Mami ce da ta fito daga ɗaki ta kalli Waheedah da ta ke kwance, tana murmushi ta ce,
"Ki tashi an kusan kiran sallah."
Hannun kujerar Waheedah ta kama tana miƙewa da ƙyar, kanta take jin kamar baya liƙe da jikinta saboda rashin nauyin da ya yi mata. Tunda aka fara azumi babu wanda ya bata wahala kamar na ƙarshen nan, ita bata damu da duk wani aikin gida ba. Amma tana azumi ace ta fita sosai take wahala. Gashi a ɗakinsu kowa zai sha ruwa ranar tunda girkin Mami ne. Amatullah da za ta tayasu wani abin. . .