Skip to content
Part 51 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ban haƙuri sosai ta yi har da hawayenta kafin ta samu ta shawo kan shi. Da safe kuma yana shirin fita don indai ita ke da girki ba ya samun abin karyawa, don ba ta iya katse barcinta.

Yana karya hularsa ta tsaya gaban shi tana shafa kirjinsa. “Ka yi haƙuri Dear, da abin da na yi maka, ba don ina ƙin Nana ba ni ma ƙanwata ce.

Sai dai ina so in ba ka shawara ka kula dangin mijinta da ta fita wurin shi Hassan sun fara ziyartarta gidan nan, wata da ta zo a ƙarshe maganganun da na ji suna yi ba zan so kunnenka ya ji ba.”

Ta buɗe wayarta “Ka ga abin da ta kawo mata.”
Zuciyarsa ta canza salon bugawa duk da bai son yarda da zancenta idonsa ya kasa ba shi haɗin kai.

Wata mata ya gani a hoton da ke kan fuskar wayar tana buɗe wata baƙar leda ga Bilkisu can zaune.

A kallo daya da ya yi wa wayar ya ga hakan sai ya mayar da kai, wucewa kawai ya yi ya bar dakin.

Ya dubi kofar Bilkisu ba zai iya shiga ba, a halin yanzu yana bukatar nazari har ya bar gidan ya shiga motarsa tunanin da yake kenan ba wai abin da ta ce an kawo ma Bilkisu ba dangin tsohon mijinta da ta ambata shi ya fi ɗaga mishi hankali yake kuma so ya tabbatar gaske ne.

Na yi barcina na tashi har na gama shiri na ya Safwan bai shigo ba. Na fita na duba kofarsa babu shi a ciki na fita ba motarsa, cike da mamakin abin da ya hana shi shigowa wajena na koma ciki na ɗauki waya na shiga kiran shi ba ta shiga sai hakura na yi na shiga kitchen na nemi abin da zan ci, da na gama na koma daki dole na hakura da shiga Sch ɗin a ranar.

Hajjo ta tura ƙofar falon Farha ta shiga da sallama ba kowa ciki ta samu bakin kujera ta zauna a ƙasa.

Ta kai minti goma sannan Farhan ta fito a yatsine ta dube ta ita kuma ta gyara ta fara kwasar gaisuwa.

Sai da ta gama ta ɗora da cewa “Na sanya ranki ya daɗe, sai dai ban samu na sanya a can dakin gadon na ta ba, a falonta na sa.

Farha ta ɗan taɓe baki “Ba ma wannan buƙatar, ba sai ya ga abin da aka ajiye ba.”
Hajjo ta ce “To to Haj, na bar ki lafiya.
Ta miƙe ta fita.

Safwan ya kasa zama a office ɗinsa dole ya taho gida, Farha ba ta gidan kiran ta ya yi tana ina ta ce tana gidansu, ya ce ta dawo yanzu yana jiran ta.

Yana kwance a dakinsa ta shigo “Kawo min Tea.”

Abin da ya ce mata kenan ta zare mayafinta ta ajiye Hand Bag ɗinta ta fita, ya yi saurin ɗaukar jakarta ya buɗe ya zaro wayarta ya kunna ya shiga Gallery bai sha wuya ba ya tura hoton da ta nuna mishi cikin wayarsa ya goge komai sai ya mayar mata da wayar cikin jaka ya koma ya kwanta, sai ga ta “Wai lafiya za ka sha Tea yanzu?

Ya ce “Lafiya lau.”

Ta raɓa ta kwanta jikinsa ya zare ta ya mike ta ga zai fice ta ce “Ba ka sha ba? Ya ce “Ina zuwa.”

Ganin ya fita ta taɓe baki kawai tana zaman ta ya azalzalo ta. Ta buɗe jakarta ta ciro wayarta.

Ina kwance muna waya da Hafsah ya Safwan ya shigo na tashi zaune na yi mata sallama na kashe wayar ina gaishe shi saboda duk yau ban gan shi ba. Ina jiran ya ba ni bayanin uzurin da ya hana shi shigowa sai na ga ya miƙo min wayarsa da ya riga ya kunna “Wace ce wannan? Na ɗauki wayar don in ga ni da kyau ganin hotona da Haj Asiya ga leda gaban ta ya sa cikina wuntsilawa, na nemi miyan da zan haɗiya na rasa.

Ina tambayarki wace ce ita? Na ce “A Kano take.”

Ya suke da tsohon mijinki? Jin wannan tambayar tuni na ƙara diriricewa.

“Ya suke na ce miki? Ya maimaita cikin hasala na kalaci yawu na haɗiye “Matar kawun shi ce.”

Wani kallo ya min da ya sa ni saukowa ƙasa na durƙusa “Da gaske ne kenan, kina gidana kina mu’amala da abin da ya shafe shi ? Wani dum! Na ji da ya hana ni buɗe bakina in kare kaina,
ya miƙe ya ɗauki wayarsa sai ya bar wurin.

Na daɗe zaune cikin tashin hankali waye ya shirya min wannan gadar zaren? Na fito na shiga dakinsa don in kare kaina ba shi ya fita na fito na ga Farha zaune ta ɗora ƙafa daya kan daya cikin matuƙar nishaɗi tana waya take zuciyata ta ɗarsa min Aunty Farha ce ta ƙulla min wannan ƙullallar duk da rashin samun nutsuwa da zargin nawa saboda ba alamar hakan a tare da ita yadda take kullum cikin faran-faran.

To kuma gidan daga ita sai Hajjo, Hajjo ina ta ga babbar waya ko ta iya yadda za a dauki hoto.

Da daddare ya Safwan bai shigo da wuri ba har na gaji da zaman jiran ya shigo na tafi ɗakinsa na kwanta.

Tun ina hana kaina barcin da ke cin idona har ya ci ƙarfina ya kwashe ni.

Na farka cikin dare na ga sai ni kaɗai gaba na ya faɗi ko bai dawo gidan ba na tashi na fita yana kwance a falo ya tada kai da hannayensa yana barci.

Na juya na koma ciki da na kwanta barcin ma ashe daɗi ke kawo shi sam na neme shi a idona na rasa, alwala na ɗauro na zo na yi sallah ta nafila raka’a biyu na roƙi Ubangiji ya ba ni mafita.

Da safe da wuri ya fice bai bi ta kaina ba dole na shirya na fita na nemi mota na tafi Sch.
Duk yadda na so in kare kaina ya Safwan ya ƙi saurare na.

Ba Aunty Farha ba hatta Hajjo na san ta fahimci ya Safwan ba ya saurare na.
Ina zaune cikin damuwa sai dai in shiga wurin Hafsah ko Khadija ko su su shigo.

Kwana bakwai da faruwar abin, duniya ta yi min ƙunci daga makaranta gidan Mami na wuce. Sai kallona take har ta kasa shanyewa ta ce “Har kin fara fargabar haihuwar ne?

Na ce “Me kika gani Mami?

Ta ce na ga duk kin sukurkuce.”

Na yi ɗan murmushi “Ban tunanin komai.
Har yamma da ta ga ban da niyyar tafiya ta ce,

Da Sadauki za ku tafi? Na ce “E.”

Sai kuwa ga shi bai kalle ni ba ni ma ban kalli inda yake ba har ya ci abincin shi da ya tashi tafiya Mami ta same ni a daki na idar da Sallah ta ce “Ki fito ku tafi.”

Na kasa gaya mata abin da ya faru don haka miƙewa na yi jiki ba ƙarfi na ɗauki jakata na bi bayan ta.

Sai da ta raka ni har kofa sannan ta koma.
Sai dai ina isa yana tayar da motarsa na dade tsaye sai na taka na koma ciki

Wani irin duba ta min “Ya ba ku tafi ba? Na zauna “Ya tafi Mami.”

Wayarta ta janyo “Ba lafiya kenan.” Kiran shi ta yi ta ce ya juyo tana neman shi.

Na rufe fuskata da hijabi har ya shigo “Me ya faru tsakanin ku, ka tafi ka bar ta? Ya yi shiru ta ce “Ba ka ji na ne? Ya ce “Ki yi haƙuri Mamina, laifi ta yi min. Ta tashi mu tafi.”

Me kika yi mishi Bilkisu? Na ɗago na ce “Baƙuwar da ta zo nema na kika tura ta wajena, aka ɗauki hotonmu tana ba ni turare aka faɗa mishi ina mu’amala da tsohon mijina.”

Mami ta kama salati sai ta rufe shi da faɗa ta yi mishi tatas! Tana faɗin “Wane zancen banza ne wannan za a ƙulla abu ka kasa ganewa? Shi mai gaya maka meye na daukar hoto idan ba masifa yake so ya ƙulla maka ba? Ka ci gaba da sauraren irin waɗannan makirce-makircen sai an kashe maka aure.”

Hakuri ya shiga ba ta ta ce “Ba ni za ka ba haƙuri ba ga wacce za ka ba nan don ita aka cutar.” Ta tashi ta yi tafiyarta.

Ya taso ya tsaya kaina “Tashi mu tafi.” Na yi banza da shi wasa gaske ya yi duk irin maganar da zai yi ban motsa ba har ya gaji ya kira Mami, ita ta ba ni hakuri na share hawayen da ke zubar min ta raka ni har na shiga motar.

Muna tafiya ya tsaya wani Mr bigs yana tambaya ta me zai karɓo min na yi banza da shi ya fita ya tafi kafin ya dawo ɗauke da ledoji.

Muna isa na riga shi fixa na shige daki na rufe.

Da safe har kitchen ya same ni Hajjo da ke dafawa Aunty Farha ruwan zafi ta yi saurin barin kitchen ɗin.

Ya ƙare maganganunshi ban tsinka mishi ba na ɗauki v da na dafa na fita ya bi baya na ɓb tsaye a falon na wuce ya bi ni ciki ina cin indomie na yana kallona na gama na shirya muka fita tare.

Kwana biyu yana bibiyata ina share shi muna zaune yana cike wasu takardu, na samu wayar Zainab ta haihu ina ta murna na ce ta sanya min kukan babyn in ji. Dariya ta yi ta ce ” Billy ho! Indai ba so kike in tsungule shi ba.” Muka kare wayar na shiga lalubo lambar Hafsah in faɗa musu Zainab ta haihu, don zama na da su sun saba ta waya.

Waye ya haihu? Na tsinkayi muryarsa na rage fara’ar fuskata “Zainab ce.”

Na ba shi amsa “Sai ki fara shirin zuwa suna ko?

Na yi kamar ban ji dadin jin zai bar ni ba don kusan kullum sai na yi mishi magiya sai ya ce Ni da Kaduna sai na haihu.

Hannuna ya janyo na faɗo mishi ina kare cikina ya zaunar da ni a ƙafarsa ya ba ni feck a kumatu “Fushin ba zai ƙare ba yammatana? Na tura baki “To a yi haƙuri, kin ga takardun nan da nake cikewa alheri ne ya samu mijinki, wata.

Wata kwangila na samu ta shigowa da wasu motoci na wani Company, sai fushi kike kin ƙi yarda mu raba farin cikin tare.”

Na yi mishi fatan alheri, ya sure ni cak da ƙaton cikina sai gadonsa.

Sai da ya more sosai ya bar ni ina barci ya yi wanka ya fita.

Karin jin dadina da haihuwar Zainab akwai Esther Monday good Friday sunan kuma ranar juma’a ya kama.

Hajjo da ke zaune gaban Farha tana ba ta labarin shiryawar Bilkisu da Safwan.

Ta ɗan tashi zaune tana jan tsaki “Kina nufin har ya yafe mata? Ta gyara zama “Ki gafarce ni uwar ɗakina, ai su irin waɗannan matan wuyar sha’ani ne da su nake gaya miki, wutar ta ba su juya ma namiji abin zama ba ko ya hango tudun ƙirjin nan tuni zai sukurkuce ya manta da laifin da aka yi masa.

Amma in ta san wata ba ta san wata ba ta daga zanenta sai ga takardu Farha ta ce “Su kuma na mene ne? “Su nake gaya miki na ji yana fadi mata kwangila ya samu, ki ɓoye su a wurin ki, nan da kwana biyu zan zo in karba.

Ta rage murya ta faɗi mata shirin ta kansu.
Farha ta jinjina kai “Shirin naki ya yi, duk tsiya ta yi mishi haka sai ya samu kokwanto kanta.”
Hajjo ta ce “Kwarai haka za mu yi ta yi mata. Ta gyara zama.

“Kishiyoyina bakwai da irin wannan kissar duk na yi ta watsa su. Guda ɗaya ta nemi ta gagare ni yadda kika ga kishiyar nan taki haka take da fasali, da na shirya mata makirci tana juya mishi abin zama ko ta kada mishi kirji sai dai in ji shewar su a daki.

Ita kaɗai na san na kai wa malami dawa ta ya yi min aiki a kanta ta fita sauran kishiyoyina duk kissata ta kora su, don haka mijina har ya mutu da baƙin cikin rashin barin shi da mata shi da yan’uwansa ya tafi.

Haj ki gafarce ni, mijin ku ko da yake miskili da ta gifta sai ya kalla, ko ta ƙasan ido ne sai ya kau da kai ya basar. Farha da ta rafsa tagumi tana wani lissafin na daban, ta jinjina kai.

Jakarta ta buɗe wadda ke cike da yan dubu dubu Hajjo ta miƙo ido kamar ta faɗa jakar guda uku ta zaro ta miƙo mata da sauri ta miƙe ta amso tana “Ala amfana Haj. Allah ya bar ki ke kaɗai da maigidan ya kore yan baƙin ciki. Hannu da Farha ta daga mata ya sa ta saurin juyawa ta fita sai da ta tsaya ta soke kudin a cikin bujenta ta kara gaba tana masifa cikin ranta. Wai dubu uku don baƙar rowa, duk wadannan uban kuɗaɗen da na gani da wata ƙafarta kamar burugali.

Tana fita Farha ta dafe goshinta idanuwanta a rufe so take ta gano gaskiyar maganar hajjo, da gaske ne Safwan na ma Bilkisu kallon da Hajjo ta ce. Ƙwarai ta san Bilkisu ta samu shiga a zuciyar Safwan shin kirar halittar ta ta ce ta ja hakan ko kuwa? Za ta sanya ido ta gano gaskiyar kallon da waccan shashashar ta fadi mata.

Ilai kuwa da daddare suna cin abinci tana hankalce da duk motsin shi ta kuwa sa’ar yin farin gani sau biyu tana kama shi yana kallonta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 50Mutum Da Kaddararsa 52 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.