ƘAUNAR KI
Sallama nake yi miki,
Saboda martabar ki.
Gaisuwa nake yi miki,
Saboda darajar ki.
Son gaskiya nake yi miki,
Saboda kamalarki.
Zuciya mararin ki take yi,
Saboda girman kyawunki.
Idanuwa begenki suke yi,
Saboda hasken zatinki.
Rayuwata buƙatar ki take yi,
Saboda ke ce ɗaya ɓarinta.
Da zarar na ji ƙamshin ki,
Tsuntsaye ke tashi a zuciya.
Da zarar na hango ki,
Furanni so ke ƙamshi a rayuwa.
Da zarar na ji muryarki,
Sauti ne ke tashi a kunnuwa.
Na zamo wani shashasha,
Saboda yawan tunanin ki.
Na bar duk wani aikin ashsha,
Saboda ƙarfin tarbiyyar ki.
Ki taimaka min da ruwan so,
Ko zan samu albarkarki.
Na riga na yi imani,
Da kyawun niyyar ki.
Komai tsawo na zamani,
Ki sani ba ni gudunki.
Ko da cikin aljanna ta,
Na fi son ga ni ga ki.
Ni son ki ɗai na sa a ƙalbi,
Ƙaunar ki taimaka ki bani.
In babu ke ki san fa ba ni,
Duk inda ki ke za’a ganni.
fatan alkairi
Muna godiya sosai.