Wani abu mai ɗaure kai shi ne, tunda Inna ta fara warkewa sau ɗaya ta tambaye shi ina ne nan, ina goggonta da wasu daga jama’arta ya gagara amsa mata sai sannu da ya mata ya tashi ya fita ƙirjinsa na bugu bata ƙara yi masa ba, har suka gama zaman jinya suka dawo gidan da aka bashi bata sake maganar garinsu ba, sai ma da taga gidan ne ta dinga shiwa Alhaji Hashim albarka, da ke a tahowawarsu ya mata bayanin shi ya kadesu a mota sanda ɗanta zai kai ta asibiti, ganin ba su da hali. . .