Sai da ya yi wanka tukunna ya ɗauro alwalar sallar Asuba, yana kuma dawowa daga masallaci jakarshi ya haɗa tukunna ya kwanta. Sai lokacin ya kunna wayarshi tun da ya zo Kano. Babban Yaya, Muhsin ne ya ba su, don shi harkar da yake yi kenan, tun yana yaron shago da yake ubangidan nashi ba mai baƙin ciki bane, Muhsin ɗin kuma akwai ladabi da kwantar da kai, kuɗaɗen duk da yake samu sai ya tattara in za a je China saro kayayyaki sai ya haɗa da nashi a ɗan saro mishi abubuwa. A haka har Allah ya saka mishi albarka, duk da ya kammala karatun shi ɓangaren Computer Science, bai nemi wani aikin ba, da sana’ar ya dogara, sai babban café da ya buɗe a wajen rijiyar lemo da shi ma yana kawo mishi rufin asiri.
Shi ma wayar hannun nashi blackberry ɗin ce, danne-danne yake, yana ma rasa abinda zai yi da wayar, lokuta da dama hakan yakan faru tunda aka bashi wayar, idan ya gaisa da su Hajja shikenan, kashewa yake, tana iya kwana biyu a kashe. Yazid ne ya turo ɗakin da sallamar da Abdulƙadir ɗin ya amsa mishi.
“Ni banga amfanin wayarka ba.”
Yazid ya faɗi yana zama gefen gadon da Abdulƙadir ɗin yake zaune ya miƙe ƙafar shi akai.
“Ina amfani da ita mana…”
Kai Yazid ya girgiza cikin rashin yarda.
“Kai ɗan BBM ɗin nan da kowa yake yi ma baka yi.”
Ƙanƙance mishi idanuwa Abdulƙadir ya yi.
“Meye BBM ɗin wai? Nawaf ma ya isheni da maganar kwanaki.”
Dariya Yazid ya yi.
“Kafar sada zumunta ce, amma wayar blackberry ce kaɗai take da shi. Idan ka yi rajista za su baka wasu lambobi haɗe da haruffa, to sune za su zama kamar…”
Hannu Abdulƙadir ɗin ya ɗaga wa Yazid, alamar baya buƙatar ƙarasa ji tare da cewa,
“Bani da ra’ayi…”
Yassar da yake wanka ne ya fito daga banɗaki don yana jin duk hirar da suke yi.
“Ai idan kana son magana da Abdulƙadir sai dai kai mishi text kawai, ko ka tura mishi saƙo ta email ɗinshi. Idan ba za ka iya jira ya kunna wayar shi ku yi magana ba.”
Yassar ya ƙarasa yana ɗaukar mai da ke ajiye a gefen Abdulƙadir ɗin ya kwance ya dangwala yana soma shafa wa hannuwan shi.
“Matar yaron nan tana da aiki.”
Yazid ya faɗi yana sa Abdulƙadir ɗin watsa mishi harara da ƙananun idanuwanshi.
“Ba fa na so Hamma, duka shekara bai fi shekara huɗu ka bani ba.”
Kai Yazid ya girgiza mishi.
“Ban ma baka ko ɗaya ba, yaro sai shegen son girma…”
Turo laɓɓa Abdulƙadir ya yi.
“Ka yi na girmanka Hamma, kar kai na uku.”
Miƙewa Yazid ɗin ya yi.
“Sallama na zo mu yi, rasa kunya…”
Daƙuna fuska Abdulƙadir ya sake yi.
“Wane irin sallama sai kace wanda za a kai kabari? Ina ce makaranta zan koma ba wani wajen ba.”
Numfashi Yassar ya sauke, Yazid na girgiza kai.
“Ba za a taɓa maka abin arziƙi ba kai kam. Allah ya tsare hanya, a kula, banda rashin kunya.”
Idanuwa kawai Abdulƙadir ya ƙanƙance mishi, bai ce komai ba har ya fice daga ɗakin. Hankalin shi ya mayar kan Yassar.
“Wai shafa mai ne haka tun ɗazun. Ka shiga uku kaikam, sai ka ce mace.”
Murfin man Yassar ya jefa mishi yana faɗin,
“Fita daga ɗakin nan don ubanka.”
Dariya Abdulƙadir ya yi.
“Ba inda zan je, ni da ɗakina.”
Ganin Yassar na ajiye robar man da ke hannun shi yasa Abdulƙadir ɗin miƙewa babu shiri, ya fice daga ɗakin yana dariya. Dama yana da niyyar zuwa ya gaisa da Hajja kuma ya yi mata sallama, tunda in ya koma bai san lokacin da zai sake dawowa ba kuma, sai dai ta waya. Da sallama ya shiga ɗakin Hajja, ya samu wasu cikin dangin Abba da su ma duk ranar za su tattafi, yawancinsu ba ya tunanin a garin Kano suke da zama, bai tabbatar ba, saboda ko taron dangi da akan yi duk ƙarshen shekara zai iya ƙirga guda nawa ya taɓa zuwa, suma idan Yassar ya ja shi.
“Sannun ku.”
Ya faɗi yana soma wucewa cikin ɗakin sosai, kafin wata mata da ya san ‘yar uwar Abba ce, amma ba zai tuna ya alaƙar take ba, ko abokiyar wasan shi bai sani ba, ta ce,
“Abdulƙadir baka iya gaishe da mutane ba?”
Juyawa ya yi yana ƙare mata kallo, kafin ya amsa da,
“Sannun kun da nace bai miki ba?”
Ɗaya daga cikin matan ta watsa mishi daƙuwa tana faɗin,
“Karɓi wannan Abdulƙadir, marar kunyar banza. Yayar gyatumin naka kake mayarwa magana haka.”
Ƙanƙance idanuwa Abdulƙadir ya yi yana fara buɗe baki ya tambayeta meta haɗa da Abban nasu da za ta mishi zagin yara, Hajja ta katse shi da faɗin,
“Abdulkadir…”
Juyawa ya yi ya kalli Hajja, ranshi ya gama ɓaci.
“Me yasa za ta yi min zagin yara Hajja? Wacce gaisuwa suke so in musu? Bayan ta musulunci daya wajaba akaina har sannu na musu.”
Runtse idanuwa Hajja ta yi, tana gujema Abdulƙadir bakin mutane.
“Abdulƙadir…”
Ta sake faɗi, wannan karon ranta a ɓace, da gajiya da halayenshi, ba za ta ce bata yi kewarshi a shekarun nan ba, amma bakinta ya huta kwana biyu. Kuma babu wanda ya zo gidan ya ganshi ballantana wani abu ya haɗa su har ya yi musu rashin kunya. Juyawa Abdulƙadir ɗin ya yi yana ficewa daga ɗakin. Hajja ta bi bayan shi, sauri ta ƙara tana wuce shi, ganin ta nufi sashin Abba yasa ran Abdulƙadir ɗin ƙara ɓaci, yasan ƙararshi za ta kai wajen Abba, shi ba ƙaramin yaro ba.
Bayanta ya bi har ɗakin Abban da ta shiga da sallama, yana zaune akan kafet da alama karyawa ya gama yi. Hajja na jin shi yana biye da ita, don haka bata tsaya ɓata lokaci ba ta ce,
“Na gaji da halin yaron nan Alhaji. Yanzun su Hajiya Salamatu ya samu a falo ya yi musu rashin kunya…”
Numfashi Abba ya ja ya fitar yana kallon Abdulƙadir ɗin da yake tsaye. Hakan yasa shi faɗin,
“Ni ba rashin kunya na yi musu ba Abba.”
Juyawa Hajja ta yi tana kallon shi.
“Na maka ta kuɗinka, ka san tambarin gidan mu ce.”
Kai Abdulƙadir ya sauke ƙasa , shi yasa da ya tafi ya shekara biyu bai zo gidan ba, sai an ganshi ne za a saka shi a gaba ana mai faɗa kamar ƙaramin yaro. Juyawa Hajja ta yi tana ficewa daga ɗakin.
“Ni ban musu rashin kunya ba Abba. Na yi sallama fa, har sannu na yi musu. Shi ne za su yi min surutu ban gaishe da su ba.”
Numfashin dai Abba ya sauke da maganganun Abdulƙadir ɗin, addu’a ita ce abinda yake bin yaron da ita, don idan ya ce zai saka ɓacin rai da halayenshi matsala za a samu. Tunda haka Allah ya yi shi da bauɗaɗɗen hali, idan zaginshi akai, ko akai mishi faɗa ba amfani yake ba, dukan ma ko sanda ake mishi ba ji yake ba. Addu’a ita kaɗai ce abinda zai tausasa zuciyar Abdulƙadir.
Hakan yake yawan kwatanta wa Hajiya Safiyya.
“Ka kyauta ai. Ina ce tun jiya da daddare kai min sallama cewar yau da sassafe za ka wuce?”
Abba ya faɗi, kallon shi Abdulƙadir ya yi yana jin wani sabon ɓacin rai, don ya ga alama, Abban na son nuna har ya gaji da shi.
“Yanzun ma sallama naje in mata…”
Kai Abba ya jinjina.
“Allah ya tsare ya kai ku lafiya. A dinga tausar zuciya dai.”
Sai da ya amsa da Amin tukunna ya fice daga ɗakin. Sosai ranshi a ɓace yake, amma ba zai tafi bai wa Hajja sallama ba. Ɗakin ya sake komawa, yana buga ƙafafunshi cikin son sanar da su Hajiya Salamatu bai yi niyyar gaishe su ba, babu kuma wanda ya isa yasa shi yin hakan, ba kuma yadda za su yi da shi tunda ba haihuwarshi suka yi ba. Ɗakin Hajja ya fara shiga ya samu bata nan, fitowa ya yi yana nufar kitchen. Acan kuwa ya sameta tana haɗa shayi.
“Hajja…”
Ya kira, inda yake bata kalla ba, aikin da take yi ta ci gaba, don sosai ya ɓata mata rai.
“Hajja mana… Bana so fa…”
Abdulƙadir ya sake faɗi, ganin bata da shirin kula shi yasa shi kama hannunta.
“Zan watsa maka ruwan shayi idan baka ɓace min da gani ba.”
Wani guntun murmushi ya ƙwace wa Abdulƙadir ɗin.
“Nine fa Hajja…”
Harara ta watsa mishi, yanayin yadda ya ƙanƙance mata idanuwanshi na sa murmushin da bata yi niyya ba ƙwace mata, tana son yaranta fiye da yadda za ta iya faɗi, amma Abdulƙadir daban take jin shi, tun yana ƙarami jin shi take har ranta, ko dukan shi ta yi tana da tabbacin yadda hakan yake mata zafi a zuciya ya fi yanda yake mishi a jiki. Wasu yaran kan zama ƙarfinka, Abdulƙadir rauninta ne.
“Hajja hanya zan hau, bana so in tafi kina min fushi, bayan ban yi komai ba.”
Duka Hajja ta kai mishi a kafaday tana yarfe yatsunta da suka amsa, dariya Abdulƙadir ya yi yana kama hannun nata da ta fisge tana harararshi, ya san ta huce don yana ganin murmushi a idanuwanta.
“Saura a yi ta kiran wayarka a kashe.”
‘Yar dariya Abdulƙadir ya yi.
“Zan kunna in sha Allah.”
Kai Hajja ta jinjina mishi.
“Don Allah ka kula…ka ga girma kake, banda rashin kunya.”
Daƙuna mata fuska Abdulƙadir ya yi.
“Nifa bana rashin kunya.”
Rausayar da kai Hajja ta yi.
“Hmm…”
Kawai ta iya faɗi, Abdulƙadir ɗin ya yi mata murmushi yana ɗorawa da,
“Sai mun yi waya.”
Kai ta jinjina mishi.
“Allah ya tsare ya bada sa’a…”
“Amin. Zahra fa? Hamma Mubarak ma ni sau ɗaya na ganshi tun da na zo.”
Kofin shayi Hajja ta ɗauka tukunna ta ce,
“Kasan wannan hidimarshi ta fi karfin shi, nima da muke kwana gida daya, sai in yini ban saka shi a ido ba. Zahra kuma tana ɓangaren Hajiya Halima nake ji…”
Kai Abdulƙadir ya ɗaga mata kawai, sai da ya samu plate ya zuba soyayyiyar doya da ƙwai da ta yi, ya ɗauki shayin da ta haɗa mishi, tukunna ya sake yi mata sallama yana ficewa daga ɗakin ya nufi ɓangaren su.
*****
Tare suka fito da Yassar, jakar Abdulkadir ɗin riƙe a hannun shi, sai wallet ɗinshi a ɗayan hannun, gaban mota ya buɗe yana jefa jakar tashi a kujerar baya ta gaban. Ya fito da jikin shi kenan daga motar ya ji an ce,
“Hamma…”
Sanyin muryarta yasa shi sanin ita ce tun kafin ya juya yana sauke ƙananun idanuwanshi akan Waheedah da take tsaye, jikinta sanye da doguwar riga ta atamfa, ta saka farar hular sanyi saman kanta, sai ya ga fuskarta tai mishi fayau. Kallon shi Waheedah take tana jin zuciyarta dake dokawa ta matse waje ɗaya a ƙirjinta. Yanayi ne da bata da kalaman da za ta yi amfani da su wajen fassara shi, bata taɓa jin kewar wani a rayuwarta yadda take jin kewar shi tun kafin ya tafi ɗin ba. Gaishe shi ya kamata ace tayi ta sani.
“Tafiya za ka yi?”
Ta buƙata, bata bari ya amsa ba ta ce,
“Hamma ba ka yi min sallama ba, tafiya za ka yi ba ka yi min sallama ba…”
Ta ƙarasa maganar muryarta na karyewa tana jin hawayen da suke tahowa daga zuciyarta sun cika mata idanuwa taf. Kallonta Abdulƙadir yakeyi, banda Hajja da Abba, babu wanda ya yi mlwa sallama a gidan. Su kaɗai ne yake jin ya zama dole ya yi musu sallama idan zai tafi, wanda ya gani yanzun da zai fito dai sun yi sallama, bai san meye a yanayinta da yake son saka shi jin kamar bai kyauta ba da bai mata sallama ba. Tsintar kan shi yayi da faɗin,
“Zan zo hutun sallah…”
Sai da ta ware mishi manyan idanuwanta tukunna maganganun da ya yi suka zauna mishi.
“Da gaske zaka zo? Don Allah kazo Hamma, ka ji… Kazo don Allah.”
Kai Abdulƙadir ɗin ya ɗan ɗaga mata, yana ciza fatar bakinshi daga ciki, bai san me yasa yace mata zai zo ɗin ba, amma hawayen da yake gani cike da idanuwanta ne baya son su zubo. Murmushi ta yi mishi da yasa fuskarta ƙara mishi haske. Su duka biyun basu kula da Yassar ba har ya wuce ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya zauna yana jiran Abdulƙadir ɗin.
“Sai na dawo…”
Abdulƙadir ɗin ya furta muryar shi can ƙasan maƙoshi. Wani irin yanayi kalmomin nashi suka jefata, ji take kamar zai tafi da wani ɓangare na zuciyar ta, lokaci ɗaya ta nemi tsallen da zuciyarta take mata na jin zai zo hutun sallah ta rasa. Sai kewar shi da ta ƙara danneta.
“Kamar karka tafi.”
Ta furta muryarta a karye, tana saka shi runtse idanuwanshi ya buɗe su tare da ƙanƙance su akanta. Hannunshi ɗaya yasa ya laluba aljihunshi duka biyun, da alama bai ji abinda yake nema ba, juyawa yayi sai lokacin yaga Yassar, kanshi ya zira ta jikin murfin motar yana faɗin,
“Dan ba ni biro…”
Cike da mamaki Yassar ya ce,
“Biro kuma?”
Daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi.
“Idan za ka bani ka bani kawai Hamma, meye namun tambaya kamar na maka wani yare?”
Kallon shi Yassar ya yi.
“Ba zan bayar ba to.”
Da alamun gajiya Abdulƙadir ya ce,
“Hamma mana… Ka bani ni kam.”
Kallonshi Yassar ya sake yi, baisan me zai yi da biro ba, amma saboda Waheedah da take tsaye yasa shi dudduba cikin motar, ya ko samo wani baƙi ya miƙa wa Abdulƙadir ɗin, karɓa ya yi yana takawa inda Waheedah take tsaye. Ba shi da takarda, ba shi da kuma lokacin zuwa nemo wata. Hannunta ya kamo, yana share yanda ta ware mishi manyan idanuwanta cike da mamaki, zuciyarta na yin wani irin tsalle ta dawo cikin hannun nata daya riƙe, bin shi ta yi da kallo tana mamakin yadda akai baya kyarma, don tana jin yana kyarmar daga ciki. Rubutu Abdulƙadir ɗin ya yi mata a hannun tukunna ya saki yana juyawa ba tare da ya ce komai ba.
Kallo Waheedah ta bi shi da shi har ya shiga mota ya ja murfin ya rufe, da ido ta rakasu har gate suka fice, ko sau ɗaya Abdulƙadir ɗin bai juyo ba balle ta yi tunanin ko hannu zai ɗan ɗaga mata cikin alamar bankwana, jikinta take jin kamar an mata allurar rashin kuzari, sai da ta ga mai gadi ya ja gate ɗin gidan ya rufe tukunna ta ɗago hannunta da take jin har zufa-zufa yake ta buɗe tafin hannun tana juyo da shi saboda ta ga me ya rubuta. Lambar wayar shi ce da adireshin shi na email, ɗayan hannunta ta sa tana shafar rubutun tare da yin ‘yar dariya, sosai Abdulƙadir yana da ƙoƙari ko da suke Islamiyya da boko, a ajinsu kaf babu wanda yake kamo shi, amma bai da rubutu me kyau, zaka rantse ɗan firamare ne ya yi duk idan ka gani.
Hannunta ta sake dubawa tana kallon lambobin tare da rufe idanuwanta ta karanta su cikin kanta inda suka samu wajen zama daram. Adireshin email ɗin ta duba ‘Abugaje@yahoo.com’ ta haɗa da lambar wayar tana samar musu waje me kyau ta adana, hannun da ke da rubutun ta ɗaga wajen tana ɗorawa a ƙirjinta inda zuciyarta take dokawa da wata irin nutsuwa tukunna ta juya tana nufar ɓangaren su, tana jin tafiyar da take kamar akan gajimare.
*****
Idanuwan shi ƙofar gidansu Nuriyya ya sauka suna fita, sai ya tsinci kan shi da sauke wani numfashi da bai san yana riƙe da shi ba, ba zai ce ga asalin abinda yake ji ba, amma idan da Nuriyya za ta kasance tsaye a ƙofar gidan hakan zai mishi daɗi, gyara zama ya yi cikin kujerar yana lumshe idanuwan shi, numfashi ya sake ja, kafin ya fitar da shi Yassar ya ce,
“Me ke damunka?”
Idanuwan shi ya buɗe yana juya kanshi ɓangaren Yassar ɗin da ya ɗan juyo ya kalle shi yana sake mayar da hankalin shi kan tuƙin da yake yi.
“Kai ido kamar an saka wa sakwara ɗan yatsa, kai ta ƙara ƙanƙance su…”
Daƙuna mishi fuska Abdulƙadir ya yi.
“Kana cewa Ma sha Allah Hamma, kyawun idanuna yasa kuka cinye mun tun ina ƙarami…”
Dariya Yassar ya yi.
“Banza. To har kai shekara wajen huɗu in za a yi hoto idanuwanka ba sa fitowa.”
Murmushi Abdulƙadir ya yi yana faɗin,
“Allah ya yafe maka…”
Dariya Yassar ya sake yi, muryar shi wannan karon babu alamun wasa ya ce,
“Da gaske, me yake damun ka?”
Ɗan ɗaga kafaɗu Abdulƙadir ɗin ya yi, bai san me yake damun shi ba shi kanshi, kawai dai wani sanyin jiki yake ji na ban mamaki, kuma ba zai ce wa Yassar ya so ya ga Nuriyya a tsaye a ƙofar gidan ba, saboda ba shi da dalilin da zai ji hakan, bai kuma san abinda ya sa yake jin hakan ba. Shiru Yassar ya yi, don ta gefen idon shi ya ga Abdulƙadir ɗin ya ɗaga mishi kafaɗa, ya kuma san ba sake wata magana zai yi ba, idan wani abin ma yana damun shi sai ya ga dama zai faɗa mishi.
“Kardai ka bari koma menene ya dameka.”
Yassar ya ce wallet ɗin shi Abdulƙadir ɗin yake wasa da ita, maɓallin yake ɓallewa yana mayarwa, kafin ya sauke idanuwan shi akan wallet ɗin lokacin daya ɓalle maɓallin, ƙaramin hoto ya gani a jiki, bayan shi a juye, daƙuna fuska ya yi, a hankali yake furta,
“Ba duka na bata ba?”
Ɗan kallon shi Yassar ya yi.
“Magana kake?”
Ɗagowa Abdulƙadir ya yi yana girgiza wa Yassar kai, kafin yasa ɗan yatsan shi ya zaro hoton yana juya shi, daƙuna fuska ya sake yi ganin hoton Waheedah, kafin dariyar da bai san daga inda ta fito ba ta ƙwace mishi. Yana da tabbacin ko gawayi aka shafa ma Waheedah a fuska sai idanuwanta sun nuna alamun farinta, yadda akai ta kubce wa zama zabiya abin jinjina ma ikon Allah ne. Juya hoton ya yi yasaka shi dai-dai a cikin wallet ɗin, haka kawai ya tsinci kanshi da saka ɗan yatsa ya shafi fuskarta da ke jikin hoton, kamar zai ga tsoron shi ya cika manyan idanuwanta.
Ji ya yi an fisge wallet ɗin, da sauri ya bita da shirin kamowa, Yassar ya mayar da ita ɗayan bangaren yana daga cinyar shi ya saka wallet ɗin.
“Tuƙi nake Abdulƙadir…”
Hararararshi Abdulƙadir ya yi.
“Hamma bana so, bana so, ka bani wallet ɗina.”
Murmushi Yassar yake yi.
“Meye kake shafawa da ɗan yatsa? Dariyar me kake kuma?”
Ƙanƙance idanuwa Abdulƙadir ya yi.
“Ina ruwanka? Karka buɗe, kabani wallet ɗina…”
Gudun motar Yassar ya rage yana zaro wallet ɗin daga ƙarƙashin cinyar shi ya buɗe, ɗan kallo ya yi tukunna ya mayar da idanuwan shi kan titi, wannan karon shi ya daƙuna fuskar shi da take ɗauke da bayanannen mamaki ganin hoton Waheedah ɗin.
“Ka bani Hamma, ni bana son irin wannan. Ai zubda girma ne kana ɗaukar abin ƙaninka. Ba sai ka ja in rainaka ba.”
Abdulƙadir ɗin yake faɗi yana miƙa jikin shi ya fisge wallet ɗin daga hannun Yassar ya ɓalleta yana ɗan ɗaga jikin shi ya saka a aljihu. Kallon shi Yassar ya yi yana rasa abinda zai faɗa, sosai mamaki yake yi.
“Karka fara abinda ba za ka iya kƙarasawa ba Abdulƙadir , karka fara.”
Yassar ya ce da wani yanayi a muryar shi da yasa Abdulƙadir ɗin kallon shi cike da ruɗani.
“Kar in fara me?”
Wannan karon sosai Yassar ya rage gudun motar, yana jin wanda suke bayan shi suna danna mishi hon, alamun idan shi bai da gurin zuwa su suna da shi, amman bai damu da su ba, Abdulƙadir ya kalla sosai yana son karantar gaskiyar abinda yake tunanin, amma banda confusion babu abinda yake fuskar Abdulƙadir ɗin. Murmushi Yassar ya yi yana girgiza mishi kai. Idan soyayya ce take shirin ƙulluwa a tsakanin Abdulƙadir din da Waheedah ba zai ƙara mata gudu ba tun kafin Abdulƙadir din ya fahimci akwaita.
“Ni banaso a fara min maganar da bangane ba, ka sani kuma.”
Gudun motar Yassar ya ƙara, tukunna ya amsa Abdulƙadir ɗin da,
“A shaƙeni a fito da sauran mana.”
Wani kallo Abdulƙadir ɗin ya yi mishi, tukunna ya kai hannu yana kunna radio ɗin cikin motar, maganar yake ƙurewa da yasa Yassar bugar mishi hannun da ya janye babu shiri, maganar ya rage yana faɗin,
“Ka ƙarata sai na ci ubanka wallahi, ba zaka cika min kunne ba.”
Daƙuna fuska Abdulƙadir ɗin ya yi ƙasa-ƙasa ya ce,
“Matsala kake da ita Hamma.”
Murmushi Yassar ya yi.
“Idan ma zagi ne ba zan zagu a fili ba, kuma ba zan daku ba…”
Gyara zaman shi Abdulƙadir ɗin yayi cikin kujerar, yana jingina kanshi da jikin kujerar. Idanuwan shi ya lumshe, hoton Nuriyya na tasowa daga inda ya samu wajen zama cikin kan shi yana bayyana a bayan idanuwan shi cikin yanayin da ya sa shi buɗe idon shi babu shiri, kallon hanya ya ci gaba da yi zuciyar shi ta mishi nauyi na ban mamaki.
*****
A ƙasan zuciyarta take jin wani irin fili da tafiyar Abdulƙadir tabar mata, za ta rantse da Allah akwai wani ɓangare nata da ya tafi da shi, sai dai ba za ta iya ɗora ɗan yatsa akan ɓangaren ba, da duk kwanakin da yake ƙarawa da yadda take jin filin na ƙara mata girma. Yanzun ma hakan take ji, komai baya mata daɗi, har littafin da ta fara karantawa na Biebee Isa (ke Alheri ce) tana kwasar dariyar Nenne da dinkum ɗinta, yau ta kasa ƙarasawa. Sosai take jin kewar shi na danne ta. Ga ranar Alhamis ce babu Islamiyya balle ta je ta rage zafi. Nuriyya kuma bata nan, ta je wajen dangin mamanta sada zumunci.
Kujera ta ɗauko ta saka a harabar gidan ta zauna, tunanin ya haɗu mata biyu. Ga na Abdulƙadir, gana Nuriyya da take yi, don ta jima tana mata maganar tsoron faɗuwa jarabawar aji shida, kasancewar makarantar gwamnatin ba wani tabbacin kirki gareta ba, duk da Nuriyya na da ƙoƙari, gashi tunda suka shiga aji huɗu su biyun, banda darasin ingilishi da lissafi, babu abinda suke iya samu su yi ita da Nuriyyan, tunda ita Waheedah ɓangaren Art take, Nuriyyar kuma commerce, a cewarta tana son karantar ɓangaren kasuwanci don ta yi aiki da wani kamfani babba. Ita kuwa Waheedah turanci take son karanta, ta kuma koyar in ta samu hakan.
To satin aka fara biyan jarabawar aji shida ta Waec, bata san ta inda zata fara yi wa Abba maganar Nuriyyan ba, saboda bata son ɗora mishi nauyi fiye da wanda yake kan shi, amma ta tambayo wata makaranta da babu nisa da su, Green olive, kuɗin jarabawar kuma kaɗan zai cika a wanda zai biya mata ita kaɗai a Sheikh Bashir su zana anan Green Olive ɗin ita da Nuriyya. Kamar daga sama ta ji an tafa hannuwa a saitin fuskarta da ya katse mata tunanin da ta yi zurfi a ciki, tana sauke idanuwanta kan fuskar Yazid dake mata murmushi har dimple ɗin gefen fuskar shi ya bayyana.
Kaf ɗakin Hajja, har matan babu mai kyawun Yazid, ga sumar dake fuskar shi ta ƙara mishi wani kwarjini na ban mamaki, abinka da wanda yake da hasken fata.
“Hamma Yazid…”
Waheedah ta faɗi tana mayar mishi da murmushin da yake mata.
“Tunanin me kike haka?”
Kai Waheedah ta girgiza mishi a hankali, ɗaga mata girar shi duka biyun Yazid ya yi, alamar bai yarda ba. Inda kujerun robar suke ya ƙarasa yana ɗauko guda ɗaya ya dawo da ita kusa da Waheedah ya zauna.
“Ban san ƙanwar tawa da karya ba.”
A kunyace Waheedah ta sadda kanta ƙasa tana wasa da yatsunta, sosai yake jin kominta har ranshi. Shi ba mutum bane mai son hayaniyar duniya, shi yasa jininsu ya haɗu da Waheedah ɗin, sanyin halinta ya mishi.
“Kinsan za ki iya faɗa min damuwarki ko?”
Ya buƙata a tausashe, numfashi Waheedah ta sauke.
“Da gaske babu komai Hamma.”
Kai Yazid ya girgiza mata.
“Aikam za mu yi faɗa yau.”
Ɗan murmushi Waheedah ta yi.
“Ina son in ma Abba magana ne, kuma ina jin nauyi.”
Sake gyara zaman shi Yazid ya yi.
“To ni ki min maganar.”
Ɗago fuskarta ta yi tana kallon yadda ya bata gaba ɗaya hankalin shi, idan wani ya gani zai rantse bashi da wani abu mai muhimmanci da ya wuce saurarenta.
“Ki faɗa min Waheedah…”
Ya umarta cikin yanayin da yasa ta faɗin,
“Nuriyya ce dama, WAEC din da aka fara registration, shi ne nake so in ce ma Abba da kuɗin da zai biya min a Sheikh Bashir, in da hali ya cika sai ya biya mana mu biyun mu yi a Green Olive, nasu da sauƙi na tambayo.”
Murmushin shi Yazid ya faɗaɗa, ya ɗauka matsalar tata mai girma ce, ƙaunar da take wa Nuriyya na tsaya mishi a rai, yana musu addu’ar ɗorewar zumuncin su, don kamar yadda rayuwa bata da tabbaci hakama mutanen cikinta sukan kasance, yana tsoron aminantaka irin haka, yana tsoron ya yi kusanci da mutane su shiga jikin shi su cutar da shi, don yasan yana da raunin zuciya, ba komai yake da ƙarfin ɗauka ba.
“Su Green Olive ɗin nawa ne?”
Ya tambaya, cikin sanyin murya ta ce,
“Dubu talatin da uku.”
Kai Yazid ya jinjina yana miƙewa tsaye tare da faɗin,
“Kiyi mata magana, ta shirya gobe in sha Allah da na ɗauko ku daga makaranta, kafin lokacin sallah ya yi sai mu je ni dake da ita Green Olive ɗin mu ji ya abin zai kasance.”
Da wani irin murmushi da yasa zuciyar shi kumbura ta cika ƙirjin shi taf Waheedah ta kalle shi.
“Za ka yi ma Abban magana ne?”
Kai Yazid ya girgiza mata, sosai yake jinta a ranshi har jikin shi yake jin yana ɗaukar ɗumi da halin da zuciyarshi take ciki a kanta.
“Zan biya mata.”
Ware idanuwa Waheedah ta yi da mamaki, kafin ta ɗago hannuwanta duka biyu tana rufe bakinta da ta buɗe cikin mamaki, kafin ta sauke su, tana sake kallon shi, dariya Yazid yake sosai.
“Ki faɗa mata yau don ta zama cikin shiri, kina ji?”
Ya yi maganar yana juyawa, farin cikin da ke fuskarta zai jima yana tare da shi.
“Hamma!”
Waheedah ta kira tana jin yafda yagama mata komai a ‘yar ƙaramar duniyarta, idanuwanta cike taf da hawayen farin ciki take kallon Yazid daya juyo.
“Na gode da karamcinka… Na gode fiye da yadda zan iya faɗa da kalmar…”
Kai kawai Yazid ya jinjina mata yana juyawa, yanzun kam yadda yake jin zuciyar shi a cike ba iya ƙirjin shi ta tsaya ba, har ko’ina na jikin shi yake jinta. Da gaske yana son Waheedah, yana mata son da yake tunanin da ƙyar ya iya Haƙura ta ƙarasa aji shidan nan bai furta mata ba. Sai dai yana duba ƙanƙantar Waheedah ɗin, yana ganin kamar ya yi wuri, amma har Abba da bikinsu Babangida sai da ya yiymishi magana cewar me yake jira? Idan aiki ne yana da shi, yana da muhallin da zai zauna tunda Allah ya yi mishi buɗi dai-dai gwargwado kasancewarshi Engineer yana kuma aiki da kamfanin gine-gine babba da yake nan garin Kano.
Bai faɗa wa Abba cewar matar tashi a gida take ba, saboda yana son ya fara furta mata tukunna. Idan suka san wacece za su daina mishi surutu kan aure, sosai yake jin lokacin da za ta sani yayi. Da wannan tunanin a ranshi ya nufi ɓangaren su.