Washegari kuma ta samu baƙuncin manyan ƙawayenta su uku da kuma yarinyar Auntynta.Ganin Bilkisu suka yi ta faɗin albarkacin bakinsu kan kishi da wannan sai ka yi da gaske.
Hakan ya tayar da hankalinta ya dagula mata nutsuwa Google ta garzaya don neman mafita da za ta sama wa kanta hips da manyan breast.
Kwana biyu tsakani Safwan ya nemi takardun da ya ajiye suka ce ɗauke mu inda ka ajiye, ya tambaye ni ya tambayi Aunty Farha kowacce ta ce ba ta gani ba.
Ko da ba a faye gane bacin ransa dukkan mu mun gane. . .