BABU NI BABU AURE!
Ya jima yana ƙare ma hoton kallo,sai kuma ya mike tsaye tamkar wanda a ka tsikara da allura. Makullin motarsa ya ɗauka,bai saurari mai-gadi dake faman tambayarsa ko lafiya ba ya fice daga harabar gidan a guje.
“Sai na nemota,ita ce rayuwata! Ina son ki Jidda soyayya mai tsanani.”
Ya faɗi haka a fili yana mai zubda kwallah tamkar wani ƙaramin yaro.
*****
Ganin motar na neman kubce mata yasa tai koƙarin sai ta kanta.
“Ina son ki Jidda soyayya mai tsanani.”
Kalmar tai ta mata amsa kuwwa a cikin kunnuwanta.
Yayyafin da a ka fara yasa tai saurin fara rufe gilasan motar.
Dai dai nan idanunsa suka ƙara hango ma shi kyakyawar fuskar da yake fatan ƙare rayuwar shi da ita.
Wata babbar mota ce ta gifta tsakaninsu,a hasale ya fito idanunsa ɓoye cikin wani bak’in gilashi,hakan ba zai hana ka fahimci irin bacin ran da mai babbar motar nan ya jefa shi ciki ba.
“Amma giyar burkutu ya birkita maka kwakwalwa ko?”
Wani tsalle yayi ganin direban babbar motar na neman take shi,kura ya bada ma sa cikin idanunsa,ya ƙara gaba bai ko waiwaye shi ba.
“Rai na fansa gareta! Amma ba yanzu ba,sai na rayu da ita! Ita ce uwar ‘ya’yana,abokiyar rayuwata,amintacciyata,kuma babbar aminiyata! Ina son ki Jidda!”
Dr Sani ya ƙarasa faɗin haka yana ƙarasowa gefen hanya yadda ya faka motarsa. Ruwan eva ya ɗauka ya ɗaga bakin goran sama yana zubawa cikin bakin sa. Wani sanyi ya ji yana ratsa dukkkan ilahirin jikin shi.
“Akwai nasara! Ina gab da mallakarta,” ya furta hakan sa’ilin daya ajiye ruwan yana koƙarin tada motar.
*****
“Lale marhabin da bak’in yamma.”
Matar dake zaune a ɗaya daga cikin lumtsatsun kujerun da a ka ƙawata falon ta furta fuskanta k’war da annuri
“Mama ina yini?” Jidda ta furta hakan cikin Hausar Katsina daya gama rike mata baki
“Ba zan amsa gaisuwar ki ba Jidda! Jikokina kaɗai zan amsa mawa! Na san Safna ce ta kira ki a waya,ba dan haka ba da sai dai ki aiko min direba da yara.”
“Laaa Aunty Safna ta zo?Kin ga ko bata faɗamin ba Hajiya Mama,ina take?”
Jidda ta tambayi Hajiya Hadiza tana koƙarin mikewa.”
“Ai dama na faɗi sabida ita ki ka zo! To tana falon Alhaji ita da waɗan nan buyagin ‘ya’yan nata,ki ƙarasa ke da yaran ku gaishe shi,don ya kusa fita masallaci.”
“To Hajiya bari mu fito.”
Jidda ta ƙarasa tana yafito Mufid daya lafe a jikin Hajiya Mama.
“Ameen wa’alaikis salam”
Safna da mahaifinsu Alhaji Taheer suka haɗa baki wajen amsa sallamar Jidda
“Daddy barka da yamma! Ya aiki?.”
Kan Jidda a ƙasa ta furta hakan,
“Barka ka dai Jidda. Aiki kin manta muna hutu? Ya mutanen gidan?”
“Duk suna lafiya sun ce a gaishe ku daddy.”
“To..to to muna amsawa.”
Ya ƙarasa maganar yana janta.
“Yaran ki ne suka dameni,wai lallai sai dai mu taho tare,to dake Daddy yai tafiya zuwa Abuja shi ne fa muka rufo gidan gaba ɗaya,Jidda wai wani abu nai maki ne ki ke gudun zuwa gidana? Safna ta ƙarasa maganarta tana mik’ewa da niyyar su bar falon.
“Mummy kinga Ammar ya dake ni ko?” Mufid ya ƙaraso da gudu yana shirin yin kuka. Hamdala Jidda tayi.
Muhib ya taimaketa daya katse tambayar da Safna ta jeho mata. Don bata da amsar tambayar.
Safna kuma bata gajiya da ganin rashin kyautatawarta. Ita ba mutum ce mai son hayaniya ko yawan jama’a ba. Yau da gobe ne…shi ne yasa ta fara sakewa da mutane tana koƙarin shiga cikin su.
Tai saurin kawar da wannan tunanin lokacin da suka ƙarasa falon
“Safna yau dai na ci albarkacin ki,yaushe rabon Jidda da gidan nan? Gaskiya ki dinga yi mata faɗa,zumunci ai shi ne mutum!”
“Hajiya nima ai ba zuwa gidan nawa take ba,sai ta shafe watanni idan har ba gidan Aunty Mami naje ba ban sanyata cikin idanuna ba,ni da muka zauna tare ma kenan tsayin wasu shekaru. Baki ga yadda Ihsan take damuna a kan Mufida ba,jinin su ya haɗu,kallassu fa,yadda suke farin cikin ganin juna,tare suka ɓudi ido suka ga junansu,kin manta Hajiya? Yan uku kowa ke kiran su,komi iri ɗaya a ke sanya masu a wancan lokacin,ko dan albarkacin wannan ai kya dinga kawo su suna mana ko weekend ne,tinda can gidan ba yara ne akwai ba”
“Zan gƴara in sha Allah. Yanzu ma da shirin kwana na taho..”
“Da gaske ki ke?”
Safna ta tambaya tana gƴara ma ɗanta data gama shayarwa kwanciya.
“Da gaske nake mana,mu ƙarasa ciki mu je mu yi sallah,lokaci ya gabato”
Tare suka fice daga falon. Dakin Safna kafin tai aure suka wuce,a gƴara yake tsaf yanata zuba ƙamshi,dama nan take sauka duk lokacin da tazo.
Sai ƙarfe takwas suka fito falo. Dinning suka nufa,Safna ta zuzzuba ma yaran abinci. Ihsan da Mufida filet ɗaya suke cin abincin. Daddy babban Ɗan Safna wanda yaci sunan mahaifinsa Alhaji Umar ya mik’e yana faɗin tare da kakansa zai ci abinci idan ya dawo daga masallaci. Mufid sarkin rikici duk yadda Ammar yai su ci tare yak’i yadda. Yana shirin tsoma hannu a nasu Jidda da Safna ta haɗa masu Jidda tai masa magana da tsawa
“Kul idan ka kai abincin nan bakin ka Mufid. Idan ba za ka ci da Ammar ba ɗauki naka,me yasa kullum ka ke abu kamar ƙaramin yaro?”
“Yaron ne mana,guda nawa yake? Abokina ta so mu je yau tare zamu ci abinci ka ji?”
Jin maganar Alhaji Taheer yasa Jidda yin ƙasa da kai. Tare suka haɗa baki da Safna
“Daddy barka da shigowa.”
“Sannun ku dai.”
Ya furta hakan yana mai jan hannun Muhib ba tare da ya kuma cewa wani abu ba suka nufi ɓangaren da falon sa yake.
“Wai nikam Dakta sai yaushe ne zaki tsayar da mutum ɗaya cikin maneman ki? Zaman bai da wani amfani ai,ni da har na fara tunanin yin…”
“Yin me? Me yasa ku ke da son takura ne wai Hadiza?”
Muryar Alhaji Taheer mijin Hajiya Hadiza ya katse mata hanzarinta.
“Alhaji ai gani nai kullum lokaci ƙara tafiya yake..”
“Komai lokaci ne,da zarar lokacin yayi zaku sha mamaki.”
Ya ƙarasa yana rike da hannun Mufid suka fice daga falon. Mamaki ya hana Hajiya Hadiza cewa komai. Sam Alhaji Taheer bai da yawan magana ko tsoma baki a batun da ba a sako shi ciki ba. Amma sai gashi yau yana mata magana gatsal har da kiran sunanta babu kara kamar yadda ya saba.
Tai saurin kawar da zancen ta hanyar barin falon. Jidda kuwa wani dadi ne ya kamata ganin Alhaji Taheer ya katse maganar da Hajiya Hadiza ta zo da shi. Sai dai tana tuno maganganun Hajiya Mama tai saurin mikewa kanta na sara mata.
“Haɗata da wani su Hajiya ke son yi bata da labari? Ko shi yasa Mami tace Hajiya Mama tace ta kawo mata su Mufida?”
Tunanin hakan da tai zuciyarta ta fara lugude,ta ke taji komi ya fice mata a rai. Da sauri ta bar falon ko hanya bata iya gani sosai.
“Kina tunanin zaman ki ke kaɗai shi ne mafita Jidda?”
Safna ta ƙarasa tambayar tana zama bakin gado kusa da Jidda.
“Ke ma kin san komai amma ki ka ɓoyemin ko? Aurar dani su Hajiya ke son yi ba tare da sani na ba? Faɗi min don Allah wa su ke son haɗani da shi? Na sha faɗi ma Hajiya cewar babu ni babu aure har abada”
“Ya isa haka Jidda!!” Safna ta faɗi hakan a ɗan tsawace. Aure kuwa ya zama dole,don shi ne cikar burin duk wata ‘ya mace..”
“Nawa bururrukan sun gama cika Safna! Buri ɗaya ya rage min a duniya,wanda na tabbata nai ban kwana dashi kenan har abada! Ki kalli girman soyayayyar dake tsakanin uwa da ɗanta! Amma tawa mahaifiyar ta ya dani tsayin shekaru ba tare data ƙara waiwayo ni ba,kin san komai Aunty Safna.
“Na sani Jidda! Amma ke ma uwa ce! Uwa kuwa uwa ce duk lalacinta,ki ka san tana a raye ko a mace? Ki ka san hujjanta da dalilinta na rashin waiwayo ki tsayin shekarun nan? Ni na tabbata akwai wani ɓoyayyan dalili,wanda Allah kaɗai ya bar ma kansa sani,batun aure kuwa da ki ke magana su Hajiya ba sa shirin haɗaki da kowa! Sai dai girman soyayyar da suke maki da tausaya maki yasa su ke son ganin ke ma kin samu nagartaccen namiji,kamili domin ki huta,komai yai farko yana da ƙarshe,ki nemi zaɓin Allah kawai,amma ki daina faɗin babu ke babu aure,kar wata rana in zo gidan ki ki koreni sabida dadi mijirodo.”
Safna ta ƙarasa tana dariya,yanayin yadda taƙarashe maganar har Jidda sai da ta dara,dama abinda Safna ke son gani kenan. Haka su ka cigaba da tattaunawar su kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu.
*****
Tinda suka idar da sallar asuba suka shige kicin,sai da suka kammala komai suka gƴara kicin din tas! Kafin ƙarfe takwas sun shirya yaran. Safna ce ta fito daga wanka tana goge fuskanta da ƙaramin towel,tana cire towel ɗin tai idanu biyu da Jidda,tana zaune a gaban madubi ta gama ɗaurin ɗankwalin daya dace da kayan jikinta. Sanye take da atampa cote d’ivore,kore da ruwan madara,tai matukar yin kyau sosai,duk da ba kwalliya tayi ba,powder da man baki kaɗai ta sanya. Safna tai dariya tana faɗin” Babu ni babu aure wannan gayun fa? Yo ai in dai zaki yi wanka ki fita cikin jama’a ko ba soso da sabulu sai kin auru,wai nikam ma ya labarin Dr Jb bawan Allah? Har yau bai hakura ba?”
“Bai da aikin yi ne shi yasa,kinsan Allah tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin mutum mara zuciya irin sa ba. Na faɗi masa babu ni babu aure amma sam ya’ki ya rabu dani,ga Dr Salima Salis nan,har hawan jini ta samu sabida soyayyar da take ma shi,hmm kin san me? Ko fa magana bata min yanzu,wai tin zuwa na asibitin farin jinin da ta ke da shi wajen kowa ya rage,har text messages na zagi fa tasha turomin su,na ce iska na wahal da mai kayan kara,don ni ba Dr Jb ba,ko wani ɗa namiji baya gabana,ko da kuwa da ruwan gwal a ka ƙerashi.
Dariya sosai ya kwace ma Safna.
Cikin dariyar ta fara magana.
“Kin san in da ni ce ke abinda zanyi?”
“Aa sai kin faɗi.”
Jidda ta amsa ma Safna da sauri. Don zatonta wata shawara zata bata da zata rabu da baƙar nacin Dr Jb har abada
“To da ni ce a matsayin ki da gudu zan amsa tayin Dr Jibrin ne ko Jb ku ke kiransa,Jidda ki yarda da shi,ku fara soyayya ko ta wasa ce mana,ni wallahi ban ga aibun Dr Jb ba sam! Yana da natsuwa da hankali,duk cikin likitocin dake ɓangaren ku na yaba da hankalin sa sosai”
“Ya na da hankali da natsuwa nima na san da haka amma dake…”
“Babu ke babu aure har abada..”
Duka Jidda ta kai ma Safna,tai saurin gocewa tana dariya.
“Ku na nan har yanzu ba ku fito ba,ya kamata ku zo ku sallami ‘ya’yan nan na ku,ga su can falon Alhaji sun dame shi,Ihsan da Mufida kuwa duk sun sha ado a nata ma sa kwainane,to kwalelen ko waccensu.”
“Hajiya ki ce kishi ki ke kawai! Ai gwara ya ƙaro biyun rana ɗaya kya samu masu taya ki hira da aikin gida”
Safna ta ƙarasa maganarta tana koƙarin zama a stool ɗin madubin da Jidda ta tashi.
“To Suda sukari sai ki fara haɗa masa lefe,Allah ya kawo su da alkhairi.”
Hajiya Mama ta faɗi tana barin ɗakin fuskanta ɗauke da murmushi
“Wannan kwalliyar fa Aunty Safna? Sai ka ce yau daddy zai dawo.”
Jidda ta faɗi haka cike da zolaya.
“Ke dai tsaya nan,mu da muka doshi hamsin ma muna kwaliya bare ke,hmmm ƙanwata dadi na dake kafiya,wannan ne kawai nakasun dana san ƙanwata tana da shi”
“Ba za ki taɓa ganewa ba yayata,duk da nasan kina fahimtar duk wani karatun kurmanci na! Goyon bayan ku da ƙarfafawar ku na cikin abubuwan da suka jagoranci tafiyata har zuwa wannan lokacin! Ku ne sila! Da bazar ku nake taka rawa! Dr Jidda Abubakar ba za ta taɓa mance girman alkhairin ku a gareta ba…
Hawaye ya ci ƙarfin Jidda. Da azama Safna ta ƙarasa gareta tana share mata hawayen.
*****
Ya kai gwauro ya kai mari,hannayensa sarƙafe a bayan sa. Tabbas ita ce! Ba zai taɓa mance fuskar ba. Fuskar da ko a cikin ciwon makanta zai iya tantanceta bare kuma da idanunsa tar masu kyau da haske. Fuskar daya ɗauki tsayin shekara tara da wata bakwai da kwana goma sha biyu yana dakon sake arangama da ita. A kanta mutane da yawa su ka ɗauke shi tamkar mahaukaci wanda baya cikin hayyacin sa. Fuskar da sau biyu tak ya taɓa sanyata cikin idanunsa,amma ji yake tamkar shi ɗinma kansa an hallice shi ne sabida mamallakiyar fuskar!Soyayya yake mata wanda a ke kira da Love at first sight(Daga kallo ɗaya) Daga kallo ɗayan da yai mata ya gane a soyayya da komai ma sun dace! Ji yake idan ba da mamallakiyar fuskar ba rayuwar sa baza ta taɓa cika ba irinta ko wani ɗan Adam mai yanci.
Sabida ita ya baro Kaduna garin Gwamna ya dawo nan Katsina ta Dikko ɗakin ƙara,tsayin shekaru shidda da suka wuce! Fuskar da ko hotonta bai samu damar mallaka ba. Sai dai siffanta ta da yai ma wani kwararren mai zane,yasa ya zana masa ita ta fito ras tamkar ka kirata ta amsa. Soyayyar da yake ma Jidda daga Allah ne. Tamkar wata halittace a jikinsa da idan ya rasata rayuwarsa ka iya shiga hatsari. Ya ci alwashin cewar idan har ya rasa Jidda a rayuwar shi,ya tabbata babu shi babu aure.
*****
Kaduna
“Haba Khausar me yasa har yau ki ka kasa gane abinda nake son ki fahimta? Auren namiji irin Alhaji Tasi’u sam ba abin alfahari ba ne! Ki kalle ki fa Khausar! Wai yau Khausar ɗin Ummanta ne ta dawo haka tamkar wacce cutur leda yaci ƙarfinta,kalli fuskar ki fa Khausar,idan ba wanda yai miki farin sani ba a baya da wuya ya shaidaki a yanzu,akwai mazan da duk yadda ka so su gƴaru ku zauna lafiya ba tare da an tauye hakkin juna ba wallahi in suka ɓaude ba wanda ya isa ya sa su yi dole! A ganina babu macen da bata son ta ganta fess! Ko da bazata sanya suturar ba. Ta kalla ta tuna waɗan nan suturar duk mallakinta ne za tai farin ciki da hakan,bana son yadda rayuwata ke shirin ƙarewa a haka Khausar a ce tarihi ya maimaita kansa,tunda da yawancin maza sun maida matayensu tamkar bayi a lokacin jahiliyya,da mace tayi magana don son samun maslaha sai ki ji namiji na faɗin “Idan ban yi ba ɗaure ni za ki sa a yi? Ko kuma duka na za kiyi?”
Ita kuma mace tun tana koƙarin tunatar da miji cewar Allah ne ya ɗaura masa nauyin,tun da ko tafi dangote kudi dole dai mijin ke da alhakin sauke wannan nauyin ko da ya fi Kamaye awon igiya talauci,ki gane Khausar namiji mai tauye mace ba yadda mace ta tarbiyantar da shi ba ne! Ra’ayi ne kawai! Da kuma ganin ta zama tamkar baiwarsa. Matukar igiya ukun nan na kanta dole tai duk yadda yai da ita.
Ba mace ke zaɓar ma kanta abokin zama na gari ba! Duk da waɗan can abubuwa hudun da a ka ce mu yi aure domin su. Sai kuma bincike da ya zama ƙashin bayan ko wani aure,don haka bazan cigaba da sanya miki ido ba watarana Alhaji Tasi’u ya zama ajalinki”
Khausar da tausayin mahaifiyarta da kuma ganin hawayen mahaifiyar nata yasa hayyacinta ya barta,tai saurin runtse idanunta
“Duk ranar da ki ka kashe auran ki da Alhaji Tasi’u ki tabbata a ranar watan zawarcinku ke da mahaifiyar ki yakama”
Tunawa da kalaman mahaifinta da tayi a wani rana da Abban Basmah yai mata dukan kawo wuka yazo har ƙofar gidan ya sauketa,tare da kiran Abbanta don ya amshi takardar saki ɗayan daya rubuta mata yasa ta ji wani k’warin gwuiwa
“Mijin auren ba kashin dankali ba ne Umma,bare ka tantance ɗan Zazzau ne ko kuma mai nagarta ne ɗan JOS,ki yi hakuri,kar soyayyar da ki ke mun yasa ki manta cewar zaman bauta nake ba zaman jin dadi…
“Ya ishe ki haka Jidda,shi kenan,Allah ya kawo miki ƙarshen waɗan nan tarin matsalolin barkatai da suka addabi rayuwar ki. Ya raya maki zuri’a,yasa su yi miki biyayya kamar yadda ki ke koƙarin yi mana ni da mahaifinki.”
Umman Khausar ta ƙarashe maganarta can ƙasan ranta cike da tausayin ɗiyarta mai sonta da tausayinta. Ta san komai! Jidda tana hakuri da mijinta ne kawai gudun karta ƙara mata dawainiya a kan wahalhalun rayuwar da tun kuruciya suka zama tamkar dabaibayi a rayuwarta.
Sosai ta ɗaura da yi mata nasiha mai ratsa jiki tare da ƙara nunar da ita muhunmancin hakuri.
Haka Jidda ta koma gidan mijinta daya zamar mata tamkar sansanin makiya cike da farin cikin samun uwa ta gari kamar Ummanta.
Allah kara basira ,mungode sosai
Allah kara basira ,mungode sosai
Masha Allah
Allah yakara basira da zakin hannu