Skip to content
Part 52 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Washegari kuma ta samu baƙuncin manyan ƙawayenta su uku da kuma yarinyar Auntynta.
Ganin Bilkisu suka yi ta faɗin albarkacin bakinsu kan kishi da wannan sai ka yi da gaske.

Hakan ya tayar da hankalinta ya dagula mata nutsuwa Google ta garzaya don neman mafita da za ta sama wa kanta hips da manyan breast.

Kwana biyu tsakani Safwan ya nemi takardun da ya ajiye suka ce ɗauke mu inda ka ajiye, ya tambaye ni ya tambayi Aunty Farha kowacce ta ce ba ta gani ba.

Ko da ba a faye gane bacin ransa dukkan mu mun gane ransa ya yi mummunan ɓaci.
Na taya shi birkita duk inda yake tunanin zai gan su babu su babu dalilin su.

Ba su aiwatar da shirin su kan Bilkisu ba sai ranar da ta kama aikin Farha da suka san Bilkisu ba ta cika fitowa don kanta ba in ka gan ta Safwan ya kira ta.

Sun fara cin abinci hajjo ta fito ta doso su sai kuma ta tsaya turus! Za ta juya Farha ta ce “Mene ne? Ta ce “Dama takardun nan Haj ta manta a kitchen tun rannan, shi ne na adana mata yanzu na buɗe inda na ajiye sai na gan su shi ne na kawo mata na ga kuma ba ta kai ga fitowa ba.

Farha ta miƙa hannu ta miƙa mata ta juya da sauri ita kuma ta shiga dubawa kafin ta ɗago “Dear ba sune kuwa kake nema ba?

Ya dubi hannunta sai ya karba mamaki ya kama shi Bilkisu ya ji an ce ta ɗauka to me za ta yi da su? Yi ya yi kamar abin bai dame shi ba bai kuma ba Farha fuskar da za ta yi wata magana ba.

Ya gama cin abincinsa ya tashi kamar ya shiga wurin bilkisun sai kuma ya fasa.

Da safe ya shigo kwance ya same ni sai da na tashi na gaishe shi ya tambaye ni game da takardun nan ganin kamar ma ban gane ba sai ya ce min ya gan su.

Da mamaki na ce a ina ya gan su ? Kallona kawai ya yi na san ba zai faɗi ba sai na ci-gaba da zancen tafiyata suna.

Ya ce ya fasa na yi ta roko da magiya sai da ya miƙe har ya kai ƙofa ya ce “Ki shirya zuwa anjima mu fita ki yi wa maijegon da baby Shopping, har ma da sauran jama’a na gidan Baba.”

Na yi ta murna bayan fitar shi.

Fitowar shi Farha da Hajjo da ke jiran ko za su ji wani abu suka kauce kamar ba tare suke ba.
Ya shiga wurin shi ta bi bayan shi ganin ba wata alama a tare da shi ta shiga saƙawa da kwancewa

Ba su ƙara shan mamaki ba sai ƙarfe uku da ya dawo gida maimakon shiri ya fita wurin wasannin shi a’a shiri ya yi cikin wani ubansun yadi da hula da agogo da takalmi duk ba na kananan kuɗaɗe ba ya yi kyau ya haɗu karshe ya yi mata sallama ya shiga wurin Bilkisu.

Ya same ni ina kwalliya ganin shi na janyo tawul na rufe ƙaton cikina da ke waje sai ya yi kamar bai ga me na yi ba ya ce “Ba ki shirya ba ? Na ce “Sallah na yi.

Na mike na isa ma’ajiyar kayana wata riga na dauko da na riga na ciro riga ce me daraja da ka gan ta ka san me tsada ce na makala ɗankunne da zobuna guda biyu na sanya agogo.

Sai da na gama muka fita

Mun jera zuwa inda motarsa take motar Farha ta shigo gidan, mun shiga har ya tayar ta iso “Dear sai ina? Zan kai Mami ta yi ma mai jego shopping.

Ta dube ni “Sai kun dawo Nana.”
Na ce “To aunty Farha.
Ya ja muka bar gidan.

Wani kasaitaccen wuri ya kai ni ya kuma ba ni iznin in dauki abin da nake so, don haka sayayya ba ta wasa ba na yi wa Zainab da yaronta.

Na sai ma Amir kaya kala- kala wata keke da ta burge ni duk da na tura kudin a saya mishi sai da na ji ina sha’awar daukar mishi ita.

Ya dube ni ganin ta cikin kayan “Wa kika sai wa keke?

Na ce “Amir.”

Waye Amir? Ƙasa na yi da kai na kuma ƙi magana ya ce “Shi kenan, ko shi ne kike waya yana so a kawo shi ya ga mahaifiyarsa?
Harshe na fiddo sai na rufe ido “Za su ba mu shi idan kanensa ko ƙanwarsa suka iso?
Na yi mamaki wato ya san labarin Amir kenan? Na ce “Ban sani ba.

Ya ce “Ya kamata su ba mu shi.”

Nan ma shirun na yi, muka gama ya je ya biya ta hanyar ba su ATM suka cire kudinsu muka fita aka biyo mu da kayan.

Muna tafiya maimakon gida gidan Farha ya wuce ya shiga da motar har ciki bayan maigadi ya wangale mishi get.

Fita ya yi ya je ya samu mai gadin da ya garzayo ganin tsayawar motar, ni kuma ina ta kallon aikin da aka ɓaro ma gidan, wanda da gani an kwana biyu ba a yi ba na girgiza kai lallai Aunty Farha da sauran zama.

Sai da ya gama faɗin abin da zai gaya mishi ya zo muka tafi.

Ana gobe zan tafi na je wa Mami sallama ban wani zauna ba na dawo don su Hafsah da ke ta min waya za su shigo mu yi sallama, ban kuma san tafiyar da ya Safwan za mu yi ta ba sai a lokacin da na ji suna maganar Mami.

Ina komawa suka shigo muka sha hirar mu har da rigunan su in kai wa baby.

Suna tafiya Farha ta kira Hajjo tana tambayarta me ta dauko a hirar ta su? Hajjo ta shiga kame-kame karshe ta ce ai shekaranjiya ta je wajen Isya hira wayar ta fadi. Ta dube ta a lalace “Isyan kenan ya ɗauke miki?

Ta shiga girgiza kai ya yi dai baki ne shiru ta yi mata Hajjo ta juya ɗaki tana tuna yadda suka yi da Isya, ya tabbatar mata waya ya aika wa matarsa a gida mero da ke so tuni ya saya mata waya mai shafa-shafa.

Ba yadda ta iya dole ta hakura.

Tun dare na yi ma Aunty Farha sallama don na san da safe tana wannan barcin na ta ba za mu ga juna ba.

Na sallami Hajjo muka kama hanya.
Da yake mun fita da wuri karfe goma motarmu ta shiga gidan Baba.

Yana gyara parking na hango Maman Ahmad ta fito sai sannu da zuwa take mana ta ce za ta kai yarinya asibiti, ni sai sannan na tuna Zainab ta faɗa min ta dawo.

Baba ya fito muka bi bayan shi muka shiga falon shi ina gaishe shi na tashi na bar ya Safwan na shiga ciki.

Sasan Mama yanzu daga ita sai Ihsan da Asma’u, da gudu suka taho suna min Oyoyo! Mama na ta masu faɗa kar su bige ni, na zauna ina gaishe ta tana tambayar su Mami, Ihsan ta kawo min kunun gyaɗa ina cikin sha Baba ya shigo da ya Safwan sai dai daga kofa ya tsaya ya Safwan ya shigo Baba na fadin “Ga ɗan ki nan da bai son zumunci yau yar ki ta kawo miki.”

Ta ce “Lallai kam tana murmushi ya Safwan dai da surukuta sosai yake nunawa sai sunkuyar da kai yake.

Baba ya juya ya Safwan ya shiga gaishe da Mama su Ihsan suka gaishe shi Mama ta ce su raka ni in shiga in huta da ta ji ya Safwan ya ce zai je ya ga wani abokinsa na ce ni dai a kai ni gidan Zainab, baki Mama ta rike “Daga zuwa ba ki huta ba ba ki ci abinci ba? Na ce To.” Nan muka zauna har aka kawo abinci muka ci, na bayar da tsarabar da na yi ma kowa.

Muka fita zuwa gidan Zainab ni da Ihsan da Asma’u.

A can muka samu Khadija da Rabi’ah.

Har dare ina gidan Zainab don anan na yi niyyar kwana sai ga ya Sadauki Najib ya fita ya shigo da shi tare yake da abokinsa da ya je wajen shi. Abokin nasa yana cikin waɗanda suka taɓa kai ma shi ziyara ina gidan Aunty Farha, har ya ce idan ya Safwan bai ciki shi yana so na.

Da za su tafi ya ce Baba fa ya kira mu taho an gyara mana wurin Najib da aka mayar wurin saukar baƙi.

Na jinjina kai “In kwana tare da kai a gidan Baba, ba zan iya ba.”

Ya ce “To ki biyo ni mu je gidan abokina.”
Na ce “Ka yi haƙuri ka bar ni in kwana da Zainab.

Miƙewa kawai ya yi na yi mishi rakiya inda ya ajiye motar, abokin nasa na jikin motar ya ce yaushe zan je ma Madam ɗinsa? Na ce sai mun gama suna.

Muka rabu akan gobe za su tafi Kano shi da abokin na shi Dr Auwal.

Washegari yaro ya amsa sunan Muhammad mun sha shagalin suna har dare anan na ƙara kwana gari na wayewa kuma na tafi gidan Baba don ban gaisa da baban ba na same shi yana karyawa muka zauna mun kusa awa na shiga ciki wurin Mama duk da ranar nake so in je in ga Amir gobe kuma mu tafi gida ɗakinmu na da na shiga na hau gado na shiga barci.

Sama sama na ji muryar Asma’u na tashi na ban tashin ba har sai da Mama ta zo da kanta Bilkisu Bilkisu. Na ji tana kiran sunana a hankali, na tashi zaune ina muttsuke ido, cikin murmushi da ba ka rabs fuskarta da shi ta ce “Duk gajiyar sunan ce Bilkisu? Na yi mata murmushi “To ki sauko tun ɗazu Safwan ya zo.”

Na ce “To.” Ta fita na miƙe na sauka yana zaune har na gama saukowa idanuwansa na kaina ya dau wanka sai ƙamshi yake kujerar nesa da shi na zauna na ce “Ina kwana? “Kin tashi lafiya? Na ce lafiya lau.

“Ya ba ki shirya ba kin kama barci kin san kuma yau za mu wuce.” Na yi saurin duban shi “Ba sai gobe ba?

Ya ce “Akwai sauran abin da za ki yi ne? Na ce “Ina son ka kai ni Malumfashi, ina son zuwa gidan Khadija da Rabi’ah ina son gano…. Na kasa ƙarasawa na yi shiru “Ƙarasa mana? Ya ce yana min wani kallo na girgiza kai “Malumfashi ba yanzu ba sai kin haihu ita da Taraba.

Na ɓata rai “Gidan Khadija da wa kika ce shirya ki zo zan kai ki, da gidan Dr Auwal.

Na mike na koma saman cikin ƙarfin hali don cikin da ke jikina hawan ba ya min daɗi.

Wanka na yi na yi kwalliya na sanya wata riga mai girma don ban son takura kaina, da na ƙare shirina na sauko ban same shi ba Mama ta ce min ya fita na yi mata sallama Asma’u da Ihsan suka raka ni har gaban motar na shiga ya tashe ta muka tafi.

Gidan Khadijah muka fara zuwa sanin yana waje ban zauna ba ta rako ni sai suka gaisa ya ba ni kudi na ba ta muka tafi.

Haka ma gidan Rabi’ah, mun bar gidan Rabi’ah Mami ta kira ni muka gaisa tana tambaya ta gajiyar suna na ce suna mun gama muna zagaya gidajen su Khadija ne da Rabi’ah.
Ta ce “Ya yi gidan Najib fa?

Na ɗan yi sukuti kafin na ce “Ba mu je ba.” Ta ce “Ki ce mishi na ce ku je.”

Na ce “To Mami.” Ta ce “Wurin Amir fa? Na yi shiru “Gane ba zan yi magana ba ta ce “Ku je ku gaishe min da shi. Na ce To mun yi sallama na dube shi “Mami ta ce mu je gidan Najib.”
Bai kalli inda nake ba ya ce “Kina son ganin shi ne? “Ganin shi na me? Mami ce ta ce in ce maka mu je.”

“Au to, na ji an ce kun buga soyayya kafin komawar ki Abuja.”

Na hangane baki “Ni dai ka rufa min asiri ba soyayyar da na yi da shi.

Mun yi shiru na dan wani lokaci ya ce Ina ne gidan?

A hankali nake nuna mishi hanya har muka kai.

Ko da ya ce in shiga ƙiyawa na yi sanin yau din Asabar karshen ta Najib ɗin na gida, in je in shiga bai rasa abin da zai ce. Sai da ya ga da gaske nake don na dage ya kira shi ta waya, ta wayar ya kira shi ya shaida mishi ga shi a ƙofar gidansa .

Cikin hanzari ya fito sanye da jallabiya a raina na ce su Najib magidanta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 51Mutum Da Kaddararsa 53 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×