Skip to content
Part 2 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

A nutse yake tuƙin shi, don ba ranar bace karo na farko da ya taka mota cikin rashin kwanciyar hankali, yana dai kula da yadda ake kauce mishi saboda ƙaton tambarin bajen sojoji da ke manne a jikin gefen motar, sai kuma sticker ɗin su a gaban motar, ko babu kayan da suke jikin shi, kallo ɗaya za ka yi wa motar ka san cewa ta soja ce. A haka har ya ƙarasa gidan shi da ke Rijiyar Zaki. kasancewar  shi First Lieutenant, akwai sojoji guda biyu masu tsaron shi a gida. Ɗaya daga cikin su ne ma ya buɗe mishi gate, bai damu da ya tsaya ya gyara parking ɗin ba, kawai kashe ta ya yi a nan harabar gidan ya fito, mukullin ma a jiki ya bar shi bai cire ba.

Cikin gidan ya ƙarasa, har sai da ya wuce tsakiyar falon da takalman shi, kamar daga sama ya ji muryarta na faɗin,

‘Babu sallama Sadauki? Takalmi har tsakiyar ɗaki, ina sallah a wajen fa.’

Bai yi ƙoƙarin cire takalman nashi ba, sallamar dai ya tsinci kan shi da yi. Jin shiru babu wanda ya amsa ya sa shi takawa cikin gidan, ya ƙarasawa ɓangaren Nuriyya, tare da sake yin wata sallamar, ya san tana can tana bacci, idan akace ba ta yi sallar Azahar ba ba zai yi musu ba, ranar girkinta ma tana bacci, balle yau da ta san ba ita ce da shi ba. Ƙarasawa ya yi ɓangaren ɗakin baccinta ya ƙwanƙwasa ƙofar tukunna ya tura ya shiga. Tana zaune akan gado, kunnenta liƙe da earpiece, ta tusa system a gaba, da alama kallo takeyi.

Jin shigar shi ya sa ta zare earpiece ɗin guda ɗaya tana kallon shi a kasalance da idanuwanta da suka fi komai a tattare da ita jan hankalin shi. Miƙa ta yi haɗi da yin hamma tukunna tace,

“Masoyi”

Kamar yadda take kiran shi ko a gaban waye. Ganin ya yi tsaye ya sa ta miƙa hannunta tana mishi alama da ya ƙarasa, ta sake yin wata hammar.

“Bacci nake ji Allah, jikina namun ciwo.”

Tsintar kan shi ya yi da tambayar.

“Me kikayi?”

Daƙuna mishi fuska ta yi.

“Kallo nayi… Me Waheedah ta dafa don Allah?”

Zuciyar shi ya ji ta yi wata irin dokawa da sunan Waheedah ɗin da Nuriyya ta kira. Bai iya amsa ta ba ya wuce kan shi tsaye ya nufi banɗaki. Da ido Nuriyya ta bi shi tukunna ta taɓe baki ta mayar da earpiece ɗin da ta cire daga kunnenta ɗaya ta ci gaba da kallon da shigowar shi ta katse mata. Rigar jikin shi ya fara cirewa yana mamakin yadda aka yi Nuriyya ba ta kula da jinin da yake jikin kayan shi ba, ba ta ma kula da damuwar da take shimfiɗe a fuskar shi ba. Kan washing machine ɗin da ke cikin banɗakin ya ajiye kayan da ya cire. Ruwa ya buɗe wa kanshi yana tsaye, sanyin ruwan na nutsar da wani abu a tattare dashi, idanuwan shi ya ƙanƙantar saboda ba ya son rufe su gaba ɗaya, bai san me ya faru ba, bai san ya aka yi ba, yana da wata irin zuciya ta fitar hankali da ba ta da alaƙa da aikin shi, tun kafin shigar shi aikin Soja yake da wannan zuciyar da har Abban shi yakan mishi addu’ar samun sauƙinta a can baya, ba ya son rufe idanuwanshi ballantana ya ga me zuciyar ta saka shi aikatawa ga Waheedah yau a karo na farko tun auren su. Ba zai ɓata lokacin shi akan tunanin abin da ya riga ya wuce ba, wannan ba halayyar shi bace sam, yau ba zai zama na farko ba, idan abu ya wuce mishi ya riga ya wuce tunda ba zai iya komawa ya sauya shi ba, gaba kawai zai duba ya kiyaye. Da wannan tunanin a ranshi ya ƙarasa wankan ya fito.

Bai bi takan Nuriyya ba, kamar yadda bata bi ta kan shi ba, da towel ɗin ɗaure a jikin shi ya fito daga ɓangarenta ya nufi ɓangaren Waheedah, don nan yake da tabbacin zai samu kayan shi a nutse, ɗakin baccinsu ya shiga, ƙamshinta na cika mishi hanci, tana son amfani da turarukan larabawa, sai dai ba zai ce da wannne da wanne takan haɗa ƙamshin su ya bada kalar da yake bayarwa ba. Kan gadonta ya hango kayan shi da ta fito mishi da su, ya ƙarasa ya ɗauka, riga ce fara ƙal, sai wando iya gwiwa baƙi mai wasu igiyoyi. Sai da ya fara saka singlet ɗin da take ta zabga ƙamshi tukunna ya saka sauran kayan ya ɗauki towel ɗin ya koma ɓangaren Nuriyya da shi.

Idan ya ce ga asalin abinda yake ji ƙarya yake, kan shi dai yayi mishi wani irin nauyi.

‘Ka sauƙaƙe min auren ka.’

Maganar Waheedah ta dawo mishi tare da saka shi kai hannu dai-dai ƙirjin shi inda yake jin wani abu na mishi ƙaiƙayi ya murza. Banɗaki ya koma ya mayar da towel ɗin ya rataye, tukunna ya ƙarasa kan gadon tare da kwanciya a gefen Nuriyya da ko inda yake ba ta kalla ba. Hannun shi ya miƙa ya zare earpiece ɗin kunnenta, ya sake miƙawa ya zare ɗayan, juyowa ta yi fuskarta babu walwala.

“Kallo fa nake yi…”

Idanuwan shi da ya ƙanƙance mata suka sa ta faɗin,

“Dan Allah mana Masoyi, kuma wallahi yunwa nake ji , nace me matarka ta dafa muku ka yi banza dani.”

Runtse idanuwan shi Abdulƙadir ya yi, duk idan yana tare da ita yakan sha wahala, komai sai ya fito fili yayi magana tukunna za ta gane, ba surutu yake so ba.

“Ba ta da lafiya… Tana asibiti.”

Sai yanzu ta gane dalilin da ya sa ya shigo mata, inda Waheedah ɗin nan ba ta tunanin jarabar nacinta zai sa ta bari Abdulƙadir ya shigo ɓangaren ta haka kawai ba tare da wani dalili ba. Taɓe baki ta ɗan yi.

“Allah ya bada lafiya.”

Ta faɗi da wani yanayi a muryar ta da ya sa Abdulƙadir miƙewa.

“Me kikayi yanzu?”

Ya buƙata muryar shi can ƙasan maƙoshi, ware mishi idanuwa Nuriyya tayi.

“Me na yi ni kuma?”

Hannun ta ya damƙo yana janta kamar ba ta da wani nauyi zuwa gab dashi.

“Abinda kika yi da bakin ki yanzu nake nufi.”

Wani irin yawu Nuriyya ta haɗiya, ta san halin shi, tun kafin ɗan zaman nan na auratayya ya haɗa su, tunda kusan fiye da rabin rayuwarta a gidan su tayi ta, ta kuma san raini na ɗaya daga cikin abinda ba ya ɗauka ko daga wajen yayyen shi, iyaye ne kawai Abdulƙadir yake ɗaga wa ƙafa, sai dai ita ɗin takan mishi abubuwa da yawa sai dai ya kalleta ya wuce, sosai ta shagwaɓe mishi fuska tana matsawa tare da shigewa jikin shi.

“Yunwa nake ji Masoyi…don Allah kar ka yi min faɗa… Ni banyi komai ba, addu’a na yi mata.”

Yadda ta narke mishi ya sa shi sauke numfashi, a hankali ya janye ta daga jikin nashi, yana dafe kan shi da hannu.

‘Kar ka fita ba ka sauƙaƙe minn auren ka ba.’

Maganganun Waheedah ne suke ta dawo mishi. Tsintar kan shi ya yi da saukowa daga kan gadon, asibitin yake son komawa ya tabbatar da ba ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta ba, ba ya jin zai samu wata nutsuwa in bai tabbatar ba.

“Ina zaka je?”

Nuriyya ta buƙata.

“Zan koma asibitin ne.”

Ya amsa ta, yana jiran ya ji ko za ta ce mishi su tafi tare ta duba jikin Waheedah ɗin. Bai san wani abu ta ji ya taso mata tun daga ƙirjinta har cikin wuyanta ya yi mata tsaye ba. Ba ta son nuna mishi kishin da ta ji, don haka tace,

“Za ka dawo da wuri? Ka yo min take away don Allah.”

Kallon ta Abdulƙadir yake yi.

“Me yake damun ki Nuriyya?”

Itama kallon shi take yi.

“Ban gane me yake damuna ba, kar ince ka taho mun da take away idan za ka dawo da wuri? Jikina ya min nauyi ba zan iya girki bane shi yasa, kuma laifinka ne da ka ƙi ɗauko min ‘yar aiki.”

Kai Abdulƙadir yake girgizawa.

“She was your Best Friend (Aminiyarki ce a baya).”

Ya furta a hankali, yana mamakin Nuriyya, yadda yake kallon ta ya sa ta cire earpiece ɗin daga kunnuwanta ta ture system ɗin, saukowa ta yi daga kan gadon tana takawa ta ƙarasa inda yake. Ba za ka kirata gajerar mace ba, amma tsayin Abdulƙadir na kwatance ne, ga girman da yake da shi kasancewar ba ya wasa da motsa jiki, sai ta ganta ‘yar ƙarama a gaban shi, matsawa ta yi ta riƙo hannun shi, ra ɗaga kanta ta sauke idanuwanta a cikin nashi.

“Masoyi yau kam laifina kake ta gani, ban san me na yi maka ba.”

Ta ƙarasa maganar tare da tattaro hawaye da ƙyar ta cika idanuwanta da shi.

“Kar ki min kuka Nuriyya… Kar ki min kuka.”

Ɗayan hannunta ta saka tana share ƙwallar da ta taru a gefen idanuwan ta.

“Ban san me nayi maka ba.”

Yadda ta yi maganar cike da rauni ya taɓa shi, numfashi ya sauke, bai san me yake damun shi ba yau. Ganin ya fara saukowa a fuskar shi kawai ya sa Nuriyya ɗora kanta a ƙirjin shi tana sakin wani guntun murmushin da take da tabbacin baya gani, ba ta san me ya faru ba yau, idan za ta yi faɗa da shi Waheedah ba za ta zama sanadin hakan ba, yaune karo na farko da ya jefeta da kalmar alaƙar da ke tsakaninta da Waheedah a baya, ba za ta bari hakan ya faru ba, tana sane sarai saboda ba ta ce za ta je duba Waheedah ɗin bane.

“Koma me na yi kaina a ƙasa Masoyi…kar a sauke Sojan a kaina yau… Umm?”

Ta yi maganar tana ƙara narkewa a jikin shi, ɗago ta ya yi yana sumbatar gefen fuskarta, ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fice daga ɗakin, bin bayan shi ta yi tana leƙawa ta tabbatar da ya yi nisa tukunna ta dawo ɗakin tana turawa tare da faɗin,

“Ni na ɗora mata ciwon… Yanzun haka ƙarya take yi… Ban san yaushe Waheedah ta koyi munafunci da baƙin hali ba.”

Da kan gadon za ta koma ta ci gaba da kallon da take yi, sai kuma ta fasa saboda cikin ta da ya yi wata irin murɗawa da yunwa. Babu shiri ta koma tare da ficewa daga ɗakin, kitchen ɗinta ta nufa, a dispenser ta ɗebi ruwan zafi ta haɗa shayi, kwalin biscuit ta ɗauka ta wuce ta koma ɗaki, ta kasa daina zagin Waheedah a cikin zuciyar ta, yau da safe Abdulƙadir ɗin ya koma ɓangaren ta, shi ya sa ta zauna tana kallon film ɗinta a system don kada ta yi tunanin yadda Waheedah take manne da shi kamar mayya, yanzun ma ba za ta bari tunanin Waheedah ya ɓata mata rai ba, hakan take maimaitawa kanta har ta samu wajen zama ta gyara system ɗin ta ɗauki earpiece ɗin ta mayar a kunnuwanta ta kunna film ɗin, tukunna ta ɗauki kofin shayin da ta ajiye ta janyo biscuit ɗin gabanta.

*****

A hanyar shi na zuwa asibitin ya ga Apple, don har ya wuce ya yi parking ya fita daga motar ya taka da ƙafar shi zuwa wajen masu Apple ɗin, hannu ya saka a aljihunshi duk da ya san bai zuba kuɗi ba, amma Waheedah ta ɗauko mishi wandon, yana da tabbacin duk wani abu dazaie buƙata ta sa a ciki, akwai kuɗin kuwa, biya ya yi ya karɓi ledar ya koma mota. Zai iya rantsewa da Allah duk idan ya dawo gida ya ganta, yakan manta yadda yake iya yin komai batare da ita a kusa da shi ba. Ɗayan aljihun ya kai hannu ya laluba ya ji I.D Cards ɗin shi na ciki yana kuma da tabbacin har da ATMs ɗin shi duk suna ciki.

Sai da ya sauke wani numfashi da bai san yana riƙe dashi ba tukunna yajae motar ya nufi asibitin. Parking ɗin motar shi ya yi a inda ake yi yana takawa zuwa cikin asibitin, hannun shi riƙe da ledar Apple ɗin da ya siya, in don ta shi ne ba za a ci Apple ba, don yana cikin kayan marmarin da ba ya kan shi sam-sam. Zama da Waheedah ya sa shi koyon ci, duk da haka ba dan yana jin daɗin shi ba, duk idan ta yayyanka yadda takan yi ta miƙo mishi ba ya ƙin ɗauka, ko idan tana ci, da ta gutsura take miƙa mishi shima ya gutsura sai ta sake karɓa, ko ruwa zata sha sai ta ba shi shima. Ba ya tunanin Waheedah na iya cin wani abu yana zaune ko ya ci nashi ba ta ba shi ba. Sosai yake shiga cikin asibitin har ya ƙarasa ɓangaren da Waheedah take, don sun kama ɗakin da ita kaɗai ce, kan shi tsaye ya nufi ɗakin da yake lamba ta sha biyu, ƙwanƙwasawa ya yi tare da murza hannun ƙofar ya shiga ba tare da ya jira an ba shi izini ba. Bai ga kowa a ɗakin ba sai Anty, da sallama ya ƙarasa ta amsa shi a sanyaye. Ledar Apple ɗin ya ajiye a gefe kan abinda akan ajiye kayayyaki, tukunna ya kalli Anty da take zaune tana goye da Ikram yana faɗin,

“Ke kaɗai? Ya jikin nata?”

Cikin sanyin murya ta amsa shi da cewa,

“Sun koma gida, ba a son hayaniya ne ko kaɗan, saboda jininta ya yi wani irin hawa. Abdulƙadir me yake faruwa?”

Kujera ya janyo ya samu waje ya zauna, fuskar shi da bata cika fara’a ba ya sake haɗewa waje ɗaya. Tambaya na ɗaya daga cikin abubuwan da ba ya so, musamman wadda ta shafi matsalar iyalin shi.

“Tambayarka nake, me yake faruwa?”

A daƙile yace,

“Tsakaninmu ne…Komai zai yi dai-dai…”

Sakin baki Anty ta yi na ɗan lokaci ta manta waye Abdulƙadir, yanzun yake tuna mata.

“Tsakanin kune take roƙon mu da mu karɓar mata takardar saki a hannun ka?”

Ɗago da kan shi ya yi yana kallon Anty.

“Kamar yadda nace, tsakanin mune. Anty kar ki wuce hurumin ki don Allah.”

Ya ƙarasa tare da mayar da kallon shi kan Waheedah da take bacci, hannunta da yake ɗaure da ruwa ya kama yana gyara mata zaman shi, bai bi ta kan Anty da take kallon shi ba, rashin kunya ce Abdulƙadir ya saba ba tun yanzu ba, ba ta san me ya sa ta yi tunanin iyalin da ya fara tarawa za su sa halayyar shi canzawa ba. Ba ta sake cewa komai ba, ta san halin rashin haƙurinta, kaca-kaca za su yi ita dashi a asibitin nan, don bakinta ba zai yi shiru ba, Abdulƙadir kuma ba zai ƙi faɗa mata duk maganar da ta fito daga bakin shi ba. Yanke hukuncin tashi ta koma wajen ɗakin ta yi, idan ya gama zaman shi ya fita ta dawo.

Yana jin buɗe ƙofarta da rufewa, juya idanuwan shi ya yi, ya ƙara matsawa kusa da Waheedah sosai, sam ba ya son baƙar tambaya, bai ga abin da shafi Antyn da matsalar gidan shi ba, ɗayan hannun Waheedah ya kama yana zagayo dashi takan cikinta tare da riƙewa.

“Wahee kin ga me kika ja mana ko?”

Ya furta a hankali, sai yanzu yake ƙara samun tabbacin cewa ba a cikin hayyacinta ta furta mishi kalaman ɗazun ba. Numfashi ya sake saukewa, sosai ya ja kujerar ya kwantar da kan shi a cikinta, kan kuncin shi haggu ya kwanta yadda zai iya kallon fuskarta, har lokacin ɗayan hannun shi na cikin nata. Wani numfashi mai nauyi ya sake ja ya fitar tare da lumshe idanuwan shi. Babu tunanin komai a cikin kan shi, kallon ta yake wata irin nutsuwa na saukar mishi, a hakan bacci mai ƙarfi ya ɗauke shi shi ma.

*****

Kanta take jin kamar an ɗora mata ƙaton dutse, idanuwanta da ƙyar ta iya ɗaga su, nauyi ta ji a saman cikin ta, a zatonta Fajr ne, don haka yakan yi mata, komin baccin da take yi za ta ji shi ya zo ya kwanta a jikin ta, ba zai taɓa kwanciya akan katifa ba, ko ta sauke shi da ya farka yake sake koma kan jikinta ya kwanta. Hannu ta kai ta ɗora akan cikin ta inda take jin nauyin, za ta rantse ɗumin shi ya banbanta da na sauran mutane. Ɗan ɗago kanta ta yi, shi ɗin ne ba magagin bacci takeyi ba. Hannu ta kai tana murza ƙirjinta inda take jin yana mata wani irin ciwo.

A hankali komai yake dawo mata, hannu ta kai da nufin tashin shi ya furta mata abinda take son ji, sai ta tsinci kanta da kasa yanke mishi baccin na shi, tunda tasan ba koda yaushe yake samu ba, duk da yazo hutune bayan shekara biyu sai yanzu ya sami hutu mai ɗan tsayi. Kallon shi take yi, zuciyarta a dunƙule waje ɗaya take jinta, shi ya sa ba ta motsa mata da duk wata ƙaunar Abdulƙadir ɗin ba. Zufa ta ga yana yi, a hankali jikin shi ke ɓari, ta san yana cikin duniyar mugayen mafarkan da kan hana mishi samun wadataccen bacci. Ganin yadda yake zabura ya sa ta kai hannunta kan fuskar shi tana shafawa a hankali.

“Sadauki.”

Ta kira a tausashe, hannunta ta ji ya damƙa kamar zai karya ta kafin ya buɗe idanuwan shi ya sake matse riƙon da ya yi wa hannunta da sai da ta runtse idanuwanta saboda azaba, sosai ta ɗauka ya karyata yau dai.

“Sadauki hannuna.”

Ta faɗi, hakan ya sa shi ɗago fuskar shi daga kan cikinta ya ƙare wama ɗakin kallo, kafin da sauri ya saki hannunta yana faɗin,

“Ban san sau nawa zance ki daina yo kusa dani inkin ganni a yanayin nan ba.”

Ɗayan hannunta mai ɗaure da ruwa ta ɗago tana murza wannan ɗin, idanuwanta har sun tara hawaye.

“Yau dai ka karyani, kayi maganarka ta ƙarshe a bakin ‘yan Amin, an amsa, ka karyani Sadauki…”

Ƙaramin murmushi ya yi ya kamo hannun nata da ta fizge, ƙarfi ya ɗan saka ya riƙo hannun.

“Kokawa za ki yi dani?”

Ya tambaya yana ɗaga mata girar shi guda ɗaya. Turo mishi laɓɓanta ta yi, hannun yake dubawa, farar fatarta ta sa hannun ya fara tara jini, shafa mata wajen yayi.

“Ban karya ki ba, in kina taɓa ni ina bacci dai zai faru wata rana, na faɗa miki ba kya jin magana.”

Fizge hannunta ta yi tana murzawa.

“Ina yarana?”

Ta buƙata a hankali, tana jin kewarsu na danne ta.

“Fajr na tare dasu Mami nake tunani, Ikram na wajen Anty…bari in karɓo miki ita…”

A hankali ta girgiza mishi kai duk da hakan take so, ba ta san lokacin da ta ɗauka a kwance ba, ta san yarinyar ta ji yunwa ba kaɗan ba, amma a karɓota daga wajen Anty, abin ya mata nauyi. Abdulƙadir bai saurareta ba ya miƙe ya nufi ƙofar ɗakin ya buɗe ya fita, Anty ya gani zaune tana danna waya, da alamar game ne da ya kalli screen ɗin.

“Ta tashi Anty, ki bata Ikram wai…”

Ba tare da ta ce mishi komai ba ta ajiye wayarta a gefe ta kama goyon yarinyar ta kwance ta miƙa mishi ita, karɓar ta ya yi yana kallon ta, idonta biyu, ta tsoma hannuwanta guda biyu a bakinta tana tsotsa. Gyara mata zama ya yi a hannun shi ɗaya tukunna ya buɗe ƙofar ya shiga sannan ya mayar ya rufe, sai da ya saka Ikram a hannun Waheedah ɗin tukunna ya zauna inda ya tashi, yana kallo ta miƙe zaune ta jingina bayanta da ƙarfen gadon, tukunna ta gyara wa Ikram ɗin zama sosai ta soma shayar da ita.

Ɗago kanta ta yi tana kallon shi, zuciyar shi ya ji ta doka ganin yanayin nan bai bar idanuwanta ba.

“Kai nake jira…”

Ta furta a hankali, kallon ta yake yana son fahimtar ma’anar kalaman da ta furta mishi.

“Abinda na faɗa maka dazun, ba na ce ka sauƙaƙe mun aurenka ba? Ko baka jini ba in sake maimaitawa?”

Yanzu ya gama tunanin ta dawo hayyacin ta, ashe ba ta dawo ba har yanzun, wace irin buguwa ta yi haka. Dole zai magana da likitocin nan, in ma barin ƙasar ya kama Allah ya yi mishi rufin asirin da ba ya tunanin zai gagare shi.

“Ka yi shiru…”

Waheedah ta faɗi tare da sake tallabo Ikram ɗin jikinta, wani irin yanayi take ji da ba ta san yadda za ta misalta shi ba, har wani ƙaiƙayi take ji a jikinta da son jin ya furta mata kalaman da za su datse igiyar da ta ƙulleta da shi.

“Kin buga kanki da yawa.”

Abdulƙadir ya faɗi can ƙasan maƙoshi, shi ne kawai bayanin da zai fassara abinda yake faruwa yanzun. Idan ba kanta ta buga ba Waheedah ba za ta nemi saki a wajen shi ba, kar ma azo maganar saki ba zata kalle shi cikin ido ta mishi magana da yanayin rashin kunya haka ba.

“Ban buga kaina ba, sakina nake son ka yi.”

Ta fara ɓata mishi rai, yana jin yanayin na barazana da haƙurin shi.

“Ki bar min maganar nan, ki bari, na ce kin buga kanki da yawa ne.”

Ya ƙarasa ya jan kujerar shi baya ya miƙe tsaye.

“Ina za ka je?”

Ɗan dafe kanshi ya yi sannan ya sauke hannun shi.

“Zan yi magana da likita.”

Wani murmushi Waheedah tayi, ta rasa me ya sa kalamanta suke mishi wahalar fahimta haka.

“Kayi magana dashi, idan ya tabbatar maka lafiyata ƙalau, sai ka dawo ka saurareni.”

Kallon ta Abdulƙadir yake yi, maganganunta na zauna mishi, a hankali ya girgiza kai, idan ya zaman bata buga kanta ba, idan ya zamana tana cikin hayyacinta bai san me zai yi ba, bai san ina take so ya ajiye kalaman ta ba. Babu shiri ya koma ya zauna yana kiran sunanta.

“Waheedah…”

Kallon shi kawai tayi ba tare da ta amsa ba, wani abu da ya zo wuyan shi ya tsaya yake ƙoƙarin haɗiyewa amma hakan ya gagara.

“Saboda haƙurina ya ƙwace a karo na farko a zaman mu ya sa kike furta min kalaman nan?”

Kai ta girgiza mishi a hankali.

“Ka min abin da ya fi na yau, ka sani kuma, na yau ɗin ne dai zai zama na ƙarshe In shaa Allah…”

Wata gajeriyar dariya ya ji ta kuɓce mishi.

“Kin san girman kalaman da kike furta min?”

Ikram ta janye daga jikinta don har ta yi bacci, tana gyarawa tukunna ta jinjina mishi kai.

“Ba zai yiwu ba to, idan ma da gaske baki buga kanki ba, ba zai yiwu ba Waheedah…”

Ya faɗa da wani yanayi a muryar shi da ya sa ta tambayar.

“Meye ba zai yiwu ba? Sakin nawa?”

A hasale Abdulƙadir yace,

“Waheedah…kina son sake gwada haƙurina ba?”

Cikin idanuwa ta kalle shi.

“Meye zai faru? Zaka sake ɗaga min hannu ne yadda ka yi? Nace idan na gwada haƙurin ka za ka sake ɗaga min hannu ne Abdulƙadir?”

Yadda ta ja sunan shi kamar ta kafa abin gurza kwakwa a zuciyarshi ta ja haka ya ji ta karce wurare da yawa a cikin ƙirjin shi. Ko a mugun tunani bai taɓa hango Waheedah za ta taɓa yi mishi rashin kunya ba, mamaki yake har ƙasan ranshi da ya kai ƙarshe wajen ɓaci, ya mata kuskure bawai bai mata ba, amma hakan ba shi bane dalilin da zai sa ta kalli ƙwayar idanuwan shi tana faɗa mishi son ranta, bai tsaya kalmar neman saki ba, harda rashin kunya tana ɗaga mishi murya.

“Sauƙaƙe miki a hannuna yake ko? Ba zai faru ba to, kina ji na? ba zai faru ba.”

Wasu hawaye ta ji masu zafin gaske suna zubo mata, ji take yi wani abu yana yamutsawa cikin kanta, rashin hankalin da yake mata tunanin take ji yana gab da cimmata idan bai sauƙaƙe mata auren shi ta huta ba yau.

“Wallahi baka isa ba.”

Ta faɗi muryarta na karyewa da kukan da takeyi, kujerar shi yaja baya tare da miƙewa, wani irin tuƙuƙin ɓacin rai yake ji har idanuwan shi ke lumshe wa.

“Ki kalleni…”

Ya furta ta tsakanin haƙoran shi, kukan ta taci gaba da yi.

“Ki kalleni Waheedah!”

Ya faɗi cikin wata irin murya da ta sata sauke idanuwanta da suka fara rinewa da kuka cikin nashi.

“Na isa…Ni Abdulƙadir Ahmad Bugaje na isa har na yi yawa. Ban san me yake damunki ba, ki kwanta ki yi bacci, bana ɓata lokacina akan abinda ya riga da ya wuce ke kin sani, zan yi kamar komai bai faru ba.”

Ya ƙarasa maganar tare da juyawa don jikin shi ya soma ɓari da ɓacin ran da yake ciki.

“Sadauki karka fita baka sauƙaƙe min ba!”

Waheedah ta furta kamar bai yi magana ba, kamar ba ta ji abinda ya ce ba, bai juyo ba, saboda bai da tabbacin abinda zai iya faruwa idan bai bar ɗakin ba, yadda ya doko ƙofar sai da ya firgita Ikram da ta zabura tare da fashewa da wani irin kuka, riƙe ta Waheedah ta yi tana jijjigata cikin alamar lallashi don itama kukan take yi. Yana fita Anty ta shigo tana kallon Waheedah dake faman share hawaye. Don haka ta ƙarasa ta karɓi Ikram ɗin daga hannunta ta goya yarinyar da da ƙyar ta samu tayi shiru.

“Don Allah kubi komai a hankali, kin ji Waheedah? Kin ga baki da lafiya.”

Saida ta share hawayen da sun ƙi daina zubar mata, da wani ɗaci a maƙoshinta tace,

“Ni bance wani abu ba Anty, ko a musulunci an bani damar neman saki idan na ga ba zan iya zama da shi ba… Me yasa ba zai min abinda nake so ba?”

Yanayin karayar da ke muryarta yasa Anty ƙarasowa ta dafa ta, itama ta ji idanuwan nata sun ciko da hawaye, don Allah ya yi mata wata irin zuciya da ko ba ta sanka ba ta ga kana kuka itama taya ka take yi , balle kuma Waheedah da hankalin yarinyar ya sa take jinta har ranta. A raunane tace,

“Ku dai bi komai a hankali, kar ki yanke hukunci cikin fushi.”
Wasu sabbin hawayen na zubar ma Waheedah tace,

“Anty ki aramun wayarki dan Allah.”

Ba tare da wata gardama ba Anty ta cire lambobin sirrin da ta rufe wayar da shi ta miƙa mata, wajen kira ta shiga ta fara saka lambobin mutum ɗayan da take da yaƙinin shi kaɗai ne zai iya saka Abdulƙadir ya yi mata abinda take so, shi kaɗai ne kuma ba zai ce ta yi haƙuri ko abi abun a hankali ba. Danna kira ta yi tare da kara wayar a kunnenta, ringing ɗaya ta yi a na biyun ya ɗaga da sallamar da ta kasa amsawa sai ma wani sabon kukan da ta ji ya ƙwace mata. Da ƙyar ta iya cewa,

“Abbah!”

Tana jin muryar shi daga ɗayan ɓangaren ya amsa da,

“Waheedah?”

Cikin son tabbatar da ita ɗin ce, kai take ɗaga mishi kamar yana ganin ta, wasu hawayen na zubar mata.

“Abbah”

Ta sake kira cikin kukanta.

“Subhanallah… Waheedah me yake faruwa ne? Lafiya dai ko?”

Kai ta girgiza mishi.

“Abbah ka yi wa Abdulkadir magana ya sauwaƙe min. Don Allah Abbah.”

Ta ƙarasa maganar kuka mai sauti na ƙwace mata, jim ya yi daga ɗayan ɓangaren da alama yana juya zancenta ne, kafin yace,

“Hajiya Halima na kusa dake?”

Da ƙyar ta iya cewa,

“Eh…”

“Ki ba ta wayar…”

Anty dake tsaye Waheedah ta miƙa wa wayar, ta ja ƙafafuwanta ta haɗe su da jikinta tare da ɗora kanta a saman gwiwoyinta hawayenta na ci gaba da zuba!

<< Abdulkadir 1Abdulkadir 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×