Tun da aka fara kamun hankalinta na kan wayarta da Amatullah ta baro mata a gida. Mutuwa ta yi, hakan ya sa ta bata don ta sa mata a caji. Ba tunanin gidan da yake shaƙare da mutane ko za a sace mata waya ta ke yi ba. Amatullah ta tabbatar mata da ta rufe ɗakin da mukulli ta kuma taho da shi. A'a, duk inda ƙarfe bakwai ta yi ta san Abdulƙadir zai kirata, a watanni shidan nan da suka wuce mata kamar ƙiftawar idanuwa, ƙarfe bakwai ya zama lokacin wayarsu. Duk da tun jiya take. . .