Kamar yadda ya faɗa, a hanya ya tsaya ya yi sallar magriba, sannan ya ƙarasa gidan Yassar. Ya gwada kiran wayar Waheedah bai samu ba, hakan ya sa shi shiga gidan kanshi tsaye tare da yin sallama. Hauwa ta amsa mishi suna gaisawa, Abdulƙadir ɗin ya ɗora da,
"Waheedah fa?"
Ɗan jim ta yi na minti ɗaya, bata san me yake faruwa ba, ba kuma ta son shiga ko ma menene, idan akwai abinda zama da Yassar ya koya mata bai wuce ƙin shiga abinda babu ruwanta a ciki ba. Don haka ta nuna mishi hanyar ɗakin da. . .