Skip to content
Part 17 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Wai meke damunka ne? Sai wani zabura kake yi kai ɗaya kamar wanda aka yiwa allurar taɓin hankali. Da ace asibitin mahaukata kake da sai ince garin ka yiwa wani ne ya kwace ya tsiramaka.” Ta ƙarashe tana dariya.

Ya ji ciwon kalamanta sai dai bai da ikon nunawa. Ya girgiza kai.

“Salma da ace kin san tashin hankalin da nake ciki da ba ki wannan zolayar ba. Mun kashe maciji ne ba mu sare kansa ba.”

Duk farin cikin da take na murnar sun kashe case ne da Halima, a gefe guda ga Fu’ad  da ya zo mata da abin mamaki, zai soma aiki a kamfaninsa. Wannan kadai ya sanyata nishaɗi, maganar da ta fito daga bakin Hayat ya sanya ta fara’arta ta ragu.

“Me kake so ka cemin?”

Son da yake mata ne ya sa ba ya iya ɓoye dukkan damuwarsa gareta. Tiryan-tiryan ya labarta mata yanda suka yi da Halima sai dai a masifar tsorace yake. Ai kuwa bai kai aya ba ta lailayo ashar ta dankarawa Halimar. 

“Ni Halima za ta zo ɓullowa ta nan? Toh wallahi na ta isa ba, ni Salma murucin kan dutse ce ban fito ba sai da na shirya. Zan nunamata karan bana shi ke maganin zomon bana. Yar jakar uba!” Tana kaiwa nan ta mike a fusace ta fisgo wayarta daga chaji. Hannunta har rawa yake ta shiga laluben lambar Halima har tana mancewa ba ta da shi, Hayat ne mai ita. Hannu ya sa ya fisge wayar. 

“Ki bi komai a sannu mana Salma! Kada ki tafka kuskuren da daga ni har ke zamu yi dana saninsa!”

Tun da ya warce take kallonsa da jajayen idanunta wadanda kishi ya rinar. Ba ta san gejin son da take yiwa Hayat yakai har haka ba sai da Halima ta tayarmata da tsohon tsimi. 

“Na bi komai a sannu da ka ce? Namiji munafiki!!” 

Ta fadi ranta a ɓace, gaba daya ta haukace masa.

“Dama na sani! Sonta kake yi! Na ga kallon da kake mata sadda ta zo! To Ni ce daidai da Halima! Hayat ka bani wayata kafin na yi maka illah!”

Fadin Salma da jikinta har wani rawa yake. Ya ga dai ba zai iya shawo kanta ba, kishi ya rufemata ido. A hangensa komai ma za ta iya aikatawa. Don haka ya samawa kanshi lafiya ya miƙamata. Ta warce har tana haɗawa da yatsunsa.  Iya lalubenta ba ta samu lambar Halima ba, sai a sannan ta gane ba ta da shi. Da azama ta dauko wayar Hayat ta dauka. Sau uku ya yi ƙara, ana hudun sai muryar Halima.

“Hello.” 

Ta soma da kunduma mata ashariya kafin ta ɗora da fadin.

“Halima karyarki! Nace karyarki wallahi domin Hayat nan gani nan bari. Ki sani kashin turmi bana wadan kare bane! Ni Salma murucin kan dutse ce ban fito ba sai da na shirya don haka ki gaggauta watsi da kudirinki na auren mijina. Kamar yanda kika ce sai dai ayi mutuwar kasko! To kuwa za’a yi shi yanzun, a shirye nake!”

Dariya sosai Halima ta sheƙe da shi.

“Um um Salma! Um um! Ina gargadinki da ki bini a sannu. Wutsiyar raƙumi fa ta yi nesa da ƙasa.  Ba ki sanni ba, labarina kike ji kawai don haka ki kiyayeni! Idan kuwa kin shirya fito na fito da ni, to shege ka fasa don uwatai!”

“Aikin banza da wofi, burgar banza kawai! Me za ki yi Halima? Ba abinda za ki iya! Sai kurin banza da wofi.”

“Dakyau! Mu zuba! A ga tukunyar wanda zai tafasa.”

Daga haka Halima ta katse kiran, Salma ta yi jifa da wayar da sauri Hayat ya cafe. Ranar ko haɗa ɗaki basu yi ba don sosai ta shaƙa da lamarin Hayat. Karshe ma cire sim din wayoyinsa ta yi da sunan za ta sauya mishi. Kamar ya ce ai tasan hanyar gidan sai dai ya kama baki don ba ya son tsokano abinda ya fi karfinsa. 

*****

“Nan ne gidan Hajiya.” Fadin Halima cike da ladabi tana mai kallon wata dattijuwar mata. Matar tana mai jinjina kai tana bin gidan da kallo, can kuwa ta yi dan murmushi gami da yiwa Halima godiya. 

“Muje Nura.” Fadin Hajiyar tana kallon ɗanta mai shekaru ashirin da takwas a duniya. Har Halima ta yi gaba sai ta tuno da shaiɗanin Maigadin nan Joshua, dawo ta yi ta soma kwankwasawa. Koda aka bude yana ganinta ya narkamata harara. Wannan karon bai hanasu shiga ba don haka kawai ya ji dattijuwar matar ta mishi kwarjini don har gaisheta ya yi. Da hannu Halima ta yi musu nunin inda zasu je sannan ta fito tana dariyar cin galaba a karo na farko. Motarta ta shige ta bata wuta ta yi gaba cike da nishadi. 

Bubbuga mishi ƙafa take akan ya tashi ya shirya ya tafi wurin aikin sai dai ko motsi bai yi ba. Tsaki Fu’ad ya ja. 

“Please Mum, ba yanzu ba.”

Murmushi Salma ta yi. 

“Karfe goma ce za ta yi Son.” Jin haka ya bude ido gami da saurin miƙewa yana fadin.

“Oh Shit!” Tana dariya ta fita daga dakin ta ja mishi ƙofa. Agogon dake daure a fatar hannunta ta kalla, direbanta da ya je shan mai take jira, yau kam gidansu za ta wuni. Ba kasafai ta fiye son zuwa gidan iyayennata ba saboda suna rayuwa ne a kuntace babu wani wadataccen fili  na shan iska a gidan. Kamar akurkin kaji. A cewarta. Yanzun ma dole ta sanya don tana son ganin mamarta. Case din Halima babba ne, karfe ɗaya ba ya amo don haka ya zame mata dole neman abokin shawara. Ta san tsoffin hannu za su fi sanin makaman yaƙi. 

Sai da ta fito falon sosai sannan ta tsinkayi sallamar mutanen da ke tsaye a falon. Ta ɗago kai ta kallesu, sun juyamata baya, a tsaye suke suna bin ko’ina na falon da kallo, daga shigar da suka yi kadai sun ishi bawa sanin ba kananan mutane bane. Wata mai aikinta mai guntun siket ta fito, gaishesu ta yi kasancewar tana jin Hausa, ta basu umarnin zama domin ta kira Hajiyar. Juyowar da zasu yi su zauna ta ji kamar an tsayar da gudun numfashinta gaba ɗaya. 

Kafin ta yi wani yunkurin har sun ganta, Nura ya ware ido yana karemata kallo. Hajiyar ma kallon mamaki take. 

“Sannu Salma kin ji!” 

Ta shanye mamaki da fargabarta, ta daure fuska. 

“Hajiya kune a gidan?”

Harararta Hajiyar ta yi. 

“Kya ce haka mana Salma, kin samu arzikin ɗana kin kunshe kina juyashi son ranki. To madallah, kin kyauta sai dai ki sani ni ba wannan ne ya kawo ni ba. Allah Ya yiwa Haisam rahama. Ya gafartamasa. Ina jikana?”

Salma ta ji kamar ta watsamata garwashin wuta a kirji, dama ba wani ɗasawa suke sosai ba da ita tun a baya ta cika masifa da sa ido a lamuran rayuwar surukanta. Itama ta san albarkacin kaza ne ta ke shan ruwan kasko. Ba ta son ta yi mata rashin mutunci, ba ta kuma kaunar Fu’ad ya fito ya riskesu don haka ta kwantar da kai.

“Ki yi hakuri Hajiya abin bai kai ga haka ba, Fu’ad bai dawo daga karatu ba yana can UK, Jami’ar Cambridge amman in Sha Allah yana dawowa ni Salma da kaina zan kawoshi har inda kike ku gaisa. Ki yi hakuri.”

“Um, naji wannan.”

Ganin ba ta yarda ba ne ta shiga kalallameta, dakyar Hajiya ta mike ta fita Nura na bin bayanta. Sai da suka tafi sannan Salma ta fita wurin Joshua. Umarni ta ba shi da babbar murya akan kada ya kuskura ya bar su su kara tako tsakar gidanta. Hakuri ya bata.

“Su na tare da wannan mata ta rannan. Mai yanka a fuska.”

Da mamaki ta ce.

“Wa kake nufi? Halima?”

“Yes, na Alima.”

Ta ji gabanta ya faɗi ta yi azamar shigewa cikin gida. Wayarta ta dauka hannu na rawa ta faɗa ɗakinta gami da sa mukulli. Kai tsaye ta kira Halima, koda ta dauka dariya ta sanya. 

“Ya akai manyan gari?”

“Halima ki fita sabgata! Tun kafin mu sa kafar wando daya da ke! Halima ki fita a idona!”

Wata dariya Halima ta kyakyata. 

“Me kike ci na baka na zuba Salma? Ai kya jira na fasa musu kwan. Kya jira har na sanar musu cewa FU’AD ba ɗan HAISAM bane. Saurin me kike? Yo me akai ma da maza?”

Maganar da ta yi sai da ta sanya Salma cire wayar a kunnenta gami da bin ko’ina na dakin da kallo don gani take kamar wani ya ji furucin Halima. Wani fitsari ta ji ya cika mararta har yana kokarin suɓuto mata. Muryarta har rawa yake ta ce.

“Aa, kar ki min haka. Ki rufamin asiri don Allah. Halima me kike so? Mene bamu ba ki ba?”

“Auren Hayat nake so. Ke kuwa kina nema ki zamemin ciwon ido. Kina neman hana ni rawar gaban hantsi kinga kuwa dole ne na nemawa kaina mafita komai ta fanjama fanjama! Kin san wacce za ta kwan a ciki.”

Ta shiga girgiza kai, tuni ta soma fidda hawayen da ba ta shirya mishi ba. 

“Kar kimin haka, ki yi hakuri. Ki bani nan da sati zan duba yiwuwar abinda kika buƙata. Kar kimin haka.”

Wani shu’umin murmushi mai sauti ya suɓucewa Halima.

“Shikenan, zan ba ki. Sai dai kar ki gaggawar yanke hukuncin da zai zame maki haɗari. Ni dama a ƙone nake bana tsoron wuta. Ki kiyaye kada ki yanke abinda zai kai ku ya baro.”

Daga nan ta katse kiran. A guje ta faɗa banɗaki ta yi fitsari ta fito tana haki kamar wacce ta yi gudu. Idan asirinta ya tonu ai ta gama yawo. Fu’ad kam ba zai ta6a yafemata ba, tasan da wannan.

Ƙwanƙwasa mata yake yana kiran sunanta, da saurinta ta share ruwan hawayen, ta saita nutsuwarta kafin ta bude. 

*****

“Yaya oyoyo!” Gaba daya yaran ke fadi suna duban Adam, Jidda ya ɗaga sama cak yana juyi da ita. Umma da Anti Khalisat na kallonsu suna murmushi. 

Har ya soma tafiya ya juyo.

“Humaira, kina ina ne?”

Jin ya ambaci Humaira tuni Amira ta karaso don ganin ta inda za ta fito. Ita kuwa Humaira girma da kyawun gidan ne ya bata tsoro. Ta karaso ciki da sanyin jiki. Umma ta kuramata idanu tana kokarin tuna inda ta san fuskar. Har sai da Humaira ta karaso falon sosai. Gaba daya kamar fuskarsa aka dasa a saman na Humaira haka ta gani. Shakka babu, shekaru kusan goma sha shida da suka wuce. Fuskar mutumin ne. Ba ta mance tsantsar damuwa da tashin hankalin da ta gani a kwayar idanunsa ba a wancan lokacin. 

“HAISAM.” Ta furta a fili sakamakon sunansa da ta tuno. 

“Waye hakan?” Fadin Anti Khalisat da ke kusa da ita. Hankalin Adam da Anti Khalisat ya yi kanta.

<< Rumfar Kara 16Rumfar Kara 18 >>

1 thought on “Rumfar Kara 17”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×