“Ba ka da hankali ne me ye wannan ɗin haka? Ta yi tambayar ta na turo masa ledar gaban sa. Cikin tsananin tashin hankali Baba mai gadi ya ce “Hajiya ƙosai ne na gani ana soyawa a ƙarshen layi to shine na sayo miki domin wallahi ban san wani abu mai laushi bayan wannan ɗin ba a irin wannan lokacin.
Lokaci ɗaya taji kwaɗayin ƙosan a rainta amma tsabar masifar dake cinta sai cewa ta yi “To dan tsabar gidadanci sai kawai ka sayo mini ƙosai saboda kaga ana soyawa a ƙarshen layi ni nace ka sayo mini ƙosan ne? Baba mai gadi yayi shiru yana sauraronta. Jin ta yi shiru ta faɗan ne yasa shi ɗako kai da nufin kallonta sai kawai yaga tana cin ƙosan. A zuciyarsa ya ce “Ikon Allah a she ana so! Ganin haka yasa Baba mai gadi meƙewa ya bar palon ba tare da ya ƙara cewa komai ba.
Ameera kuwa sosai taji ƙosan ya shiga ranta hakan yasa ta ɗauki guda ɗaya ta ci, jin yayi mata daɗi sai kawai ta cigaba da ci har bata san lokacin da Baba mai gadi ya bar palon ba. Tashi ta yi ta koma kicin ta ƙara haɗa shayi ta fito palo ta zauna ta sha kayanta sosai sannan ta ƙulle sauran ƙosan ta koma ɗaki ta sake kwantawa ba tare da ta gyara gidan ba, tana kwanciya barci ya ƙara ɗauketa.
Tana cikin barci taji ana kiran sunanta hakan yasa ta miƙe fuska a haɗe ta nufi hanyar waje. Koda ta buɗe sai taga Kadija ce hakan yasa ta ɗan saki fuska. Cikin yanayin barci tai mata maraba sannan ta juya izuwa cikin gidan.
“Ameera ta Adam yau dai Allah ya amshi addu’o’in mu ya bamu baby da muke ta nema. Kadija ta faɗa lokacin da ta zauna. Murmushin yaƙe ta yi tana jin babu daɗi a ranta. Ganin haka yasa Kadija sake cewa “Kawai sai mukaga Yaya da sassafe wai kin kora shi aiki ko taƙalmi babu a ƙafarsa kamar ɗan gudun hijira hala wani laifin yayi miki? Kadija ta faɗa duk domin ganin ta jata da hira ganin kamar ranta a ɓace yake. Daidai lokacin Ameera ta ce “Kice gulma ce ta kawoki gidan ba komai ba, ina ruwanki idan ma laifin yayi mini, shima zai dawo ya sameni daga cewa ya tashi ya tafi aiki shine zai ɗauki ƙafa yaje gidanki yana kai miki ƙara ke ga uwarsa ko uwata ko? Shine harda zuwa ki kuma zaki ɗauki mataki ko? To gani dan Allah ki ɗauki mataki nice na koreahi. Tana faɗa tana ƙarasowa gaban Kadijan cikin tsananin ɓacin rai domin har ga Allah abun da Adam ɗin yayi ya sosa mata rai, daga cewa ya tafi aiki shine harda zuwa ya kai ƙaranta kamar wacce tayi wani abun laifi. Cike da tsananin mamaki Kadija ke kallon Ameera wacce ada ko iya magana ma batayi da ita tsabar kunya, hasalima wani lokacin har faɗa take mata cewar ki saki jikinki dani ni ƙanwar mijinki ce ba yayar mijinki ba, amma haka Amera zatayi dariya ta kawar da kai.
Ganin Amearan a gabanta kamar zata saka mata hannu ne yasa tayi ƙarfin halin cewa “Ameera ni kike faɗawa haka dan na tambaye ki? Cikin harzuƙowa ta ce “An faɗa miki ɗin uwata, ke ɗin banza kika iya shigowa gidana da niyar gulma bakiji kunya ba sai ni ce zanji kunyar faɗa miki gaskiya to na faɗa ko ƙarya nayi ba gulmar kika zo yi ba, ina ruwanki da tsakanina da mijina, mijina ko mijinki?
Duk yadda Kadija ta kai da tayiwa Ameera azuri amma sai take jin wannan ba laulayin ciki bane, wallahi kawai iya shige ne da alama asalin halintane take baiyana wa yanzu,to da ma a ce laulayin ciki ne ai nata cin mutuncin yayiwa, dama itama Kadijan ba haƙuri gareta ba. Hakan yasa Kadija faɗin “Ya isa haka ƙaramar mara kunya, ke har kin isa nazo gidan Yayana kina zagina, to ƙaryane baki koreahi ɗin bane? Kuma idan bai zo gidana ba duk duniya wayakeda shi da ya wuce ni, wato zakiyi ƙarya da ciki kina cin mutuncin munatane ko, to wallahi ƙarya kike yi yarinya. Kadijan ta faɗa itama ta na cire mayafin kafaɗan ta tana ɗaurawa a ƙuƙunta alamar shirin faɗa. Kasancewar su ɗin kusan sa’anye ne domin ko Kadija zata girmewa Ameera to sai dai ko irin da shekara ko watanni, domin ko auransuma tare a kayi, kuma dukkanninsu babu wacce Allah ya baiwa ciki sai yanzu da Ameera ta samu.
Jin abun da Kadijan ta faɗa ne yasa Ameera jin kamar an watsa mata garwashin wuta cike da fushi da jin cewar a zo har gidanta a naimi buɗe mata ido, ga kuma duk ƙuncin da take ji yazo ya tsaya mata a wuya bata son magana sam, hasali ma ita bata son ganin kowa a kusa da ita, hakan yasa ta ɗauke fuskar Kadija da mari wanda Kadijan batai tsammani hakan ba, shi yasa marin ya shige ta da kyau. Ji kake tass tass tass har sau uku. Sannan ta chakumeta ta watso ta waje ta rufo ƙofar gidan ta tana cigaba da zagin ta.
Ita kuwa Kadija tsabar shigan marinne yasa bata ma san lokacin da a ka watsota wajenba, sai ji tayi ta ƙara buga kanta a jin abun da bata san ko meye ba, ai kuwa take ta baje a gurin sumammiya. Cike da ɓacin rai Ameera ta ɗauki wayarta domin kiran Adam ta sauke masa kwandon masifar amma taji wayar na ƙara a cikin ɗaki. Sosai wannan karan ranta yayi mugu-mugun ɓaci, azo har gida a naimi cimata kashi. Ɗakin ta shiga ta ɗauki wayar tana ji kamar ta bugata da ƙasa, sosai take jin ɓacin rai fiye da kullum, ji take da Adam zai shigo gida yanzu da sai ta kusa ɓallashi tsabar ta kaici, yanzu kenan duk abinda sukayi sai yaje yana sanar da ƙanwarsa tsabar rainin hankali, to ko ita an faɗa masa bata da ƙannen ne, to Allah ya kawo shi gidan lafiya, ita kuma wannan ta nuna waje sai na yi maganinta bata san wacce ni ba. Haka ta zauna tana jiran shigowar sa.
Adam kuwa haka ya saka kayan Najib ya ɗauki motar Najib ɗin ya tafi gurin aiki, kasancewar Najib ɗin yau ba zai fita aiki ba saboda bashi da lafiya. Koda yaje gurin aikin yana ta tunanin halin da matar tasa ke ciki idan kuma ya tuna da cewar Kadija tana gidan sai hankalinsa ya kwanta. Yana aiki yana tunanin Allah yasa zuwan Kadija gidan yasa Ameera ta dawo asalin Ameeran sa, sosai halin da ta sauya yake damunsa daga jiya zuwa yau duk ya fita a haiyacinsa gashi yana son kiranta yaji halin da take ciki amma wayar tasa tana gida haka yaci gaba da aiki yana tunanin rikicin Ameera.
Ta kai minti ashirin a gurin kafin Baba mai gadi ya hango ta a kwance a gurin, hakan yasa ya nufo gurin da sauri domin yasan da shigar ta gidan. Cikin tashin hankali yake runtumawa Ameera kira bayan ganin jini ya wanke mata gaban fuska gaba ɗaya. Sosai yake kiran hajiyar tasa, jin bata amsawane yasa ya nufi ɗakinsa ya ɗebo ruwa a buta ya watsa mata,ai kuwa watsawa ɗaya ta ja wani dogon numfashi haɗi da buɗe ido. Daidai lokacin kuma wayarta ta fara neman ɗauki. Da sauri Baba mai gadi ya ɗaga haɗi da zaiyana halin da Kadijan ke ciki tun kafin ma yaji wanda ke kiran. Cikin tsananin tashin hankali Najib ya ke tambayar sa waye shi ɗin? kuma a wani guri suke? a rikice Baba mai gadi ya sanar da shi cewar shine mai gadin gidan Alhaji Adam kuma suna cikin gidan.
Ita kuwa Ameera ta na zaune ta haikince a Palo tana jiran shigowar sa sai taji Mai gadi na mata irin wannan kiran, far ko ta tsorata domin da ihuu ya kirata, har tayi nufin ta fita ta sauke masa buhun masifar dake cinta, amma tana buɗe ƙofar idon ta yayi gamo da aika-aikan da tayi , hakan yasa tayi saurin rufe ƙofar palon ta koma batare da mai gadin ya kula da itaba. Sosai ta tsotsa da ganin irin jinin da Kadijan ke fitarwa, zaunawa tayi tai shiru tana tunani, ko dai turata ɗin da tayi ne ta faɗi a kan ƙarfe, take jikinta yayi sanyi, amma har yanzu ƙasan zuciyarta zafi yake mata. Tana zaune a gurin har taji isowar ƙarar motar, ko bata leƙa ba tasan Najib ɗin ne yazo ya tafi da ita asibiti bata ko iya loƙowaba har suka bar gidan.
Misalin huɗu da rabi Adam ya turo ƙofar gidan haɗi da sallama yana wurga idanunsa cikin palon domin ganin ta ina zai hango ta. Ganin bai ganta bane yasa shi nufar cikin ɗakinta yana kiran sunanta “Honey…”Honey. Daga cikin kicin yaji ta amsa da “Na’am Honey welcome back. Har ya juya zai nufi kicin ɗin ya hango wayarsa a gefen gado, hakan yasa ya je ya ɗauka ya nufi waje cike da mamakin sauyin matar tasa, yana tafiya yana godiya ga Kadija domin yasan itace ta lallasheta. Yana shiga palon ya ganta sai girki take yi ita kaɗai ta haɗa zufa. Yana shiga ya rungumota ta baya yana faɗin “Waye ya saki girki keda baki da lafiya Honey?
Murmushi tayi haɗi da cewa “Ni lafiya ta ƙalau kawai girki nake marmari kuma na gargajiya.
Adam ya ce “To me kike dafawa ne haka? Cikin ƙosawa ta ce
“Kaje waje idan ya ƙarasa zaka gani ai.
“A’a ai tunda Allah yasa na dawo baki gama ba to sai dai na tayaki mu ƙarasa. Adam ya faɗa yana ƙoƙarin zagayowa ta gabanta. Ita kuwa Ameera gaba ɗaya ma bata son ganinsa hakan yasa cikin masifar dake cinta da take ta dannewa ta ce
“To sai kazo ka dafa kai ɗaya haba mana dan Allah na ce Kaje waje yanzu zai ƙarasa kazo ka dameni to gama kicin ɗin nan ka dafa harda kanka. Tana faɗa ta bar masa palon cikin ɓacin rai. Shi kuwa Adam da sauri yabi bayanta yana bata haƙur a kan wallahi zai fita, ita kuwa jin haka yasa ta ce yayi wanka zai kaita sufa makert zata sayo abun sha domin duk irin wanda take so ɗin sun ƙare. Jin haka yasa shi amsawa da sauri ya shiga ɗaki domin yin wanka ita kuma ta koma kicin domin ƙarasa aikin nata.
Tun lokacin da Ameera taji fitar Najib da Kadija tasan asibiti zasu nufa, hakan yasa ta fita da sauri ta samu mai gadi taja masa kunne akan kar ya sake ya sanar da Adam komai, kuwa da wasa ya sake ya ji to sai ya bar aiki a gidan. Shi kuwa Baba mai gadi jin haka yasa ya riƙa bakinsa da hannu a lamar ya kulle bakinsa. Gurin da Kadijan ta ɓata da jini tasa mai gadin ya wanke sannan ta shiga ɗaki ta ɗauki wayar sa tasa a jirgi (plane mode) sannan ta shiga kicin domin yin girki.
Ko kafin ya fito daga wanka itama har ta gama girkin ta zuba a plas ta rufe ta jera su a dainin tebul sannan itama ta shiga ta ƙara shiryawa. Yana fitowa itama ta fito cikin shigar abaya baƙa ta yane kanta da mayafin a bayar sai kuma baƙar jaka mai shigen kayan sai taƙalmi ja mai irin adon duwatsun gaban abayar. Batayi kwalliyaba amma ta ɗan shafa hoda, sosai tayi kyau ga ƴar ramar da tayi ya ƙara fito da haskenta.
Shi kuma sanye yake da riga da wando flawa yad masu ruwan ganye, sai hula mai shigen kayan sosai shima yayi kyau dukda bai wani tsaya ya gyara kansa sosai ba. Kallo ɗaya tai masa ta kawar da kai ta nufi hanyar fita. Amma jin tambayar da yayi mata ne yasa hantar cikinta kaɗawa. ” Wai ni Kadija har ta tafi ne daga zuwanta? Duk da razanar da tayi bai hanata dakewa ta ce “Eh ai bata dade ba ta juya wai tana sauri. Ta faɗi maganar hankalinta a kwance kamar batayi komai ba. Adam ya ce “Ok ai ina shigowa gidanan daga irin tarɓar da na samu nasan sister tazo gidanan. Ya faɗa daidai lokacin da ya ɓude mata motar ta shiga shi kuma ya zagayo ɓangaren direba ya shaga yana cigaba da yabon sister ɗin tasa. Ita kuwa Ameera ƙara ɓaci ranta keyi jin da gaske dai gulma ya kai mata shine yasa tazo. Sai yanzu ma take jin daɗin abun da ya faru da Kadijan Allah ma ya ƙara maganin masu gulma, sai yanzu ma take jin bata tsoron ya sani domin ko ya sani ai maganin magulmaciya tayi. Ganin ya ɗauko wayarsa zai sa a caji ne yasa ta kalli wayar taga har yazu a jirgi take hakan yasa taji daɗin cewar babu yanda za’ayi ya sani har sai gobe dan uban magulmaciya. Sosai ta cika tayi fam a cikin motar jin yadda yake ci gaba da yabon kirkin sister ɗin tasa jin yaƙi dainawa ne yasa ta ce “Wai dan Allah ko dai mu koma ne kaje ka ɗauko wannan kadijar sai kaci gaba da mata godiyar ne, haba dan Allah ni kazo ka dameni kamar wani kai ne kaɗai mai ƙanwa. Jin haka yasa Adam yin shiru yana kallonta ganin tana ƙara ɓata rai.
Bayan sun shiga sun maga sayan komai da take buƙata ne sun zo hanyar fita daga cikin supar makert ɗin sai ledar hannun wata ƙaramar yarinya ya suɓuce daga hannun yarinyar bai tsaya a ko ina ba sai a ƙafar Ameera, take ledar ta wargaje kayan ciki suka watse wanda Ameera ta je taka gurin da ake sauƙa, sai kawai bata ankaraba ta taka gwanganin matar ai kuwa sai ji kayi tayi sama ta dawo tim a kan gurin. Da ƙarfi ta saki iho wanda kowa na gurin saida ya tsaya yana kallonta. Da sauri Adam ya iso gareta yana mata sannu ya ɗagota tana kuka wurjanjan domin kuwa ta bugu. Kuka take yi tana kallon gurin da yarinyar ke tsaye da uwarta ko irin su zo domin ɗagata ma babu wacce tayi. Ai kuwa cikin ɓacin rai da zafin ciwo yasa tana tashi ta nufi gurin da yarinyar take babu wata-wata ta ɗauke ta da mari hanu bibbiyu. Tana kuka tana marin yarinyar a gaban uwarta, wacce hakan yasa itama yarinyar rushewa da kuka, Amera na kuka yarinyar ma tana kuka. Uwar yarinyar ce tayi kan Ameera domin ramawa ƴarta amma Adam yayi saurin shiga tsakiya yana baiwa mata hakuri. Ita kuma Ameera baki yaƙi mutuwa sai zagin uwar yarinyar take yi, itama uwar yarinyar na ramawa kamar zasu buɗa. Ganin haka yasa Adam juyawa ga Ameera ya ce “Wai wannan wani masifane ina miki magana amma bazaki saurareni ba. Amma Ameera sai ƙundumawa uwar yarinyar asher take yi. Uwar yarinyar ta ciro wayarta da ke ruri ta ɗaga ta na ɗagawa ta ce “Abban Hanifah ka shigo ciki wata mara kunya ce ta bari Hanifah. Ta na faɗa ta sauke wayar tana jin yadda Ameera ke cigaba da kutuntumu zagi kala-kala tana surfa mata. Babu yadda Adam baiyi da itaba amma taƙi yin shiru ƙarshe shima ta shiga surfa masa nasa masifar tana faɗin “Kana kallo zata kasheni baza kace komai ba sai ni da nazo ƙwatarwa kaina ƴanci shine zakace na yi shiru to wallahi baka isa ba idan ma bakinku a haɗe yake to nafi ƙarfi ku, Banza mara kishin matarsa kawai. Yau kam iya kunya Adam ya gama jin kunya jin irin zagin da take masa a cikin mutane.
Ana cikin haka sai ga wani gurjejen mutum sanye da rigar sojoji yana zuwa ya nufin gurin yarinyar da suka kira da Hanifah ya na zuwa ya rungumota ya fara lallasheta haɗi da tambayar waye ya taɓata kuma mai ya faru. Ai kafin yarinyar ta fara magana uwar yarinyar ta kwashe ƙarya da gaskiya ta sanar masa harda cewa wai ita da mijinta ne suka daki Hanifah itama harda zabga mata mari sannan ta rushe da kuka tana riƙe ƙunci. Ai kuwa wannan sojan jin haka yasa ya na juyawa ya ɗauke Adam da wani lafiyayyen mari ya riƙe kwalar rigarsa ya dinga zabga masa naushi, dukansa yake yi yana ihu yana ƙara masa, ita kuwa Ameera ganin haka yasa da gudu ta nufi gurin motarsu ta shiga, amma ganin kamar za’a biyota ne yasa ta fita daga motar ta tare mai a daidaita ta shiga ta bar gurin gaba ɗaya. Sai da wannan sojan yayi wa Adam ɗan banzan duka wanda har sai da bakinsa da hancinsa suka fitar da jini kafin ya barshi yana tambayar matartasa ina ita matar mutumin take. Nan suka naimi Ameera sama da ƙasa basu ganta ba, sannan sojan ya kalli Adam ya ce “Daga yau ka ƙara dukan matar wani dan ubanka idan baka da hankali, yana faɗa ya ƙara takurinsa a ruwan cikinsa sannan ya kama hannun matarsa da ƴarsa suka bar gurin.
Sai da ya bar gurin kafin mutane suka zo da sauri suka ɗaga Adam ɗin dake ta zubar da jini ta baki da hanci. Sosai ya daku ko tsayuwa ma baya iya yi, hakan yasa suka saka shi a mota suka nufi asibiti.