Tunda suka shiga gidan Yassar ta gaisa da matar shi Hauwa da 'yar kanin Abba ce ya aura, ta samu kujera a falon ta zauna. Bata san me Yassar ɗin ya ce mata ba, ta ga dai ta zo tace mata ta tashi ta je ta huta, ɗaya daga cikin bedrooms ɗin ɗakin ta rakata. Fajr ƙin binta ya yi saboda yana kallon cartoon, da yake Yassar ɗin ma yakan je ya ɗauko shi ya yi hutun ƙarshen mako a gidanshi wasu lokuttan, yaron ya saba da su. Tana shiga ta kwantar da Ikram, banɗaki ta shiga ta ɗaura. . .
Please inason complete din book dinnan a’Ina zansamu
Kamar yadda kika gani muna dora babi ko wacce rana. Insha Allah nan ba da dadewa ba zamu dora har na karshe.