iya faɗawa Fatima cewar tana da aure mijinta ne ya shiga matsala ba, don ba iya Fatima ba kaf abokanan hulɗar ta a makaranta ba wanda ya san da wannan ɓoyayyen sirrin.

Ranar litinin ta shirya ta koma makaranta a wannan ranar ne kuma aka fara jarabawa, sati biyu suka kwashe ana abu ɗaya, kasancewar a kan sanya musu interval na kwanaki don su samu damar yin karatu cikin nutsuwa. Sai dai ita Nu’aymah har a ranar da ba ta da exam fitowa take da sunan makaranta ta ɓige da kurɗe-kurɗen a gari.

Bayan kammala jarabawar sun samu sakamako mai kyau kamar yadda suke tsammani duk da sun san ba su yi wani abin a zo a gani ba, malami ɗaya ne ya yi disappointing ɗin su ta hanyar kayar da su course ɗinsa bayan sun ba shi abin da yake buƙata.

Nu’aymah da Fatima sun ji baƙin ciki sosai a ransu ba ma kamar Nu’aymah da sai maimaita karanta takardar ta ke kafin ta kalli Fatima ta ce ‘Lallai mutumin nan zan tabbatar masa da cewa bakin rijiya ba wurin wasar makaho ba ne, zai san ya yi kashi gonar fara don kuwa komai ta daɗe zan yi ramuwar gayya.’

Da wannan haushin ta fice daga makarantar ba ta nufi gida ba sai ta je gidan baƙin alhajin da ta yi wa alƙawarin za su haɗu a ranar. Don tun lokacin da ta samu damar fita karatu sai ta fake da shi ta ci gaba da aikata masha’arta har wadda mijinta bai san da ita ba. Idan ta je ta yi gaban kanta ba tare da sanin mijin nata ba a ranar duk abin da ta samu nata ne ita kaɗai don ba ta nuna masa. Fiye da rabin kuɗin kuwa takan ƙarar da su ne wurin sayen mayukan gyaran fata, sabulan gyaran jiki, ko kuma turaruka masu ƙamshi. Ba ta wasa da duk waɗannan shi ya sa take ƙara burge mazajen da take mu’amular soyayya da su a waje.

Bayan kammala jarabawar su ta shawarci mijinta da ya kai ta asibiti don kuwa ta tsorata da yanayin ciwon ciki da amai da ya ta’azzara gare ta har yana shafar sana’arta ta yawo, ga kuma ƙiba ta ban al’ajabi da ta ƙara yi cikin ƙankanin lokaci.

********

Ranar talata da misalin ƙarfe sha biyu na rana zaune suke a gaban likita kowannen su fuskarsa da alamun damuwa ba ma kamar ita Nu’ayman da take cike da fargabar yiwuwar jin mummunan labari, ba ta fatar likita ya ce tana da juna biyu ko kaɗan don ba ta shirya haihuwa nan kusa ba. Har ma ta fara tunanin idan inflanon shekara biyun ta kusa ƙare aiki za ta je a kuma sanya mata wata ko kuma a yi mata allura ba tare da sanin shi ba.

Ta yi nisa a cikin karatun wasikar jaki ta jiyo buɗaɗɗiyar muryar likitan yana faɗar “Ku yi haƙuri, amma kamar bayananku sun nuna matarka ta saka robar tsarin iyali wanda idan har haka ne to ina tabbatar maka da cewa effects ɗin da aka faɗa mata na robar ne suka fara bayyana a jikinta.”

“Da ma robar na da illa ne a jiki Likita.” Salis ya tambaya da yanayin mamaki a cikin muryarsa.

Likitan ya kalle shi sosai kafin ya ce “Akwai abubuwan da ka iya faruwa bayan saka ta wanda illa ne ga lafiyar ɗanAdam, kuma ina da yaƙinin ina dai a wannan asibitin aka muku aikin to ba za su saka mata ba har sai sun sanar da ita illolin.”

Salis ya maida duban shi zuwa gare ta ita kuma ta sunkuyar da kai ƙasa alamun rashin gaskiya, ganin hakan ya sake duban likitan yana ƙara yi wa damuwar da ke fuskarsa mazauni a saman ta. “Likita ko za ka taimaka ka sanar da ni illolin sannan da hanyoyin magance su?”

Ɗan lukuti farin matashin likitan ya sake satar kallon siririyar baƙar fuskar Salis kafin ya ajiye idanunsa kan tebur yana faɗar “Daga cikin matsalolin da ka iya faruwa bayan saka ta akwai; Ciwon baya, yawan amai, ciwon ciki, ciwon kai, ƙaruwar ƙiba ko raguwar ta a jikin macen, kumburin matantaka, raguwar sha’awa da rikicewar al’ada ko ɗaukewar ta gaba ɗaya. Wanda kuma faruwar wasu daga cikin illolin ne ya zo da ku asibiti yanzu.”

Ya ɗan tsagaita kafin ya sake cewa wani abu Salisu ya yi caraf ya ce “Ko akwai wasu hanyoyi da za a bi don magance wannan jinyar ba tare da cire robar ba?”

“Ba zan ce babu kai tsaye ba, sai dai a tunanina babbar mafitar ku ita ce a cire robar in dai ba wata ƙatuwar damuwa ba ce.”

Ganin yadda suka yi duru-duru suna kallon juna ya saka likitan ya fara bin su da kallon tuhuma kafin ya ce da Salis “Na ga duk kun shiga damuwa ko dai ita ɗin ba matarkan ba ce kamar yadda ku ka faɗa?”

Girgiza kai ya hau yi yana faɗar “Matata ce mana me ka gani ne?”

“Ba komai, amma kun taɓa haihuwa?” Nan ma girgiza masa kai Salis ya yi alamar a’a cike da ƙosawa da tambayoyin ƙwaƙwafin likitan.

“Kuma shi ne ka amince ta yi tsarin iyali tun ba ka bari kun ga yadda buwayi gagara misali ya tsaro muku rayuwa ba? Shin ba ka san hakan hatsari ne mai girma ba ga matar da ba ta taɓa haihuwa ba?”

Salis bai kuma ba shi amsa ba duk da kalamansa sun saka fargaba ta ziyarci zuciyarsa kuma sun sanyayar masa da jiki, amma sai ya kalli matarsa yana neman amincewar ta don cire wannan robar ko ta huta daga hatsarin da likitan yake yi mata fata.

Amma sam-sam Nu’aymah ta kasa amincewa da shawarar da likitan ya ba ta tun daga farko, ta fi gwammace ta rayu da matsalolin da take fuskanta a kan a cire robar ta samu cikin da ba ta da lokacin renon shi a yanzu. Cikin da take ganin samuwarsa da haife shi zai dakatar da ita daga rawar gaban hantsi kuma ya canza mata sifofi daga yadda take a yanzu don haka ta nuna ƙin amincewar ta ƙarara. Salis bai yi mata musu ba tunda jikinta ne ya ajiye a ranshi cewa ‘Ai jiki magayi, masara kuma idan ta gasu ita ke magana.’

Don haka a maimakon ya amsawa likitan tambayoyin nasa sai kawai ya yi masa sallama ya kwashi matarsa zuwa gida bayan sun biya pharmacy na cikin asibitin ya sayi magungunan da likitan ya rubuta musu.

********

Kwanci tashi asarar mai rai bayan shekaru biyu Nu’aymah ta kammala karatun diplomarta a ƙarshen shekarar 2019. Cikin sa’a takardunsu ba su ɗauki wani tsayin lokaci ba suka fito, har zuwa lokacin kuwa tana tare da Ma’aruf bayan ya yi duk iyakacin ƙoƙarinsa a kan ya ga ya aure ta tana turjewa sai kawai ya juya soyayyarsa a wani ɓangaren ya biye mata suka ci gaba da sheƙe ayarsu kamar yadda ta nuna ra’ayi. Shi ne ma ya nemo mata aiki a Unity FM/TV Jos kamar yadda ya alƙawarta mata, ta yi farinciki na ƙara samun wata dama.

Cikin sa’a kuma tana fara aikin muryarta ta karɓu sosai a wurin jama’a, kan ta rufa wata adadin masu bibiyar tashar sun ƙaru, dalili kenan da aka sakar mata ragamar jan wani shiri mai taken Ina Matsalar Take? Shiri ne da ake gabatar da wani topic kan wata matsala da ta shafi al’umma sai kuma a ba wa al’umma damar shiga shirin don faɗin ra’ayoyinsu.

Da motarta take zuwa wurin aikin duk da tsufan da motar ta yi. Ta damu da son canza motar saboda matsololin da take ba ta koma ba wannan ba ita ba ajin Honda Civic ba ce a tunaninta malejin rayuwa ne kawai ya sa ta fara hawan ta.

Wataranar Lahadi da misalin ƙarfe goma na safe da take gabatar da shirin ta na Ina Matsalar Take, a cikin jerin kiraye-kirayen da take karɓawa ne wani kira ya shigo ta layin maza. Cikin nutsuwa ta ɗaga kiran tana faɗar “Assalamu alaikum da wa nake magana, kuma daga ina?”

“Wa’alaikumus salam kina magana da Alhaji Sani Musa Jibiya, ina kiran ki ne kai tsaye daga nan anguwan rogo.”

“Madallah! Ina maka barka da shigowa wannan shirin, wace gudunmuwa za ka ba mu a kan wannan maudu’in na mace-macen aure da muke magana a kai? A ganin ka ina matsalar take? Daga matan ne ko kuwa mazajen?”

Sai dai mutumin da ke kan layi ya yi murmushi mai sauti kafin kamilalliyar muryarsa ta ratso cikin akwatin wayar “Da farko dai kafin na amsa ina mai farin cikin riskar wannan shirin ni masoyinki ne tun ranar farko, ina saurar shirin amma ban taɓa kama ku ba sai yau, kina da hikima da azanci…”

Ganin yana ƙoƙarin sauka daga kan tsarin shirin ya sa ta yi saurin ankarar da shi ta hanyar faɗar “Madallah ina godiya, yanzu dai mu je kan amsoshin kai tsaye saboda lokaci.”

Wani murmushin ya sake yi kafin ya shiga ba ta amsa a taƙaice

“Haka ne hajiya Nu’aymah, to a taƙaice dai abin da zan iya cewa kan mace-macen aure wasu lokutan laifin duka ɓangarori biyu ne tun da sanannen abu ne rashin haƙuri daga duka ɓangarori biyun kan taka muhimmiyar rawa wurin mutuwar aure, tun da a zahiri dai munduwa ɗaya ba ta amo dole sai ta samu abokiyar haɗi. Ina nufin idan mijin ya hayyayaƙo mata ta ƙyale dole dai shi ma ya haƙura don ba zai yi rigima shi kaɗai ba balle har a kai ga ɓacin ran da zai haddasa ambaton saki.”

“Masha Allah! Alhaji muna godiya da ra’ayinka.” Daga haka ta daƙile kiran duk da tana jin yana yunƙurij magana sai kawai ta ci gaba da gabatar da shirin ta tana amsar mabanbantan kira daga na maza zuwa na mata kafin daga bisani ta yi sallama da masu sauraron shirin ta miƙe tare da cire Earphone da ke kunnenta ta buɗe ƙofar studion ta fito tana sauke huci.

A lokacin Shamsiyya da Mu’azzam suka nufo ta suna faɗar “Well-done sis shiri ya yi kyau, kamar kin shekara a aikin.” Ta yi musu murmushi kafin ta ce wani abu muryar manaja ta ratso kunnuwanta “Nu’aymah ina son ganinki yanzu a office ɗina. Ba tare da ta amsa ba ta juya ta bi bayan shi a lokacin da yake shigewa, ya riga ta isa ofis ɗin don haka a kan kujerarsa ta same shi zaune, ya dube ta ido cikin ido. “Wani babban ɗan kasuwa ne a nan garin ya kira ni wai yana son yin magana da ke in ba laifi, to ban san ra’ayinki ba shi ya sa ban ce da shi komai ba amma fa mai kuɗi ne sosai.”

Wani irin nishaɗi ne ya mamaye zuciyar Nu’aymah a lokacin da ta ji wannan zancen ganin a tashin farko tarkonta ya kama babban tsuntsu. Ta muskuta tana yin murmushinta na ɗabi’a kafin ta ce “Badamuwa, kana iya kirawo shi.”

“A’a, ina ga wannan ba girmanmu ba ne, idan ya damu da kansa zai kirawo ko ya zo. Ta fi abin ki kawai.”

Ranta ya sosu ganin manaja yana neman ɓarar mata da damarta a irin wannan lokacin da take cikin tsananin buƙata. Lokaci ɗaya ta ji dattin da ya saka ruwa da omo ya wanke mata a farfajiyar zuciyarta ya sake yaɗuwa a ciki. Haka ta juya ranta ba ya mata daɗi ta bar ofishin tana ƙunƙuni da yan maganganu ƙasa-ƙasa “da ma muna da wani girma ne in ba kuɗi?”

Ranar a haka ta ƙarasa cinye lokacin aikinta ranta a jagule ta nufi gida.

Washe gari ta kama ranar Litinin ba ta da program ɗin safe don haka ba ta fita da wuri ba sai wuraren ƙarfe goma sha ɗaya ta gama caɓa adonta. Har za ta fita ta tuna sabuwar manhajar da Shamsiyya abokiyar aikinta ta tura mata, a lokacin ne ma’adanan sautinta suka yo mata tariyar maganganun Shamsiyya a sa’in da take tura matan.

“Kin ga wannan manhajar, tana da daɗin amfani kuma tana tafiya da zamani, cikin sauƙi za ki yi vedionki mai kyau ki yi editing idan kin so ki fitar wa jama’a su gani idan kin so ki yi saving abinki iya ke kaɗai. Amma fa ta hanyar sakin vedion ne za ki yi saurin samun mabiya kuma ki zama celebrity cikin ƙanƙanin lokaci.”

Murmushi ne ya suɓuce mata bayan ta tuno wannan sai kawai ta janyo wayarta ta shiga manhajar sannan ta bi duk hanyoyin da Shamsiyyar ta nuna mata, ta jingine wayar a jikin wundon ɗakinta bayan ta yaye labulen da ya yi wa windown sutura. Ta lalibo waƙar Hausa ta soyayya mai ɗan karen daɗi ta saka sannan ta fara karkaɗa jiki a hankali tana mamin waƙar tare da yin fari da ido.

Bayan ta gama rera baiti ɗaya ta ɗauko wayar ta dakatar da bidiyon tare da zama gefen gadonta tana kallon bidiyon da bai fi sakanni talatin ba. Filtar ta hau sosai a jikinta ta ƙara mata hasken fata da sulɓi kamar ba ita ba. Sai ƙara kallon bidiyon take yi tana ganin yadda ramar da ta ɗan yi ta ƙara mayar da ita tamkar budurwa mai ƙananun shekaru, idan har ka gan ta a bidiyon za ka rantse ‘yar shekaru 16 ce kasancewar har a lokacin ba ta yarda ta haihu ba. ‘Na fa yi dabara da na koma asibiti a sace na yo allurar nan, yo hauka nake ina kan ganiyar ƙuruciyata na yarda haihuwa ta tsofar da ni ban cika buruka ba?’ ta faɗa a ranta tana sakin wani shu’umin murmushin da yanayin zuciyarta ya harbo zuwa saman fuskarta.

Tana gama maimaita kallon cikin nishaɗi ta danna inda aka nuna mata ta yi post na ɗaukar inda aka ce idan ta saka mutane za su gani. Sa’annan ta miƙe ta saɓa mayafinta kalar pink da ya saje da adon yadin da ke jikinta ta fito tare da kullo ƙofar falon ta ɗauki motarta ta fice da ita waje kana ta fito ta rufe gate ɗin duk da ta ga babur ɗin Salis a ciki alamar ba nisa zai yi ba, amma hakan ba zai saka ta bar gidanta a buɗe ba don bahaushe na cewa kula da kaya ya fi ban cigiya.

Isar ta wurin aikin kedawuya ta je ofis ɗin manaja wanda ta je ne da manufar tunatar da shi zancen jiya amma ta fake da gaishe shi sai ta tarar da baƙo hakimce a kujerar baƙi. Ba ta damu da hakan ba ta kwashi gaisuwa gun ogan nata da ma baƙon shi sai ta juya za ta fita tana kwarkwasa a fakaice.

“Nu’aymah!” Sautin manaja ya ratso masarrafar jinta.

Ta ci birki tare da juyowa lokaci ɗaya tana furta “Na’am Oga!”

“Dawo ki zauna wannan baƙonki ne ai, shi ne wanda ya kirawo waya jiya.” Yana gama faɗa ya ɗauke makullin motarsa da wayarsa ya saka a aljihu ya fara tafiya yana faɗar “Zan je na duba wani abu a sashen masu gudanar da wasar kwaikwayo, idan kin fito ki rufe mini office ɗin.”

Wani irin daɗi ta ji yana ratsa tsakiyar zuciya da har saura ƙiris ta fito da maitarta a fili amma sai ta kanne ta matsa wurin kujerar da ke fuskantar shi ta zauna suka yi ‘yar gajeruwar tattaunawa da alhaji Sani Jibiya ya sanar da ita shi ne ya shigo cikin shirinta jiya, kuma yau ma ya zo a kan manufar da yake kai ne. Ba musu ta ba shi lambarta ya adana sannan ya fita da alƙawarin za su dinga gaisawa kafin ya zo gida.

A wannan ranar ne kuma kafin ta tashi daga aiki mummunan labari mai firgitarwa ya zo kunnensu. A lokacin ta razana sosai ba, ma iya ita kaɗai ba har abokanan aikinta maza da matan, saboda haka da wurwuri ta kammala abin da za ta yi ta koma gida jiki a saɓule kamar kazar da aka watsawa ruwan zafi.

Wuraren ƙarfe 6:30 na yamma ta isa gidan a matuƙar sanyaye. Tun daga yanayin sallamar ta Salis ya ji a ransa cewar ba lafiya ba don haka ya ɗago idanunsa daga kan tv ya zuba mata su a lokacin da take shigowa falon.

“Me ya faru ne yau Habibtie? Na gan ki a dame.”

Ba ta tamka ba ta ƙaraso kan kujerar da yake zaune ta zauna a gajiye tare da ajiye jakar hannunta tana ƙara narkar da murya kamar za ta yi kuka ta ce “Wani labari ne mai matuƙar firgitarwa ya same mu yau a wurin aiki.”

Wane irin labari ne haka?” Ya tambaye ta da yanayin damuwa.

“Wallahi kai dai mummunar cutar nan ta mashaƙo da muke jin labarin ta a ƙasashen ƙetare ne ta hauro ƙasarmu. Zancen da ake ma yanzu cutar ta ɓulla a Legos ta zo Kano ma, akwai yiwuwar za ta iya haurowa nan ma saboda ɗauka ake.”

Ta ƙarasa zancen fuskarta na bayyanar da matsananciyar damuwa kamar za ta fashe da kuka.

Kafin ma ya ce wani abu tashar da yake kallo ta NTA sun fara haska labarin wasu mutane biyu da aka killa ce a birnin Legas bisa zargin sun kamu da cutar ta mashaƙo. Don haka shi ma yanayin sanyin jiki ya dirar masa ganin yadda aka ƙebance mutanen ba mai raɓar su. Ya ɗora hannu a gaban goshi yana faɗar

“Allah ya yi mana maganin wannan musibar, duk da ni na fi tunanin kawai an ƙirƙiri cutar ne don a saka mutane a ƙunci amma babu ita.”

Ya sake kallon farin matashin da yake gabatar da labarun sannan ya kalli ƙasan screen inda aka rubuta sunan ma’aikacin. Kafin ma ya ɗago sautin kyakkyawan matashin ya ratso kunnensa inda yake faɗar “Duka-duka iyakacin labaran namu kenan sunana Abba Abubakar Yakubu nake cewa….”

Bai jira ya ƙarasa jin abin da zai faɗa ba ya sauya tashar da yake kalla ta hanyar yin amfani da masarrafin tvn da ke hannunsa ya koma Arewa24 yana taɓe baki da faɗar “Kan su ake ji, bari na dawo wannan tashar kada su yi nasarar zurma ni na yarda da ƙirƙirarren labarin nasu.”

Ita kuma Nu’aymah sai ta miƙe tare da nufar hanyar ciki mayafinta a hannu tana faɗar “Bari na watsa ruwa na huta kafin magariba, na ɗebo gajiya wallahi.”

Bayan ta watsa ruwa ta fito ta kwanta kan gadonta da nufin hutawa sai ta tuno bidiyon da ta saki a kafar sada zumunta ta TikTok. Ta janyo wayarta tare da hawa shafin nata don ta ga ko ya samu karɓuwa. Ga mamakinta sai ta ga a cikin awanni shida da ‘yan mintuna da ta yi da ɗorawa har ta samu makallata ɗari shida da motsi, da kuma sharhi guda goma.

Da ƙyar ta yi nasarar gano yadda za ta buɗe sharhin, ta shiga ciki ta fara karantawa kamar haka.

“An samu sabuwa kenan.” Ta tsallake saƙon farko ta je kan na biyu inda shi kuma namiji ne ke cewar “Wow! Ka ga wata kyakkyawar zinariya.” Ya saka alamun shauƙi kafin ya ɗora rubutunsa da “Ina yinki, wannan ba za ki jima ba tauraruwarki za ta haska a wannan kafar.”

Tana karanta saƙon farinciki na ziyartar zuciyarta koda ta gama karantawa tsabar murna ba ta san lokacin da ta wuntsilo daga kan gadon ba tana faɗar “Yes!” da ƙarfi. Abin da ya janyo hankalin Salis kenan ya yi saurin cewa “Mene ne? Me ya faru kike ihu ke kaɗai, an yi mana wani babban kamun ne?”

Duk wannan tambayoyin a jere ya yi su cike da zaƙuwa da son jin amsar su.

<< Danyar Guba 5

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×