In Ajali Ya Yi Kira
Tun da suka shiga motar Salmanu ke kallon wayar da ke hannun matashin da wani irin mugun nufi. Tun da yake ƙwacen waya bai taɓa ganin wayar da ta shigar masa rai irin wannan ba. Wataƙila saboda bai taɓa ganin irinta ba ne. Amma dai ya ji kwaɗayin wayar ya shige shi. Tabbas ba don a mota suke ba da babu abinda zai hana shi ƙwace wa matashin wayar nan ko ta halin ƙaƙa ne.
Daga Jos suke za su je Kaduna, kuma tun da suka shiga motar matashin ke latse-latse a cikin wayar. Wannan abu kuwa ba ƙaramin jan hankalin Salmanu yake ƙara yi ba. Ji yake kawai kamar ya fizge wayar ya gudu. Ya sha yin hakan ya fi sau a ƙirga. Lashe baki kawai ya yi kamar tsohon maye, a cikin zuciyar shi kuma yana addu’ar Allah ya kawo dalilin da zai samu damar sace wayar nan. Shi kuwa wannan saurayi, mahaifin budurwarsa ne ya rasu zai je yi mata ta’aziyya. Har ce mishi ta yi ya barshi tunda har sun yi waya da mahaifiyarta ya yi mata ta’aziyya. Amma ya nace shi dai zai zo yi mata ta’aziyyar addu’ar sadakan bakwai.
Sun wuce Gadan Gayan kenan sun kusa isowa Amuna Mai Maɗaci sai kuwa motar ta ƙwace wa direban. Ya yi iya ƙoƙarinsa amma ina. Abin ya fi ƙarfinsa. Nan take motar ta ƙwace da wani irin gudu, sai da ta yi tambul ta wuntsula sau uku sannan ta je ta bugi wata bishiyar ɗorawa. A wannan lokaci tuni mafi yawancin mutanen da ke cikin motar sun mutu. Shi kanshi direban kunnen shi ɗaya ya fita. Wata mata kuwa da ta yi ƙoƙarin fita ta tagar motar, gilashin motar ne ya fasa mata kai kwanyarta sai zuba take yi. ‘Ya’yanta guda biyu kuwa mace da namiji duk sun rayu. Sai dai macen gashin tsakiyar kanta ya tuge gaba ɗaya. Shi kuwa namijin gefe fuskarsa na ɓangaren hannun dama ne ya gurje.
Shi kuwa Salmanu wani ƙarfe ne ya shige cikin cinyar ƙafarsa ta dama ya fito ta ɗayan ɓangaren. Ga wasu ciwuka kusan guda shida a kansa kowanne na zubar da jini. Amma shi kuwa wannan saurayi mai waya, tuni rai ya riga ya yi halinsa. Bai samu rauni ko ɗaya ba face buguwa, hannunsa na riƙe da wayar. Wani abin ikon Allah kuwa babu abinda ya samu wayar.
Salmanu kuwa da ke ta faman numfashi da ƙyar, rai a hannun Allah. Ko da ganin cewa wannan saurayi ya mutu. Sai ya miƙa hannu da nufin ya zare wayar daga hannun saurayin. Ya kai hannu kenan, har ya fara zare wayar. A daidai wannan lokaci ne shi kuma Allah ya aiko Mala’ikan mutuwa ya zare masa rai.