Mafari
Rigima ce ta saka shi biyo mota daga Lagos zuwa garin Kano, don tashi motar in ba hutun ƙarshen shekara zai zo ba, baya tahowa da ita, babu yadda Waheedah bata yi da shi akan ya biyo jirgi ba, ya ce mata ba shi da kuɗi, wata ya yi nisa, ga hidimar gida da sauran hidindimun da ke gaban shi. Sai da ta ce mishi ya biya kawai, akwai kuɗi a hannun ta, Abba ya bata kyautar kuɗi, bata yi amfani da su ba, akwai kuma kuɗin da shi ma yake bata, duk. . .