Skip to content
Part 12 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Da kayanshi rungume a ƙirji ya shiga ɗakin tare da yin sallama, bai samu kowa a falon ba sai Yassar da ya amsa mishi sallamar yana kuma binshi da kallo yana faɗin,

“Meye a jikin kayan da ka rungumosu kamar sabon jariri?”

Murmushin shi Yazid ya ƙara faɗaɗawa, Waheedah ta goge mishi kayan, akwai kalar ƙamshin da ya kula tana yi duk idan ta gifta shi a cikin gida, idan za ta fita ne kawai baya jin tana ƙamshin, sosai kuma yake jinjina ma ƙoƙarinta na wajen ganin ta gujema abubuwan da addini ya haramta mata da mata kan ɗauka ƙananun zunubi a zamanin da ake ciki. Haka kawai yau da ita ya tashi manne a ranshi fiye da kowanne lokaci, shi yasa ya kai mata kayan ya ce ta danne mishi ta kuma shafa mishi turare. Tunda ya amso yake jin kayan har ƙasan zuciyar shi.

“Hamma…”

Yassar ya faɗi ganin yadda murmushin Yazid ɗin yake ƙara faɗaɗa da duk daƙiƙa.

“Karka dame ni Yassar.”

‘Yar dariya Yassar ya yi, harda shi cikin ‘yan gidan wajen yi wa Yazid surutun ƙin nemo matar aure, amma yanayin da yake nunawa yanzun kamar na sabon kamu a soyayya.

“Anya Hamma? Ba ka kamu ba kuwa?”

Daƙuwa Yazid ɗin ya yi mishi, yana tsintar kanshi da jin wata irin kunyar ƙanin nashi da ta bashi mamaki. Sosai Yassar yake dariya yanzun kam.

“Yaa Rabb… Hamma da gaske soyayya kake? Wace mai sa”ar ce?”

Ya ƙarasa tambayar da farin ciki nannaɗe a muryarshi, a ƙasan ranshi har ya fara addu’a da fatan ta gari ce, akan ce ba a shaidar mutum, amman zai tashi tsaye ya yi min yawa shaidar ɗan uwan shi, duk a cikin gidan Yazid ne kawai zai ba da shaida akan shi ba tare da wani shakku ba, ya yarda da nagartar shi ɗari bisa ɗari. Yana da tabbacin matar da duk za ta kasance ƙarƙashin kulawar shi ba za ta taɓa samun dalilin yin koke ba. Yazid mutum ne mai haƙuri da kauda kai akan al’amuran duniya.

“Wacece Hamma? Ka ji? Don Allah wacece?”

Yassar ya sake jero mishi tambayoyin yana saka shi sauke numfashi mai nauyi. Bai taɓa faɗa wa kowa sirrin da yake zuciyarshi ba, har ita Waheedah ɗin da sirrin ya shafa, amma yau yana jin ya faɗa wa wani, yana kuma jin son raba sirrin da wani, wataƙila ya samu ƙarfin gwiwar faɗa wa Waheedah ɗin itama. Ya kuma san Yassar na da sirri ba kaɗan ba, idan ba shi ya ce ya faɗa wa wasu ba, maganar ba za ta taɓa wuce tsakaninsu ba. Cikin sanyin murya Yazid ya ce,

“Bata sani ba har yanzun ai.”

Ɗan ware idanuwa Yassar ya yi.

“Jiran me kake to? Me yasa baka faɗa mata ba?”

Kafaɗun shi duka biyun Yazid ya ɗan ɗaga cikin yanayin da ke fassara shi ma bai san dalili ba.

“Ina ganin kamar ta yi yarinta ne, hakan nake faɗa wa kaina saboda bana son tabbatar da na rasa ƙarfin gwiwa ne.”

Fuskar Yassar ɗauke da murmushin fahimta ya ce,

“Ba a yarinta da sanin ‘So’ Hamma, saboda abu ne mai wahalar sha’ani…”

Kai Yazid ya iya jinjina ma Yassar ɗin, yana jin jikin shi ya yi wani irin sanyi, da gaske ne ya kamata Waheedah ta san yadda ya gama tsara musu sauran rayuwar shi idan yana da rabon gani, bai taɓa hango komai na rayuwar aure da wata idan ba ita ba. Ko a titi ya ga budurwa da saurayi, ita ce take faɗo mishi a rai. Idan kallo yake ya ga wani abu da ya burgeshi, da ita yake hasaso aiwatar da shi. Yana mata kyauta lokaci zuwa lokaci, amma yana jin tamkar ya janyo ranar da zai kashe mata duka kuɗin da suke cikin aljihun shi, ranar da zai siyo duk rigar da ya gani yake tunanin za ta yi mata kyau ya kawo ta saka mishi ya gani.

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskarta na mishi yawo a cikin kwanyar shi, wucewa ya yi da niyyar shiga ɗaki ya saka kaya, Yassar ya dakatar dashi da faɗin,

“Ka faɗa min sunanta idan ban santa ba.”

Sai da ya murza hannun ƙofar ɗakinsu tukunna ya ce,

“Waheedah… Waheedah ce Yassar.”

Wani dum Yassar ya ji cikin kanshi, kafin hanjin cikin shi su hautsina suna saka shi miƙewa babu shiri ya rufa ma Yazid ɗin baya. Yadda ya tura ɗakin ya saka Yazid ɗin tsorata, wani irin yanayi yake gani a fuskar Yassar da ya saka zuciyarshi soma dokawa yana faɗin,

“Yassar?”

Cike da shakku da alamar tambaya, kai Yassar yake girgiza wa Yazid ɗin yana son ya tabbatar mishi ba Waheedah bace yake so, yana son ya gaya mishi bai haɗa soyayya da Abdulƙadir ba, kallon Yazid ɗin yake da idanuwan shi yana roƙon shi da cewar zuciyar shi bata mishi haka ba.

“Yassar…”

Yazid ya sake kira wannan karon muryar shi na rawa cike da tsoro, ko kaɗan baya son abinda tunanin shi yake shirin hasaso mishi, hannu ya ɗan ɗaga wa Yassar ɗin yana saukewa, ƙafafuwan shi har rawa yake jin suna yi, don shi mutum ne mai raunanniyar zuciya. Gadon da yake ɗakin ya laluba ya zauna a gefe, yana jin yadda zuciyarshi ke dokawa har cikin kunnnuwanshi. Yanayin shi kawai da Yassar yake gani na ƙara tabbatar mishi da yadda ya daɗe da soyayyar Waheedah adane a cikin ƙirjin shi batare da kowa ya sani ba. Wani abu Yassar ɗin ya ji yana danne shi, yadda akai bai kula ba na ba shi mamaki, don shi mutum ne mai kula da al’amuran ‘yan uwan shi. Cikin wani yanayi ya ce,

“Hamma…”

Yana tsintar bakin shi da yi mishi nauyi wajen ƙarasa maganar da yake son yi. Halin da Yazid ɗin zai shiga yake tunani. Amma ko jiya da yana neman canji, bayan Abdulƙadir ɗin ya zo ya ɗauki wallet ɗinshi ya buɗe hoton Waheedah na jiki a manne, ya kuma ga ya sake wallet ɗin, amma hoton na manne. Ya san ƙanin shi, ya san ƙaninshi fiye da kowa a gidan. Idan har ya cire hoton Waheedah daga ɗayar wallet ɗin ya mayar a sabuwa tana da muhimmanci a wajen shi, idan har zai ajiye hoton daga farko to yana da tabbacin wani abu na faruwa a tsakaninsu. Idan har zai iya ba zai bari su haɗa yarinya ɗaya da Yazid ba, yana numfashi ba zai taɓa bari wannan rikicin ya faru ba.

“Don Allah Yassar ka ce wani abu, a tsorace nake wallahi.”

Yazid ɗin ya ce yana sa wani abu tsagewa biyu a ƙirjin Yassar ɗin da yake tsaye yana tattaro duk wani ƙarfin halin da zai iya.

“Ba Waheedah ba Hamma, kowacce yarinya banda ita.”

Kai Yazid ɗin yake girgiza mishi yana jin iskar da ke ɗakin na fara yi mishi kaɗan, cikin sabon tashin hankali ya ce,

“Yassar…”

Da sauri Yassar ɗin ya girgiza mishi kai, ganin yanayin da yake fuskar shi, ya tabbatar Yazid na tunanin shi ne yake son Waheedah.

“Ba ni bane, Hamma ba ni bane ba.”

Kanshi Yazid ya ɗan dafe da ya fara ciwo, yana jin alamar zazzaɓi na son rufe shi.

“Abdulƙadir ne, ba zancen soyayya suke ba kai tsaye, amma hoton tane a jikin wallet ɗinshi shekara ɗaya kenan…”

Wannan karon da duk hannayen shi Yazid ya dafe kan shi yana wani irin sauke numfashi kamar wanda ya sha gudu. Zazzaɓin da yake ji na saukar mishi gaba ɗaya. Ɗago fuskar shi ya yi yana saka hannu ya ɗauki hular shi da ke ajiye akan gadon ya soma fifita da ita, don sosai iskar ɗakin ta mishi kaɗan har baya jin tana kai mishi inda ya kamata ballantana ya iya tunanin wani abu. Shi kanshi Yassar ɗin wani irin nauyi yake ji yana danne shi da ba zai ce ga daga inda yake tasowa ba, amma Yazid ɗin ya kamata ya san abinda ya sani shi ma.

“Ko ni ba kullum nake kallon fuskar Abdulƙadir in faɗa mishi magana ba, ba don ina tsoron shi ba, sai don ina gudun ya faɗa min maganar da zan dake shi sai na karya shi. Ina kula da su Hamma, cikin ido Waheedah take kallon shi ta yi mishi magana…”

Sosai Yazid yake fifita fuskar shi, muryar shi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Ka ɗan bani waje…”

Cike da wani irin yanayi Yassar yake kallon shi.

“Hamma…”

Kai Yazid ya girgiza mishi, zuciyarshi yake ji ta kumbura ta cika ƙirjin shi taf, ba ya son ta tarwatse a gaban Yassar, ba ya son ta tarwatse a gaban kowa.

“Don Allah Yassar… Bana son in breaking a gabanka… Abin zai min yawa…”

Numfashi Yassar ɗin ya sauke yana kallon Yazid sosai, cike da son tabbatar da koma meye zai biyo baya, ko ya Yazid ɗin zai karye, zai iya komawa dai-dai. Kamar Yazid ya san me Yassar ɗin yake tunani ya ɗan tattaro sauran ƙarfin da yake ji yana mishi murmushi tare da jinjina mishi kai cike da son tabbatar mishi cewar wannan abin ba zai kashe shi ba, tukunna Yassar ya juya ya fita daga ɗakin. Ƙofar na rufewa Yazid ya kwanta kan gadon yana dunƙule jikin shi. Wani irin ciwo yake ji da bai taɓa tunanin akwai kalar shi ba.

Numfashin shi har tsai-tsayawa yake da yadda kuirjin shi yake zafi, yana jin yadda da duk daƙiƙa wani abu a zuciyar shi yana karyewa tare da faɗuwa a cikin ƙirjin shi da wani irin ciwo da ba shi da kalaman da zai ɗora shi. Bai san tunanin me ya kamata yayi ba, asalima tunani ɗaya yake cike da kan shi da zuciyar shi da ke karyewa.

‘Ba zai haɗa soyayya da ƙanin shi ba.’
Ko rana aka saka mishi da Waheedah ya gane Abdulƙadir ɗin na jinta a zuciyar shi fiye da matsayin ƙanwa zai haƙura ya bar mishi, idan ma Allah bai nufa zai aureta ba, su biyun za su haƙura ta samu wani. Amma soyayyarta za ta kashe shi kafin ya haɗa ta waje ɗaya da ta ƙanin shi. Yanzun yake ƙara gode wa Allah da bai furta mata ba, yana kuma tabbatar da wannan ne dalilin da ya riƙe shi har ya kasa furta mata. Ya fi minti goma a kwance yana son ciwon da yake ji ya lafa mishi ya tashi ya saka kayan shi don masallacin idi zasu tafi su duka gidan.

*****

Tana fitowa wanka, mai ta shafa ta zura doguwar rigar sabuwar atamfarta, ɗankwalin ta ɗaura yadda za ta iya ɗora hijab akai ba tare da ya dameta ba. Fuskarta ta duba a mudubi, atamfar yellow ce da ja, ta yi matuƙar karɓar hasken fatarta, maiƙon fuskarta ta ga kamar ya yi yawa. Farar hodar da take shafawa ta ɗauka ta zazzaga a jikin soson hodar Amatullah don ba za ta tuna ko tana da soson hoda ko bata da shi ba ma. Murzawa ta yi a fuskarta ta ajiye tana sake dubawa. Kayan kwalliyar da banda farar hodar da wasu cikin turarukan dukan su sauran na Amatullah ne take dubawa.

Rasa wani abu da za ta ɗauka ta yi amfani dashi tai. Ko a gida za ta zauna bata tunanin za ta yi wata kwalliya fiye da wadda take fuskarta, ballantana fita za su yi, su dukansu suke zuwa masallacin Idi a gabatar da sunnar da take cikin zuwa sallar Idi. Fuskar mace kan shiga cikin al’aura, wato abinda ya kamata ya zama a rufe duk lokacin da ta tsara mata kwalliya, sharaɗin saka niƙab ya faɗa akanta ko da bata da kyawun da zai karya alwalar maza. Tana yawan tunasar da Amatullah da Nuriyya, amma biris suke da ita, wasu lokutan ma Nuriyya kan ce mata ita ta cika tsawwala lamurran addini.

Sai dai ta san zunuban da yawancin mutane kan ɗauka ƙanana, su ne suke taruwa a hankali har su yi girman da mutum ba zai iya ɗauka ba. kwalli ta hango ta ɗauka ta saka wa idonta, tana ganin yadda fuskarta ta sake fitowa. Da gaskiyar Mami, kwalli na mata kyau. Miƙewa ta yi ta ɗauki turare ta tuna fita za ta yi, ta mayar ta ajiye. Hijabinta da ke a linke ta ɗauka ta warware tana sakawa a jikinta. Dogo ne har ƙasa, sai dai babu hannu a jiki, tana kuma sane ta ɗauko don ƙunshin da yake hannuwanta.

Ƙafafunta ma safa ta saka musu, bata yi ƙunshi don mazan da ba muharramanta ba, ta yi ne don kwalliya. Dogayen takalmanta da suke ajiye ta saka. Amatullah kan mata tsiya cewar tana saka dogayen takalma ne don bata da nauyin da za ta dinga gurɗewa. Dariya kawai Waheedah kan yi, ta riga ta saba ne da dogayen takalman tun yarinta, gashi kuma hijabanta wani lokaci suna ɗan jan ƙasa, idan ta saka dogayen takalman sai ta ga sun fi kyau. Bata ga Mami a gidan ba, har ɗakinta ta leƙa bayan ta fito, tana da tabbacin suna ɓangaren Hajja don yin hidimar bikin sallar da suke haɗuwa su duka huɗun su yi.

Don haka ta fice daga gidan ita ma, yau dai ta shirya da wuri, ba don gugar da ta yi wa Yazid ba ma da tuni ta jima da shiryawa. Babu mai mata mita ta cika sanyin jiki. Takawa ta yi har inda ake ajiye motocin gidan tana samun guda ɗaya ta tsaya a jikinta, saitin da zata iya hango ɓangaren su Abdulƙadir, don shi take so ta gani tunda ta tashi. Ta fi minti biyar a tsaye kafin ta hango shi ya fito, jikin shi sanye da farin yadi da hula riƙe a hannun shi cikin yanayin da yasa bugun zuciyarta ƙaruwa. Ɗago kai ta ga ya yi yana tsayar da shi akanta. Bata hango idanuwan shi daga inda take, murmushi ya ƙwace mata.

Sosai take murmushi da yadda mazaunin idon Abdulƙadir ɗin kawai take iya hangowa daga inda yake. Hakan ya sa ta sauke kallonta daga kan shi, zata rantse idanuwanta kawai ta sauke tana kallon takalmanta, ta sake ɗago su ta ga Abdulƙadir ɗin tsaye a gabanta yana ƙanƙance mata idanuwan shi, zuciyarta ta ji cikin maƙoshinta inda ta yi tsaye tana ci gaba da dokawa.

“Murmushin me kike yi?”

Ya tambaya yana tsare ta da idanuwa, don shi bai ga abin nishaɗi a safiyar ranar ba, kan shi ciwo yake. Gashi komai ba ya mishi daɗi, kai ta girgiza mishi tana saka shi faɗin,

“Taƙabbal Allaahu minna wa minkum.”

Ya ɗora da,

“Ba a yi min ɗinkin sallah ba.”

Cikin yanayin da ya saka wani murmushin ƙwace mata, don yadda ya yi maganar kamar ƙaramin yaron da aka yi wa gagarumin laifi ya sakata jin tamkar tana kan lilo. Komai nashi ya mata, komai a tattare da shi. Amsa gaisuwar sallar da ya yi mata ta yi a hankali har lokacin tana murmushi.

“Ba abin murmushi bane ba, kayan Hamma Yassar na saka, basu min ɗinkin sallah ba, kowa an mishi banda ni.”

Abdulƙadir ɗin ya faɗi yana rasa dalilin da yasa yake gaya mata. Kawai ya tsinci kanshi da son gaya mata ba a yi mishi ɗinkin sallar ba, yana kuma jin son gaya mata duniyar ma bata mishi daɗi, bai san ta inda zai fara ba. Idan tana kusa da shi yakan tsinci kanshi da yin abubuwan da bai san dalilinsu ba. Abu ɗaya yake gani a fuskarta, zai iya yin komai a gabanta, ba za ta taɓa raina shi ba, bai taɓa ganin hakan a fuskar kowa ba sai tata, ko Yassar ba komai yake iya yi a gaban shi ba, a hakan ma ya raina shi don yana ganin ya bashi wasu ‘yan shekaru, shi yasa yake ƙoƙarin ganin ya kama girmanshi a gaban Yassar ɗin.

Ɗayan hannun shi ya ɗago ya buɗe mata shi, links ne a cikin tafin hannun nashi. Hakan yasa ta tattaro hijabin jikinta ta fito da hannayenta da Abdulƙadir ɗin ya bi da kallo, zuciyarshi na faɗa mishi bai taɓa ganin hannuwa masu kyau irinsu ba. Links ɗin ta saka hannu ta ɗauka, Abdulƙadir na riƙe hannun nata.

“ƙunshi kika yi?”

Maganar ta fito daga ƙasan maƙoshin shi lokacin da ya ɗago ɗayan hannun shi yana kamo ɗayan hannun nata da shi tare da duba ƙunshin nata da yake jin na kwance wasu ƙusoshi cikin kanshi. Wani irin yanayi yake ji da ba zai faɗu ba. Motsi yaji a bayan shi, amman bai juya ba, asalima ba ya son ya ɗauke idanuwan shi daga hannuwan Waheedah ɗin, a karo na farko da ko kaɗan tunanin hasken fatarta bai zo mishi ba, baya ganin komai sai jan lallen da ya wani irin fitowa a hannunta.

Tun daga nesa Yazid ya hango su, yana jin zuciyar shi kamar za ta fito waje, don zazzaɓi ne a jikin shi ruf, da ƙyar ya iya fitowar ma, bai san ƙafafuwan shi sun motsa ba lokacin da ya ga Abdulƙadir ɗin ya riƙe hannun Waheedah sai da ya ganshi tsaye a bayan shi, amma daga Waheedah ɗin har Abdulƙadir sun yi kamar ba su san yana wajen ba. Musamman Waheedah da yake ganin tsayuwar duniyarta akan Abdulƙadir ɗin ta cikin idanuwanta, tana saka shi tuna duka lokutan da yake ganin hakan a idanuwanta idan Abdulƙadir na wajen, yana sakashi tunanin kalar sakarcin shi wajen kasa fahimtar abinda yake faruwa a tsakaninta da Abdulƙadir ɗin, don yana tunanin ta yi yarinta ta fahimci wani So ballantana har ta faɗa cikin shi.

“Waheedah…”

Yazid ɗin ya kira yana saka ta zame hannuwanta daga cikin na Abdulƙadir ta ɗan kalli bayan shi inda Yazid yake tsaye.

“Hamma…”

Ta faɗi tana saka Abdulƙadir ɗin juyawa ya kalli Yazid ɗin shi ma.

“Taqabbal Allaahu minna wa minkum.”

Abdulƙadir ya faɗi yana miƙawa Yazid ɗin hannu, karɓa ya yi ya amsa yana kuma yi musu murnar sallah a bisa tsarin addinin musulunci tukunna ya zagaya ta bayan motar ya tsaya, don ƙirjinshi yake ji kamar zai buɗe. Juyawa Abdulƙadir ya yi yana miƙa wa Waheedah hannuwan shi. Dai-dai lokacin da Yazid ɗin ya juyo yana kallon su, links ɗin Waheedah ta ɗaura mishi, idanuwan shi na kan hannayenta da yake jin kamar ya yanke ya koma Kaduna da su, ya manna a jikin bangon ɗakin shi, duk lokacin da ya yi ra’ayi ya juya ya kalla. Hakan da ya yi tunani ya saka shi laluba aljihun shi ya zaro wayarshi daga ciki.

Waheedah na kallon shi, zuciyarta kamar za ta fito waje. Tana kuma kallon shi yana danna wayar, kafin ya kamo hannunta yana miƙar da shi, ya kuma kamo dayan ya ɗora a kan ɗayan cikin yanayin yadda yake son ya gansu, ita kam a gabanshi takan koma kamar ‘yar tsana mai batir da remote, remote ɗin kuma yana hannun Abdulƙadir, yadda duk yake so ta yi hakan yake juyata. Idanuwanta tsaye yake kan fuskar shi, tana jin yadda yake riƙe da’ yan yatsunta, kafin ya saki yana duba wayarshi tare da ɗan ɗaga mata kai cikin yanayin da yasata sauke hannuwanta tana murza su cikin hijab, har lokacin tana jin nashi hannuwan manne a jiki.

Kanshi Abdulƙadir ya ɗan dafe daga gefe yana runtse idanuwa, tukunna ya buɗe su akan Waheedah yana faɗin,

“Kaina na ciwo…”

Bata ce mishi komai ba ya ga ta juya da sauri, yana bin takalman ƙafarta da kallo, ko tunanin ta faɗi cikin dogayen takalman nan bata yi. Yana kuma kula da yadda kusan duka takalmanta dogaye ne. Bayan shi ya jingina da motar yana duba hoton hannuwanta a cikin wayar tashi, blackberry ba dai camera ba, sosai hoton ya ɗauku, shi ya mayar kan wallpaper ɗinshi dama hoton wani lallen ne, wannan dai ya fi mishi kyau. Bai san lokacin da yasa hannu ya shafi screen ɗin wayar ba, yana ƙara wa Yazid Zazzaɓin da yake ji. Don yana kallon duk abinda yake faruwa, bai dai san haka zai mishi zafi na gaske ba.

“Abdulƙadir…”

Ya kira a hankali yana saka Abdulƙadir ɗin juyawa ta ɓangaren da yake ya kalle shi.

“Karka sake riƙe Waheedah, akwai haramci a hakan, ka sani ba saina faɗa maka ba, ba muharramarka bace ba.”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ɗin ya yi.

“ƙunshi ta yi Hamma…”

Ya faɗi kamar hakan zai zama dalilin da zai sa ya riƙe hannuwanta.

“Na dai faɗa maka, ranka zai mugun ɓaci idan na sake gani.”

Yazid ya faɗi cikin yanayin da Abdulƙadir ɗin bai taɓa gani a tare da shi ba. Hakan ya saka shi ɗaga kai a hankali kawai tukunna ya juya yana haɗa bayanshi da motar wajen. Ranshi bai ɓaci ba yau, ba shi da wannan wajen, ƙunshin Waheedah ya ɗauke mishi wannan yau kam, ba shi da lokacin faɗa da Yazid ɗin, duk da ya tsoma mishi baki cikin lamurran da bai ga ta inda ya shafe shi ba. Waheedah ce ta dawo da robar ruwa a hannunta, ɗayan hannun a dumtse, tana sake goge mishi komai da yake cikin kan shi. Robar ruwan ta miƙa mishi, ya karɓa, idanuwan shi kafe kan hannuwanta, don ya ji suna danna mishi tunanin Nuriyya inda yake son ɓoye shi don kar ya sake dawo mishi.

Ɗayan hannun Waheedah ta ware mishi yana ganin Panadol guda biyu, kai yake girgiza mata, a duniya babu abinda ya tsana irin magani, ko rashin lafiya yake baya sha. Yassar ya taɓa tura mishi cikin ayaba yana ce mishi ko ita ce ya ci zai ji ƙarfin jikin shi, kawai yana gutsura ya tauna magani a ciki, kuma ya tsare shi da sai ya haɗiye, har amai ya yi.

“Ba zan sha wani panadol ba.”

Ya faɗi yana ƙanƙance mata idanuwa. Kallon shi Waheedah take yi.

“Kanka na ciwo fa Hamma…”

Daƙuna mata fuska Abdulƙadir ya yi.

“Ni fa ba zan sha wani magani ba.”

Yazid Waheedah ta kalla da yake tsaye yana kallon su, shi ma Panadol ɗin yake buƙata, ji yake kamar ya yi ihu ko za ta ga yana buƙata fiye da Abdulƙadir ɗin ta ba shi.

“Hamma ka yi mishi magana. Kanshi yana ciwo wai ba zai sha magani ba.”

Kallonta Abdulƙadir ya yi yana tunanin idan Zainab ce da yanzun ya kwaɗa mata marin da bakinta ba zai sake gigin kai ƙarar shi ba, amma Waheedah ce, bata yi hakan don ta raina shi ba, yana ganin damuwa tattare da muryarta.

“Ki ƙyale shi tunda ba zai sha ba.”

Yazid ya faɗi, yana kuma jin maganar ta fito daga zuciyar shi da ke wani irin ciwo.

“Hamma…”

Waheedah ta kira cikin sanyin muryarta da ya saka Yazid ɗin juyawa yana dana sanin fitowar da ya yi. Ba zai yiwu yana jin azababben kishin Abdulƙadir ba, Abdulƙadir ne, ƙanin shi, ɗan uwan shi ciki ɗaya. Amma zuciyarshi bata san wannan ba, kishi yake ji har idanuwan shi na lumshewa.

“Me yake faruwa ne?”

Yassar da ya ƙaraso wajen ya tambaya.

“Bakomai…”

Abdulƙadir ya faɗi a lokacin da Waheedah ta ce,

“Kanshi ne yake ciwo kuma wai ba zai sha magani ba, har na ɓallo kuma.”

Kallonta Abdulƙadir ya yi ciwon kan da yake ji na ƙaruwa.

“Ba zan sha ba, ni babu maganin da zan sha. Na ce ki ɓallo min?”

Yake faɗi cike da masifar shi.

“Karɓi maganin nan kafin in ci ubanka, tunda ta ɓallo sai ka sha wallahi. Ka ji na rantse.”

Hannu Abdulƙadir ya miƙa wa Waheedah da take murmushi tana saka shi ƙanƙance ido cikin son watsa mata harara.

“Mincika…”

Yassar ya faɗi yana kwashewa da dariya tare da ɗorawa da,

“Anya ba a yi wa Hajja musayarka a asibiti ba? Abdulƙadir wanne irin ido ne wannan?”

Maganin Abdulƙadir ya saka a bakin shi ya buɗe robar ruwan ya haɗiye tukunna ya watsa wa Waheedah da Yassar ɗin harara, yana saka Yassar sake kwashewa da dariya, mukullin motar shi ya saka a jiki ya buɗe. Bayan motar Abdulƙadir ya buɗe ya shiga, yana daƙuna fuska, tsakanin shi da Allah fushi yake an sakashi shan magani. Yazid ma bayan ya buɗe ya shiga ta ɓangaren shi. Hakan ya sa Waheedah buɗe gaban motar za ta shiga, hango Nuriyya ta yi ta shigo gidan, don tare da ita sukan tafi tunda Babansu ba zai taɓa jerawa ya tafi idi da ita ba.

Irin atamfar jikin Waheedah ce ta saka ita ma, don tare Abba ya yi musu da duka sauran matan gidan. Hijab ne da ko gwiwarta bai kai ba, daga inda Waheedah take tana hango kwalliyar da take fuskar Nuriyya, musamman jambakinta. Tana kuma hango yadda ƙugunta ya fito cikin skirt ɗin da take sanye da shi, don ita riga da skirt ta yi. Kai kawai Waheedah ta girgiza don in ta yi mata magana kan cewa hijab ɗin ya yi ƙarami faɗa za su yi da safen nan. Dama sunyi wani kan Anas. Ƙarasowa Nuriyyar ta yi.

“Wallahi na ɗauka kun tafi, ina ta sauri.”

Kai Waheedah ta girgiza mata.

“Yanzun dai za mu tafi. Na ɗauka ba za ki je ba.”

Harararta Nuriyya ta yi, tana ganin ta mata wani irin kyau na ban mamaki. Dariya Waheedah ta yi ta buɗe gaban motar ta shiga. Zagayowa Nuriyya ta yi ta buɗe bayan motar ta ɓangaren Abdulƙadir da tunda ya ji muryarta ya runtse idanuwan shi yana buɗe su da wani irin bugawa da zuciyarshi ta yi. Har addu’a ya yi kar ya ganta har ya tafi, yanzun ma ƙoƙarin ƙin juyawa yake ya ji ta buɗe ƙofar, bai san lokacin da ya juya ba, ya yi nasarar sauke idanuwan shi cikin nata. Janbakinta na saka wani abu cikin kanshi yamutsawa. Tsarin kwalliyar da take fuskarta na samun wajen zama cikin kanshi.

Kallon shi Nuriyya ta yi, bugun zuciyarta na yin dai-dai da nashi. Yayi mata wani irin kyau cikin farin yadin shi, ga wani irin ƙamshi da yake, yau kam sosai take jin kasancewarta sallah. Murmushi ta yi tana zama cikin motar ta rufe murfin tukunna ta ce,

“Ina kwananku.”

Yassar ne ya amsa yana ɗorawa da,

“Nuriyya an yi sallah lafiya?”

Amsa shi ta yi, turarenta na cika hancin Abdulƙadir ɗin, yana saka shi sauke numfashi a wahalce da yanayin da yake ji. Ɗan matsawa ya sake yi jin yadda ta yi kusa da shi da yawa, amma hakan bai rage mishi komai ba, sai ma hannunta da ya kalla da take gyara hijabinta da shi, itama ƙunshi ne, ja da baƙin lalle da ya saka shi runtse idanuwan shi yana ƙirga ɗaya zuwa hamsin, har ya ji Yassar ya tayar da motar ya juyata suna ficewa daga gidan.

Idanuwan shi ya buɗe yana gyara zaman hannun shi da ya ɗauke babu shiri jin ya taɓa na Nuriyya, ta gefen idanuwan shi yaga ta kalle shi da idanuwanta da ta ja da eyeliner suna ƙara fitowa. Wani abu Abdulƙadir yake ji tun daga ɗan yatsan ƙafarshi zuwa tsakiyar kanshi da kusancin da Nuriyya ta yi dashi. Ita kam yau ranta ƙal ta zauna kusa da Abdulƙadir, ta kuma lura da a takure yake, za ta ji daɗi idan ya zamana ita ce ta yi affecting ɗinshi haka, yana nufin koyayane ya damu da zamanta. Inda idanuwan shi suke kallo take nema kafin ta kula da hannunta ne, ɗayan hannun ta zaro tana ci gaba da wasa da yatsunta.

Abdulƙadir na kula da yadda har cikin tafukan hannuwanta ita ma ƙunshi ne, sai dai nata da ratsin baƙi, na Waheedah kuma gaba ɗaya jan lalle ne. Da ƙyar ya raba idanuwan shi da hannayenta. Don yana gab da riƙe su, ita kanta ji yake kamar ya sa ɗan yatsa ya dangwali jambakin da yake leɓenta ya ji yana da maiƙo ko idanuwan shi ne kawai suke gane mishi har Kjyalli yake. Da gaske zuciyar shi raini take neman ja mishi, yana da wannan tabbacin yanzun.

‘Kar mu yi haka da ke, don Allah, term four na shiga. Ba yanzun zan yi settling ba, sai na gama NDA na fito, an yi posting ɗina wajen da zan yi aiki na nutsu tukunna.’

Abdulƙadir yake magana da zuciyar shi yana roƙon ta da ta saurare shi, ba shi da wajen soyayya yanzun. Baya komai a rayuwarshi babu tsari. Wannan ne karo na farko da hakan ya ƙwace mishi akan Nuriyya, shi yasa yake jin komai ya cunkushe mishi, komai baya mishi daɗi don bai san yadda zai yi da ita ba. Ya rasa yadda zai yi da ita. Kokawa yake da kan shi da zuciyarshi akanta, yanzun kasancewarta kusa da shi yasa shi jin komai ya ƙara ƙwacewa daga hannun shi. Motar ya ji Yassar ya tsayar alamar sun ƙaraso. Ƙoƙarin buɗe ƙofar Nuriyya take amma ta kasa.

“Hamma na kasa, ƙofar ta ƙi buɗewa.”

Nuriyya ta faɗi tana kallon shi cike da wani irin rauni da yake ji har bayan zuciyarshi. Bai san lokacin da ya kai hannu ya buɗe mata ƙofar ba.

“Na gode…”

Ta faɗi tana ficewa, idanuwan shi ya runtse ya buɗe su, yana ɗan dafe kanshi da yake ƙara sarawa.

“Ya zan yi ne wai?”

Ya yi tambayar yana dukan jikin motar kamar ita ta yi mishi laifi.

<< Abdulkadir 11Abdulkadir 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×