Skip to content
Part 54 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Wani ɗaki ta buɗe muka shiga gado ne sai mirror da wardrobe sai kujera guda daya.
An gyare shi tsaf yana fitar da ƙamshi.

Ta wuce bathroom ta haɗa min ruwa ta fito ta ce “Mu kwana lafiya.”

Na ce “Sannu da kokari, na gode kwarai.
Ban shiga wankan ba bisa kujerar na zauna na ciro wayata ganin Zainab online na ce “Mai jego ba ki kwanta ba?

Ta amsa muka ci-gaba da hira har ya Safwan ya shigo ganin bai kalli inda nake zaune ba nasan fushi yake da ni.

Bathroom ya shiga can ya fito guntun wando kawai ya sanya ya hau gado bayan ya kashe hasken dakin, ban kunna ba da hasken da ke fitowa daga cikin bayin na yi amfani na tuɓe kayan jikina na shiga wankan, ruwan da ta haɗa min har ya fara hucewa na ƙara na zafi na yi wanka ruwan na fitar da daddaɗan ƙamshin turarukan da ta sanya na fito daure da tawul da ƙaton cikina kawai na rufe zuwa mazaunaina amma har cinyoyina a bude suke.

Na kunna wutar dakin ina kallon inda yake zaune ya tare bayan shi da fillow haske ya gauraye dakin ya ɗago ido daga wayarsa, muka haɗa ido na zauna a kujerar madubi na shafa mai na fesa turare na taje gashin kaina na shafe shi da wani mai da na gani na gashi sai na tubke shi.

Sau biyu muna haɗa ido ta madubi yana kawar da kai na gama na dauko rigar a kusa da shi na zura na kashe wutar na sanya miskul dahara tun a bayi na hau gadon.

Bayan shi na wuce na kwanta na ɗora kaina saman kan shi ina ba shi haƙuri a hankali tare da taɓa duk inda nasan zan taɓa shi, don tun ina zaune gaban mirror nasan na kunna tasharsa.

Zaune ya tashi sai ya koma bayana ya rungume ni ta bayan.

Mun kai wani lokaci kafin ya janye yana mayar da numfashi, sai kuma ya sauka gadon ya shiga bathroom.

Barci ya fara fizgata ya fito ya kunna wutar haske ya gauraye dakin na bude ido don ban son haske ina barci ya tako inda nake yana tsayen ya ce “Daure ko alwala ce ki yo.”
Na amsa barci na cin idona na sauko gadon na wuce da na yi tsarki har zan yi alwalar sai kuma na yi wankan kawai na fito ina digar ruwa.

A jikin window na hango shi tsaye ya zura wa harabar gidan ido, ga iska ta taso ana ta cida alamar ruwa na dab da sauka.

Na hau gadon na kwanta bayan na goge jikina na ɗauko rigar na mayar na koma bisa gadon na rufe ido na ji isowar shi daidai da saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Gadon ya hau ya ɗora kaina bisa cinyarsa yana rada min “Tashi hira nake so mu yi.”

Na ƙara rufe idona Barci nake ji.” “Yi haƙuri, tarihinki nake so ki gaya min da bakinki.” Ban san sadda na yi saurin buɗe idona ba ya ɗaga min kai “Daure ki gaya min, a yau mun zama daya ba na son ki boye min komai ina son jin ke wacece daga bakinki.”

Na lumshe idona na ɗan jima sai na buɗe na shi idon yana kan fuskata.

Tarihina ba mai daɗin ji ba ne ya Safwan, ban san ka ji kar ya canza zamantakewar mu
Ya kara daga kai “Ina son ji hakanan, ina jinki a raina har ban san yadda baki zai furta ba, ba abin da zai canza ko da a cikin labarin naki kin yi kisan kai kin san dai shi ne karshen abu mai muni.
Ina tare da ke, zan kuma cigaba da kasancewa a tare da ke har karshen numfashina, in sha Allah.”

Jin kalaman shi sai na ji na samu karfin gwiwa, na dan gyara kwanciya don cikina da ke motsawa da karfi shaidar na danne shi.

Zan faɗa maka ya Safwan daga kana son ji.
Ina jinki.”

Na rufe ido na fara daga rabuwar aure tsakanin mahaifiyata da mahaifina, zama na hannun Iya mahaifiyar Inna keso, har aurena mutuwar auren, komawa ta Dukku, aurena da Malam a Gombe yadda ta kaya na bar shi na koma Dukku har na tafi Malumfashi na auri Hassan da yadda rayuwata da Inna ta kasance, na koma Dukku bayan macewar auren Hassan na auri Alh Buhari auren da bai je ko’ina ba don kasa tarawa da ya yi da ni, auren ya mace a wata uku kacal da ƙulla shi.

Dawowa ta gidanmu mutuwar Babana, nan na tsagaita na shiga kuka don a duniya idan akwai abin da na kasa sabawa da shi mutuwar Babana ce.

Tissue ya sa yana share min share min wasu na zuba ko tari bai yi ba sai da na natsa ya ce Allah ya ji kan Baba.

Na cigaba yadda na koma Kaduna da karatun da na samu har komawa Abuja sai na ce Momi ta roki Baba ya ba ta ni wata irin mata mai matukar karamci da kirkin da ban taɓa ganin irin na ta ba na same ta da wani irin da miskilin gaske da kallon mutane ma yake yi mishi wuya.

Ina kawowa nan ya ɗaka min duka a mazaunaina da na tashi ba shiri saboda zafin da na ji ina tura baki na koma nesa da shi na kwanta ya isko ni ya janyo ni na fara ƙwace jikina ya ce “To yi haƙuri mana, in gaya miki ina sonki ina tausayin ki jin labarinki ya sa na ƙara tausayin ki, duk da na gwammaci ina ma na hakuri jin maza uku sun… Shiru ya yi ya kasa ƙarasawa sai ya ja wata ajiyar zuciya jin ya dade shiru na ce “Shi ya sa na ce a bar maganar ya Safwan. Na fadi muryata na rawa ya kara janyo ni “In ina numfashi in sha Allah ba za ki ƙara kukan maraici ba zan zame miki bango abin jingina, kar ki ƙara jin ke marainiya ce zan tare miki duk abin da kike jin kin rasa.

Na gode ya Safwan.” Yayin da hawaye suka ɓalle min suna ta gudu ina Babana yau ya ga Allah ya ba ni miji daya da daya kuma na yi dace yana yi mini so mai yawa godiya nake ta ma Allah a cikin zuciyata tare da yin alkawarin azumi uku don yin godiya bisa wannan niima.

Kwanciya muka yi ya rungume ni ta baya saboda cikina, ina fara barci na ji ya zare jikinsa ya shiga bathroom na dubi agogo uku da rabi har ta gota na rufe ido na ga fitowar shi pray mat ya hau ya kabbara sallah.

Ni dai ban san yadda aka yi ba sai ji na yi yana tashina in yi sallah, jin an fara sallah a masallatai na buɗe idona da kyar don uban barcin da nake ji ga kaina da ya yi min nauyi.

Na ɗauro alwala na yi sallah ban karanta Alkur’ani ko azkar ɗin da na saba ba na koma gado har na ji shigowar shi ya bi sahu na muka koma barci.

Karfe tara da aka fara knocking, Safwan ya buɗe ido ya amsa, muryar Dr Auwal ya ji yana cewa su fito a karya kumallo.
Ya ce yana zuwa sai da ya yi brush ya zura jallabiya ya fita.

Maimuna ta shirya komai tana ganin fitowar shi ta ce “Ina Aunty Billy? Ya ce “Ba ta tashi ba.”

Suka karya shi da abokinsa suka koma bisa kujeru suna hira, yana yi yana duba agogo har Dr Auwal ya ce “Yaya dai mutumin? Ya ce “10am na so mun kama hanya amma Mami ba ta tashi ba.”

Ya ce “Ka taso ta mana? Ya girgiza kai “Sai ta tashi.”

Har Maimuna ta zo ta zauna ta ce “Har yanzu ba ta tashi ba? Ya ce “E.

Karfe goma ya ce wa Dr Auwal ya zo su dan fita ya raka shi sai da suka fara tafiya ya ce mishi Bilkisu zai sawo ma rigar da za ta sa don kayanta suna gidan Baba.

Sha daya daidai na farka ban yi mamakin gani na Ni kadai ba don ya Safwan ina zai iya wannan uban barci da ya same ni ba duk da jiyan ban samu na yi shi kan lokaci ba.

Wanka na shiga na yi na fito na zauna a kujerar madubi ina yan shafe-shafena turo ƙofar na daga kai ina kici-kicin jan tawul ɗin da har cikina bai rufe ba iyakar shi mazaunaina bakin gado ya wuce ya zauna ya yi kamar bai ga me na yi ba.

Ledar hannunsa ya miƙo min na karba na buɗe ganin riga free size na ji dadi na ce Na gode ya Safwan. Bai ce komai ba na sanya rigar ya ce “Mu je ki yi break fast mu tafi.”

Muka fita ina bayan shi na gaishe da Dr Auwal da na gani a falo jin motsi a kitchen na nufi can.

Ta dube ni da murmushi “A kwana a hantse?
Ni ma na yi mata murmushin ina mika hannu ta ba ni wukar da ke hannunta ta noƙe “A’a Mamin SA Safana, rufa min asiri wurin honey ki, mu je ki karya. Ta kamo hannuna muka fito har wurin cin ta kai ni na zauna ya Safwan ya iso ya zauna gaba na sai ta juya, suka zauna ita da mijinta a kujera daya.

Tea ya fara haɗa min yana faɗin kin tashi lafiya?

Na rufe bakina da hannuna “Laa! Ya Safwan ni fa zan gaishe ka ya miko min kofiin, ya zuba min dankali da kwai ina ci a hankali yana kallona kamar ranar ya fara gani na duk sai ya sa na fara jin kunya don su Dr Auwal sun sa mana ido .

Na gama na ce na koshi ya ce “To mu je in yi wanka sai mu tafi.” Ina gaba yana baya na muka tafi.

Yana shiga wanka na gyara shimfidar gadon sai da ya gama shirin shi muka fita Maimuna ta kamo hannuna muka shiga bedroom ɗinta sai da na zauna ta ciro su man habbatus sauda da garin ta da man zaitun sai ganyen magarya da tazargade.

Na sanya a jaka ina mata godiya sosai bisa karamcinta, muka fita.

Kudade masu yawa ya Safwan ya ajiye mata mu ma da muka shiga mota Dr Auwal ya ajiye min, mun rabu da su cikin kewar rabuwa da juna.

Kamfanin motocin Baba muka yada zango ya fita ya shiga wurin ya bar ni a mota ana ta sallar azahar lokacin, sai da ya yi suka fito tare da baban ina daga ciki na gaishe shi ya yi mana addu’a ya Safwan ya shigo muka tafi.

A dakin Mama na yi tawa sallar na ci abinci kadan don ban jin yunwa.

Tsaraba sosai aka haɗa min har da man gyada na kuli da na ci shinkafa da wake mai da yaji ranar da muka zo na ce ya min daɗi.

Karfe biyu da kwata muka bar garin tun kuma da ya zo Ɗirkaniya na lumshe idona na fara barci duk maganar da yake min ba ta sa na tashi ba.

Duk da lalacewar hanyar Kaduna zuwa Abuja karfe biyar mun shiga Abuja kamar kuma yadda ya saba duk tafiyar da zai yi gidan Mami nan ne wurin da yake fara sauka yau ma can muka yada zango, Mami na ta nuna murnar ta ta dawowar mu.

Na raba duk tsarabar da aka yo min na ajiye mata da tulin kayan sunan da aka haɗo ni da shi in kawo mata.

Karfe tara muka bar gidan don sai da ya jira Daddy ya dawo, ina ji yana amsa kiran Aunty Farha.

Ba mu samu kowa a falon ba ya shiga wurin Aunty Farha na shiga wurina shirin kwanciya na yi na kwanta .

Karfe biyar na safiya kuma aka balle da ruwan sama wanda ya yi matuƙar yi min daɗi na fasa niyyata ta kin komawa barci in gyara ɗakina daga ƙurar da ya yi a tafiya ta ta kwana uku.
Na haye gadon na lulluɓe har ban san sa’adda ya ɗauke ba.

Shafa fuskata da ake ya sa na buɗe ido ya Safwan ne cikin shiri na tashi zaune ina gaishe shi ya ce ya gajiya na lura dai ba ki gajiya da barci, cikin nan ya mayar da ke sarkin barci.
Murmushi na yi na yaye rufar “Ni zan fita ki tashi ki nemi abin da za ki ci. Na ce to ina mishi addu’a ya fita.

Na yi wanka da ruwa mai dumi dan sanyin da garin ya dauka saboda ruwan saman da aka tafka.

Na fito na shirya sai na fita zuwa kitchen

A falo na samu Aunty Farha zaune Hajjo na goge-goge ta zaburo ta gaishe ni na zauna muka gaisa da Aunty Farha tana tambaya ta hanya.

Na isa kitchen ɗin ina aikina Hajjo ta shigo “Sannu Haj Barka da sauka, ai sosai kewar ki ta baibaye mu tun da kika tafi bakinmu bai ƙara jin dandano mai daɗi ba, yanzu ma ƙamshin da ya buwayi hancina ya sa ni garzayowa.”

Na ce “Hajjo kenan.”

Ina zuba abincin a plate ban juye duka ba na rage sauran a tukunya na nuna mata da hannuna sai na fita, fitata ta yi daidai da shigowar Khadija da Hafsah.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 53Mutum Da Kaddararsa 55 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×