Da sunan Allah mai Rahma mai Jin Ƙai
Tsaye yake a jikin bangon wurin, lokaci zuwa lokaci yakan saka hannun shi cikin sumar kan shi, ba zai iya tuna ranar ƙarshe da wani abu ya ɗaga mishi hankali haka ba, yanayin yake ji ya zame mishi baƙo. Kayan da yake jikin shi ya bi da kallo, gajeren wando ne na kakin sojoji da ko gwiwar shi bai taɓa ba, sai rigar wandon mai yankakken hannu, wuyan shi da alamar sarƙar da ba ka ganin ko ta mecece, sai shi da take wuyan shi. Wani ɗan dogon ƙarfe ne maƙle a jiki da yake ɗauke da sunan shi da kuma lambar aikin shi, don lokuta da dama idan mutuwa ta gifta, sarƙar ce kawai shaidar gane waye da waye ta rutsa da shi.
Duk da kalar kakin bai hana shi ganin jinin da ya ɓata kayan ba, jinin da kallon da yake mishi ya sa wani abu tsinkewa a cikin shi, bai da kalmar da zai ɗora abin da yake ji, saboda jini ba ya ɗaga mishi hankali, ko kafin aikin shi yana da wata irin dakakkiyar zuciya ta ban mamaki, yau shine yake jin alamun zufa a goshin shi da ganin jini a jikin rigar shi.
“Paapi zan sha ruwa…”
Muryar Fajr ta doki kunnuwan shi tana tuna mishi cewar ba shi kaɗai bane a wajen. Ɗan juyawa yayii yana kallon su, Fajr da yake cikin shekarun shi na biyar yanzun, ɗan dai yana da girman jiki da tsayin da zai sa ka yi tunanin ya wuce shekara biyar ɗin da bai ma ƙarasa ba. Yana zaune da ƙanwar shi da duka watan ta hudue a duniya, yadda ya riƙe ta dam ya sa Abdulƙadir leƙa yarinyar ya ga ko tana numfashi.
“Wanne irin riƙo ka yi wa Ikram haka?”
Kallon shi Fajr yayi yana shagwaɓe mishi fuska, don shi ya gaji da riƙon yarinyar.
“Ni ina so in sha ruwa. Paapi, Omma fa?”
Hannu Abdulƙadir ya miƙa ya karɓi Ikram ɗin daga hannun Fajr. Bacci take yi hankalinta kwance, ɗan daƙuna fuska ya yi yana son tuna ko ya tabay jin kukan yarinyar tun dawowar shi, ba ta da rigima ko kaɗan. Idanuwan shi yake hangawa ko zai hango inda zai samo ma Fajr ɗin ruwa ba tare dayya bar wajen ba, ba ya son motsawa daga inda yake ko likitan zai fito da wani bayani. A can ƙasan zuciyar shi yake jin wani abu tamkar bargo da yake ta haɗuwa yana ƙara kauri, ya san shi yake so ya lulluɓe da rashin gaskiyar da yake yawata mishi a ko’ina na jikin shi.
“Fajr ina zan ga ruwa anan?”
Ya faɗi, yana gyara wa Ikram kwanciya akan kafaɗar shi, yadda ta kwantar da kanta a jikin shi na nutsar da kaɗan daga cikin abin da yake ji. Ɗaga idanuwa ya sake yi ya kuwa sauke su kan Mami da ta turo ƙofar glass ɗin wajen tana takowa, yanzun yake dana sanin kiranta da ya yi, amma lokacin dayae kira ɗin a rikice yake. Bai san abin da ya kamata ya yi ba, ita tace ya ɗauko Waheedah ɗin ya kawota asibiti, da ya tashi sai ya kwaso har da su Fajr.
Aminu ya hango ya rufo mata baya, sai kuma Salim da Zainab. Ya manta yadda ‘yan gidan su suke, yanayin aikin shi ya manta yadda ko Kjurjewa ka yi in dai za a kaika asibiti mota ɗaya ta yi kaɗan, don kusan rabinsu sai sunje, in kuka jima ba ku dawo ba za ku ga sauran rabin da aka bari a gida sun biyo bayan su, yana tunanin duk wani asibiti da suke da file a garin Kano sun san ‘yan gidan Bugaje da wannan al’adar tasu, ba a ma hanasu shiga. Suna ƙarasowa Zainab ta miƙa hannu ta karɓi Ikram daga hannun shi, bai yi musu ba ya miƙa mata ita.
“Ya jikin nata?”
Mami ta tambaye shi, idanuwan shi ya sauke ƙasa yana tsintar kan shi da kasa haɗa idanuwa da ita. Sai dai kafin ya amsa Fajr ya riga shi da faɗin,
“Mami Omma ta faɗi, jini mai yawa a kanta…”
Hannu Mami ta miƙa ma yaron da ya taso yana kama hannunta tare da zagaya ɗayan hannun nashi a jikin ƙafafuwanta, ɗaga idanuwan shi ya yi yana saukewa cikin na Abdulƙadir da yake tsaye, harshen shi yake ji ya mishi nauyi, don ya kasa amsa ma Mami tambayar da ta yi mishi. Rashin gaskiya ne shimfiɗe a fuskar shi. Da wani irin yanayi da yake ji ya mishi wani iri da Fajr yake kallon shi. Sosai yaron yake kallon shi yana ƙara shigewa jikin Mami, idanuwan shi na cikin na Abdulƙadir ya ce,
“Paapi ne yai pushing (Turewa) ɗinta ta faɗi… Mami Paapi ne…”
Wani irin shiru ya biyo bayan maganar yaron, shiru ne da hayaniyar shi tafi ta surutu, don ko wani ya zo wucewa shirun da yake wajen zai iya taɓa shi, daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi yana son nemo kalmar abin da ya lulluɓe shi.
‘Kunya’
Wata murya ta furta can ƙasan ƙwaƙwalwar shi, sai dai kuma tsakanin shi da kunya akwai wata irin tazara da ba za ta misaltu ba, ba ta taɓa kamo shi ba ko acan da, bai san ma ya ake jinta ba, kai tsaye yake dukkan al’amuran shi, yau kam ba kamoshi kawai ta yi ba, lulluɓe shi tayi ruf. Bargon rashin gaskiya mai kaurin gaske na bin bayanta, numfashin shi ma kamar a lissafe yake jin fitar shi.
“Mami kinga abinda nake ce miki ko?”
Aminu ya faɗi yana korar shirun da yake kewaye da wajen.
“Aminu!”
Mami ɗin ta kira cike da kashedi. Akan ce yaro ba ya ƙarya, musamman mai ƙarancin shekaru kamar Fajr, sai dai yaran yanzu ƙuruciyar su cike take da abin mamaki. Ba komai da ya fito daga bakin su bane abin yarda, hakan shi take ta faɗa wa kanta don kar ta yarda da abinda Fajr ɗin ya furta, duk da yanayin Abdulƙadir ɗin ya gasgata maganganun yaron nashi, amma ba ta son ta yarda da hakan. Sam ba ta kula da girgiza mata kai da Aminu yake ba sai da yace,
“Kar ki ce in yi shiru wannan karon ma, kina jin abin da Fajr ya faɗi, Wallahi na jima da sanin Hamma Abdulƙadir ne ajalin Adda Wahee…”
Cikin tashin hankali Mami ta kalli Aminu, yanayin kallon ya sa shi kasa ƙarasa maganar da yake yi, ɗauke idanuwan shi ya yi daga kanta yana watsa wa Abdulƙadir da yake tsaye wata irin harara. Wani ɗaci Aminu yake ji a ƙasan maƙoshin shi. Ba tun yanzu Abdulkadir ya gama ficewa daga ranshi ba, Mami na ce mishi Waheedah ta faɗi ta fasa kai ya san Abdulƙadir na da hannu dumu-dumu cikin faɗuwar nata, sai dai ko kaɗan bai hango sanadin zai zamana da hannun shi ba. Ya ɗauka ɓacin ranshi ne ya sa ta faɗuwa tun da duk sun san tana da hawan jini.
Da yana da iko akan igiyar auren Waheedah da Abdulƙadir da tuni ya sa almakashi ya datse ta, datsar da babu hanyar da za a bi a sake ɗaurata har abada.
“Hamma…”
Zainab ta kira cike da wani yanayi da ya sa Abdulƙadir ɗin sake ƙasa da kan shi, don ko ya ɗago ma bashi da kalaman da zai musu amfani da shi, bai san me zai ce musu ba, yawan magana ba ɗabi’ar shi bace ba tun da can, ko da yana da abin faɗi kuwa, ballantana yanzu da babu abin da yake so kamar ƙasar wajen ta buɗe dai-dai inda yake ta yi ƙasa da shi. Kafin ta sake cewa wani abu likitan ya fito daga ɗakin da Waheedah take, wasu Nurses guda biyu na biye da shi a bayan shi. Idanuwan shi ya sauke kan Abdulƙadir, sai dai kafin ya ce ya bishi office kamar yadda Mami ta sani, ta riga shi magana da faɗin,
“Ni mahaifiyarta ce, waɗannan ƙannenta ne, duk abin da za ka faɗa mishi zai mai-maita mana ne, gara ka faɗa anan ɗin kawai…”
Abdulƙadir ɗin dai likitan ya sake kallo, kai ya ɗan jinjina mishi a hankali yana ba shi izinin yin magana, numfashi ya sauke tukunna yace,
“Babu wata matsala In shaa Allah, munyi mata ƙaramar tiyata saboda buguwar ta shiga sosai… ba dai yanzun za ta tashi ba, amma za ku iya shiga ku ganta, banda yawan surutu don Allah, kar a tasheta, tana buƙatar hutu sosai ko don jininta da ya hau fiye da na da…”
Kai Mami ta jinjina tana mishi godiya tukunna ya wuce, hannun Fajr ta kama sannan ta raɓa Abdulƙadir ta shiga cikin ɗakin. Daga inda take tsaye tana hango ramar da Waheedah ta yi, ta yi wata irin ramewa da duk da idanuwanta a rufe suke kana ganin ramin da yake ƙasan su, kanta nannaɗe yake da bandeji, hannunta ɗaure da ƙarin ruwa. Wani irin abu Mami ta ji ya matse a cikin zuciyarta, a hankali ta taka tana jan kujera ta zauna, ta ɗora Fajr akan cinyarta. Hannu yaron yakai kan jikin Waheedah.
“Omma…”
Ya faɗi, Mami ta kama hannun shi ta janye.
“Kar ka tashe ta Fajr, bacci take yi ka ji…”
“Ni zan sha ruwa…”
Fajr ya faɗi yana sa Mami ɗin juyawa ta kalli Aminu da suma duk sun shigo ɗakin. Kafin ta yi magana Salim ya ce,
“Bari in karɓo… Ruwan kawai ake buƙata? Ko zan taho da wani abin…”
Waheedah ta kalla, tasan babu abinda Abdulƙadir ya ɗauko, hakan ya sa ta faɗin,
“Ka fara kawo ruwan dai, sai ka zo kuje gida kai da Zainab akwai ‘yan abubuwan da za ku ɗauko mana…”
Kai Salim ya jinjina mata yana juyawa ya fice daga ɗakin. A bakin ƙofa ya ga Abdulƙadir a tsaye, kallon shi kawai Salim ya yi yana girgiza kan shi tukunna ya wuce, kan kujerun da suke wajen. Abdulƙadir ya ƙarasa ya zauna, yau gaba ɗayansa shi jin abubuwan da yake tunanin ya yi bankwana dasue shekaru da dama da suka wuce yake yi, yanzu kallon da Salim ya yi mishi ya sa shi jin wani irin abu na lulluɓe shi, so yake ya ga halin da Waheedah take ciki, amma ya kasa shiga ɗakin, kunyar haɗa idanuwa da Mami yake ji, ba zai iya shiga in tana nan ba. Kanshi ya saka cikin hannuwan shi yana dafewa. Tunani barkatai na soma kawo mishi ziyara.
*****
Salim na kawo wa Fajr ruwan suka juya su duka ukun, har da Aminu, don Fajr ɗin ma manne musu ya yi, dole ta karɓi Ikram daga hannun Zainab. Towel ɗin da yarinyar take ciki ta yi amfani da shi ta goyata. Tukunna ta ɗan yi dabara ta zauna kan kujerar ɗakin, tunda ta roba ce. Shi ya sa tace har babbar darduma a ɗauko musu. Sosai ta nutsar da hankalinta kan Waheedah, hannunta da ya ƙara zama siriri, dama abinka da ba ƙibar kirki ba, yanayin ƙaddarar yarinyar ya sa idanuwan Mami cika taf da hawaye.
Tana da haƙuri da kauda kai ta sani, amma na Waheedah ya yi yawa. Ita ko baki ba za ta iya buɗewa ta ce ana mata abu ba, in kuma ka tambaya murmushi kawai takan yi.
Mami rayuwar duka babu yawa, komai zai wuce kamar bai faru ba.’ Shi ne maganarta a koda yaushe idan ka so sanin halin da take ciki. Da ba a ganewa in ba ka kula da yanayin ramewar da take yi a tsaye ba, ko murmushinta da ba ya kaiwa cikin idanuwan ta. To ita dai kam Mami za ta iya cewa tun yawon arba’in ɗin Ikram da ta zo musu rabon da ta saka ta a idanuwan ta, sai dai a waya, ta kuma hana su Aminu kawo mata zancen gidan Waheedah ɗin, don haka ko sun kula da wani abin in sun je ba zuwa suke suna faɗa mata ba.
Ba ta san iya lokacin da ta ɗauka a zaune a wajen ba, sai da ta ji sallamar su Zainab ɗin. Amsawa ta yi a hankali, yawan su na ba ta mamaki, kusan su duka gidan suka dawo, ƙasa-ƙasa suke magana, tarkacen da ta ga sun kwaso za ka rantse watanni za su yi a asibitin, da alama abincin ranar da duk ba su ci bane ba za su ci shi yanzun a asibitin. Kujera Zainab ta miƙo wa Anty, don a wajenta ma suka je suka amshi abinci suke faɗa mata Waheedah na asibiti, ta biyosu suka taho tare.
“Haj. Halima wai ɗauko ki suka yi kenan.”
Mami ta faɗi, Anty ta zauna tare da faɗin,
“Ai ba ki kyauta min ba, ko ba za ki shigo ki faɗa min Waheedah na asibiti ba ai sai ki aiko min ko? Ke ce za ki kwana da ita?”
Murmushi kawai Mami ta ɗan yi, dama ta yi niyyar Zainab ta kwana ne, ita da dare sai ta tusa su Aminu a gaba, kirkin Anty ba zai gaji da bata mamaki ba.
“Ya jikin nata?”
Anty ta tambaya.
“Gata nan dai ba ta tashi ba har yanzun…”
Mami ta faɗi, su Nabila da suka fara faɗa da Salim Anty ta kalla.
“Zan ci ubanku wallahi, ku kamar kaji, ba kwa zama waje ɗaya?”
Harara Salim yake watsa wa Nabila.
“Anty hannuna ya fara taɓa plate din…”
“Ni na riga gani, Anty kice ya bar min su ci shi da Aminu…”
Nabila ta faɗi a taɓare, Salim ya samu damar fisge plate ɗin.
“Ku ci tare ke da shi…”
Shagwaɓe fuska Nabila ta yi, idanuwanta na cika da hawaye.
“Ni ba zan ci da shi ba.”
Numfashi Anty ta sauke.
“Na sake magana akan ku sai kun koma gida, tun da ba yara bane ku, da ina son yin surutu da na taho da Albarkah…”
Sanin halinta ya sa suka nutsu, tare suka zuba abincin, tana kallo suna kaiwa cokulan juna karo, ɗauke idanuwanta ta yi daga kansu, don sun saba, kullum cikin faɗa suke, ko makaranta za su je haka suke kamar kaji. Kuma ta rasa kalar faɗan nasu, randa ya jibgeta kuma tana kuka haka za ta bishi su tafi tare. Indai ka ce za ka shiga rigimar su kaine za ka sha kunya.
“Ikram ce kika goya haka?”
Anty ta tambaya tana ɗaga hijab ɗin Mami, ta ga yarinyar ta farka tana ta kalle-kalle.
“Idon ta biyu ma…”
Cewar Anty.
“Ikon Allah…”
Mami ta faɗi tarey miƙewa ta kwance goyon ta sauko da Ikram.
“Ke baiwar Allah babu magana…”
In ji Mami yayin da take gyara wa Ikram ɗin zama, da alamu haƙurin mahaifiyarta ta biyo. Sam yarinyar ba ta da rigima, ruwa ta karɓa ta zuba a murfin tana ba Ikram ɗin.
“In kuma ba sa ba ‘yarsu ruwa fa?”
Anty ta bukata.
“Ni dai ai na bata, wannan shirmen nasu na zamani ba danie za a yi shi ba, cikin su babu wanda ba wayruwa ba, me ya same su?”
Dariya Anty tayi.
“Ni kaina ba zan iya ba wallahi, gani nake ɗaukar alhaki ne…”
Hira suke a hankali a hankali, Anty ita tasae Mami ɗan tsakurar abinci, don damuwa ce fal ranta.
“Ba za a zuba a mika wa Abdulƙadir ba kuwa? Yana wajen nan.” Mami ta faɗi, hakan ya sa Anty kallon ta.
“Ni rabani da wannan don Allah, ya koma gida ya ci wajen ɗaya matar tashi, ban zubo abincina da shi ba ni kam.”
Shiru Mami ta yi, sai dai duk yadda taso ta nuna halin ko in kula da Abdulƙadir ɗin sai ta kasa, Ikram ta miƙa wa Anty tare da miƙewa ta taka zuwa ƙofa ta sa hannu ta buɗe ɗakin ta leƙa kai, yana zaune kuwa ya haɗe kanshi cikin hannayen shi.
“Abdulƙadir…”
Ta kira shi a hankali tana kallon yadda ya ɗago kai, idanuwan shi sun sauya launi. Yanayin ƙaddarar su na yi mata nauyi.
“Ba za ka shigo ka gan ta ba?
Abinda yake son yi kenan, amma ya kasa, yanzun ɗin ma kunyar Mami ta sa shi sadda kanshi kasae ya kasa cewa komai.
“Ka shigo ka ganta…”
Mami ta umarta, sai da ta ga ya miƙe tsaye tukunna ta dawo da kanta cikin ɗakin, a hankali ya tako yana shigowa, daga bangon kusa da ƙofar ya tsaya ya jingina bayan shi a jiki, inda Mami take zaune ta koma ta zauna. Idanuwan shi ya tsayar kan Waheedah da nata suke a rufe da alamun bacci, duk da haka yana jin gaba ɗaya idanuwansu na yawo a jikin shi. Ya zaɓi ƙin kallon su ne kawai don ba ya son yagae kallon tuhumar da suke mishi.
Zuciyar shi yajie ta yi tsalle tana shirin dawowa cikin maƙoshin shi, kafin ta koma mazauninta ta ci gaba da wani irin bugawa da yake ji ba cikin kunnuwan shi kawai ba, har a ko’ina na jikin shi, bai tsammaci Waheedah za ta buɗe idanuwanta da sauke cikin nashi ba.
“Waheedah… Alhamdulillah…”
Ya ji muryar Anty ta faɗi, yana kuma jin motsin ƙannen shi da suke miƙewa suna tahowa suka yi wa gadon Waheedah ɗin rumfa, ya dai daina gane me suke ta faɗa, saboda har lokacin idanuwan Waheedah na cikin na shi, kallon shi take da wani irin yanayi da ya sa zuciyar shi rawa. Ya sha ganin yanayi da dama cikin idanuwanta, ƙaunar shi na ɗaya daga cikin yanayoyin da suka rinjayi sauran, suka rinjayi lokutan da ko a ƙasan ɓata mata ran da yakan gani akwai ƙaunar shi. Wannan yanayin baƙo ne, kuma ba zai wa kan shi ƙarya ba, ya soma ganin alamun shi wajen kwana huɗu da suka wuce. Sai dai duk idan ya ga giccin yanayin yakan ga alamun ƙaunar shi da yake son rinjayar ko menene ɗin yake gani.
Yau kam kallonta yake, duba idanuwanta yake yi sosai yana neman alamar ƙaunar shi a cikin su ya rasa, a hankali yake girgiza mata kai, akwai inda ta ɓoye soyayyar shi, ba za ta yi mishi haka ba, Waheedah ce ya sani, ƙaunar shi wani ɓangare ne na rayuwarta da ba ta ɓoye mishi, ba za ta fara ba yau, bakinta ya ga ya fara motsawa kafin yajie dirar muryarta cikin kunnuwan shi da faɗin,
“Mami dan Allah ku bani waje inyi magana dashi…”
Ba zai ce ga asalin abindae yake ji ba, amman ya san ba ya son su bar ɗakin, ba ya son fuskantar ta, a karo na farko da yake son guje wa fuskantar wani abu, bai taɓa hango zuwan ranar nan ko a mafarkin shi ba.
“Ko ruwa ki sha…”
Anty ta faɗi, yana kallo Waheedah ta girgiza mata kai, har lokacin shi take kallo da yanayin nan cikin idanuwan ta.
“Ina son magana da shi don Allah…”
Ta sake furtawa, yana kallo daga Mami har Anty suke miƙe, su Salim suka fara wucewa sue fita daga ɗakin. Anty ce ƙarshe, ba ta fita ba sai da ta ɗan tsaya tana mai wani irin kallo kamar tana son yawo da idanuwanta cikin zuciyar shi ta ga abinda yake ɓoyewa kowa, tukunna ta fice tana turo musu ƙofar.
“Ka zo ka zauna…”
Waheedah ta faɗi, daga inda yake ta ga ya girgiza mata kai. Zuciyarta take jin ta daskare a ƙirjinta, ta dunƙule waje ɗaya kamar dutse, ta ɗauka da ta yi hakan ba za ta yi mata ciwo ba, ba za ta ji yadda take dukan ƙirjinta da wani yanayi da yake barazana da numfashinta ba.
“Magana zamuyi Abdulƙadir…”
Ita kanta sai da ta ji sunan ya dira cikin kunnuwanta da wata murya da ta sa jikinta ɓari, balle Abdulƙadir da yake jin ƙafafuwan shi na rawa, yaune karo na farko a tsawon rayuwar shi da ta furta sunan shi kai tsaye haka.
“Waheedah…”
Ya kira da bayanannen mamaki a fuskar shi da muryar shi.
“Idan ba za ka zauna ba shikenan.”
Cewar Waheedah cikin sanyin muryarta ɗin nan, da yau yake taɓa shi a wuraren da bai san akwai su a jikin shi ba.
“Waheedah…”
Ya sake kira yana jiran hakan ya yi tasiri a kanta kamar ko da yaushe. Sai dai cikin idanuwanta yake ganin katangar da ya kasa ko motsi balle ya yi wani abu akanta tana ginuwa a tsakanin su, kai yake girgiza mata a hankali, kamar hakan kaɗai ya isa ya hana abinda yake faruwa ya faru.
“Aurenka zakae saukakey min!”
Maganar ta jima tana mishi yawo kafin ta samu wajen zama tana sa shi kokawa da shaƙar numfashin da yake yi ta hanci, buɗe baki ya yi ya fara shaƙar iskar ta bakin shi ko za ta wadace shi, ya kai mintina biyu a haka kafin ya ja wani irin numfashi, buɗaɗɗiyar muryar shi ya sake buɗewa da wani yanayi ya ce da ita,
“Kar ki sake min irin wasan nan, ba na so, kar ki sake.”
Wata dariya ta yi da sautinta ya yi mata wani iri har a cikin kunnuwanta, kafin wasu hawaye masu ɗumi da ba ta da iko da su suka zubo mata.
“Ba wasa nake ba, Sadauki ba wasa nake ba.”
Lumshe idanuwan shi yayi yana buɗe su, Sadaukin da ta kira shi ya rage bugun da zuciyar shi take yi, ya kuma ba shi ƙarfin raba jikin shi da bangon wajen ya ƙarasa in da take ya ja kujerar ya zauna gab da gadon nata, hucin numfashin shi da taji kan fuskarta ya sa ta runtse idanuwanta, wani irin abu na tsirga mata har ƙasan zuciyarta, sanannen yanayin da ta kan ji duk idan ya yi kusa da ita haka take jira ya dirar mata, amma shiru, babu ko alamar shi, hakan yasa ta buɗe idanuwan nata tare da jan jikinta ta miƙe zaune, bayan ta jingina da gadon da take kai tana kallon shi.
A duk jikinta take jin lokacin da take jira ya yi, lokacin da ba ta san ta ɗibar wa zama dashi ba sai yanzu take ji har a ƙasusuwanta ya cika.
“Ka sauƙaƙe min auren ka.”
Ta sake maimaitawa, wannan karon shi ya yi wata ‘yar dariya yana kallonta kamar ta samu taɓin hankali.
“Doctor ɗin nan ya ce babu wata matsala, haka yace ba ki samu wata matsala ba…”
Abdulƙadir yake faɗi, maganganun Waheedah ɗin na tabbatar mishi ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta, da hankalinta ba za ta furta mishi irin waɗannan kalaman ba, ba zai yiwu ta sake maimaita kalaman ya sauƙaƙe mata auren shi ba.
“Ki kwanta ki huta sosai kina ji na?”
Ya yi maganar yana ɗaga mata girar shi, cikin yanayin da take jira hannunta da ta ji ya motsa ya sauka akan fuskar shi, sai ta ji shi akan tata fuskar tana shafa kuncin ta, cikin yanayin da ya sashi saurin faɗin,
“Waheedah…”
Wasu hawayen ta ji da suka fi na ɗazu ɗumi sun sake zubo mata.
“A gaban yarana, Sadauki a gaban yarana…”
Take faɗi tana jin wani ɗaci na taso mata daga ƙirjinta, kalmar haƙuri na ɗaya daga cikin kalaman da ba ya amfani dasu, shi ya sa yanzu da yake neman
ta inda zai fara furtawa ya kasa, in dai abinda take son ji kenan zai kokarin furta mata ko za ta dawo cikin hayyacinta.
“Ka sauƙaƙe min aurenka, don Allah ka sauƙaƙe min aurenka.”
Take faɗi tana kamo hannun shi, da sauri ya riƙe hannun nata yana dumtsewa, yana jin siraran yatsunta da suke barazanar ballewa a kowane lokaci cikin nashi, su suka sa shi sassauta riƙon da ya yi mata.
“Ba ki san me kike faɗa min ba ko? Ba ki san kalaman da suke fitowa daga bakin ki ba ko?”
Abdulƙadir yake maganar yana yawata idanuwanshi akan fuskarta, yana so ta kalle shi, yana so ta ga shine Abdulƙadir. Kamar ta san hakan yake nufi ta furta,
“Na gan ka…ka yarda dani na ganka, na kuma san me nake faɗi. Ka sauƙaƙe min aurenka nace, kuma wallahi da gaske nake… Don Allah Sadauki.”
Waheedah ta ƙarasa maganar a lokacin da wani irin kuka ya ƙwace mata, ji take in ta ƙara kwana ɗaya da igiyar auren shi a kanta hauka za ta yi.
“Ka ji don Allah…”
Hannun ta ya saki yana jan kujerar shi baya, kai yake girgiza mata, bai san akwai wani waje mai laushi daya rage a zuciyar shi ba sai yanzun da Waheedah ta sa kalaman ta a dai-dai wajen tana dannawa. Yana ala=anta wannan hargitsin da yake ji da yadda ya jima bai ji tashin hankali ba. A gaban shi abokan aikin shi babu adadi suka tarwatse, wasu daga cikinsu sassan jikin su na dukan jikin shi harda fuskar shi, a gaban shi harsashin bindiga ya sha fasa kan abokan aikin shi, mutanen da ya yarda da su da rayuwar shi, mutanen da ya kwashi shekaru yana kwana waje ɗaya da su a ƙarƙashin ƙasa ko a samanta.
Ba ya jin akwai sauran tashin hankalin da zai gani ya taɓa shi, asali ma ya ɗauka ya jima da katange zuciyarshi da faruwar hakan. Sai yanzun da Waheedah take ƙaryata shi, take nuna mishi raunin katangun da ya gina
“Don Allah Waheedah…kin ji… Don Allah ki daina min wasan nan.”
Da mamaki take kallon shi, take hango raunin da bai taɓa bari ta gani ba wanda da ace sati ɗaya da ya wuce ne ta ji irin taushin nan a muryar shi, ko ta hango rauni haka a cikin idanuwan shi, da tana da tabbacin zuciyarta ta gama narke mata da soyayyarshi da ta jima tana ɗawainiya da ita, da yanzu tana jikin shi ta riƙe shi cike da tsoron kar ta bar ƙofar da wani abu zai sake shiga tsakaninsu fiye da yadda ya riga da ya faru. Amma yau babu abin da hakan ya ƙara banda sa zuciyarta yin wani tauri fiye da yadda take jin ta a ƙirjinta.
Ganin da gaske bai ɗauka cikin hankalinta take magana ba yasa ta faɗin,
“Mami…”
Cikin wani sabon hargitsin Abdulƙadir yake kallon Waheedah da take hawaye kamar an buɗe famfo.
“Mami!”
Ta sake faɗi da karfin da ya sa Mami turo ƙofar babu shiri, ganin kukan da Waheedah take yi ya sa Mami faɗin,
“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un….Waheedah? Me yake faruwa haka?”
Salatin da Mami ta yi ya sa Anty biyo bayanta tana ma su Salim alamar da su tsaya nan inda suke kar su biyo su, ita ta ƙarasa da sauri gefen Waheedah ɗin ta zauna tana riƙo ta jikinta. Kuka Waheedah take yi kamar numfashin ta zai ɗauke , kallonta Abdulƙadir da ke zaune yake yi yana jin shi kamar a mafarki, yana jin irin shirun da ya ji lokacin da bomb ya fara tashi da abokan aikin shi a karo na farko a gaban shi, shiru ne da bai taɓa fatan ya sake jin irin shi ba, bai ɗauka akwai abin da ya isa ya sake saka shi jin irin shi ɗin ba ma, sai yanzun.
“An…Anty…”
Waheedah take faɗi tana jin numfashinta na mata wani sama-sama.
“Waheedah don Allah ki daina kukan nan… Kin ji…duk gamu nan, ko ma menene, muna nan tare dake, kina ji na?”
Kai Waheedah take girgiza wa Anty tana ci gaba da wani irin kuka da yasa jikin Mami yin sanyi, don ita kam tana tsaye ta rasa abin da ya kamata ta yi.
“Anty ku ce ya sauƙaƙe min, don Allah ku ce Sadauki ya sakeni!”
Ba Abdulƙadir ɗin ba, har su Mami sai da suka girgiza da kalaman da Waheedah ɗin ta furta.
“Kun ji, ku ce kar ya fita daga ɗakin nan bai rabani da auren shi ba…”
Wannan karon Anty nata idanuwan cike yake da hawaye, fuskar Waheedah ɗin ta ɗago tana kallon ta,
“Waheedah kin san me kike faɗa?”
Anty ta tambaya cike da tashin hankali, ta san auren Waheedah da Abdulƙadir wani irin aurene da yake cike da hargitsi, ta hango mutuwar shi a watanni kusan takwas da suka wuce, amma bai mutu ba, ba ta san dalilin da ya sa sai yanzu ba. Duk da za ta yi ƙarya idan ta ce a watannin baya ba ta so mutuwar auren ba, ko don kwanciyar hankalin Waheedah ɗin, amma yanzu da take ganin abin na shirin faruwa a gaban idanuwanta, tashin hankalin da take ciki ba zai misaltu ba.
Miƙewa Abdulƙadir ya yi.
“Ina zaka je? Ka dawo fa, kar ka fita ba ka rabani da auren ka ba… Ka dawo.”
Waheedah take faɗi tana kai hannu ta fisge ƙarin ruwan da ke jikin ɗaya hannun nata. Mami kallon ta take tana da tabbacin ba a cikin hayyacinta take ba. Hannu Abduladir ya ɗaga ya kasa magana, kafin da ƙyar yace,
“Iskar da ke ɗakin ta min kaɗan… Zan fita in shaƙi iska ne.”
Ya yi maganar muryar shi can ƙasan maƙoshin shi.
“Ka sauƙaƙe min sai ka fita ka sha iskar…”
Waheedah ta faɗi tana sa hannu ta share hawayen da ke fuskarta, ta tsayar da idanuwan ta akan fuskar shi da wani irin yanayi da ya sa bugun zuciyar shi ƙaruwa. Juyawa yayi.
“Sadauki… Sadauki!”
Bai ko juya ba, tafiya yaci gaba da yi yana ganin ƙofar ɗakin ta mishi nisa, kafin ya samu ya fice, ko ƙofar bai ja musu ba, Anty ta riƙe Waheedah gam, don shirin sauka take daga kan gadon ta bi Abdulƙadir.
“Anty ki sakeni, kuna kallo fa ya fita, Mami ki bi shi ki karɓo min takardata, idan ba zai rubuta ba ya faɗa miki da bakin shi ki dawo ki faɗa min…”
Kallon ta Mami take yi kawai.
“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”
Ta furta a hankali tana ci gaba da maimaitawa, don ba ta san wani abu da ya kamata ta faɗi ba. Wannan tashin hankalin da yake faruwa a gaban idanuwanta ya fi ƙarfin ta.
“Anty don Allah ku kira shi, kin ji… Ku kiraa sh…”
Ba ta ƙarasa maganar ba, ta sulale jikin Anty da ta saki wani irin salati a firgice, cikin tashin hankali take girgiza Waheedah.
“Hajiya Sakina ba kallona za ki yi ba, ku kira likita mana…”
Da sauri Mami ta fita tana ma su Aminu magana da su kira likitan, kafin kace meye sai ga likitan da gudu, wani ma yana biyo bayan shi, ɗayan ne ya ce wa su Anty su fita daga ɗakin, ya rakasu har bakin ƙofa ya ja ƙofar.
“Me yake faruwa wai? Anty me yake faruwa?”
Zainab ta tambaya cike da damuwa.
“Me ya sameta? Na ga Hamma ya fita a hargitse shi ma… Don Allah ku yi mana magana.”
Cewar Nabila muryarta na karyewa. Hamma da ta faɗi ya sa Anty kallon su Aminu da faɗin,
“Ku bishi don Allah, kar ya ce zai yi tuƙi a yanayin da yake ciki…”
Tsayawa suka yi suna kallon ta cike da rashin fahimta, tsaki ta saki ta kama hanya cikin sauri ta fita daga wajen, sai dai ba ta ga Abdulƙadir ɗin ba, ko alamun shi ba ta gani ba, har wajen asibitin ta duba amma ba ta ganshi ba, wajen da ta ga an ajiye motoci ta nufa tana duddubawa, duk da ba ta jin ta san wacce irin mota Abdulƙadir ɗin yake da ita, kawai dai ta duba ne ko Allah zai sa ta gan shi. Ɗan dafe kai Anty tayi tana faɗin,
“Oh Allah na…”
Ƙasan zuciyarta take addu’ar Allah ya kai shi gida lafiya idan can ɗin ya nufa, kafin ta juya ta nufi hanyar da za ta mayar da ita cikin asibitin Aminu Kano ɗin, a duk jikinta take jin wannan abin ba na lafiya bane!
Masha Allah vry interested stry
Very captivating story. Good luck
#haimanraees