Skip to content
Part 24 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Ya ƙare maganar yana nuna Nuradden, likitan ya ce, “OK, ba damuwa, dama abinciken da muka yi mun gano kanta ya samu buguwa, wanda har jini ya tab’i cikin kwakwalwarta, shi yasa ta firgice ta fita out of her sense, a dalilin hakan dole sai an yi mata aiki an goge jinin sannan ne za ta dawo cikin hankalinta idan an dace, amman fa gaskiya aikin akwai had’ari sosai don d’ayan biyun ne ko a yi nasara ko kuma akasin hakan, wanda bama fata. Saboda rashin nasarar zai janyo abu biyu,; ko tab’in hankalin ya k’aru ko kuma ma a rasa rayuwarta gabad’aya.”

Mummy ta k’ara sautin kukanta, Basarake zuciyarsa ta shiga bugawa dam-dam! Saboda tsananin tashin hankali har sai da jijiyar kansa ta fito, a take ya ciro wayarsa ya fara rubuta text, minti biyu a tsakani text d’in ya shiga wayar Nuradden da sauri ya ciro ta jikinsa ya duba, saboda ya gano akwai magana tun daga kallon fuskar abokin nasa da kalar tashin hankalin da yake ciki, aikuwa sai gashi ya tabbatar saboda abin da ya ga ya turo masa.

_Ka yi amfani da damarka saboda a yi gaggawar fitar da ita waje nan da awa biyu masu zuwa._ 

A take Nuradden ya kalli Dr ya ce, “Za mu fitar da ita waje can a yi mata aikin.” 

Dr cikin farin ciki ya ce, 

“Alhmdllh hakan ma shi ya fi dacewa, bari na je a had’o muku file d’inta”

Dr ya fita da sauri Daddy da ke rakub’e jikin bango jikinsa ya yi sanyi k’alau saboda tsoron da ya shige shi, don ba ya son a ce shi ne ya yi sanadin mutuwar ‘yarsa da hannunsa. Yana jin maganar da Nuradden ya yi kaso mafi rinjaye na tashin hankalin ya ragu, sannan ya k’ara girma a idonsa linkin wanda yake da shi a baya, kuma ya ci alwashin da taji sauk’i ko sati ba za’a yi ba zai d’aura mata aure da shi, ko da son ta ko ba ta so, domin ba zai tab’a bari wannan dama ta sub’uce masa ba. 

Mummy kam hamdala ta yi a zuciyarta, saboda jin abin alkhairin da Nuradden zai yi masu na ceto rayuwar ‘yarta, haka kawai ta ji tana tausayin shi saboda yadda yake ta d’awainiya da ita kuma ba shi ne a gabanta ba. 

Cikin awa d’aya zuwa biyu Basarake ya yi wa Munawwa cuku-cukun zuwa wata babbar asibitin da ke k’asar India, tare da rakiyar Mummy, Munara, Nuradden tare da shi da da ya yi basajar rufe fuskarsa ruf, wajen saka wata jacket da hular da ta rufe fiye da rabin fuskarsa. Sannan ya k’wama k’aton bak’in tabarau ya zauna nesa da inda suke amma duk wani motsinsu a kan idanuwansa. 

Jirgin ya tashi da misalin k’arfe sha biyu da rabi na dare, ko da awa uku da rabi ta yi suna filin jirgin babban birnin India waton New Delhi, har airport motar asibitin ta zo ta d’auki Munawwa da aka yiwa allurar bacci wanda har a lokacin ba ta farka ba, kasancewar ba sa buk’atar d’an jinya ita kad’ai suka d’auka su Mummy suka bi Nuradden, suma wata motar ta zo ta d’auke su. 

Abin Mamaki sai ga Basarake cikin motar asibitin, hannunsa cikin na Munawwa ya k’ura mata ido sosai yana kallon yadda ta rame a cikin k’ank’anin lokaci, a take hawaye ya sirnano masa wanda ya manta tsawon lokacin da zai iya tuna ya yi kuka, amman sai ga shi yana sharb’ar hawayen tausayin abar k’aunarsa, yana rik’e da hannunta har aka je asibitin da shi aka saka ta d’akin da za’a yi mata gwajin kwakwalwa, wanda tun kafin su zo har an turo musu bayanin komai dangane da file d’inta, aikuwa ba b’ata lokaci suka shiga binciken kwakwalwarta, sai ga shi sun gano ba jini ba ne ya tab’i kwakwalwar ba, tsabar firgici ne ya janyo mata shiga halin ruɗuwa, nan take suka duk’afa wurin ba ta agajin gaggawa saboda suna hangen matsalarta mai sauk’i ce a wurinsu, cikin d’an lokaci suka shawo kan matsalar, sannan suka ajiye ta wani d’aki wanda za ta d’auki tsawon awa goma sha biyu kafin ta farfad’o, sannan sun yi hani ga kowa a kan ya matsa kusa da ita har sai lokacin da awannin suka cika, amman Basarake ya samu damar da zai zauna wurinta shi kadai, da sharad’in ko motsi mai k’arfi ba a son a yi balle har ta kai a yi mata hayaniya.        

Nuradden ya yi wa su Mummy bayanin ba a buk’atar d’an jinya akwai masu kula da ita, saboda haka su zo ya kai su masaukinsu don a lokacin dare ne su a wurinsu, Mummy ta kafe a kan ita dai tana son ta ga ‘yarta, sai da ya kai ta ta glass d’in k’ofar ta hango Munawwa da ke kwance sambal na’u’rori mak’ale a kanta da hannunta sai sharar bacci take da oxygen a hancinta dake k’ara taimakonta wajen zuko numfashi, numfashinta sai sauka yake a hankali, sannan hankalinsu ya kwanta Munara ma ta ji tausayin ‘yar uwarta sosai, Mummy kam hawayenta bai daina zuba ba har suka je inda aka tanadar musu, waton wata had’ad’d’iyar hotel ce wadda fad’in kyawunta a baki b’ata lokaci ne, sai da suka yi sallah suka ci abinci duk da Mummy tsakurawa kawai ta yi saboda alhinin yarta, sannan suka yi wanka. Munara kam bajewa ta yi tana ta baccinta bayan taci ta koshi, Mummy ta dukufa tana ta jero nafiloli tana rok’on ALLAH ya bai wa ‘yarta lafiya, ya yaye masu matsalolin da suka kunno masu kai da wad’anda suka dad’e cikin gidansu ba tare da an shawo kansu ba, don ta san ko an gama wannan akwai sauran wata rigima a k’asa, tun da dai kam Munawwa ba ta son Nuradden ga shi kuma Daddynsu sam ba zai canza ra’ayinsa ba, Musamman yanzu da ya ga wannan babbar bajinta da ya yi masu. 

A can asibitin kuwa, Basarake yana zaune sai sak’awa da kwancewa yake yi, yana wurin sallah ce kawai ke tayar da shi tare da rok’on ALLAH ya bai wa Munawynsa lafiya, abinci ma kwata-kwata ba ya jin sha’awar ci duk da ya ji an ce ciyon da sauk’i, amman ya fi son sai ya gan ta tashi garas sannan hankalinsa zai kwanta. 

Dak’yar wani likita, wanda akwai sanayya tsakaninsu ya shawo kansa ya d’an kurb’i tea a office d’insa, sannan ya dawo ya zauna yana jiran tashin ta sai duba agogo yake yi. Awa goma dam ta fara motsa k’afarta cikin tantama ya k’ura wa k’afar kallo, aiko sai ga shi ta k’ara motsa hannunta da sauri ya fita ya kira Doctors suna zuwa suka tarar da ita dafe da kanta da hannunta d’aya da ba a saka wa komai ba, tana yamutsa fuska alamar tana so ta bud’e idonta, da sauri wani likitan ya cire mata na’u’orin da aka mak’ala a kanta, ta bud’e idonta tana k’are wa d’akin kallo, caraf idonta suka sauka a kan fuskar honey’n Munara dake tsaye yana kallon ta, Murmushi kwance a kan fuskarsa babu shiri ta runtse idanuwanta gam ta k’i bud’ewa har sai da ta ji k’arar rufe k’ofa sannan ta bud’e. Sai ga d’akin babu kowa sai ita kad’ai, ta nutsa sosai domin ta gano ina take, k’arar wata na’ura dake d’illll! d’illll ta d’aga kai ta kai kallonta ga na’urar tare da k’ok’arin tab’o ta da hannunta dake mak’ale da k’arin ruwa, zafin da ta ji ya ziyarce ta ne ya sa ta d’ago hannun tana kallon ruwan da ke mak’ale da shi, sai a lokacin ta tabbatar wa da kanta a asibiti take, nan take ta tambayi kanta a zuciya ta ce,, _”Ta ya ya? Kuma ni me ya kawo ni asibiti kuma?_

K’arar bud’e k’ofar d’akin ne ya dawo da hankalinta a kan k’ofar, ya doso gadon da take kwance fuskarsa cike da yaltaccen murmushi, da sauri ta sake runtse idonta da karfi saboda tsammaninta ko mafarkin da ta saba yi ne, sai kuma ta ji an rik’o hannunta da sauri ta sake bud’e idonta suka sauka akan fuskarsa, ta k’ara bud’e idanuwa tare da tsayar da su a kansa, mamakinta ya k’aru lokacin da ta ji ya duk’o ya sakar mata kiss a goshi, kuma har a lokacin murmushi kwance a kan fuskarsa, saboda tsananin farin cikin da yake a ciki, domin Doctors sun sanar da shi ta samu lafiya nan da kwana biyar idan sun ga brain d’in ta yi normally sosai za a sallame ta. 

Munawwa ta d’ago fuskarta daga kwancen tana k’are masa kallo, zuciyarta ta tabbatar mata da cewa _”Lalle shi ne HAIDAR d’in Munara, to shin ita mene ne had’inta da shi ne? Kuma ina Mummy da suka bar ta ita kad’ai ko dai ya yi tunanin Munarar ce?”_

Ta matsu ta san amsar tambayoyin, ta bud’a baki da nufin ta tambaye shi wani sak’o ya shigo wayarsa, da sauri ya fiddo wayar a aljihu ya duba, yana ganin abin da ke ciki ya mayar da wayar da sauri, ya k’ara duk’awa ya sakar mata kiss a baki sannan ya ce, 

“Congrats my heartbeat.” 

Sannan ya juya ya fice d’akin da sauri ko minti biyar ba a yi da fitarsa ba, Mummy, Munara tare da Nuradden suka shigo, Munawwa ta kasa gano meke shirin faruwa da ita, saboda wannan muryar da ta ji ya yi amfani da ita wurin yi mata magana, da ita Aliyunta yake yi mata magana wani lokaci. Shin me hakan yake nufi? Ta yi imani ko kad’an ba danganta ko alak’a tsakaninsa da Haidar d’in Munara balle ta ce ko ‘yan’uwa ne, to ko da ‘yan’uwa ne ai bai zama dole sai sun yi murya d’aya ba, babu shiri ta dafe goshinta a fili tana furta, “Shin me ke faruwa da ni ne? Anya ba aljanu ba ne suke damuna ba kuwa?”

Da sauri Mummy ta k’araso cike da farincikin ganinta ta ce, “Ba wasu aljanu ki kwantar da hankalinki duk inda kike ina tare da ke.”

Munawwa ta kai kallonta ga Mummy wani sabon hawaye yana zuba a kan fuskarta, wanda ba za ta ce ga ko na mene ne ba. Mummy ta rungume ta tana lallashinta, Munara ta fito d’akin ba tare da ta ce da ita k’anzil ba, ta je kan wata kujerar silba da ke ajiye corridon ta zauna tana wulla idanuwa tana kallon mata da mazan Indiya da ke safa da marwa a cikin asibitin sai kai komo suke a wurin, caraf idanuwanta suka kai kan fuskar wani da ke fitowa office d’in dake gabanta tare da wani Dr suna magana, juyowar da zai yi da nufin ya bar wajen ta yi tozali da honey’nta. Da sauri ta bud’e ido tare da murza su, kafin ta tantance ya yi mata nisa da gudu ta bi bayansa tana kiran sunan HAIDAR, amma duk da ya gan ta kuma ya ji sunansa da take kira bai sa shi ya juyo ba, har sai da ya kai inda mutane ba sa yawan zirga-zirga sannan ya tsaya yana latsar waya kamar bai san tana biye da shi ba, tana zuwa ta ja ta tsaya gabansa tana haki tare da dafe gabanta da ke tsananin bugawa ta ce, “Honey?” 

Ya yi saurin kai kallonsa gare ta a cikin ko in kula ya ce, “HAIDAR dai”

Ta zaro ido a waje ta ce, “Kana nufin daman da gaske kake yi za ka iya rabuwa da ni?”

A cikin kallo mai cike da raini ya ce, 

“Kin ga zahiri ai.”

Babu shiri ta cakumo shi tana wani masifaffen kuka ta ce, “WALLAHI ka yi kad’an ka ce za ka yaudare ni! Ni za ka gudu…to me na yi maka? Wallahi ka sani tun da nike son ka sai ka aure ni ko ba ka so! Ko kuma na mayar da kai abin kwatance daga kai har matar da tsautsayi zai hau kanta.”

Cikin zafin nama ya fisge daga wawan rik’on da ta yi masa tare da mazga mata wani arnen mari, sannan ya nuna ta da yatsa ya ce, “Ko da wasa kika sake kika koma kawo kanki inda nake to ki sani zan yi ajalinki.”

Yana k’are maganar ya buga mata tsaki tare da yi mata wani kallo mai cike da gargad’i sannan ya yi fuuuu ya bar wajen, ta bi shi da kallo baki a sake….

<< Bakon Yanayi 23

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×