Skip to content
Part 53 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ya tari ya Safwan cikin fara’a da girmamawa, ban tunanin ya san da ni ba sai da ya Safwan ya zagayo inda nake ya ce “Fito mana.”

Na buɗe na fita, Najib ya dubi inda nake na ce “Sannu ya Najib.” Yawwa kawai ya ce min ya ce ma ya Safwan “Bismillah babban yaya.”

Ya bi bayan shi ni ma na bi su a hankali.
Ya fara ƙwala kiran sunan matarsa ta fito tana mana sannu da zuwa na karbi yarinyarta da ke hannunta ta kawo ruwa da lemo.

Ni dai ina sauraren su suna magana ina ma yarinyar wasa da ke ta miƙewa a jikina, uwar ta ce “Ko za ki sauke ta kar ta buge ki kina fama da kanki, Ilham akwai tsalle-tsalle.”

Dukkan su suka dube ni Najib da ya Safwan.
Ya miƙe “Za mu koma sai gani na biyu.” Ya ce “Shi kenan sai mun shigo Abujar.”

Na mike tare da yarinyar, kamar yadda ya Safwan ya ajiye kudi ya ce a saya ma baby Sweet ni ma haka na ciro na ajiye mata.

Muka fita wurin mota na miƙa ta ga uwarta.
Yana hawa titi ce min ya yi nuna min gidan su Amir, na ce “To.”

A raina ina jin sabuwar ƙaunar ya Safwan na lulluɓe ni ya nuna son shi ga mahaifiyata, ya nuna ga gudan jinina. Hawaye suka taho min na so Babana ya rayu zuwa yau, don ya ga yadda rayuwata ta sauya.

Hawayen suna ta gudu kan fuskata na ce “Na gode ya Safwan.” Ya juyo ya dube ni kaɗan sai ya maida idonsa titi “Me kika ce? “Na maimaita “Na gode bisa ƙaunarka a gare ni.” Hankacif ya miƙo min na goge hawayen.

Mun shiga kurmin mashi ina nuna mishi hanya har muka kai ya tsaya a daidai ƙofar gidan mahaifiyar Aminu. Akwai yara masu yawa a kofar gidan hakan ya alamta min ana wani taro a cikin gidan.

Yaran da suka san ni suka yo kaina har da Amir a cikin su, ya Safwan ya fito ya tsaya a gefena ya ce “Ki kula fa kar su bige ki.” Na daga mishi kai shi da kan shi ya kamo hannun Amir yaron ya bi shi zuwa cikin mota ,ban mamakin yadda aka yi ya gane shi don tsananin kamar da yake da ni.

Na wuce cikin gidan da yake cike da mata, ashe suna suke yi na matar yayan Aminu, kafin ka ce me mata sun rufe ni da yawa waɗanda na zauna da su ne wasu ma ba su gane ni ba, ana ta min sannu da zuwa, matan yan’uwan shi suka kasa ɓoye mamakin su suna faɗin yanzu nan Bilkisun Aminu ce ta koma haka?

Aka kawo min tuwon suna da shinkafa,maman Aminu ta buɗe fridge ɗinta ta ciro ruwa pure water da lemo da na san tana saidawa tun ina nan ta ajiye gaba na, ita da Abu sai rawar jiki suke kamar su duƙa min, wayata ta yi ƙara na daga ya Safwan ne ya ce ki duba na turo miki sako.

Na sauke wayar na fara lalubar sakon *Zan tafi masallaci idan na fito ina son ganin baban Amir.* Na faɗa wa maman shi nan da nan ta ce a dubo shi.

Ina son tashi in yi sallah amma matan nan sun rufe ni har Aminu ya leƙo ya ce mahaifiyarsa ta zo tare da ni.

Suna tsaye tare da ya Sadauki muka fita zo ka ga gaisuwar da take mishi abin har kunya ya ba ni. Aminu ya ce “Mama mijin Bilkisu ne ya zo da rokon in ba su Amir.”

Ta ce “Ai duk daya ne ka ba su mana.” Ya girgiza kai “A’a mama ba zan rasa uwar shi ba kuma in rasa shi, Babban ɗa na da nake so.”
Na saci kallon ya Safwan fuskarsa ta sauya ya harɗe hannaye a ƙirji “Ba zan iya ba Mama.”

Da yake ita uwa ce mai haƙura da ra’ayin ta ta bi na ya’yanta matuƙar za ka ba ta sai ta kada kai “Shi kenan Alh ku yi haƙuri don Allah.”
Ya ce “Ba komai, amma don Allah ina son canza mishi makaranta kuma idan ya samu hutu a riƙa barin shi wurin maman shi.”

Ta ce “Wannan ba damuwa Alh an amince.
Aminu ya ce “Ba kowane hutu ba, makaranta kuma wacce?
Ya ce “A Abuja ne.”

Kai ya girgiza “Ka dai sanya shi a nan jihar Kaduna. Ya ce “To na gode zan bincika anan ɗin.” Ya dubi Maman “Mama na gode za mu koma.” Ta ce “To Alh mun gode mun gode, Allah ya sa ka maka da alheri ya bar zumunci.”

Kuɗi ya ciro ya miƙa mata ta dafe tana sake sabuwar godiya. Na ce “Bari in shiga in yi wa mai jegon barka.” Na taka na bar wurin Amir ya biyo ni a baya yana cewa “Ina keken da kika ce za ki turo a saya min? Na ce “Ba a sai maka ba? Ya ce “E. Na ce “Yana Boot zan ba ka idan za mu tafi.” Ya hau tsalle na shiga na yi mata hassafi na fito na shiga gidan Maman Aminu na yi ma matan sallama tare da alheri dubu goma na ce su raba, ai kam rakiya har waje.

Ya Sadauki ya buɗe Boot yana ciro abin da na kawo ma Amir ina tsinkayo muryar wata cikin matan tana faɗin “Ikon Allah wannan hamshaƙin namijin ne mijin Bilkisu? Amir na ta tsallen keke, Abu da ke gefena tana ta kame-kame. Ni dai na gama sauke komai sai na buɗe motar na shiga ya zagaya ya shiga suna ta daga min hannu ya ja motar.

Wasu sabbabin hawayen na ji suna gudu kan kuncina ban damu da share su ba barin su na yi suna ta zuba “Saboda wancan sankaran ya ce ya rasa ki kike kuka? Na dube shi da sauri sai na koma na cigaba da kukana yana ta gaya min bakaken magana kan Aminu sai da ya ga mun shiga kinkino ban da alamar tsaida hawayen ya miƙo min hankacif “To yi haƙuri ki share hawayen.” Na karɓa na share.

Gaban wani hamshaƙin gida ya yi horn aka buɗe get ya cusa hancin motar gidan bene ne hawa daya matar da mijin suna tsaye, yana tsaida motar suka iso ina fitowa ta rungume ni “Oyoyo Aunty Bilkisu.” Abin da take fadi kenan cikin farin ciki duk da na san za ta girme ni da da shekara daya ne ko biyu.

Ta riƙe hannuna zuwa ciki sai da ta ajiye ni a kujera ta matso da wani tebur da aka cika da kayan ciye-ciye da shaye shaye ban taɓa komai ba na ce zan yi sallah, nan ma hannuna ta kama har bedroom ɗinta na yi alwala na fito na kabbara Sallah, ina idarwa tana ƙara shigowa don ina cikin sallar ta shigo muka dubi juna ta yi min murmushi na mayar mata “In kawo abinci nan ko za ki fito? Na ce “Mu je can ɗin.”

Muka fita na ci abincin tana min hira kamar mun daɗe da sanin juna, sai da na kammala ta ce “Ko za ki watsa ruwa ? Na girgiza kai “A’a na yi wanka sai kuma dare.

Mijinta da ya Safwan suka shigo ya ce min “Ina miƙo godiya ta musamman Madam.”

Na dube shi don son jin abin da na yi yake gode min, “Dole in gode miki don kin yi sanadiyar kawo min abokina da muke tare tun a shekarun ƙuruciya.

Tun da aiki ya cillo ni garin nan bai taba kawo min ziyarar kwana ba sai sanadin ki ga shi har ya kwana min biyu zai yi na uku.”

Muka murmusa ni da matarsa Maimuna, mace mai labari ya Sadauki ya kasa tanka mata sai dai ya ce “Auwal matarka ta sanya ni gaba.”

Har sai da aka yi la’asar suka fita Masallaci muka yi ta mu a daki da muka idar ta dube ni cikin murmushi “Kin ji daɗi, daga yin aure Allah ya ba ki ciki, ni kam sai da na shekara biyu na samu, wajen haihuwa kuma aka yi min Cs yaron ya zo ba rai tun daga nan shiru yau shekara uku kenan.

Na ce Allah ya kawo masu albarka.”

Ta amsa da Amin.

Ta gayyace ni kitchen tana shirya abinci ina mamakin gida kamar wannan ita kaɗai ke gyaran shi ba ta da me aiki.

Kamar ta san tunanina ta fara ba ni labarin illolin yan aiki da ta ce sai da ta yi uku duk ba ta ji dadin su ba daga mai son ƙwace mata miji sai mai sata, karshe ta haƙura da su ta kama hidimar gidanta. “Abin da ma kake neman aljanna, aljanna kuma ba ta samo ta sauki.” Na ɗaga kai “Haka ne.”

Kiran mijinta ya shigo ta dauki wayarta ta amsa, muka ci gaba da aikin, kafin mu gama ya kira ta ya yi sau biyar na lura suna matuƙar son juna kamar sabon aure.

Da muka fito na ƙura ma ƙaton hotonsu ido shi ɗin fari ne kyakyawa mai saje, irin dai mazan da mata ke so.

Ita kuma baƙa ce doguwa mai murzajjen jiki don ba ta kiba kuma ba ka sa ta cikin ramammu, haka nan ba wani kyan fuska take da shi ba.

kadaran-kadahan sai dai kwalliya da wayewa da kallo ɗaya za ka yi mata ka samu tabbacin ta kwankwaɗi madarar ilmi..

Muna idar da sallar Isha’i ta shiga ta yi wanka ta fito tana fara kwalliya dakin gabaɗaya ya cika da ƙamshi.

Ta juyo inda nake “Ki shiga ki yi wanka.” Na ce “Sai na koma gida, ban zo da kaya ba.”
Ta ce “Tafiya kuma yau ba za ki yi min kwana ba? Ni S.A Safana kwana ya ce za ki yi min.

Na ce “Ban ce musu zan kwana ba.
Kafin ta yi magana mijinta ya kira sunan ta ta fita da sauri ta dawo ta ce in fito mu ci abinci.

Na fito na zauna ana cin abincin ina yawan kallon ya Safwan ya gaji da kallon da nake mishi ya ajiye cokalin ya tsura min ido na dubi agogo na ce “Mu je gida kar dare ya yi.”
Uhmmm! Kawai bai ƙara cewa komai ba har ya gama cin abincin, Maimuna ta mike ta shiga kitchen mijinta ya bi bayan ta, na dubi ya Safwan na langaɓe wuya “Mu je gida ya Safwan.” Cikin kwanciyar hankali ya ce “Anan za mu kwana.” Cikin mamaki na ce “Kwana kuma?

Ya daga kai “Tun da muka zo ba mu zauna wuri ɗaya ba, yau kaɗai ki bari mu kwana tare gobe za mu gida.”

Na ce “Su Mama ne damuwar ban ce zan kwana ba.”

Waye zai tsaya neman inda kike ko tambayar inda kike daga an san muna tare.” Na ƙara karya wuya “Ina jin nauyi ya Safwan.

Ina rufe bakina ya mike ya dauko makullansa kan wani ɗan stool “Tashi mu tafi.” Kalmar da ya ambata kenan sai a kunnen masu gidan da suka fito tare turus suka dube mu Dr Auwal ya ce “Yaya dai mutumina? Ya ce “Zan kai ta gida ne.”

Ya matso kusa da shi “Gida kuma nan ma ba gida ba ne? Hannuna kawai Maimuna ta zo ta kama na miƙe muka shiga bedroom ɗinta “Me zai sa ki bata ran mijinki? Abin da ta fara ce min kenan da muka shiga kafin ta fara gaya min maganganu masu kama da nasiha yadda ake tafiyar da miji, ta rufe da cewa “Ki ba shi haƙuri.”

Na daga mata kai “Za ki yi wanka ne ko sai kin je can? Na ce “Bari in je can ɗin.”

Ta buɗe wardrobe ta ciro wata rigar barci a ledarta ta ajiye min kafin ta ce min ina zuwa sai ta fita cikin sauri ta dawo ɗauke da farar leda cikin ta tazargade ce wadda tun kan ta iso ni kamshinta ko warinta zan ce ya shiga hancina.

Ta zauna kusa da ni “Ina fata kin san muhimmancin tazargade a wurin mace ? Na girgiza kai alamar ban san amfanin na ta ba.
Ta ce “Bai kamata a ce an rasa ta wurin mace ba ita da ganyen magarya, don ban ga abin da ke gyara gaban mace ba irin su, matuƙar ta yaƙi sanyi. Ganyen magaryana ya ƙare, amma kafin ki tafi za a kawo min.”

Ta ɗora da bayanin yadda zan yi amfani da tazargaden na shiga bayinta na yi na fito tana nan zaune wata yar jarka mai dauke da zuma ta miƙo min “Ki sha.”

Ban amsa ba cikina na nuna mata “Haba abin da tausayi ma Aunty Maimu.”

Ta yi yar dariya “Normal ne kar ki wani damu.
Wani dan karamin kwali ta ciro miskul ɗahara ne ki yi amfani da shi da zarar za ki kwanta.”

Na ce “Na gode.

Mai kyau ne Aunty Billy, daga Saudiya na Zo da su da su man zaitun da habbatus sauda da zuma, duk kar ki taɓa zama ba ki da su.

In sha Allah kafin ku wuce duk zan haɗa miki su.

Na ƙara cewa na gode.

Na ɗauki miskul ɗahara na jefa jaka ta ɗauki rigar muka fita dakin.

Suna nan zaune a falo suna hirar su ni ma na san ba karamar shaƙuwa ba ce tsakanin shi da abokin na shi yadda na ga yake hira da shi

<< Mutum Da Kaddararsa 52Mutum Da Kaddararsa 54 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.