Minna
Gajiya ta ke ji har a ƙasusuwanta, wannan ne karo na farko a rayuwarta da ta taɓa zuwa wani waje da ya wuce ƙauyen Bugaje. Ji ta yi kamar za su je ƙarshen duniya, kamar tafiyar kwanaki ce a maimakon ta yini ɗaya. Sosai ta gode wa Anty Aisha da ta haɗa mata ruwa mai zafi ta ce ta je ta yi wanka. Sosai ta ɗan ji daɗin jikinta, wasu kayan ta samu an ɗauko mata, doguwar riga ce ta atamfa sabuwa fil, ɗauka ta yi ta saka tukunna ta ɗauki hijabin da ta. . .