Ƙaramin ɗakin taro da ke gefen masallacin mata, a Babban Masallacin Jumma’a na Ɓukur ya ƙayatu sosai, kamar ba shi ba. An shirya kujeru cikin da’ira kowacce kujera an lullube ta da farin yadi mai santsi, ga jikin bangon wajen taron an kewaye shi da ado da yadi mai launin ruwan hoda (pink) da mai launin ruwan ƙasa da fari.
Daga saman teburin da aka sa a gaban kujeru uku na manyan baki an dora wasu jajayen furanni da ke jere a cikin wani farin karamin kwando na roba, sun kara ƙawata wajen. Sautin karatun Alƙur’ani mai girma na fita a hankali daga lasifikar da aka sanya a cikin ɗakin taron, don amfani da amsa-kuwwa da zai isar da saƙo ga duk wanda ya ke cikin ɗakin taron.
Daga waje kusa da bakin ƙofar shiga Hadiza ‘yar agaji ce sanye da fararen kaya da koren hijabi na masu aikin agaji a Babban Masallacin Jumma’a tana taimakawa wajen faɗakar da baƙi su wanke hannu a robar da ke gefenta wanda aka sa ruwa mai haɗe da sinadarin kashe ƙwayoyin cuta, a hannun ta kuma ta riƙe wata doguwar roba mai ɗauke da wani sinadari mai launin ruwan garai, da ake shafawa a hannu, don kashe ƙwayoyin cuta, wato hand sanitizer.
Duk wacce ta wanke hannu kafin ta shiga sai Hadiza ta fesa mata wannan sinadarin ta mitstsika a hannu sannan ta wuce. Da alamun waɗanda suka ba da shawarar a gayyato Hadiza ‘yar agaji don ta tsare bakin kofa sun yi dabara, saboda kuwa kowa ya ganta ya san ta wuce raini. Dirarriyar mace ce mai tsayi da jiki, wacce ba a saba ganin murmushi a fuskarta ba. Ko da yake a zahiri duk wanda ya kusance ta zai gane ba muguwar mata ba ce, kuma tana da raha da barkwanci, amma yanayin fuskarta na tsare gida yana tsorata ba mata kaɗai ba, har da maza.
A gefe guda kuma dogon layi ne na mata sanye da dogayen hijabai masu launi daban daban, wasu na rike da hannun yara ƙanana wasu ɗaiɗaiku kuma da goyon jarirai a bayan su. Ga wanda bai sani ba, idan ya zo wucewa ya ga yadda mata suka yi dafifi a ƙofar shiga masallaci ta bangaren mata, zai yi zaton ko taron addini ake yi, kamar wa’azi ko tafsiri. Cikin natsuwa matan ke shiga ɗaya bayan ɗaya, suna kuma ba da haɗin kai ga yadda aka tsara zaman jama’a a wajen.
A ƙarƙashin wata bishiyar mangwaro da ke gefen masallacin, wasu masu Keke Napep ko A Daidaita Sahu, su uku suka tsaya. Wasu mata su bakwai suka fito, biyu daga cikin su ne kawai ba su sanya hijabi ba, amma duk sauran kowacce da irin nata samfurin kwalliyar da aka dora mata hijabi a kai, masu dogayen hijabai da masu karami.
Su kuma waɗancan biyun da alamun ‘yan mata ne, saɓanin sauran matan da suka ɗan manyanta, sun sa dogayen riguna ne na shadda waɗanda aka yi wa adon zare a jiki, a kafadar su kuma sun sa hijabai kanana da ba su sauka zuwa kirjinsu ba. Wata daga cikin manyan matan ta fito da kuɗi daga ‘yar ƙaramar jakar da ke hannunta ta biya masu babur din da suka kawo su, sannan suka juya suka nufi ƙofar masallaci.
Hankalin sauran matan da ke tsaye suna layin wanke hannaye ya koma kan zugar matan da suka nufo su. Kusan kowaccen su idanunta na kan mace ɗaya ne, wacce kuma ko daga shigarta ta bambanta da sauran.
Ga kwarjini, ga kuruciya da taku mai ɗaukar hankalin duk wanda ya shagaltu da kallonta. Ruƙayya! Tana daga tsakiya, a gefen damarta mahaifiyarta ce da suke kira Ummi, sai kuma Aunty Amina kishiyarta tana daga gefen hagu, sai kanwar babarta Hajiya Hauwa da babbar yayarsu Sumayya, sai babbar aminiyar ta, Zainab, da kannenta mata biyu, Hassana da Hussaina. Suna isa daidai inda matan suke tsaye cikin layi za su shiga cikin ɗakin taron sai ta yi musu sallama, tare da yi musu maraba, tana yi musu godiya da samun damar halartar wannan taron Birthday da ta kira.
A daidai lokacin ne kuma wata babbar mota baƙa, kirar Jeep ta tsaya a daidai ƙofar shiga masallacin, gaba ki ɗaya kuma sai kallo ya koma kansu. Daga kowanne bangaren kofa aka buɗe wasu manyan mata biyu suka fito. Kowacce ta sa manyan hijabai ta rufe fuska da niqabi. Daya ta sa kaya mai launin ruwan goro, dayar kuma ta sa nata mai launin ruwan ganye mai duhu, wato dark green.
Malama Nafisa Sautus Sunnah ce da Malama Karima Adam. Wasu manyan malamai mata da suka shahara a sassan Jihar Filato da makwaftan jihohi, inda suke zuwa hidimar yaɗa koyarwar addinin Musulunci bisa tafarkin Sunnah, musamman a tarukan mata, da suka shafi saukar karatu ko walimar bukin aure.
Malama Karima har wa yau babbar malama ce a Kwalejin Horar da Malamai Mata ta Arabiyya da ke karkashin kungiyar Jama’atu Nasril Islam da aka fi sani da Kulliya, kuma mijinta ne Alkalin Alkalan kotunan shari’ar Musulunci da ke Jos. Kuma wannan motar mijinta ne ma ya sa a kawo su wajen wannan taro, wanda babbar aminiyar ta Malama Nafisa Sautus Sunnah ta garin Bukur ta gayyace ta.
Ita kuwa Malama Nafisa da ake wa lakabi da Sautus Sunnah fitacciyar malama ce da ke harkar wa’azi da karantarwa. Mata da dama sun santa saboda yadda take tsatstsayar wa mata bisa abubuwan da suke sakaci da shi game da ibada, tarbiyyar yara, da zamantakewar aure. Saboda yawan gayyata da take samu daga gari gari, ba kasafai ake ganinta a ƙananan tarukan irin wannan a cikin gari ba. Ko yanzu ma da ta zo ba ƙaramar sa’a aka ci ba, don dai tana tsananin jin nauyin tsohuwar abokiyar karatunta ce, wacce kuma suka taso tare, wato Hajiya Sa’adatu Mohammed wacce ita ce mahaifiyar Rukayya, yarinyar da ta shirya wannan liyafa, don murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Babu shakka ta ji daɗin yadda ƙawarta Hajiya Sa’adatu ta bata labarin yadda ‘yar ta Ruƙayya ke da shauƙin son addini da kishin faɗakar da ‘ya’ya mata da ke tasowa, a wannan rikitaccen zamani da aka samu kai a ciki, na taɓarɓarewar tarbiyya da ƙaryar wayewa. Cikin fara’a da sakin fuska, Rukayya da mahaifiyarta suka tarbi waɗannan manyan baƙi nasu, yayin da suka rungumi juna suna gaisuwa irin ta manyan matan da suka gina rayuwarsu kan ilimi da riƙon addini. Sai ruwan larabci ake yi, tsakanin malaman da Hajiya Sa’adatu, mahaifiyar Rukayya, wacce ita ma tsohuwar malamar mata ce a makarantar Higher Islam da ke garin Bukur.
Ruƙayya kuwa sai washe baki take yi cikin fara’a da jin daɗin halartar waɗannan manyan baƙi nata, waɗanda ko da wasa zuciyarta ba ta gama gamsuwa da za su zo wannan taro nata ba, ganin cewa ita ba kowa ba ce. Duk kuwa da yadda mahaifiyarta ta yi ta ba ta ƙwarin gwiwar cewa za su zo.
Idan akwai wata mace da Ruƙayya ke yi wa kallon madubi abin kwaikwayon ta bayan mahaifiyarta to, Malama Nafisa ce, saboda yadda take matuƙar burgeta da jin daɗin wa’azin ta. Ko a cikin wayarta ma tana da karatuttukan ta sun kai goma, wasu dogaye wasu kuma ƙanana da aka raba su, gwargwadon darussan da ta yi magana a kai.
Wani abu da yake burge Ruƙayya game da wa’azin Sautus Sunnah kuwa shi ne, kowanne darasi aka bata ta yi magana a kai, tana da wata irin baiwa ta saje wa da tafiya daidai da fahimta da wayewar waɗanda ke sauraronta. Idan manyan mata ‘yan boko take yi wa wa’azi sai ki rantse duk rayuwar ta a turai ta yi, haka idan masu ƙarancin wayewa ne, sai ki zaci ba ta san hanyar Abuja ba ma, ballantana idan yaran mata ne ko ‘yan mata da ke tsakiyar tashen ‘yam matanci, ai nan ne ma abin mamaki, haka za ta kwantar da kanta tamkar yayarsu ce da ba ta wuce shekara ashirin ba zuwa ashirin da biyar. Alhalin kuwa a zahiri ta bai wa arba’in da biyar baya.