Skip to content

A Daren Farko | Babi Na Daya

4.3
(8)

Murfi

Shin me murfin ke lullube da shi? Makaranci kaɗai ke da damar ɓude sirrin da ke rufe cikin murfin.

Godiya

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki. Muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafararsa, muna neman jagorancinsa a dukkan ayyukan mu na alkhairi da muka sanya gaba.

Tsira da Amincin Allah

Tsira da amincin Allah masu yawa su tabbata a gareka fiyayyen hilitta Annabi Muhammad (S.A.W). Ubangiji Allah ka ƙara mana soyayyar ma’aiki Abban Zarah.

Tin kafin ta gama faka tsayuwar motarta da kyau matar ta ƙaraso a guje tana koƙarin buɗe murfin motar

“Yar nan ki taimakeni! Rayuwar ‘yata na cikin hatsari,fiya-fiya ta sha,don Allah likita ki taimakeni! Don girman Allah,ke kaɗai ce nasan zaki dubeni a wannan lokacin,naje wajen likitoci sama da uku ko wanne ya kasa duba girman damuwar data kawo ni nan,ki taimake ni Dakta Jidda.”

“Ina yarinyar taki ta ke?”

Ta tambaya lokacin da ta ke fitowa daga cikin motar. “Gata can yashe a ƙasa rai a hannun Allah!”

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!! Tun yaushe abin ya faru da ita?”

Matashiyar likitar ta tambaya tana gwale idanun yarinyar dake kwance bata da maraba da gawa.

“Tun jiya da daddare misalin karfe goma abin ya faru,na bata manja da madara,amma har wayewar garin Allah jikin nata babu wani cigaba.”

Matar da ba zata gaza shekaru talatin da haihuwa a duniya ba ta faɗi haka tana share kwallah da bayan hannunta.

Jakar hannunta kawai ta ajiye,ta ɗauki labcot ta ɗaura a saman kayanta,ba tare da ɓata lokaci ba ta shiga ba ma yarinyar agajin gaggawa. Bayan ganin numfashin yarinyar ya daidaita ne ta ɗaura mata ƙarin ruwan da tai ma allurai a cikin sa. Ba ita ta samu natsuwa ba sai kusan ƙarfe hudu da rabi na yammacin ranar. A matukar gajiye take. Don fuskarta ya gaza ɓoye hakan. Ƙarshe dai ba tare da sanin sauran marasa lafiyan dake son ganinta ba tabi ta kofar baya ta fice. Hakan ba halinta ba ne,sai dai ta tsinci kanta a cikin wani yanayi da ta ke son keɓancewa a yau,tana son ta sami natsuwar jiki da ta zuciya ko hakan zai bata damar tunanin abinda zai fissheta. Da gudu ta figi motar ta fice daga harabar asibitin. Tana tukin ne kamar baza tayi ba,hakan yasa ba tsammani taji motar na neman kwace mata,da sauri ta taka birki ji ka ke “kiiiiii” Motar taci kwalta,ganin Allah ya tsare bata bugi motar dake gabanta ba ta shiga yin godiya ga Allah tare da ƙara sautin kira’ar Abdullahi Abba dake tashi cikin motar

“Likita bokan turai sannu da shigowa.”

Malam Ado mai-gadi ya faɗi haka yana ƙara wangale mata tafkeken gate ɗin gidan.

“Oyoyo Mummy oyoyo Mummy.”

Muryar yaran ya sata kwakwalo murmushin dole,tana fitowa suka zo suka rungumeta.

Sai da ta ba kowannen su sumba a gefen kumatun sa kafin taja hannun su suka ƙarasa cikin gidan.

“Mami barka da war haka? An yini lafiya?”

“Lafiya lauuu Dakta,ya aikin naki?”

“Aiki gashi can mun baro shi,yau a matukar gajiye nake Hajiyata,don gudowa ma nayi ta kofar baya sai tashin motata suka ji.”

“Ai kina kokari ma Jidda! Allah kaɗai zai biya ki,ko lokacin kan ki ishasshe fa baki da shi. Allah ya ƙara lafiya.”

“Ameen Hajiya Mami bari in shiga daga ciki.”

Kafin Hajiya tace wani abu tuni ta shige ciki,kai tsaye banɗaki ta faɗa bayan ta rage kayan jikinta,wanka tayi kafin ta fito,don babu bashin sallah a kanta,sai da tayi la’asar kafin ta fito daga asibiti. Cikin wata doguwar riga ta atampa da a kai ma dinkin bubu ta shirya,mai kaɗai ta murza ma jikinta sai turare data feshe ko ina na jikinta da shi. Tana gƴara zamanta a bakin gado ne yaran suka shigo a guje.

“Mummy kin ga akhi ya cinyemin cakulet ɗina ko?”

“Mommy Allah fa ita ta bani da kanta ai kin hanamu kwaɗayi ko?”

“Duk ku zo nan in ji dumin ku,nayi missing din ku sosai yaran mummy.”

“Mummy muma mun yi missing naki.”

Yaran suka haɗa baki wajen faɗin hakan.

“Oya ku je ku taya Hajiya hira gani nan fitowa kun ji ko?”

“Mummy ni tare dake zan fito yunwa nake ji kuma nak’i cin abinci sai kin bani a baki” Namijin ya faɗa yana ƙara rungume mahaifiyar sa.

“Hooo Muhib rigima,Muhibba ta amshi girman,sai ka ce ita ce Hassana ba Hussaina ba.”

“Mummy ai dama na girme shi,kinga fa na fi shi girma,kuma idan Ammar ya dake shi ni nake rama masa ko Akhee?”

“Na ce ku je falo gani nan fitowa ko?”

Ta faɗi haka cikin faɗa wanda tin kafin ta kai ƙarshe yaran suka fice a guje.

Hawayen data ke ɓoyewa suka shigo gangaro mata.

Lokaci ya ja,kwanaki masu yawa sun shuɗe sun bada watanni,in da watannin suka linku suka bada shekaru,abubuwa da yawa sun faru a shekarun. Na farin ciki da akasinta. Na cigaba da kishiyarta. Na samu dana rashi. Abin farin cikin bai wuce na samun sanyin idanuwanta ba. Haihuwar yan biyun nata Hassan da Hussaina. Waɗan da tai ma huduba da Aliyu Hydar da Hauwa’u mai-jidda. Mufid da Mufida kenan. Su ne komai nata. Sabida su ne take rayuwa a wannan duniyar,ba don Allah yayi zasu shak’i numfashi a cikin duniyar nan ba da tuni an shafe babinta tamkar ba a yi ta ba ma. Abin cigaban data samu kuwa bai wuce na zamarta cikakkiya kuma kwararriyar likitar mata da yara ba. Wanda duk wani mazaunin asibitin ya san da zamanta. Hatta masu yawan shige da fice cikin asibitin babu wanda bai san Dr Jidda Abububakar Aliyu ba. Duk da bata jima da fara aikin ba. Jaruma ce kuma kwararriya a fannin aikin nata. Ta samu Mufid da Mufida ta kuma rasa komi da kowa nata da su kai mata saura. Sai gashi cikin kudirar Allah ta ƙara samun _wasu_ ahalin da suke tafiyar da rayuwar su cikin so da aminci.

*****

Bata damu data share hawayen dake ta rige-rige kan kuncinta ba. Mikewa tayi ta ɗauko wata ƙaramar akwati ta zuge zip dinta. Bata taɓa gajiya da kallon wannan hoton. Fuskar da ko tana cikin ciwon makanta haskenta zai sa ta fidda ta cikin ɗaruruwan mutane. Mafarkin da tai jiya da daddare shi ne yasa ta rasa gane kanta. Sam hakan ba mai yiwuwa ba ne. Shekaru takwas kenan tana mafarkin abu ɗaya amma har yau ya kasa zama gaskiya? Yo ina gaskiya a abinda a ka san idan an rasa shi an yi bankwana dashi kenan har abada! Mafarkin da duk ranar da ta yi shi yake tafiyar mata da duk wani farin-ciki da walwalan data dibi shekaru tana kokarin ganin ta dawwamar dashi a kan fuskarta! Ta ƙara shafa hoton hawayenta na diga a kansa kamar kulum. Begenta da tarin mafarkanta ba abu bane da take da tabbacin sake arangama dasu a wannan duniyar! Watakil sai a lahira. Wani shashi na zuciyarta ya sanar da ita hakan kai tsaye.

Sai da tayi kuka mai isarta kafin ta ƙara faɗawa bandakin ta wanke fuska tare da ɗauro alwalan mangariba ganin lokacin ya gabato. Sai da ta idar da sallar mangariba da ishha’i kafin ta fita waje jikinta sam babu wani k’warin kirki. Bata samu Hajiya a falon ba,don haka da sauri ta ƙarasa kan teburin cin abinci ta ɓude ta zuba daidai wanda take jin zata iya cinyewa. Kan kujerun dake zagaye da falon ta dawo ta zauna tana koƙarin fara cin abincin sallamar Larai ya katse mata hanzarinta. Muhib da Muhibba suka ƙara so jikinta a guje fuskokin su cike da farin-ciki.

“Mummy mun yi sallah tare da mama Larai,kuma mun yi miki addu’a sosai! Cewar Mufida.

“Mummy ni kuma nayi addu’an Allah yasa ki kai mu wajen baban mu,mummy ina so in ganshi don Allah ki kai mu ko sau ɗaya ne.”

Muhib ya ƙarasa faɗin haka yana shirin yin kuka.

Bata san lokacin data mike tsaye ba,sam ta manta da filet din abincin dake wajen. Dakinta ta ƙarasa a guje tai saurin murza key ɗin kofar,kuka mai tsanani ya kwace mata. Kuka takeyi tamkar wata ƙaramar yarinya. Tun jiya da tai mafarkin data jima tana addu’ar kasancewar sa gaskiya hayyacinta ya barta. Jarumta da dagiya irin nata yasa ta shirya tare da ficewa wajen aiki ba tare da yanayinta ya nuna halin data tashi da shi ba. A hankali ta mik’e ta ƙarasa tagar dakin,sararin sama yayi haske,taurari masu ban sha’awa sun ƙara taimaka ma farin wata wajen haska garin. Yanayin mai dadi ne ga ma’abotan da suke cikin farin ciki! Saɓanin ita da lamarin yazo mata a shammace! Abubuwa da yawa suka shiga yi mata yawo a kwakwalwa,tai saurin rintse idanunta hawaye na bin gefensu.

“Jidda ki ɓudemin kofar nan idan na isa dake.”

Muryar Hajiya Mami daya dawo da ita hayyacinta yasa tai saurin goge fuskarta. Da azama ta ƙarasa ta ɓude mata kofan. Kanta a ƙasa ba tare da tace da Hajiyan komai ba ta koma bakin gadonta ta zauna.

“Haba Jidda! Wai sai yaushe ne zaki maida komai ba komai ba? Yaushe ne zaki watsar da komai ki fuskanci abinda yake gaban ki? Baya-baya ne yawuce kamata yai kici gaba da fuskantar gaba! Kamar yadda ki ka ɗauko tin farko. Yanzun ina ranar haka? Ke kin shigo ɗaki kin kulle kan ki kinata faman kuka, yara ma suna can wajen Larai ba yanda ba muyi dasu da su yi shiru ba amma sun ki sauraran mu! Haba ko so kike yaran su fara tunanin muna cusguna maki ne? So ki ke su matsa ma kwakwalwar su a ƙananun shekaru irin nasu don gane wani abu game da rayuwar ki na baya daya wuce!”

“Hajiya kiyi hakuri” Jidda ta faɗi haka tana ɗaura kanta jikin Hajiyar. Hajiya har yanzu dai mafarkin da nake yi ne,jiya ma na ƙarayin kwatankwacin sa shi yasa tin safiya na ji komai ya fice min a rai
Hajiya dake ta faman shafa bayanta tamkar ƙaramar yarinya ta nisa kafin ta fara magana

“Kina addu’oin kwanciya kuwa Jidda?”

“Ina yi Hajiya”

Jidda ta bata amsa a gajarce.

“To kiyi kokari ki ƙara a kan wanda kike yi. Ki cire komai a ranki,in sha Allah komai zai yi daidai kin ji ko? Maza tashi mu je kici abinci,ki janyo yaran a jiki ki rarrashe su,sam bana son ganin angon nawa da kishiyata cikin damuwa.”

Ba musu Jidda ta mike tana gƴara zaman ɗankwalinta daya fice daga kanta.

“I am so sorry mummy!Ba zan ƙara saki kuka ba kin ji.”

Mufid ya faɗi haka yana rike kunnuwan sa da hannyen sa alamun ban hakuri

“Na hakura Allah yai maku albarka baki ɗaya.”

Jidda ta faɗi haka tana jan hancin Muhib dake ƙara shigewa jikinta.

Abinci Larai ta sake zuba mata,ba musu ta amsa ta fara ci,tana ci tana ba ma yaran a baki har suka kammala. Ba jimawa bacci ya ɗauke yaran. Itama tanada buƙatar hutu don haka tai ma Hajiya da Larai sallama bayan ta kwashe yaran ta kwantar da kowanne a makwancin sa.

Bandaki ta shige ta wanko bakinta tare da ɗauro alwala. Bayan ta idar da sallar shafa’i da wuturi ta jima a zaune a wurin tana kaima Allah kukanta. Mafarkin da tai jiya ya shiga dawo mata tiryan-tiryan.

*****

Duhun dare ne da baka iya ganin komai sai hasken wata da da taurari da suka ƙawata ko ina. Gudu yake yi sosai yana cin tuntube amma hakan bai sa ya tsaya ba. Ita dai tana tsaye a gefe tana kallon sa. Duk yadda ta so taga fuskansa hakan ya gagara. Sai dai surar jikinsa da tafiyar sa baza su taba gushewa ba cikin idanunta. Yunkuri take ba adadi da niyyar zuwa garesa don ganin fuskarsa hakan na cin tura. Ganin wajenta yake nufowa gadan-gadan yasa ta tsinci kanta tana mai sakin wani murmushi,sai dai yana gab da cimmata wata budurwa da bata ga fuskar ta ba ta bayyana a gaban sa. “Ƙarya kake yi wallahi! Babu wata mace data isa ta rabamu har abada! Babu wannan mahalukin kuma ba a hallice sa ba,kai koda ya wanzu a wannan duniyar sai naga ƙarshen sa! Ni zan kashe shi da wannan hannun nawa!” Ta ƙarasa tana ɓude tafukan hannayenta,sai a lokacin Jidda ta samu damar mikewa. Amma kafin ta ƙarasa garesu matar ta janye shi sun yi nesa da ita. Hakan bai hana shi juyowa ba. Murmushin daya sakar mata a lokacin ya _sanya_ taja da baya tana mai ambaton sunan Allah tare da farkawa daga baccin.

*****
Addu’ar da ta keyi a mafarkin ta farka tana mai ƙarasa shi cike da razani. Alwala taje ta ɗauro ta shimfida sallaya ta fara jera nafilfilin da bata san adadin su ba. Sai da taji ta fara samun natsuwa kafin ta ɗaura da karatun alqur’ani.

*****

Ta share hawayen dake fitar mata ta ido ɗaya tana jan hanci. Shekaru biyu ta ɗauka tana waɗan nan mafarkan marasa kan gado wanda har yau ta kasa gane fassarar sa. Tayi kuka, tayi addu’oi,tayi sallolin dare da duk wani abu daya kamata ganin ta rabu da wannan mafarkin amma har yanzu abin yaci tura. Mikewa tayi ta ƙarasa kan gadonta. Addu’a ta sa ke yi ma mufid,ta shafe masa ko’ina na jikinsa. Ta ɗauke shi ta gƴara masa kwanciya a kan gadon sa. Hayewa nata gadon tayi,tare da jan bargo kasancewar ruwan da a kayi dazu da yamma ya saukar da sanyi a garin.

Tuni Muhibba ta gudu ɗakin Hajiya can take kwana,ranar kuma da rikici ya tashi ta gudo ta kwana tare da ita.

*****

Koda tayi sallan asuba wani sabon bacci ne ya kuma ɗauketa. Muhib kuwa tinda suka idar da sallan ya gudu ɗakin Hajiya.

“Mummy! Mummy!! Mummy!!!”

“Kai Muhib wannan kiran ai sai ka fasa min dodon kunne.”

Jidda ta faɗi haka tana gƴara ɗaurin dankwalin shaddarta a gaban madubi. Dariya yaron ya shiga yi.

“Mummy ina dodon kunnen naki yake in ganshi.”

Ya ƙarasa yana kokarin leƙa kunnen nata.

“Mummy yau baza ki je office bane?” Muhibba ce ta shigo dakin tana tambaya bayan ta gaida mahaifiyarta.

“Yau babu aiki babyna! Mun sami hutu sabida bikin easter daya gabato” Ta faɗi haka tana ƙare ma yaran kallo. Sanye suke da shadda galila iri ɗaya. Kayan yai matukar yi masu kyau. Jin tace bata da aiki yau yasa suka shiga tsalle suna murna. Don idan ba hutu irin haka tasamu ba koyaushe bata da ishasshen lokacin kanta. Sosai duk wani wanda yasan Dr Jidda Abubakar Aliyu yake jinjina mata,kasancewarta gwarzuwar likita da a ke ji da ita.

Hakan bai hanata shakuwa da ‘ya’yanta ba. Shakuwa ce irin ta uwa da ɗa mai ƙarfi tsakaninta da yaran. Babu wani abu da suke ɓoye mata. Mufid da Mufida ‘ya’ya ne masu shiga rai.

Dakin Hajiya suka nufa ita da yaran. Tana zaune kan sallaya hannunta rike da casbaha tana lazimi.

“Ina kwana Hajiya an tashi lafiya?” Jidda ta faɗi haka bayan ta samu wuri ta zauna kusa da Hajiyan.

” Lafiya lauuu Jidda! Ya gajiyan aiki? Nasan gajiya ce ta hanaki fitowa yau ki mana abin breakfast. Kin san ina son cin girkin ki!”

“Hajiya nawa kuma hakuri ki ke kina turawa ko?” Larai ce ta ƙaraso tana faɗin haka dariyar da ta ke ɓoyewa ya kwace mata.

.”Yoo Larai banda abinki ai ‘yata gwanace a fannin girke-girken zamani. Ke kuma a girke-girken mu na gargajiya ki ka fi kauri,kuma yau girkin zamanin nake son ci,sai kiyi hakuri”

Kowa da yake wurin saida ya dara. Duk lokacin da Hajiya da Larai suka fara irin haka abin kan matukar birge Jidda! Tai kokarin ɓoye damuwar daya soki ƙahon dimanta

“Hajiya kar ki damu yanzun nan zan haɗa maki abin karin da kike matukar so fiye da kowanne bari in ƙarasa kicin ɗin” Jidda ta ƙarasa maganarta tana ficewa daga ɗakin da sauri gudun kar Hajiya ta gane sauyin da fuskarta tayi.

Shigarta kicin ya ɗauke mata duk wata damuwar dake damunta. Daki-daki take komi nata,cike da natsuwa da burgewa.

Tana gab da kammalawa ne yaran suka shigo kicin ɗin

“Woww mummy gidan yanata kamshi,kin min favourite ɗina ko mummy?”

“A’a mummy favourite ɗina zaki dafa,kinga akhee shi baya son cin abinci fa shi yasa ba shi da ƙarfi”

Dariya suka bata sosai. Wanda saida gefen kumatunta suka lotsa. A haka ta ƙarasa aikin Mufid da Mufida na taya ta hira.

“Allah yai maki albarka Jidda! Ni ba don baki da lokacin kan ki ba ai da kin ɓude gidan abinci,zaki samu kasuwa sosai”

“Ahh lallai Hajiya bari in tashi in ɗauko waigi,don bani da ƙarfin ɗaga ki idan ki ka tuntsura” Larai ta faɗi tana ƙarasa haɗiye abincin data cika bakinta da shi. Cike da nishadi da farin-ciki kowa ya kammala cin abincin sa. Ba laifi itama Jidda taci abincin amma ba mai yawa sosai ba.

“Dazu mu kai waya da Hajiya Mama,tace tana so ki kai mata yan biyu su yi mata hutun kwana biyun a can,sai ku shirya zuwa anjima ki kai su”

“To Hajiya,zuwa ƙarfe hudu idan nai la’asar sai in je in sauke su,don akwai ayyukan dana ke son kammalawa zuwa gobe”

“To agogo sarkin aiki,ina laifin ke ma ki kwana,zuwa gobe sai ki dawo ki baro su a can,wai ni ina naga yadda a ke gudun mutane? Sai yaushe zaki sake da kowa ne Jidda?”

Tinda Hajiya ta fara maganar kan Jidda na ƙasa,sai da ta ɗisa aya kafin tace

“Hajiya kiyi hakuri,duk yadda ki ka ce haka za’ayi.”

Tana ƙarasawa ta mike jikinta a matukar sanyaye.

Yanzu na fara!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

1 thought on “A Daren Farko | Babi Na Daya”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×