Gidansu Abbakar
Yau shirye shirye suke sosai, dan har su Nurat sun zo. Aunty Zainab ce zata zo dan ganin amaryar yayan nata, dan ita ba tasanta ba.
Lokacin da ta zone, Aunty Zee tasha mamaki. "Qanwarmu, ashe kece amaryar tamu?" Ummu ma ta mamaki. Aunty Zee, daman ke, yar nance? "Eh, aure ya kaini Katsina." Kowa yai mamakin sanin juna da su kai.
Aunty Zee ta dubu Hajiya. "Umma, ai na santa. Qanwar Yah Nasir ce, kuma qawar Farida, qanwar Salma, wato qannen mijinta." Hajiya just smiled. "Ikon Allah."
Da yake duk gida daya suka zauna da su Salman. . .
