"Aure Asma'u zata yi?" cikin tsananin tashin hankali ya jefo ma kansa tambayar da ba mai amsa mashi ita. Take duk wata tsika ta jikinsa tashi, wani irin sanyi ne ya shiga ratsa shi har ya tsinke da karkarwa, kan ka ce me haƙoransa sun fara gugar juna, kamar wanda aka watsa ma kwanannen ruwa da asubahin lokacin hunturu.
Wayar kuwa bai san lokacin da ta ɓille kan katifa ba, lokaci ɗaya kuma tana ta ratsa status ɗin mutane ba tare da saninsa ba. A hankali ya lumshe idanunsa da suka ciko da ƙwalla, hannayensa rungume da ƙirji. . .
Allah ya kara basira aunty Hadiza Asmau ta debo ruwan dafa kanta