Gidansu Mahfuz
Hankalin Hajiyar Mahfuz ya gama tashi, musanman ganin an yi bikin Nasir, an gama, babu Mahfuz, babu labarinsa. Tun tana tsanmaninsa harta dena hakan, yasa ta kira number din matarsa. Danshi ko an kirashi, aka kashe take.
Bugu hudu ta qari ringing dinta, ba a dauka ba. Sai ana biyar, dinne aka daga, cikin tsiwa take fadin, "Wai waye haka ya isheni da kira? Na tsani! Irin haka ka kira sau daya sau biyu, ba'a daga ba, Basaika haqura ba"
"Eyye! Sannu maras mutunci! To, uwar mijinki ce." Taja tsaki. "In uwar mijina ce, ai ba ita. . .
