Skip to content
Part 27 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

A waya Hajja ta kira mishi Abba, amma cewa ya yi bayason ganin Abdulƙadir ɗin, idan sulhu yake nema ya je wajen Waheedah, shi kam ba zai saka musu baki ba. Da wani irin sanyin jiki Abdulƙadir yabar gidan. Amma tsintar kan shi ya yi da nufar hanyar gidan Yassar, ba zai iya zuwa gida ba, har a ƙasusuwan shi yake jin buƙatar Waheedah a kusa da shi. Bai taɓa zaton zai yi kewarta irin haka ba, ko watannin da yakan shafe ba tare da ita ba, in ya tuna cewar tana gidan shi, tana jiran komawar shi kan nutsar da wani ɓangare na zuciyar shi.

Amma yau yana gari ɗaya da ita, da auren shi a kanta ace ta kwana bakwai bata cikin gidan shi, gidan su, abin yana ci mishi zuciya fiye da yadda zai iya faɗi. Gidan Yassar ya ƙarasa ya yi parking ɗin motarshi, a jiki ya bar mukullin yana fitowa, ya ƙarasa bakin ƙofa ya ci karo da Yassar ɗin da yake girgiza kai.

“Abdulƙadir…”

Katse shi Abdulƙadir ya yi da faɗin,

“Hamma don Allah, bana jin tashin hankali, magana kawai zan mata, don Allah karka ce min wani abu, na roƙe ka.”

Da bayyanannen mamaki Yassar yake kallon Abdulƙadir, yasan kaf gidan su daga su Hajja sai shi Abdulƙadir kan ɗaga wa ƙafa lokuta da dama, amma Yassar yasan su Hajja kawai yake saukewa murya irin haka, ya kasa yarda da Abdulƙadir ne a gabanshi yake roƙon shi alfarma yau. Mutane kan ce in da ranka ka sha kallo, kallon yake sha yanzun. Raɓa shi Abdulƙadir ya yi ya wuce cikin gidan, ya ji daɗi da bai ci karo da Hauwa ba har ya ƙarasa ɗakin da Waheedah take ya ƙwanƙwasa tukunna ya murza hannun ƙofar ya shiga.

Ta sake kaya, rigar bacci ce a jikinta, doguwa har ƙasa. kalar rigar bata dami Abdulƙadir ba, idanuwan shi na kan fuskar Waheedah da take kallon shi da gajiya shimfiɗe cikin idanuwanta, takawa ya yi ya ƙarasa gefen gadon ya kama hannuwanta ya dumtse cikin nashi.

“Me yasa zaki karya alƙawarin ki? Kin ce ba za ki barni ba, da bakin ki kin sha faɗa min za ki kasance tare da ni…. Wahee in ke za ki iya barina ni bazan iya barin ki ba…. Wallahi ba zan iya ba.”

Kallon shi Waheedah take tunda ya fara magana, amma zuciyarta a bushe take ballantana kalaman shi su yi mata tasiri, a hankali ta tara abinda ya kawota inda take yanzun, bata jin akwai kalaman da za su canza ra’ayinta. Hakan Abdulƙadir ya kula da shi, ya sake dumtse hannuwanta da ta fara zamewa daga cikin na shi.

“Waheedah ni ne fa, ki kalle ni, ni ne, ban aureki don in rabu da ke ba…”

Ya kuarasa maganar da wani nisantaccen yanayi a muryar shi, yana kasa yarda Waheedah ce take son barin shi. Yana tuna lokacin da aiki ya kaishi tsakiyar inda ake tarzomar ‘yan Boko Haram a Maiduguri.

*****

Ta ɗauka tashin hankalinta kan aikin shi ya fara tsagaitawa, sai da aikin ya ɗaukar mata miji ya yi Maiduguri da shi. Tana da cikin Fajr wata kusan bakwai. Ko yaushe wajen awo ce mata suke ta kwantar da hankalinta, amma ta san ita da kwanciyar hankali sun yi hannun riga har sai Abdulƙadir ya dawo gida. Kasancewar in da suke babu network, duk Asabar yana samu ya fito ya kirata, idan bai kirata ba, wani idan ya fito cikin abokan aikin nashi zai turo mata da sakon Abdulƙadir ɗin. Yadda kwanaki kan wuce mata tsakanin Asabar zuwa wata Asabar ɗin ba zatace ba.

Sai dai duk wani tashin hankali da take tunanin ta taɓa shiga, ko ta taɓa jin labari bai kai wanda take ciki a yanzun da satika uku suka wuce ba tare da labarin Abdulƙadir ba, wata na huɗu yake nema lokacin a Maiduguri, bai kuma taɓa wuce sati biyu bata ji daga wajen shi ba. Ya faɗa mata idan sati huɗu suka wuce bai kira ba, ko sakon cewar yana lafiya bai sameta ba, to wani abin ya faru da shi, ta yi mishi addu’a. Kukanta bai tsananta ba sai da satika huɗun suka cika babu labarin Abdulƙadir, musamman da su Hajja suka fara kiranta su ji ko Abdulƙadir ɗin ya kira, Anty ma cewa ta yi zata zo ta ɗauke ta su koma gida, tunda ga cikin ya tsufa, ga kuma tashin hankali, sai dai ba za su gane ba.

Ba gida take son zuwa ba, mijinta take son sanin yana lafiya. Ba zata ce ga abinda take tunani ba, safiyar Asabar ɗin da Abdulƙadir ya cika sati biyar bai kirata ba. Zata iya tuna sauka daga kan gado ta shiga bandaki, yadda ta yi wanka bata sani ba, don hankalinta ya yi nisan da ba zata iya taro shi ba. Da kayan da ta shiga banɗaki ta fito, hijab kawai ta ɗora a saman su, ta ɗauki jakarta ta zuba duka kuɗin da ta ciro na hidimar gida a ciki, ta saka wayarta da bata da wani amfani yanzun a wajenta ta ɗauki jakar, takalma ta ƙarasa ta zira a ƙafafuwanta, ba tare da ta kula na wanka bane.

Lokaci zuwa lokaci take share ƙwallar dake bin fuskarta. Maiduguri zata je neman shi, bata san ina yake a Maiduguri ɗin ba, amma zai fi mata zaman da zata yi cikin gida ba tare da sanin halin da yake ciki ba. Fita ta yi daga gidan, tana tsaye tana kulle gidan da rashin nutsuwa yasa ta kasa saka mukullin a mazaunin shi harta rufe gidan, ga idanuwanta da suke cike taf da hawaye, a cikin kanta kawai ta kasa yarda tayi tunanin cewar wani abu ya sami Abdulƙadir ɗin.

“Wahee….”

Ta ji muryarshi cikin kanta, ɗan jim ta yi na wasu daƙiƙu, kafin ta share wasu hawaye masu ɗumin gaske da suka zubo mata, jin muryarshi cikin kanta ba baƙon abu bane ba, yau ɗin ne ta ji ta kurkusa sosai.

“Waheedah…”

Ta sake ji ya kira, juyawa ta yi tana sauke idanuwanta akan Abdulƙadir da yake tsaye, duka hannuwanta biyu ta saka wannan karon ta share hawayen fuskarta, tsaye yake cikin uniform har da hularsu ta Sojoji, hana sallah a saman kan shi, hannun shi ɗaya riƙe da jaka.

“Yanzun kuma gizo kake min Sadauki?”

Ta furta wasu sababbin hawayen na sake zubo mata. Kai Abdulƙadir ya girgiza mata, yana jin da akwai sauran hawaye tattare da shi babu abinda zai hanasu zuba, ya riga ya fitar da rai da sake ganinta, tashin hankalin da ya gani a watannin bai ɗauka zai fito da ran shi ba, in ya fito da ran nashi ma bai ɗauka ba tare da wata naƙasa ba. Duk da akwai tabbai na tsofin ciwuka da sababbin da ko warkewa basu gama yi ba, don ɗinki ne waje huɗu a fuskar shi, akwai wasu guda uku cikin kan shi da hular da ya saka ta ɓoye. Sai jikin hannuwan shi da cikin shi. Sai dai ganin Waheedah ya saka duk wani raɗaɗi da zugi da yake ji ɓace mishi.

“Waheedah”

Ya kira a karo na uku, yana kallon yadda ta ware mishi manyan idanuwanta cike taf da hawaye, kafin ta soma kokawa da numfashinta cikin yanayin da ya saka shi ƙarasawa ya riƙo damtsen hannunta, amma har lokacin kokawa take da daidaiton numfashinta, da gaske Abdulƙadir ɗin ne a gabanta, ba gizo yake mata ba, jikinta ko ina ɓari yake, bata san ta yarda jakar da take hannunta ba, ta saka hannunta kan fuskar shi cike da son tabbatar wa kanta shi ne.

“Sadauki…”

Ta kira wani irin kuka me sauti na ƙwace mata, hannuwan shi Abdulƙadir ɗin ya zagaya ya riƙe ta gam, ba tare da damuwa da yanda ƙaton cikinta yake tokare shi yana hana mishi riƙe ta yadda ya kamata ba. Kuka take da yasa ko ina na jikinta ɓari.

“Babu abinda ya same ni Waheedah…. Gani… Babu abinda ya same ni.”

Abdulƙadir yake faɗi yana jijjigata, kukan da take yana taɓa zuciyarshi, sai da ya tabbatar jikinta ya daina ɓari tukunna ya ɗauki jakarta, har lokacin tana jikin shi, da dabara ya ja su ya buɗe ƙofar suka shiga cikin gidan, jakunkunan ya ajiye, ya kama hannun Waheedah da take sauke ajiyar zuciya ya zaunar da ita a ƙasa, yana kallon yadda sai da dabara ta samu ta zauna. Ruwa yaje ya zubo a kofi ya kawo yana bata, da sauri ta karɓa ta shanye tas ta miƙa mishi kofin, ajiyewa ya yi a gefe ya zauna. Ko takalman ƙafarshi bai yi yunƙurin cirewa ba, kanta Waheedah ta kwantar a jikin shi, ya ƙara matsawa yana riƙe ta a jikin shi sosai.

Idanuwan shi ya lumshe yana jero duk wata addu’a ta godiya ga Allah da ya dawo da shi gida lafiya, ya ba shi damar riƙe matar shi a jikin shi haka. Ɗayan hannun shi ya ɗago ya ɗora kan cikinta, sai da ya sumbaci kanta tukunna ya ce,

“Ya kuke?”

Hannu Waheedah ta kai ta share wasu hawayen da tambayar Abdulƙadir ɗin ta fito da su, muryarta a dishe saboda kukan da ta sha ta amsa shi da faɗin,

“Ka tsorata mu, Sadauki ka tsorata ni.”

Sumbatarta ya sake yi yana riƙe ta gam a jikin shi. Cikin kuka ta ce,

“Karka barni, don Allah karka barni, ban san in da zan saka rayuwata ba, ban ma san ta in da zan fara ta babu kai a ciki ba.”

Shiru ya yi, baya yarda bakin shi ya buɗe da alƙawarin da ba shi da ikon cikawa a tsakanin su, tunda rayuwar ba a hannun shi take ba, a lokacin cikin kan shi ya roƙi Allah ya ba shi aron rayuwa mai tsayi a tare da ita.

“Ina za ki je da?”

Ya buƙata cikin sanyin murya.

“Maiduguri.”

Waheedah ta amsa tana saka Abdulƙadir ɗin kallonta da murmushi a fuskar shi.

“Bansan me zan yi bane ba…baka barni da zaɓi da yawa ba.”

Kai Abdulƙadir yake girgizawa, Waheedah da ko bindiga ya shigo da ita gidan in ta sani sai dai bindigar ta kwana wani ɗaki, su kuma su kwana ɗakin su daban. Ita ce zata bishi Maiduguri.

“Baki da hankali ko? Ta ina za ki fara nemana?”

Kafaɗunta ta ɗaga mishi, ita ma bata sani ba, binshi ɗin ne abinda ya fara zuwa mata a kaima

“Karki ƙara tunanin yin wannan kasadar.”

Jin ta yi shiru yasa Abdulƙadir ɗagota daga jikin shi yana kallon cikin idanuwanta.

“Da gaske nake Waheedah…”

Abdulƙadir ya faɗi yana ɗora wa da,

“Bambancin kowacce rana na tare da yadda take ƙara kusantani da ke.”

Dan sanin cewa tana gida tana jiran shi ya ishe shi kwanciyar hankali.

“Nutsuwar da take rage min shi ne sanin kina lafiya, kina gida a kwance, kina lafiya, karki hargitsa min da tunanin ko kina shirin bina inda nake. Kullum maganarki kar in barki… Kin taɓa tunanin ke idan kika barni ya zanyi?”

Yanayin dake fuskar shi yasa idanuwanta sake cika da hawaye.

“Babu inda za ni, ba zan barka ba, mutuwa ce kawai abinda zata sa in barka.”

Ta tabbatar mishi tana saka shi jinjina mata kan shi kafin ya riƙe ta a jikin shi.

*****

Yanzun ma hannunta ya ɗago yana ɗorawa kan fuskar shi.

“Kin ce babu in da za ki barni, me yasa kika bari na yarda da hakan bayan kin san ƙarya kike yi?”

Hannuwanta take zamewa daga cikin nashi, wannan karon bai hanata ba, wata irin gajiya yake ji har cikin zuciyar shi, numfashi ya sauke ƙirjin shi na wani irin ciwo. Cikin sanyin murya ya ce,

“Fajr fa?”

So take yi ta amsa shi, yanayin shi take jin kamar zaiyi tasiri a kanta, shi yasa ta zaɓi yin shiru. Don ko kusa bata tunanin komawa gidan shi, tana jin shi ya mika hannu ya ɗauki Ikram da ke bacci, riƙe yarinyar Abdulƙadir ya yi a jikin shi, ya nutsu yana kallon yadda take bacci ba tare da tunani ko damuwar wani abu ba, yana jin kamar su yi musayar matsayi da yarinyar, ya kai mintina biyar a zaune a wajen, kafin ya mayar da Ikram inda ya ɗauke ta. Numfashi ya ja yana sake fitar dashi, kafin ya miƙe, Waheedah yake kallo da ta ƙi ɗago fuskarta ballantana su haɗa idanuwa.

“Sai da safe Wahee, ki yi haƙuri ni kam, bazan iya faɗan nan ba wallahi, don Allah ki yi haƙuri. Zan dawo gobe in shaa Allah, ki kula da ku.”

AbdulKadir ya ƙarasa maganar yana juyawa ya fice daga ɗakin yana nufar hanyar da zata fitar da shi zuwa harabar gidan. Ko da ya shiga motar shi ya daɗe zaune a ciki, ya haɗe kan shi da abin tuƙin yana rasa abinda ya kamata ya yi, rayuwa bata taɓa gwada ƙarfin halin shi ta irin wannan fannin ba, yanzun da hakan ya faru yake gane shi raggo ne na gaske, don kam baya jin zai iya jurewa. Tuƙi yake a karo na farko ba tare da nutsuwa ba, yanajin mutane na zagin shi, bata su yake ba, gida kawai yake son ƙarasawa ba tare daya kashe wani ko wani ya kashe shi ba, da ya gan shi cikin gida ma ba zai ce ga yadda ya ƙarasa ba. Mukullin a jiki ya bar shi tunda ya shigo da motar, ya wuce cikin gida, kan shi tsaye ya nufi ɓangaren Waheedah, bedroom ya shiga ya kwanta yana lumshe idanuwan shi ba tare da ya san tunanin da yake yi ba.

*****

Yadda ta ga rana haka ta ga dare, da safe fuskarta a kumbure ta tashi da ita, saboda rashin bacci da kuma kukan da ta sha. Daɗinta ɗaya, a satin su Fajr suka yi hutun makaranta saboda gabatowar azumi. Ikram ta fara yi ma wanka ko da ta tashi, ta bata tasha da ta ga ta yi bacci ta ajiyeta ta je ta yi wanka itama. Sai da ta fita suka gaisa da su Hauwa da suketa sauri da alama sun makara, tukunna ta koma ɗaki, kusa da Ikram ta kwanta jin idanuwanta har yaji suke mata saboda rashin bacci. Ta lumshe idanuwanta ta ji Fajr a jikinta, hannu ta sa tana ɗaga shi.

“Fajr ka kwanta a katifa…. Karka dame ni don Allah.”

Kallonta ya yi, da alama yanayin fuskarta ya gani yasa shi zagayawa ta ɗayan ɓangaren ya hau gadon ya kwanta, juya kwanciya ta yi ta fuskance su, ta kama hannun Ikram da kamar ta ji ta, ta damƙe ɗan yatsanta guda ɗaya. Murmushi Waheedah ta yi zuciyarta na cika fam da ƙaunar yarinyar, kullum sai ta ɗauka babu yadda za ayi ta so yaranta fiye da son da take musu, sai su yi wani abin da zai sa zuciyarta cika fam da wata irin ƙaunar su. Bata san lokaci na tafiya ba, baccin kuma bai ɗauke ta kamar yadda ta yi tsammani ba.

Babu komai cikin kanta da ya wuce su Fajr da take kallo sun nutsu suna bacci. Ƙwanƙwasa ƙofar da ta ji ana yi ne yasa ta lumshe idanuwanta don a tunanin ta Abdulƙadir ne, muryar Anty ta ji.

“Waheedah…”

Da sauri ta diro daga kan gadon ta je ta buɗe ƙofar.

“Anty…”

Ta faɗi cikin sigar gaisuwa tana ɗan matsawa Antyn ta shiga cikin ɗakin, mayar da ƙofar Waheedah ta yi ta rufe tukunna ta ƙarasa gefen gadon kusa da Anty ta zauna suna gaisawa sosai.

“Ya jikin ki?”

Ɗan rausayar da kai gefe Waheedah ta yi.

“Alhamdulillah… Na ji sauƙi.”

Kai Anty ta jinjina, tausayin Waheedah na cika zuciyarta. Duka cikin su babu wanda yasan da maganar auren Abdulƙadir ɗin, Nabila ce ta je gidan ta dawo musu da labarin, ita Anty ta fi awa ɗaya a zaune jin Nuriyya ce Abdulƙadir ya aura, kafin daga baya ta je har ɓangaren Mami tana sauke takaicinta a can, don ce wa Mami ta yi lokacin su je su taho da Waheedah ɗin tunda Abdulƙadir ba shi da hali ballantana kunya, murmushi kawai Mami ta yi duk da a idanuwanta za ka ga tsantsar damuwar da take tattare da ita.

Kawaici irin na matar har mamaki yake ba Anty. Shi yasa take ganin girmanta ba kaɗan ba, don da Waheedah ‘yarta ce ikon Allah ne kawai zai sa ba zata kashe aurenta da na Abdulƙadir ba, tunda farko ma bata ga dalilin da zai sa ta ɗauki yarinya ta bashi ba, musamman mai sanyin hali irin na Waheedah. Numfashi Anty ta sauke.

“Bansan me kikai ta bari a ranki har zuwa lokacin nan ba, ni bazan baki haƙuri ba Waheedah, amma ki je gida ki yi magana da Maminki, na san kawaici ba zai barta furta komai ba, ki je ta ga kina lafiya ba wai a waya ba.”

Hannu Waheedah takai tana share hawayen da ta ji sun zubo mata. Cikin sanyin murya ta ce,

“Idan gidan za ki koma bari mu wuce tare.”

Kai Anty ta jinjina mata, ba gida zata koma ba, amma hidimarta za ta jira, in ta sauke Waheedah ɗin sai ta sake fitowa. Hijabinta ta ɗauko, sai jakar goyon Ikram ɗin ta saka ta a ciki ta goyata ta gaba ta tallabe, Fajr zata tasa Anty ta hanata, saɓa yaron ta yi a kafaɗarta, wayarta kawai Waheedah ta saka a jaka ta riƙe a hannu, mukullin da Hauwa ta bata na gidan guda ɗaya, ko da zata fita ta ɗauka , sannan ta bi bayan Anty. Kulle gidan ta yi suka nufi motar Antyn, a cunkushe Waheedah take jin kanta da zuciyarta gaba ɗaya. Da tunani fal a kanta suka nufi gida.

Har suka ƙarasa gida Waheedah bata ma sani ba, sai da ta ji Anty ta buɗe mata ƙofar motar ta ɓangarenta, saukowa ta yi da Ikram tallabe a ƙirjinta. Fajr ya tashi bata ma sani ba, jakarta ta ɗauka tana ratayawa ta kama hannun shi, ko sallama bata yi wa Anty ba ta wuce tana nufar ɓangaren su, Antyn ma mota ta koma ta fice daga gidan, zuciyarta cike da tunanin Waheedah ɗin. Da sanyin jikinta ta ƙarasa gida tana shiga da sallama, a falo ta samu Mami a zaune, Fajr kam bai bita ciki ba ya wuce ɓangaren Hajja, ita ma bata bi ta kan shi ba. Sallama ta yi tana cire takalmanta ta ƙarasa, tunda Mami ta amsa ta ta ji idanuwan ta sun cika da hawaye.

Kan kujera ta zauna kusa da Mami ta sauko da Ikram ta kwantar da ita a gefe, hijabinta ta cire, tana saka ɗan yatsa ta share Kwallar da ta taru a gefen idonta, kallon ramar da ke ƙasan idanuwanta Mami ta yi, zata yi ƙarya idan ta ce bata kwana da yarinyar tana tashi da ita a rai, kwanakin nan yinsu kawai take ba don suna mata daɗi ba, duk da Yassar kullum da safe saiya kira ya haɗa ta da Waheedah ɗin sun gaisa, baccin kirki ma ba sosai take samun shi ba, haka takan raya daren da salloli tana yi wa Waheedahr addu’a.

“Waheedah…”

Mami ta kira tana rasa ta inda zata fara mata magana, maganar cewar bata taya Waheedah jin abinda Nuriyya ta yi mata ba bai ma taso ba, har ƙasan zuciyarta ta ji zafin abin, musamman ita da ta fi kowa sanin yadda Waheedah ta ɗauki Nuriyyar, amma rayuwar haka take tafiya, wanda ya fi kusa da kai shi ya fi kowa samun damar cutar ka, yanzun mutanen kirki ba su bane wanda za su ɗauki abu su baka, mutanen kirki sune wanda za ku yi tarayya tare da su ba su cutar da kai ba. Auren da Abdulƙadir ɗin ya yi bai saɓa wa addini ba, ya taka matakai da yawa na rashin kyautawa ne kawai a al’adance.

Taso yi ma Waheedah maganar sai ta ce mata,

‘Babu komai Mami, ya riga da ya faru, ki mana addu’a Allah yasa hakan alkhairi ne.’

Duk da ta bar zancen, wani abu a ƙasan ranta sai da ya faɗa mata Waheedah na ɓoye kishin da ta san yana damunta ne, ta kuma jima tana tsoron rana irin wannan. Tana kallon yadda Waheedah take kai hannu tana share Kwallar da take tarar mata lokaci zuwa lokaci, numfashi Mami ta sauke.

“Waheedah…”

Ta sake kira a tausashe, wannan karon kamar hakan Waheedah take jira wani irin kuka mai sauti ya ƙwace mata, jikin Mami ta kwanta tana kukan da take ji yana fitowa daga ƙasan zuciyarta inda yake mata ciwo na gaske. Kuka take da bata taɓa yin irin shi ba a rayuwarta, kukan ranar da Abdulƙadir ya faɗa mata ya ƙara aure ta text saboda bai darajata ba, kukan ranar da ya shigo mata da ƙawarta, Nuriyya da ta ɗauka ‘yar uwa a matsayin kishiya, kuka take da duk ranar da Nuriyya ta rike Abdulƙadir ɗin a gabanta, kuka take da ya kamata ta yi shi watanni takwas da suka wuce, ta jima tana riƙe da shi a ranta, yanzun da ta fara bata san ya zata daina ba, muryarta a karye cikin wani irin kuka ta ɗago daga jikin Mami tana faɗin,

“Ma… Mami duk mata… Duk matan garin Kano da inda aiki yake kai shi… Mami bai ga kowa ba sai Nuriyya….me yasa Nuriyya?”

Waheedah ta ƙarasa maganar tana kai hannu ta dafe ƙirjinta da yake wani irin ciwo kamar zai tsage. Kishi take ji har wani duhu-duhu take gani. Riƙe ta kawai Mami ta yi, tasan kukan ma rahma ne, amma har ranta take jin shi, duk ƙarfin hali irin nata hawaye take ji cike taf da idanuwanta, yanzun ta gane kishi ne yake cin ‘yar tata.

“Kuma Nuriyya ta aure shi, ni bazan taɓa mata haka ba, bai haramta ba, amma bazan auri mijinta ba…me yasa zata auri nawa? Mijina Mami, Sadauki ta gani duk faɗin Kano…”

Waheedah take faɗi ba tare da ta sani ba, don yadda take maganar tana wani irin kuka kasan ba a cikin hayyacinta take ba, sosai take kuka tana sambatun da ba zata ce ga daga inda suke fitowa ba, riƙe ta kawai Mami ta yi tana jijjigata kamar ƙaramar yarinya. A jikin Mamin ta yi kuka har bacci ya ɗauke ta, banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, a hankali Mami ta zame Waheedah kan kujerar tana ɗauke mata Ikram. Bacci ta yi har Azahar, lokacin da ta tashi wani irin zazzaɓi ya rufe ta ruf, da ƙyar ta ja jiki ta wuce ɗakin Mami ta yi alwala, sai da ta ba Ikram tasha don duk haƙurin yarinyar harta fara kuka, tukunna ta samu ta yi sallah.

Duk yadda Mami ta lallaɓata kasa cin abinci ta yi, shayi ta haɗa ta samu ta sha rabin kofi, da idanuwa Mami take binta duk inda ta yi , har sai da ta gama jijjiga Ikram ta yi bacci, Mami ta karɓe ta ta saka zani ta goyata. Waheedah ɗin na zaune kan kujera, tana jin kamar ta shige ciki don guje wa magana da Mami ɗin.

Cikin sanyin murya Mami ta ce,

“Na ɗauki ido na saka miki ne tun farko saboda na yi tunanin in har kina da matsala ina da kusancin da za ki same ni da ita. Ba zance miki haƙuri ba abu bane mai kyau, duk da akan ce idan ya yi yawa yana zama cuta. Babu inda haƙuri yake yawa, a zamantakewa ta yau da kullum, ko a zamantakewa ta aure, musamman ma ta aure…”

Gyara zama Waheedah ta yi, tana jin yadda hawaye suka cika mata idanuwa, magana Mami ta cigaba da yi.

“Ba haƙuri bane yake yawa ya zama cuta, rashin yafiya ne, akwai banbanci tsakanin ai maka abu ka haƙura bakace komai ba, da ai maka abu ka haƙura ka yafe. Yafiyar ita ce take saka duk yawan lokutan da kai haƙuri kake samun riba, idan har za ka haƙura ba za ka yi magana ba ka bar abin a ranka ba shi da wani amfani, gara ka fito da shi kawai…”

Mami ta ƙarasa maganar tana sake sauke muryarta da faɗin,

“Abdulƙadir halin shi ne ya fito fili, shi yasa babu wanda ya tambaye shi me ya faru, babu ma wanda ya yi tunanin ya ji nashi uzurin, kowa laifi ya ɗauka ya ɗora mishi. A karo na farko ko ya dace ko bai dace ba Waheedah, ko da za’a ce na yi son kai zan faɗi raina ya sosu da auren Nuriyya da Abdulƙadir ya yi, bai taka addini ba, amman ban ji daɗi ba ko kaɗan, saboda halin da za ki shiga na yi tunani.”

Wannan karon Waheedah bata ko yi ƙoƙarin share hawayen da ke zubar mata ba, yadda muryar Mami take a karye kawai na ƙara taɓa zuciyarta, ita kanta Mamin ƙoƙarin tarbe hawayen da suke ta mata barazana take, yanayin Waheedah ɗin na gwada ƙarfin zuciyar ta fiye da yadda ta zata.

“Mutuwar aure ta fi yin shi wahala, duk yadda ake ganin da kalamai kawai za’a yi ta. Ban taɓa ganin inda uwa ta so mutuwar auren ‘yarta ba Waheedah, ko ya ƙaddara ta rubuto hakan, ni shawara kawai zan baki a wannan matakin, ba zan yi ƙoƙarin haramta miki abinda addini ya halarta miki ba, abu ɗaya zan ce miki, ki yi magana da Abdulƙadir…”

Kai Waheedah take girgiza wa Mami wasu sabbin hawayen na zubar mata, har ranta ta gaji da auren shi, tana jin idan ta koma komai zai iya faruwa, ciki har da tarwatsewar zuciyarta, ba zata iya ɗaukar wani ciwon bayan wanda ta yi ta ɗauka ba.

“Wallahi Mami na gaji, na gaji har raina…”

Waheedah ta faɗi cikin kuka, kai Mami ta jinjina mata.

“Bance wani abu ba nima, ki yi magana da shi, magana ta fahimta, lokutta da dama aure kan samu tangarɗa ne saboda rashin tattauna matsala har a samu maslaha, kowa na ganin laifin ɗan uwan shi ne, babu kuma wanda yake ƙoƙarin sauke girman kai ya saurari ɗayan har a gano bakin zaren, ki faɗa mishi matsalar ki, ki saurari uzurin shi.”

Shiru Waheedah ta yi tana share ƙwalla.

“Kina jina?”

Mami ta faɗi, kai kawai Waheedah ta iya ɗaga mata, tana sake shigewa cikin kujera. Numfashi Mami ta sauke, komai baya mata daɗi sam, kitchen ta wuce ba don tana da wani abu mai muhimmanci da zata yi a ciki ba, sai don in ta ci gaba da kallon Waheedah ɗin hawayen da take ta ɓoyewa ne za su zubo. Duk wannan kishin da yake nuƙurƙusarta, da gajiyar da take faɗin ta yi, zaka fahimci yadda rabuwa da Abdulƙadir shi ne ƙarshen abinda take son yi.

<< Abdulkadir 26Abdulkadir 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×