Skip to content
Part 14 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

“Sadauki don Allah… Ka sauƙaƙe min auren nan.”

Muryar Waheedah ta daki kunnuwan shi tana dawo da shi daga dogon tunanin da ya tafi, runtse idanuwan shi ya yi yana sake buɗe su akanta. Dubawa yake ko zai ga alamar wasa a tata fuskar, ko zai ga hijabin da ta saka tsakanin su ta yaye. Kan hannun kujerar da ke kusa da shi ya zauna yana maida numfashi, sosai ya girgiza, ba zai tuna ranar ƙarshe da wani abu ya girgiza shi haka ba. Kallon Waheedah ya sake yi da ya ji kamar ƙafafuwan shi na rawa saboda tashin hankali. Hannu ya ga ta sa tana share ƙwallar da ta tsiyayo kan kuncinta. Ƙirjin shi ya ji yana zafi, gani yake yau ɗin gaba ɗaya duk wani abu da ta san baya so take yi, kamar kuma tana yi ɗin ne don ta ɓata mishi rai.

“Wahee…”

Ya kira muryarshi can ƙasan maƙoshi, bata ɗago ba, ta ji shi, ta saurara ne ko tsikar jikinta za ta tashi kamar ko da yaushe, tsawon shekaru bai sa ta dai na jin yanayin soyayyar shi ta daban da take taso mata duk idan ya kira sunanta ba. Wannan karon babu abinda ta ji banda gajiya da komai, duniyar take ji ta haɗe da ita a waje ɗaya, kamar tana cikin ɗakin da babu ko da taga ballantana ƙofa, ji take fitarta daga dakin zai zo da saukake mata auren shi da zai yi.

“Wahee magana nake miki.”

Abdulƙadir ya faɗi, yana ƙoƙarin danne ɓacin ran da yake ciki, yanayin da ya zo mishi a wahalce, saboda Waheedah ce, bai taɓa ɓoye wani yanayi nashi ba a tare da shi. Bai taɓa tsoron buɗe mata komai nashi ba, tare da ita bai taɓa jin akwai wannan buƙatar ba, idan ranshi a ɓace yake yana nuna mata saboda ta san yadda za ta yi da shi, idan farin ciki yake takan gani. A gabanta yake dariya sosai don yasan ba za ta taɓa raina shi ba, a ‘yar ƙaramar duniyar shi daga ita sai Yassar yake tsokana sosai. Ita fiye da kowa, ko Yassar kan yi shakkar mishi wani wasan, amma cikin ido Waheedah kan kalle shi ta tsokane shi.

Ganin ta yi shiru har lokacin yasa shi saukowa daga kan kujerar yana tsugunnawa kusa da ita. Hannuwanta ya kamo duka yana riƙewa cikin nashi. Kusancin shi bai taɓa ƙin yin tasiri akanta ba, ya sani, lokuta da dama ko damun shi ta yi da surutunta, matsawa zai yi ya riƙe hannunta bakinta zai yi shiru. Idan wani abu ya yi mata da ya riƙeta a jikin shi ya ji ta zagaya hannuwanta a bayanshi yasan ta karɓi haƙurin shi ba tare da ya furta ba. Yanzun ma hakan yake so ya yi amfani da shi kafin komai ya ƙarasa kubce mishi.

Ita kanta Waheedah mamaki take yi, don ta san abinda yake ƙoƙarin yi ɗin, lokutan duk da ya yi ta sani, amma hakan bai taɓa hanashi tasiri akanta ba, wannan karon zuciyarta ta gama bushewa. Hawayen da ke shirin zubo mata ta ji sun tsaya cik, kamar taɓatan da ya yi ya ƙara busar mata da zuciya. Hannuwanta ta zame daga cikin nashi, tana yawata idanuwanta akan fuskar Abdulƙadir ɗin.

“Ka kwashi yaranka, ka bani takardata…”

Ta yi maganar muryarta na mata baƙunta cikin kunnuwanta, balle Abdulƙadir da yake kallonta idanuwanshi na ƙanƙancewa da ɓacin rai. Kallon shi take, yanayin da take gani a fuskarshi a da zai tsoratata, sosai zuciyarta za ta fara rawa da abinda zai faru, amma yau ko a jikinta take ji. Ita ma ranta a ɓacen yake, karo na farko da take jin son ɗora buƙatarta sama da tashi. Wani murmushi ya yi mai sauti yana miƙewa, bin shi da kallo Waheedah ta yi ganin ya soma tafiya, amma ba ƙofa ya nufa ba, hanyar da za ta kai shi ɗakin Anty. Wani sabon zazzaɓi take ji yana lulluɓeta, da gaske Abdulƙadir yake yi yaranta zai ɗauka. Hawayen da suka bushe mata take jin sun fara farfaɗowa.

Tana kallon shi har ya ɓace mata, ɗakin Anty ya nufa kanshi tsaye. Ko ƙwanƙwasawa bai yi ba ya tura ƙofar yana samunta a tsaye.

“Ikram za ki bani.”

Kallon shi Anty take yi, ta san taurin kanshi tun yarinta, amma na yau da take gani daban ne, musamman Waheedah, bata taɓa ganin ran yarinyar a ɓace irin na yau ba, ko menene Abdulƙadir ɗin ya yi i mata mai girma ne. Amma hakan ba ya nufin tana son ganin mutuwar auren nasu, ko don yara da ke tsakani.

“Abdulƙadir karka yi haka, karka yanke hukunci cikin fushi don Allah. Ka duba yarinyar nan duka watanta nawa a duniyar? Idan zaka tafin ne ma, ka ɗauki Fajr shi. Ka barta ta huta idan an kwana biyu sai ka dawo ku yi magana, ita ma ta hau dokin zuciya ne.”

Ƙanƙance idanuwan shi Abdulƙadir ya yi, yana wani irin sauke numfashin ɓacin rai, Waheedah ita ta ja mishi tonon sililin nan. Da ta saka kowa ya zo yana tsoma mishi baki a cikin maganar iyalin shi.

“Kiban yarinyata Anty…”

Abdulƙadir ɗin ya faɗi yana ƙoƙarin danne sauran maganganun da suke kan harshen shi. Ita ma Antyn ranta take ji yana ƙara ɓaci.

“Ba za ka ji magana ba kenan ko? Ba za ka ji ba ko Abdulƙadir…”

Runtse idanuwan shi ya yi yana buɗe su.

“Idan da na so jin ra’ayinki kan abinda yake faruwa ina da bakin da zan buƙaci hakan…kiban yarinyata.”

Hannu Anty ta saka tana kwance goyon Ikram ɗin, miƙa mishi ita ta yi tana furta.

“Allah ya shirya.”

Karɓar yarinyar ya yi da take ta bacci kamar komai bai faru ba, nutsuwar da take ciki na saka shi sauke numfashi, sai da ya gyarata cikin hannun shi tukunna ya kalli Anty,

“Amin.”

Ya juya yana ficewa daga ɗakin, yadda ya doko ƙofar na saka Anty yin da na sanin marin da ta ƙi ɗauke shi da shi. Sai dai ta san Abdulƙadir idan bai rama ba, sai ya gaya mata maganganun da za ta yi satika tana juyi don ƙunar rai. Wani abin da zai maka ko da an samu igiya an kulle shi a baka kulki ka jibgeshi ba za ka huce ba. Kan gado ta koma ta zauna, zuciyarta na tafasa. Shi kam falon ya ƙarasa yana kallon yadda Waheedah take kallon shi cikin sabon tashin hankali. Hakan ya mishi daɗi, gara ta ga da gaske yaranshi zai ɗauke, sai ta tashi su koma gida gaba ɗaya.

Idan rigima take ji zai bata dai-dai wadda za ta isheta har da ƙari idan buƙatar hakan ta taso. Waheedah bata san ta miƙe ba sai da ta ga kallon da Abdulƙadir ɗin yake mata. Ta ɗauka zuciyarta ta bushe, ta ɗauka babu wani abu da zai sake taɓa ta, sai da ta ga yarinyarta a hannun shi tukunna take jin yadda yake son rabata da sauran nutsuwar da ta rage mata, muryarta a karye ta soma magana.

“Me kake so da ni? Sadauki me kake so da ni haka? Mene ne ban baka ba? Lokacin da suka zo saura suka samu daga zuciyata, saboda kaso mafi girma na tare da kai…”

Shiru ta yi tana mayar da numfashin da ya taso mata mai haɗe da kukan da yasa ta kasa ƙarasa maganar da ta fara.

“Ki biyoni mu tafi gida, koma mene ne za mu gyara shi mu biyu…”

Abdulƙadir ya faɗi yana roƙonta da duka zuciyarshi da ta amince, sai dai a fuskarta yake ganin hijabin da bai san daga inda ta samota ta saka a tsakaninsu ba, hannu ta sa ta share hawayenta tana girgiza mishi kai, yanayin da ya ƙara mishi zafin da ƙirjin shi yake yi. Kai ya jinjina yana faɗin,

“Ki yi abinda kike so Waheedah…”

Ganin ya juya yana shirin barin ɗakin ya sa ta furta,

“Takardata Sadauki…”

Abdulƙadir bai nuna alamun ya ji ta ba ya fice daga ɗakin. Aurenta a hannun shi yake, yara nashi ne, zai ɗauka duk sanda ya ga dama. Ya ɗauka idan ya yi amfani da su za ta haƙura ta dawo hayyacinta daga rashin hankalin da take ciki. Hakan bai faru ba, zai ɗauki yaran yanzun, zai tafi da su. Zai kuma ga wanda ya isa yasa shi sakinta, tonon asiri ne ta gama yi mishi, abinda bai taɓa tunanin za ta taɓa yi ba, sosai ta girgiza shi, don har ya shiga ɓangaren Mami yana mamakinta, yana kuma duba cikin kanshi ko zai tuna asalin laifin da ya yi mata banda na ranar amma ya rasa.

Bai samu Mami a falon ba, Aminu ne zaune da Fajr da hankalin shi gaba ɗaya akan Tom and Jerry ɗin da yake kallo a babbar talabijin ɗin ɗakin yake. Ba tare da ya yi magana ba ya ƙarasa yana saka hannun shi ɗaya ya ɗago da Fajr ɗin da a shagwaɓe ya ce,

“Paapi…”

Gyara mishi tsayuwa Abdulƙadir ɗin ya yi yana faɗin,

“Wuce mu tafi…”

Da rashin fahimta yaron yake kallon shi da idanuwan shi irin na Waheedah ɗin.

“Omma fa?”

Sai da Abdulƙadir ya sauke numfashi tukunna ya ce,

“Banda ita…”

Maƙale kafaɗa Fajr ya yi, yana shagwaɓe fuskarshi sosai.

“Zan zane ka Fajr… Ka wuce na ce.”

Wucewar Fajr ya yi don duk ƙarancin shekarun shi yasan cewa Abdulƙadir ɗin zane shi zai yi kamar yadda ya faɗi, kukan shi ma bai bari ya fito ba, don yana bala’in tsoron duka, ko tsintsiyar kwakwa ya ga Waheedah ta fito da ita ta ajiye waje ɗaya zai nutsu. Abdulƙadir kuwa ya taɓa saka charger ya zane shi, sosai yake tsoron yin wani abu a gaban shi. Sai lokacin Aminu ya ce,

“Tunda ba za shi ba ka ƙyale shi.”

Kallon shi Abdulƙadir ya yi yana kafe shi da idanuwa, bai manta maganganun da ya faɗa mishi a asibiti ba ɗazun, kawai ya ƙyale ne bai ce komai ba saboda a lokacin yana cikin jin kunyar Mami.

“Ka manta ni ko? Aminu ka manta wanene ni.”

Kai Aminu ya sauke ƙasa yana jin zuciyarshi na dokawa cike da tsoro. Bai manta ko waye Abdulƙadir ba, haushin shi da yake ji ɗin ma a yanzun ya nemeshi ya rasa.

“Zan dakeka, zan fasa maka bakin da sai ka yi sati magana da kowa na maka wahala balle ka yi tunanin yi min rashin kunya…”

Abdulƙadir ya ƙarasa yana directing ɓacin ran nashi kan Aminu. Sosai yake jiran yaron ya yi motsin da bai mishi ba, ya ajiye Ikram kan kujera ya dake shi kamar ganga. Zuciyarshi za ta yi mishi sanyi ko yaya ne idan ya zane wani, tunda ba zai iya zane Waheedah da ta ɓata mishi ran ba. Amma Aminu ko ɗago da kai bai yi ba ballantana ya yi ƙoƙarin cewa wani abu. Kai Abdulƙadir ɗin ya jinjina ya juya ya kama hannun Fajr yana janshi suka nufi hanyar da zata kai su harabar gidan inda motarshi take a ajiye.

*****

Yassar ya hango ya buɗe motar shi ya fito, cikin shigar manyan kaya da hula da suka ƙara mishi wani irin kwarjini. Tsaye Abdulƙadir ɗin ya yi ba tare da ya san dalili ba, yana nan har Yassar ɗin ya ƙaraso ya same shi.

“Ina kuma za ka je da yara?”

Yassar ya buƙata, ya kai hannu ya dafa kan Fajr da ya faɗa jikin shi yana faɗin,

“Uncle…”

Yana gidan shi a kwance ya ga wayar Hajja. Sai da zuciyar shi ta doka, don yasane ba lafiya ba, indai Hajja zata ɗaga waya ta kirashi sai da wani babban dalili. Bai yi mamakin jin dalilin Abdulƙadir bane ba.

“Baka yi min sallama ba Hamma…”

Abdulƙadir ya faɗi yana ƙanƙance idanuwan shi, don ya ga yanayin Yassar ɗin shima yasan abinda yake faruwa. Wani irin kallo Yassar ya watsa mishi.

“Yaran ka ɗauko? Ka sake tan?”

Kai Abdulƙadir ya girgiza mishi, hannu Yassar ya miƙa yana karɓar Ikram da Abdulƙadir ɗin ya kasa hana shi.

“Na san baka da hankali ko kaɗan, amma ban yi tunanin ya kai haka ba. Gidan ubanka za ka je da jaririya? Ko Nuriyyar ce za ta shayar maka da ita?”

Sosai Abdulƙadir ya daƙuna fuskar shi.

“Karkai min faɗa Hamma, idan za ka ɗauki sides sai ka tsaya ka ji nawa ɓangaren tukunna.”

Tsaki Yassar ya ja, da ya ce ba zai sake shiga matsalar Abdulƙadir din ba, yanzun ma don Hajja ta kirashi shi yasa ya ɗauko ƙafarshi ya zo. Hannun Fajr ya kama yana shirin raba Abdulƙadir ɗin da nufin wucewa.

“Hamma ina za ka je min da yara?”

Kallon shi Yassar ya yi.

“Idan ka biyo ni saina watsa maka mari, mahaukacin banza…”

Murya can ƙasa Abdulƙadir ya ce,

“Yarana, a gaban yarana Hamma…”

Tsakin Yassar ya sake ja yana wucewa abin shi, yana jin Abdulƙadir ɗin na biye da shi. Bai ko juya ba har ya ƙarasa ɓangaren Anty, tunda Hajja ta ce mishi suna can da ta kira. Waheedah ya samu ta haɗa kanta da kujera, yanayin ta na sa wani abu tsaya mishi a rai, ɗagowa ta yi fuskarta har ta tara jini saboda kuka. Sosai Yassar ya ji ƙirjinshi ya yi nauyi. Ƙarasawa ya yi ya zauna kan kujerar yana miƙa mata Ikram. Da sauri ta karɓi yarinyar tana riƙeta a jikinta, duminta na saukar mata da wata irin nutsuwa ta ban mamaki.

“Na gode Hamma…”

Ta faɗi cikin wata irin murya da ta sa Yassar sake kallon Abdulƙadir ɗin yana watsa mishi wani kallo. Ƙanƙance mishi idanuwa Abdulƙadir ɗin ya yi, ya ɗauka Yassar na bayanshi, kamar ko yaushe akan abubuwa da dama. Tun a watanni baya ya gane cewa shi ma bayan Waheedah yake, ba shi da matsala don Yassar ya so Waheedah, ko bakomai ƙanwarshi ce, amman shi ma ƙaninshi ne, kuma yana da kishin da ba ya so a fifita soyayyarshi akan ta kowa. Ko Hajja ba ya son ya ga tana nuna ma su Yazid soyayya fiye da wadda take nuna mishi.

“Ki yi haƙuri Waheedah…”

Kai Waheedah ta girgiza wa Yassar da take jin maganar shi kamar ya watsa mata ruwan zafi. Shi ma kan yake girgiza mata yana saurin ɗorawa da,

“Ba ina nufin ki yi haƙuri da koma mene ne ya yi miki ba…”

Da mamaki Abdulƙadir yake kallon Yassar.

“Hamma?”

Ya kira, ko kallon shi Yassar bai yi ba, asalima maganar da yake yi ya ci gaba.

“Idan nan ɗin za su dameki ki tashi mu tafi gidana…”

Wani murmushi mai sauti Abdulƙadir ya yi da ba shi da alaƙa da nishaɗi.

“Kana magana kamar izinin fitarta yana hannun ka.”

Zama Waheedah ta gyara tana ɗaga Ikram ta miƙe, towel ɗinta ta zame ta sakata a bayanta. Goya yarinyar ta yi a bayanta. Kamar yadda Yassar ɗin ya faɗi, tana buƙatar hutu, bata so kowa ya dameta ko ya yi ƙoƙarin bata haƙuri, tana kuma da tabbacin Yassar ba zai bar kowa ya zo ya dameta ba. Za ta jira takardarta a gidan shi. In yaso daga baya ta dawo gida. Don dama bata yi niyyar zama ɓangaren su ba, balle Mami ta tambayeta me ya faru. Bata san ta inda za ta fara ba, ya sauƙaƙe mata shi ne abinda ta fi buƙata.

“Ina za ki je?”

Abdulƙadir ya buƙata yana kallon ta cike da sabon mamaki.

“Ka aiko min takarda ta gidan Hamma, ko ka ba wa Abba, duk wanda ya fi maka sauƙi dai.”

Ta yi maganar tana kallon Yassar da faɗin,

“Hamma mu je…”

Ta kama hannun Fajr, bai cika yawan magana ba, amma bai taɓa tunanin zai rasa abin cewa gaba ɗaya ba sai yanzun, don ba kalaman shi bane kaɗai suka kubce mishi, har da abinda ya kamata ya yi tunanin da ya wuce tsananin mamaki.

“Waheedah tsinuwar mala’iku da duk takun da za ki yi ba tare da izinina ba…”

Ya tsinci kanshi da furtawa ganin ta saka ƙafarta ɗaya wajen ɗakin. Juyowa ta yi da wani irin yanayi a fuskar ta.

“Tunda safiyar yau nake zubar da hawaye, kuma kai ne sila, tsinuwar za ta yi balance Sadauki… Ina jiran takarda ta.”

Ta ƙarasa tana ficewa daga ɗakin. Wani murmushi Yassar yayi, tunda ya san yarinyar bai taɓa tunanin tana da ƙwarin gwiwar karɓar wa kanta ‘yanci ba sai yau. Lokuta da dama yakan ji kamar har da laifin shi a abinda take fuskanta na zama da Abdulƙadir, yakan ji a kaso ɗari ma aurenta da Abdulƙadir yana da hannu cikin kashi tamanin har da ɗoriya. Musamman watannin baya haka yake jin duk laifin shi ne, amma yanzun ta fara rage mishi nauyi. Duk da can ƙasan zuciyarshi ba zai so mutuwar aurenta ba, amma hakan ba zai hana shi goyon bayan gaskiya ba. Wannan karon son Abdulƙadir ba zai rufe mishi idanuwa ba. Ba tare da ya ce komai ba ya bi bayanta.

*****

Ba zai ce ga yadda ya kai gida ba, nutsuwar shi bata taɓa ƙwacewa akan tuƙi ba sai wannan karon. Ɓangaren Waheedah ya wuce yana shiga har ɗakin baccin su, wannan karon takalman shi ya cire bayan ya zauna kan gadon tukunna ya kwanta. Pillow ɗinta ya ɗauka yana riƙewa a jikin shi, ƙamshin turarukan ta ya shaƙa yana lumshe idanuwan shi. Yakan yi kewarta duk idan yazoe ya koma wajen aikin shi. Bai taɓa tunanin zai yi kewarta yana gida ba, amma ya fara, cikin ƙasa da awa biyu komai ya birkice musu.

‘Sadauki zaka karya ni…’

Ya ji muryarta cikin kanshi da ta saka shi buɗe ƙananun idanuwan shi, kafin ya sake mayarwa ya rufe su yana ƙara matse pillow ɗin a jikin shi, sanyin shi na sake tunasar da shi cewa ba ita bace ba.

“Ba za ki min haka ba, Waheedah ba za ki min haka ba…”

Ya furta a hankali yana jin an ƙwanƙwasa ƙofar dakin, wata irin dirowa ya yi daga kan gadon.

“Nasani, nasan ba za ki iya nisa da ni ba… Na sani.”

Yake faɗi yana ƙarasawa ya buɗe ƙofar, Nuriyya ya gani, a karo na farko da ya ji bai so ta kasance a bakin ƙofar ba. Rigarshi ce a jikinta sai wandon da ko cinyoyinta bai rufe ba. Ta kama gashinta da yake a kwance ta ƙulle shi a tsakiyar kan nata. Kwalliya ce a fuskarta sosai, da alama ta yi wanka bayan fitar shi. Sosai yake kallonta yana neman samun nutsuwa koya take daga hakan.

“Na ji motar ka…”

Nuriyya ta faɗi, tana jin zuciyarta ta yo tsalle zuwa wuyanta da yanayin da ke fuskar shi, za ta yi ƙarya idan ta ce bata ji tsoro ba da ya buɗe ƙofar, saboda ta ga wani abu kamar disappointment shimfiɗe kan fuskar shi, kamar ba ita ya tsammaci gani a tsaye a gaban shi ba, sosai hakan ya tsoratata. Ganin ya ƙanƙance idanuwan shi yana kallonta har lokacin yasa ta faɗin,

“Ya jikin Waheedah ɗin?”

Tana jin ɗacin ɗora sunan nata kan harshenta, wani irin tuƙuƙin kishi na danne ƙirjinta da yadda zai kasance sunan Waheedah za ta yi amfani da shi yau don ta yi nasara kan shi.

“Da sauƙi.”

Ya furta can ƙasan maƙoshi, kai ta ɗan jinjina tana shagwaɓe mishi fuska.

“Abinci fa?”

Sai da ta kira abinci tukunna ya ji cikin shi ya murɗa mishi da yunwar da yake ji, numfashi ya sauke, duk ranar bai ci komai ba, Waheedah ko damuwa da cikin shi ba ta yi ba. Yadda baya jure yunwa idan yana tare da ita har mamaki yake ba shi.

“Ki dafa koma menene.”

Ya yi maganar yana shirin rufe ƙofar a fuskarta, kallon shi Nuriyya take yi tana jin cikinta ya murɗa mata da yunwar da take ji ita ma. Ba za ta ce ga rana ɗaya da ta yi wani girki ƙwaƙƙwara ba tun da ta zo gidan. Da ta ce mishi,

‘Abinci fa?’

Ba tana nufin me za ta dafa bane, tana nufin me za su ci ya fita ya siyo musu don ita yunwa take ji ta fitar hankali, biscuit ne kawai a cikinta duk yinin ranar. Saurin dafe ƙofar ta yi.

“Masoyi…”

Ta faɗi tana tattaro duk wata kissa da za ta iya ta naɗe muryarta da ita. Numfashi Abdulƙadir ya sauke, ɓacin ran da yake ji a kusa yake. Da Waheedah ce da ta gane gab yake da fashewa, ko bata bashi space ɗin da yake buƙata ba za ta kama hannun shi ta zaunar da shi, za ta ɗora kanta a kafaɗarshi su zauna shiru har sai ya ɗan nutsu. Amma da alama Nuriyya bata karanci ranshi a ɓace yake ba.

“Na ga yamma ta yi, na ɗauka ma ka siyo mana…”

Ta yi maganar tana kallon shi fuskarta a shagwaɓe. Numfashi ya sake saukewa yana ɗorawa da,

“Idan ba za ki dafa ba ki barshi…”

Da mamaki a fuskarta take kallon Abdulƙadir, bai taɓa mata magana cikin yanayin da ya yi mata ba yanzun.

“Masoyi…”

Ta kira.

“Kinjini ai.”

Ya faɗi yana rufe ƙofar a fuskarta ya koma kan gadon ya kwanta. Wani ɓacin ran na sake danne shi. Don yasan ba laifinta bane ba, ba ita ta ɓata mishi rai ba, bai kuma kamata ace ya sauke akanta ba. Ya gani a fuskarta yadda hakan ya taɓa ta, ba Waheedah bace ba, ita kaɗai ce a duniyar shi yake saukewa ɓacin ranshi ko da ba ta da alaƙa da hakan, saboda ta barshi, saboda ta nuna mishi bakomai don ya yi hakan, ta fahimta yana son saukewa a wani waje, don ya zaɓe ta bai dameta ba. Ƙaramin tsaki ya ja. Ko kaɗan baya son yawan tunane-tunane, Waheedah ta san hakan ta zaɓi ta saka shi cikin tunani.

Nuriyya ta kai mintina biyar a tsaye a bakin kofar, ranta idan ya yi dubu a ɓace kowanne yake. A rayuwarta bata son wulaƙanci ko ya yake, idan akai mata shi takan ji kamar an mata hakan ne don a nuna mata ita ɗin bakomai bace, amma tunda can idan wulaƙancin ya kasance daga ɓangaren shi ne takan ji kamar za ta haɗiye zuciya ta mutu. Yanzun ma haka take ji, ƙirjinta har zafi yake mata. Bata san me akai mishi a waje ya ɓato mishi rai ba, don ita ta san bata yi mishi komai ba. Yunwar da take ji na ƙara sa ɓacin ran ya haɗe mata, wucewa ta yi ta koma ɓangaren ta tana nufar kitchen.

Fridge ta buɗe ta rasa abinda za ta dafa, akwai kaza a ciki ɗanya. Abdulƙadir na ƙoƙari sosai wajen kula da su ta sani, kaji ne da yawa a nata fridge ɗin, Waheedah kan zo har ɓangarenta ta kawo mata, bata cika amfani da su bane shi yasa suka taru, ranar da ta ji kwaɗayi ya kamata ne take ɗaukowa ta soya. Yanzun ma ƙulli ɗaya ta fito da ita duk ta yi ƙanƙara, ta rufe fridge ɗin ta saka ta cikin abin wanke-wanke ta buɗe fanfo. Tukunya ta fito da ita ta ajiye, kazar da take a yayyanke ta kwashe ta zuba cikin tukunyar, ruwa ta zuba a ciki ta ɗora kan gas tana kunnawa.

Wajen fridge ɗin ta ƙarasa tana dubawa ta ga ko tana da cefane. Gani ta yi babu, tunda ba girkin take yi ba, bata kula ba. Fita ta yi zuwa ɓangaren Waheedah ta shiga kitchen ɗin nata ta buɗe fridge, akwai kayan miya a cikin robobi a ajiye wajen roba biyar. Na farkon ta fara ɗauka ta wuce ta koma, ɗiba ta yi ta zuba cikin kazar, sosai take ganin ya mata yawa, don robar na da girma,a fridge ɗinta ta saka don ba mayarwa za ta yi ba, ko da za ta sake amfani da shi.

Maggi ta zo ta ɓare ta watsa, taliya za ta yi jalof. Tana gama zuba maggin ta ji kiran sallar La’asar. Ɗaki ta koma ta yi alwala, zani kawai ta ɗaura saman kayan jikinta ta saka hijab ta gabatar da sallar. Ko dardumar bata linke ba ta cire hijab ɗin da zanin tana watsa su kan gado ta koma kitchen ɗin, yunwa take ji ta fitar hankali, buɗewa ta yi ta ga ya tafaso, amma wani ƙarni ya daki hancinta don kazar ko wankuwa bata yi ba, kuma kayan miyar babu albasar kirki a markaɗen su. Ɗauka ta yi ko don bata ƙarasa dahuwa bane ba, ludayi ta sa ta ji ko kazar ta ɗan yi laushi, rufewa ta yi ta tsaya kamar minti biyar a kitchen ɗin, har lokacin ranta a ɓace yake, tukunna ta buɗe ɗaya daga cikin locker ɗin ɗakin ta ɗauko taliya guda ɗaya. Kakkaryawa ta yi ta zuba cikin tukunyar tana jujjuyawa tukunna ta koma falo ta zauna. Gara ko kallo ne ta yi ta rage zafi.

Tana kunnawa ta ɗauki remote suna ɗauke wutar su, wani dogon tsaki ta ja.

“Tsinannu…”

Ta furta a fili tana miƙewa. Kitchen ɗin ta koma ta ga taliyar har ta fara laushi don ƙanana ce, da tana gidan su takan jima bata ci taliyar turawa ba, filawa Babansu yakan siyo a kaɗo musu taliyar Hausa, ita ko lokacin sai ta yi sati biyu bata ɗora tukunya ba, tun Mama na mata faɗa har ta gaji ta haƙura, idan ta matsa mata abincin ba za a ga dai-dai ba, garama idan da mai da yaji ne, ko wake da shinkafa ce wani lokacin waken a tsai-tsaye za a ci shi bai gama dahuwa ba, shi yasa ta daina saka ta, tunda ba wadatar abincin suke da shi ba da za a dinga ɓarnar shi.

Ta ga alamar taliyar ta kusan dahuwa, amma sosai ruwan ya yi yawa. Abin kama tukunya da ke ɓangaren Waheedah ta ɗauko shi bata mayar mata ba ta saka tana ɗauke tukunyar daga kan gas ɗin, rage ruwan ta yi cikin abin wanke-wanke tukunna ta sake mayar da tukunyar kan gas. Tunawa ta yi bata zuba mai ba, shi yasa ta ga taliyar ta mata wani iri, dubawa ta yi ta ɗauko man a cikin roba, da yake na ‘ya’yan itatuwa ne suke amfani da shi. Tana ma da man gyaɗa da Waheedah ta bata ya kai kwalba biyu, a cewarta ƙanwar babanta ce ta kawo mata da ta zo gidan. A ludayi ta tara man tana zuba ludayi biyu ta cakuda, gani tayi kamar ba zai wadata ba, ta ƙara ludayi ɗaya tukunna ta rufe tana mayarwa.

Jujjuya taliyar ta sakeyi, ta daddaga ludayin a hannunta ta ɗanɗana. Gishiri ta ɗauko ta zazzaga don ta ji kamar bai mata ba, hannunta ya kubce kuwa, cikin hanzari tai kokarin saka ludayi ta kwashe amma duk ya narke don abincin na ta tafasa, tsaki ta sake ja, komai baya tafiya mata dai-dai. Dabara ce ta zo mata, ta dinga kwaso romon da ludayi tana zubawa cikin wajen wanke-wanke tukunna ta ɗan ɗibi ruwa ta ƙara ciki, gani ta yi cefanen naso ya yi mata kaɗan, ta zaro taliya ɗaya ta saka a bakinta, duk da hakan gishirin na son mata yawa, kuma bata ji cefane kamar yadda ta Waheedah kan yi ba. Robar ta ɗauko ta ƙara ɗibar wani ta zuba ta cakuda, sai taga ta ɗan mata kyau a ido. Ƙamshi ne kawai baya tashi.

Faranti ta ɗauka tana zuba musu ita da shi a haɗe, kusan duka naman ta kwashe ta saka musu a ciki. Ɗauka ta yi zuwa falon ta ajiye ta koma ta ɗauko cokula masu yatsu ta saka a ciki, tukunna ta taka zuwa ɓangaren Waheedah da bata san me yake acan ɗin ba tunda bata nan, a falo ta same shi zaune.

“Ka taso mu ci abinci.”

Ta faɗi tana kallon shi har ya miƙe ya taka ya wuce ta ba tare da yace komai ba. Yunwa ke cin shi sosai da sosai. Bayanshi Nuriyya ta bi har falonta. Kan kafet suka zauna, cokali Abdulƙadir ya saka cikin abincin yana jujjuyashi, yanayin taliyar bai mishi ba sam, yakan ci ko me Waheedah ta dafa ta bashi, bai saba faɗa mata ga abinda yake son ya ci ba, idan unguwa ta je ma sai ta gama mishi girki take fita indai yana nan. Zubawar kan zame mishi aiki, da lokacin cin abincin ya yi za ta kirashi a waya ta ji ko ya ci.

Lokuta da dama zai saka mata rigima sai ta baro duk inda take ta dawo sun ci tare, ko ya ce shi bai san yadda zai zuba ya isheshi ba, haka za ta faɗa mishi ludayin da zai yi amfani da shi, ko guda nawa zai zuba, miya ta sa ya samo wajen zubawa ya zuba ta ce ya dinga ɗiba yana sakawa a abincin in ya rage saura ya saka mata a fridge. Sai dai Waheedah ce, ta san abinda yake son ci, ta san abinda ba ya so, taliya na ɗaya daga cikin abincin da bawai ya dame shi bane, gara da miya, amma jalof haka tsuranta bata dame shi ba.

Idan Waheedah ta yi tana haɗa mishi salad sai ya ci, idan ya ce ta dafa taliya, takan ce mishi tana son ya dinga cin komai saboda in ya koma wajen aiki bata kusa. Sosai yake cakuɗa taliyar yana tunanin sakata a bakin shi, naman ma ko kaɗan bai mishi ba, idan a wajene babu yadda zai yi sai ya ci, amman cikin gidanshi bai saba da abinci irin hakan ba. Ba ya son yin wani dogon nazari ya nannaɗo taliyar yana sakata a bakin shi. Nuriyya yake kallo da take cin abincin hankalinta a kwance, kamar yana mata daɗi, abinda bai sani ba, ba wai abincin ya mata daɗi bane, ita kanta ta ji yadda gishiri ya ɗan yi yawa. Sai dai yunwa take ji ta fitar hankali, inda baya nan ma za ta je ta haɗa shayi. Amman bata son nuna mishi yadda abincin bai mata ba.

Da ƙyar Abdulƙadir ya haɗiye taliyar da ke bakinshi yana dubawa don ya ɗauki ruwa, bata kawo mishi ba.

“Baki ba ni ruwa ba…”

Ya furta, sai lokacin ta ɗago tana kallon shi, miƙewa ta yi ta ɗauko mishi ruwa a fridge ta kawo mishi. Ganin ya kalleta yasa ta komawa ta ɗauko kofi ta zo ta ajiye, buɗe ruwan ta yi tana zuba mishi, dauka ya yi ya sha, ruwan ya ƙulle mishi ciki lokacin da ya dira cikin hanjin shi, ko kaɗan ba zai iya cin taliyar nan ba, ganin bai ɗauki cokalin ba yasa Nuriyya faɗin,

“Har ka yi me?”

Daƙuna mata fuska ya yi.
“Bana son taliya Nuriyya…”

Da rashin fahimta take kallon shi.

“Idan Waheedah ta dafa kana ci.”

Kai ya jinjina mata da ta ji kamar ya watsa mata garwashin wuta, tabbatar mata yake tata ce ba zai ci ba, amma yana cin ta Waheedah, magana za ta yi ya ɗora da,

“Ba irin wannan bace.”

Cokalinta ta ajiye ita ma , tana danne kishi da tuƙuƙin baƙin cikin da ya taso mata ta yi mishi wani murmushi.

“Ka ci naman to.”

Bai yi musu ba, cokalinshi ya ɗauka yana ƙoƙarin saɓulo tsokar naman, amman ya ji abu ya gagara, idan abincin Waheedah ne yana saka cokali a jikin naman yake raboshi da ƙashin shi saboda ya dahu. Ajiye cokalin ya yi yasa yatsun shi ya tsamo cinyar yana kaiwa bakin shi ya kafa haƙori a ciki, ƙiri-ƙiri ya ji naman, ko na waje ya fi shi dahuwa, gutsura ya yi yana taunawa, ruwan naman na sauka bakin shi da wani ɗanɗano marar daɗi, gashi ko maggin kirki bai kama shi ba. Ajiye na hannun shi ya yi yana daƙuna fuska.

“Wanne irin nama ne wannan? Bai dahu ba…”

Abdulƙadir ya faɗi yana kora wanda ya gutsura da ruwa.

“Bangane bai dahu ba…”

Nuriyya ta yi maganar a ƙufule, ƙanƙance idanuwan shi ya yi yana kallon ta.

“Ki ci a bakinki…”

Naman ta sa hannu ta ɗauka ta gutsura, ita kanta ta ji bai dahu ba, ajiyewa ta yi kunya na kamata, ta san bata iya girke-girken nan ba, girman kanta kuma ba zai taɓa barinta ta ce Waheedah ta koya mata ba, shi yasa take ta damun shi da ya ɗauko mata ‘yar aiki, kuma ko da ta iya ma, Allah ya ɗora mata ganda, ba za ta iya girke-girken da Waheedah ke yini tana yi ba. Duk ranar girkinta takan ja jiki, ko ta jashi ta ce su je ɓangaren Waheedah ɗin su taya ta hira, don su ci abinci a can ɗin.

Farko-farko ta ɗauka Waheedah ɗin kan basu saboda Abdulƙadir ɗin ne kawai.

Sai da ta ga ko baya nan ta je bata hanata, wani lokacin takan aika Fajr ya kirata ta zo ta ɗibi abinci. Yadda Abdulƙadir ɗin bai taɓa kula tana gujema girki ba har mamaki yake bata. Addu’a take Waheedah kar ta jima a asibitin, don ta ga alamar za su samu matsala da Abdulƙadir kan abinci. Miƙewa ya yi da alama ranshi a ɓace yake, yana sawa ta miƙe ita ma.

“Don Allah Masoyi ka yi haƙuri, cikin sauri na yi girkin ne don na ga yamma ta yi…”

Bai ce mata komai ba ya raɓa ta ya wuce, ranshi a ɓace yake, kuma yunwa yake ji , idan ya yi magana bai da tabbacin abinda zai fito daga bakin shi, addu’a yake kar ta yi ƙoƙarin binshi don bai san me zai faru ba.

<< Abdulkadir 13Abdulkadir 15 >>

1 thought on “Abdulkadir 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×