Skip to content
Part 11 of 15 in the Series Abbakar by Fadimafayau

Kairiyya na fita daga office din kai tsaye school ɗin ta  bari,  saida ta hau Ɗan sahu sannan ta ɗauko wayarta tafara dialling ɗin number ɗin Aisha yafi sau hudu bata ɗauka ba, wanan yasa ta kira Fatima ita ma dai bata ɗaga ba, tsaki ta ja wanda har yasa mai Ɗan sahun jiyowa, “sorry ba da kai nake ba,” da zura wayarta a jaka.

Saida taje gida sannan kiran Aisha ya shiga, “lafiya dai irin wannan kira haka, ina ta son biyo kiran yana cewa network busy” Khairiyya bata amsa ba Aishan ta kuma tambayarta “kina ina ne ke muke jira fa, kar muyi dare a school ɗin nan”

Nisawa Khairiyyan ta yi tun ɗazu fa nake neman ku ban gankuba, shine na tafi gida, nakirama in ce muku na tafi gida nema yanzu, se mun hadu gobe, in shs Allah” tsaki Aisha taja Fatima tai saurinn karbar wayar cikin faɗa take magana “anman wallahi ummu bakida muntuci inba rashin mutunci ba kinsan bazamu tafi ba sai mun jiraki kawai saikiyi tafiyarki”

“ayi haƙuri naga tun wajen fitowa ta banganku ba, kofa office ɗin ban shiga ba,” Khairiyya ta yi ƙarya.

A kufule Fatima ta ce ” kutt baki shiga ba kika ce?, muna kallonki fa kika shiga munfi awa biyu baki fitoba.”

Ganin yadda Fatima ke fada yasa Aisha karɓar wayar, a nitse ta ce ” haba ummu taya zaki mana haka, tsaya ma, mai naji fatima tana cewa wai kince ko office ɗin baki shiga ba, yau she kika fara ƙarya”

No ta girgiza kai tamkar taka gaban su “bata fahince ni bane, kinsan ta da fushi inta hau bata tsayawa cin ribar zance zata hau fada.”

Nisawa ta yi tana tunanin mai zata ce bata so singa shigar ta ba, dan bata son zargi a nutse ta ce “Cewa nayi ina shiga na fito fa baku dai kula bane, ni kuma banyi zaton kuna nanba natafi masallaci nemanku da bangan ku ba na tafi gida” ta faɗa duda tasan da wuya su yadda.

A’isha ɗin ce ta ce “anya ummu?, idanuna fa nakan office ɗin, nidai shawara zan baki, kar ki biyewa Lecturer, kinsan dai karatu mukazo ko?” Ajiyar zuciya ta yi bataji komi kan maganar Aishan ba dan tasan ta da tsantseni da faɗar gaskiya gama kowaye, ta kuma san ita take faɗa mata duda ba abinda suke tsammanin bane ya zaunar da ita.

“Ki yadda dani abinda ya kaini kawai nayi, magana ta fatar baki kawai ta haɗa ni da shi wallahi, banmayi make up dinba cewa yayi in answering all question 2 for test in yaso 3 for exam” ta faɗa fatanta su yadda.

Ba sai kin rantse ba mun yarda fa,  ki shafan kan Abbakar sai gobe”

” zai ji in sha Allah” sukayi sallama.

Hawayen da take riƙewa suka kwaranyo, tun a offis ɗin Abbakar jarumta kawai take, ta goge hawayen da ya zubo mata wani dacin rai na taso mata, rasa me ke mata daɗi ta yi, ji take inama batazo duniya ba ko inama ta mutu kafin a haifeta da duk bata faɗa wannan masifar ba.

Gidansu Mahfuz
Ummi da saukowa daga bene ɗauke da kofi tana cin fruit salad ce ta ƙaraso inda Hajiya ta zauna jugun da alamu tunanin ko damuwar Mahfuz ke damun ta. Wash yau na gaji da yawa Ummi ta ce kafin ta samu wuri ta zauna, cokalin da ta ɗebo fruit ɗin ta kai baki sannan ta dubi Hajiya wadda hankalin ta har lokacin baya kanta ta ce.

“Hajiya  bakya ganin haƙƙin ummulkhairi ke ɗawainiya da dangin nan namu musanman ma yah Mahfuz?”

Tsak Hajiya ta ja “me muka mata da haqainta zai ɗawainiya mu eyye mara mutunci?”

Turo baki Ummi ta yi ” don’t get me wrong, Gani naifa yah Mahfuz ya haukace, gashi an kasa gano me ke damunsa”

Hajiya tai shiru, kafin ta ce  kin tunan wani abu nasan tabbas da sahannun yarinyar nan a abinda ya same shi, sai yanzu na fuskanta aljanu suka turo masa suka masa farraqu da ɗan uwansa maza kiramin doctor Yusif.” Hajiya ta faɗa a ƙagare.

Ba tare da damuwa ko ɗaukan batun Hajiyar ba Ummi ta fara kiran Dr Yusuf a kasalance, yana ɗagawa ta miƙawa Hajiya wadda tana amsa ta hau magana “Yawwa Doctor so nake Mahfuz ya dawo gida mu gwada ruqiyya tunda naga na asibitin ba sauqi” ta faɗa tare da yin shiru dan saurarar mai zai ce.

” Nayi tunanin haka agwada ruqiyya ɗin tun da mu nan har yanzu dai muna bincikawa in yaso na dinga zuwa gida in duba shi” Doctor ɗin ya faɗa daga waya.

Numfasawa Hajiya ta yi, “tom shikenan Doctor zamu zo tafiya da shi Please kamana processing everything before we arrive”

Tom kawai ya ce suka lashe wayar.

Miƙa ma Ummi wayar Hajiya ta yi kafin ta ce “Kiramin Musa”

Miƙewa Ummi ta yi bayan ta dire kofin hannun ta a ɗan ƙaramin teburin da ke falon Hajiya ta ce “wa kike nufin zai ɗauke miki” a shagwaɓance Ummi tasa hannu ta ɗaula tare da yin waje.

Mintina basu fi huɗu ba saigata ta dawo da Musa yana biye da ita , ya russina ya gaida Hajiya gami da cewa ” gani.”

Duban sa Hajiya ta yi ” Yawwa Musa so nake kaje ka ɗauko min Mahfuz a asibiti”

“Alhaji Mahfuz ɗin” yadan fada da razana Hajiyar Mahfuz ta ɗaure fuska  “eh shi so nake ya dawo gida mu masa na gida tunda na asibitin yaqi.”

Fuskar tausayi Musa ya yi a murya kasalance ya ce “Hajiya ya warkene?” ya fada cikin rawar murya.

Cikin fushi Hajiya ta ce “inda ya warke ai da ba zance ma zamu masa maganin gargajiya ba ko?”

Jikinsa har kyarma yake yace “anman hajiya taya zan iya tawo dashi cikin sauqi, ina tuqi kar ya tunzura ya janyo mu yi haɗari”

Kufula Hajiya ta kuma yi ” to me kake nufi?” yai zuru-zuru da ido ummi tasa dariya “wallahi Hajiya da gaskiyarsa taya zai ɗauko mahaukaci a mota shi ɗaya, wanda yake cewa zai kashe mutane kawai ya shaqeshi.”

Hajiya ta cilla mata daquwa “ungonan dan uwan naki ne mahaukaci?”

Juya ido irin na shagwaɓaɓɓu Ummi ta yi,  to hajiya aiba qarya akaiba”

“ok to naji ku tafi tare sai ki riqe masa shi” Hajiya ta faɗa.

Zaro ido Ummi ta yi tare da dafe ƙirji “Hajiya ni kuma?”

Kuma tsuke fuska Hajiya ta yi kan ta ce “eh ke inkuma bazaki ba to, kinsan ba ke daya na haifa ba” tasan indai hajiya ta fadi haka to takai qololuwar jin haushi.

“Ta miqe muje” ya ce da Musa, kan ta hau sama ta dauko gyalenta, Hajiya mun tafi ta ce ” Allah ya kiyaye” kawai Hajiya ta tace inda Ummi ta ce “amin.”

Tunda suka fara tafiya ba wanda yacewa kowa ci kanka, kowa zulluminsa ta ya zasu tawo mahaukaci cikin mota ne.

Koda suka isa office ɗin doctor Yusif ɗin suka nufa inda suka yi cike cike kafi abasu Mahfuz, yadda Ummi ta ganshi ya daga mata hankali, dan mahaukaci sak tagani yayi dauɗa sosai.

Koda ummi taje dab dashi amai ne kawai batai ba sabida wani tsamin dauda da yake tace ” yah Mahfuz ka gane ni?” ya kalleta kafin ya yi Murmushi lallai yarinyar nan tana nufin baida hankali da gaske ko me yayin da a zahiri kuma ya ce “ba Ummi bace?” ta ɗanyi ajiyar zuciya aqallah ya ganeta.

“Lafiya me ya kawoki?” Ya tambaya, a nutse ta ce nazo mutafi ne? Tsuke fuska ya yi ” nine nace miki inasan mu tafi?” yadda yake magana cikin fushi da faɗa ya tsorata ta “a’a” ta faɗa tana Girgiza kai “to ba inda zani” ya faɗa sanyaya murya ta kuma yi “pls yah….” Ɗaga mata hannu ya yi “kinga alamar wasa a idona?”

Girgiza kai ta hau yi inda shi kuma ya cigaba da faɗin “Ni nariga na yanke shawar qare rayuwata anan, dan haka zaki iya tafiya”

Daurewa ta yi dan duk a tsorace take da shi ta ce “yah kayi haquri kazo mu tafi, kowa na kewarka”

Hararar ta ya yi “qarya kike kowa yafisan Yah Nasir, gashinan sabida shi kowa ya mance dani kowa ya tsaneni kowa ya gujeni.” Jibi in da suka kawo ni duk sabida shi.

Cikin sauri tace “yah kayi haquri inkasa wa ranka kowa ya tsaneka ka cire Hajiya, kasan tana sanka kullin burunta kasamu sauqi pls kazo mu tafi kodan Hajiya,in kana nan ta yaya kake tunanin za’a gano sharrin da Yaya ya ma, dole sai kaine zaka gano ka kuma fahimtar da mutane,” shiru ya yi yana nazarin zancen ta.

Miqewa yai yabi bayansu ummi ta fara yadda da batun Hajiya anwa yayun nata Mahfuz da Nasir farraqu tunda gashi har yasama ransa anfi san Nasir duda yana cikin hauka.

Suna tafe tana kaf kaf dashi cikin mota dan tsoronta karya shaqo me tuqi ko ya bude ya fice, yana fuskantar ta sosai, kasan tuwarsa bayan yai degree dinsa a fanni ƙere ƙere yaje yayi wani sabon degree din a psychology baisan sanda dariya ta kufce masa ba, aikuwa gabaki dayan su Ummi da Musa hankalinsu ya ƙara tashi fuskantar haka ne yasa shi yin shiru.

Agida ma kowa kaf kaf yadingayi dashi har suka isa sashen Hajiya sai asannan ummi ta saki sanyayyar ajiyar zuciya aƙallah sun zo lafiya.

<< Abbakar 10Abbakar 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×