Tsugunnawa ya yi yana fitar da numfashi a wahale, cikin shi ke ciwo saboda hanjin shi da yake ji sun tattaru sun ƙulle a gefe ɗaya. Ko ina na jikinshi ciwo yake, har wajajen da bai taɓa sanin za su yi mishi ciwo ba tare da zubar jini ba. Waheedah na tsaye tana kallon shi, yadda yake yi kamar shi ya yi watanni da ciwon da ta yi fama da shi, a karo na farko halin da yake ciki bai taɓa zuciyarta ba, tana jin daɗin yadda yake jin kaɗan cikin ƙuncin da zuciyarta take fama da shi.
“Ƙirjin ka kamar zai buɗe ko Sadauki?”
Ta buƙata cikin wani irin sanyin murya da yasa Abdulƙadir ɗaga idanuwan shi da har sun canza launi yana kallon ta, rausayar da kai ta yi.
“Haka nake ji duk idan na ganka tare da Nuriyya…”
Miƙewa Abdulƙadir ya yi ya ƙarasa inda Waheedah take, hannuwan shi yasa ya kama kafaɗunta yana ɗan dannawa cikin alamun ta zauna, bata yi mishi musu ba ta yi ƙasa tana zama kan kafet ɗin ɗakin, shi ma zaman ya yi a gefenta, don dakin ya fara jujjuya mishi da jirin tashin hankali. Idan ta ci gaba da magana baisan inda zai saka rayuwar shi ba, ya buɗe bakin shi ya kai sau biyar amma ya kasa furta komai. Sai da ya ja numfashi yana fitar dashi, kafin ya iya cewa,
“Waheedah…”
Kalmar na fitowa daga wani sashi na zuciyar shi da yau ɗin ne ranar farko daya san da zaman shi, runtse idanuwan shi ya yi yana buɗe su, cikin kan shi yake ji babu komai, bai san ko yana jin alamun ƙwaƙwalwa ba a baya, amma a yanzun baya jin komai sai ƙoƙon kan, balle ya yi tunanin ƙwaƙwalwar shi zata taimaka mishi da wasu kalamai, amma ƙirjin shi ciwo yake kamar zai buɗe, da gaskiyar zancen Waheedah, bai gane yadda zai fassara abinda yake ji ba sai da ta faɗa, kan shi babu komai, amma zuciyar shi cike take fam da yanayoyi daban-daban, buɗe bakin shi ya yi yana barin zuciyar shi ta mulki abin zai fito daga bakin shi.
“Ina da son kai, ban taɓa sanin ina da son kai ba sai yau, kina da rashin adalci…”
AbdulKadir ya ƙarasa maganar cikin muryar da ta dira kunnuwanshi kamar ta wanda ya sha gudu, yana saka ƙwayar idanuwan shi cikin na Waheedah da take ware mishi nata cike da maiƙon hawaye, kai ya ɗaga mata a hankali.
“Me yasa baki faɗa min ba? Me yasa baki faɗa min ba Wahee? Kin ce kina sona, ni na gani kina sona, me yasa kika ɓoye min?”
Kai Waheedah take girgiza mishi, idanuwanta na tsiyayo da wasu hawayen masu ɗumi, ba zai mata haka ba, ba zata bar shi ya ɗora mata laifin da bata da shi ba.
“Me yasa ka ɓoye min za kai aure? Ka ɓoye min ka yi aure har wata ɗaya? Ka ɓoye min ƙawata ka aura sai da ka shigo min da ita cikin gida?”
Jinjina kai Abdulƙadir ya yi, kalamanta duka suna dirar mishi kamar zubar ruwan gishiri a sabbin ciwukan da kalamanta na baya sukai mishi, yasan tana da muhimmanci a rayuwar shi fiye da yadda zai misalta da kalamai, bai dai san a tattare da muhimmanci akwai iko akan abubuwa da yawa da suka shafe shi ba, ciki har da zaman lafiyar shi, kwanciyar hankalin shi, nutsuwar shi gaba ɗayanta.
“Hakane…”
Abdulƙadir ya iya furtawa yana kallonta da wani nisantaccen yanayi, muryar shi yake ji na fitowa da wani sauti da bai da fasali.
“Ba uzurin da ya sani yin abin da na yi nake so in baki a ƙurarren lokaci irin yanzun ba…”
Ya faɗi yana maida numfashi kafin ya ce,
“Banda komai, ko kalaman ban haƙuri bani da su, wallahi banda kalaman baki haƙuri.”
Don har zuciyar shi yake jin haƙuri ya yi kaɗan ya wanke girman laifin da ya yi mata.
“Shi yasa zan baki wani abu daban, zan baki dukkan gaskiyata, ban san zan yi aure ba, lokaci ɗaya tunanin ya zo min…”
Kai Waheedah take girgiza mishi, bata son ji, bata son jin yadda ya yi aure, tunda ya riga da ya yi, shi ma kan yake girgiza mata.
“Za ki ji ni, ba za ki yanke min hukunci gaba ɗaya ba, ki min adalcin da ban miki ba don Allah, na roƙe ki.”
Cikin rawar murya da ta fito cike da sautin kuka Waheedah take girgiza mishi kai.
“Son kai Sadauki, son kai ne wannan.”
Kafaɗa ya ɗan daga mata, ita hawayenta sun zuba, an ce kana samun sauƙi duk idan ka zubar da su, shi bai samu wannan zaɓin ba.
“Na sani, halina ne dama…”
Cewar Abdulƙadir ɗin yana ɗorawa da,
“Da sanin zan yi auren da auren duka a kwana biyu ya faru, na samu awanni 48 da zan ɗauki mintina talatin in faɗa miki zan yi auren, ban yi ba, kuskurena ne wannan da zai zauna dani har ƙarshen rayuwata…”
Hannunta ya kamo yana haɗa yatsunsu waje ɗaya, yana jin yadda ta dumtse nashi cike da neman alfarmar da ba zai iya mata ba, idan bai faɗa mata na shi ɓangaren ba, yana da tabbacin ƙirjin shi buɗewa zai yi.
“Ammanm ni ne, bana tunani, ban fara tunani ba sai bayan na yi auren, na kasa faɗa miki, ban ji maganar su Hajja da suka faɗa min akwai rashin kyautawa a abinda na yi ba saboda ina ganin addini ya halarta mun, ban yi tunanin ke yadda za ki ji ba har lokacin, na yi tunanin ban kyauta ba da ban faɗa miki ba, kin san me yasa?”
Kai ta girgiza mishi a hankali, akwai yanayin da yake tattare da muryar shi da bai hana gwiwoyinta yin sanyi ba duk da a zaune take,
“Saboda ban saba ɓoye miki abu ba, lokacin ya kamata in san ban kyauta ba…”
Wannan karon ajiyar zuciya mai nauyin gaske ya sauke.
“Ina miki maganar Nuriyya ne saboda ke ce, ba don na raina ki ba Wahee, ba don in nuna miki na isa ba, Wallahi babu ko ɗaya a ciki, ki yarda da ni…”
Ya ƙarasa maganar muryar shi na karyewa, kafin ya ci gaba da faɗin,
“Ina faɗa miki ne saboda ke ce.”
Ya sake maimaitawa kamar ‘Ke ce’ ɗin ta isa ta fassara mata abinda yake nufi, shi kuma kalaman da zai yi amfani da su don ta fahimta yake nema.
“Tun ban san zan aureki ba kike sanin abubuwa a kaina da ba kowa ne yake sani ba, saboda ke ce, ke kaɗai kike jin maganata idan raina yana ɓace, saboda ke ce, su Hajja na sona, amma ba sa son da yawa cikin halayena, suna magana a kai, baki taɓa ba, kina sona da komai nawa, shi yasa na bari kika san ni yafda kowa bai sanni ba.”
Idanuwanta Waheedah ta runtse tana ƙoƙarin haɗiye yawu ko zai wuce mata da abinda take jin ya tsaya mata a ƙirji , shagwaɓe mata fuska Abdulƙadir ya yi cikin yanayin da bata taɓa gani ba, sai da ta ji zuciyarta ta doka da tunanin ko kuka zai yi.
“Ban miki maganarta don in sosa ranki ba, na miki maganarta ne saboda komai nawa ina faɗa miki, ban yi tunanin kishin da za ki ji ba, saboda ina son kaina da yawa, wannan ma kuskurena ne… Auren ƙawar ki.”
Abdulƙadir ya ƙarashe maganar yana runtse ido kamar kalaman nashi sun raunani shi, kafin ya buɗe su ya ci gaba da faɗin,
“Wahee ina so in ce ki yafe min, amma ina jin hakan ma zai ƙara zama rashin adalci…”
Kai ta ɗaga mishi tana tabbatar mishi da ta yarda da kalaman shi, hawayen da suka zubo mata na ƙara tafasa shi, numfashi ya sauke yana ɗago hannun su da yake haɗe ya kai kan goshin shi, ya lumshe idanuwan shi yana ƙara sauke numfashi mai nauyi, duniyar ta mishi tsaye waje ɗaya, ya kai mintina biyu a haka, kafin ya iya ɗago da kan shi.
“Son kai halina ne, shi yasa zan faɗa miki ba zan iya rabuwa da ke ba….Wallahi ba zan iya ba, da tunanin aikina zai yi sanadiyyar mutuwata nake kwana nake tashi kullum, cikin sati ɗaya kin nuna min kin fi aikina wannan haɗarin, Wahee za ki kashe ni in kika barni….”
Abdulƙadir yake faɗi a susuce, babu komai cikin kanshi har lokacin, ba lallai bane kalaman da yake faɗi suna da wata ma’ana tunda baya jin taimakon ƙwaƙwalwar shi a fitarsu, zuciyar shi ce kawai take haukanta.
“Idan lokaci kike buƙata zan baki… Komin tsayin lokacin da kike so ki huce zan baki…”
Kallon shi Waheedah take tana girgiza mishi kai cikin rashin yarda da cewar zai bata duk lokacin da take so, shi kuma yana fahimtar hakan da cewa tana nufin bata yarda ba, ya sauƙaƙe mata auren shi, hakan yasa shi ƙara rikicewa da faɗin,
“Ba zan dinga zuwa ba, ba zan dame ki ba, duk lokacin da kike buƙata…”
Ɗayan hannunta ta sa tana goge fuskarta, ta ja hancinta da take ji yana mata raɗaɗi kamar ta shaƙi barkono.
“Shekara ɗaya…”
Ta furta cikin dakusasshiyar murya, wannan karon dokawar da ya ji zuciyar shi ta yi da a ƙasar wajene ya tabbatar likitoci za su ji mishi tsoro bugun zuciya na farat ɗaya.
“Shekara biyu.”
Waheedah ta sake faɗi da wani nisantaccen yanayi a muryarta.
“Uku… Huɗu… Biyar….”
Taci gaba, ba iska kaɗai yake ji ta mishi kaɗan ba, hasken ɗakin ya ga yana raguwa, ga zuciyar shi da take ci gaba da dokawa tana mishi barazanar tsayawa, hannun Waheedah ya saki yana dafa gadon da ke kusa da shi ya miƙe da ƙyar. Bata ce mishi komai ba, asalima da idanuwa take bin shi har ya fice daga ɗakin, bai ko ja mata ƙofar ba, bai taɓa ganin nisan daga cikin gidan Yassar ba zuwa harabar gidan inda ya ajiye motar shi. Wannan tashin hankalin baƙon abu ne a wajen shi, kamar yadda tunanin da ya yi mishi ɗaurin goro yake baƙo a wajen shi.
Da ƙyar ya kai wajen motar shi, dishi-dishi yake gani lokacin da ya buɗe ya shiga, bakomai na cikin tuƙi yake iya tunawa ba, ya taka motar ne ta baya ya fita daga gidan, yana jin yadda ya daki gefen gate ɗin da ko gama buɗewa maigadin bai yi ba, haka ya hau titi yana nufar hanyar gida, a ran shi yake karanto duk wani sunan Allah da ya zo mishi, cike da yabo saboda yadda yake jinjina ikon Allah, ya san ba hankalin shi ya kai shi gida ba.
Lokacin da ya yi parking ɗin motar cikin gidan lumshe idanuwan shi ya yi yana girgiza kan shi, ya sake buɗe su yana ganin duhun da yake son lulluɓe mishi su ruf, da ƙyar ya fito daga cikin motar yana wani irin mayar da numfashi. Dishi-dishi yake gani duk yadda yake ƙara ware idanuwan shi, ga jiri da yake ji yana ɗibar shi. Ganin kamar Khalid yake hangowa ya saka shi ƙara ware idanuwan shi sosai, amma sai yake ganin Khalid ɗin na rabe mishi gida wajen huɗu. Da hannu ya yi wa yaron alama da ya zo, yana sake runtse idanuwan shi, can sama-sama ya ji muryar Khalid ɗin na faɗin,
“Hamma…Hamma lafiyar ka kuwa?”
Ko kai Abdulƙadir ya kasa girgiza mishi, don iskar wajen ta sake mishi kadan, Khalid kuwa a karo na farko da ya kai hannu yana kama na Abdulƙadir ɗin da tsoro daban, don yadda yake kokawa da numfashin shi kamar mai asthma.
“Hamma…”
Khalid ya kira cike da tsoro, kafin Abdulƙadir ɗin ya lumshe idanuwan shi ya yi wani irin faɗuwa da ya saka Khalid sakin wani ihu daya fito daga ƙirjinshi da yake cike fal da tsoro.
“Hamma AbdulKadir!”
Ya faɗi yana tsugunnawa tare da girgiza Abdulƙadir ɗin da bai san a wacce duniya yake ba, da gudu Khalid ya tashi yana nufar ɓangaren Mami da shi ne ya fi kusa da shi, a falo yake kiran,
“Mami, Hamma…. Hamma Mami.”
Cikin tashin hankali Mami ta kama Khalid ɗin, zata ce a yaran gidan yana daga cikin wanda basu da hayaniya, baya shiga harkar kowa, daga gaisuwa sai ka yi da gaske za ka sake jin maganar shi, duk cikin yaran Mama ya fi kowa fita daban, bata taɓa ganin shi a hargitse ba, shi yasa lokaci ɗaya hankalin ta ya tashi.
“Wanne Hamman? Me ya faru Khalid?”
Ya kasa magana, da hannu kawai yake nuna mata alamar waje, bin bayan shi kawai ta yi, daga nesa ta hango Abdulƙadir ɗin, da gudu ta ƙarasa, cikin bayyanannen tashin hankali ta ce,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…. Abdulƙadir… Khalid kira Hajiya Safiyya…”
Juyawa yaron ya yi zuwa ɓangaren Hajja da ko mintina biyu ba’a cika ba ta ƙaraso wajen ta tsugunnawa ta kama Abdulƙadir ɗin ta ɗago shi jikinta tana kasa yarda yaronta ne a kwance kamar gawa.
“AbdulKadir…”
Ta kira tana ɗora hannunta a kan ƙirjin shi, bugun zuciyarshi a cikin tafin hannunta na nutsar da wasu ɓangarori a tare da ita da bata san a tashe suke ba sai lokacin, wani irin numfashi take saukewa, Mami da take tsaye cikin tashin hankali ita ma ta ce,
“Mu tafi asibiti…”
Kai Hajja take girgiza mata, su biyun duka tana da tabbacin ba za su iya ɗaga Abdulƙadir ɗin ba, balle su saka shi a motam
“Ki kira min Yassar.”
Hajja ta faɗi, ba don babu wasu manyan yaran gidan da in aka kira su za su zo ba, sai dai duk wani abu da ya shafi Abdulƙadir ɗin Yassar ne yake fara sani, wani lokaci yana ma rigan su sani, kuma shi ne mutum na farko da ya fara zuwa ma Hajja a kai. Har Mami ta bar wajen ta kuma sake dawowa Hajja na zaune riƙe da Abdulƙadir, zata kirga lokutan da ta ga ba shi da lafiya a tsawon rayuwar shi, rashin lafiya dai wadda zata kwantar da shi. Shi yasa yanzun bata ma san asalin abinda take ji ba, lokacin take gani baya mata sauri duk da ba agogo bane a gabanta, sai ta ga kamar ta yi awanni zaune a wajen kafin motar Yassar ta shigo cikin gidan.
Ko kasheta bai yi ba ya fito, kallo ɗaya za kai mishi kasan a hargitse yake, bai ko bi ta kan su Hajja ba ya tsugunna yana ɗago Abdulƙadir ɗin tare da girgiza shi.
“Abdulƙadir ba za kai min haka ba fa.”
Yassar yake faɗi muryar shi ɗauke da wani yanayi na karaya da tsantsar tashin hankali, baya tunanin ko su Hajja suna shiga tashin hankalin da yake shiga duk lokacin da aikin Abdulƙadir zai kai shi wani waje mai hatsari, yana da Yasir, amma a duniya ji yake idan ya rasa Abdulƙadir ya yi rashin da har nashi numfashin ya tsaya ba zai taɓa komawa dai-dai ba. Su Hajja na da wasu yaran, shi kam ji yake ba shi da wani ɗan uwan, shi yasa yanzun ma yake da tabbacin ba sa cikin tashin hankalin da yake ciki. A kafaɗar shi ya saɓa Abdulƙadir ɗin yana miƙewa da shi, bayan motar shi ya buɗe ya saka shi a ciki, ya rufe murfin.
Har ya zagaya ɓangaren direba ya shiga yana jin nauyin Abdulƙadir ɗin a tare da shi, bai bi ta kansu Hajja ba, bai ma kula da ta shigo motar ba, ja kawai ya yi yana nufar hanyar da zata kai shi wani asibitin kuɗi da yake ‘Yan Albasa na Rijiyar Lemo, don abokin shi yana aiki a wajen shi yasa har yasan da asibitin, tunda a cikin lungu yake. Gudu yake yana jin kamar ya bi ta kan motocin da suke gaban shi saboda saurin da yake yi, a haka suka ƙarasa asibitin, a kafaɗar shi ya sake ɗaukar Abdulƙadir ya shiga asibitin da gudu, wasu Nurses na hango su suka taho don su taimaka musu, ko ba mata bane Yassar baya jin zai miƙa musu Abdulƙadir, wani ɗaki suka nuna mishi, ya nufa da Abdulƙadir ya shimfiɗe shi kan gadon ɗakin, ana kiran likitan da ya shigo a rikice shima.
Ya gane Yassar ɗin, don yana zuwa wajen Dr. Isah sosai.
“Ka ɗan fita please…”
Ya ce mishi, yadda Yassar ya ɗaga ido ya kalle shi cikin yanayin da ke fassara ‘Wasa kake amma ko?’ yasa likitan mayar da hankalin shi kan Abdulƙadir da ko motsi baya yi har lokacin, bugun zuciyar Abdulƙadir ɗin na tabbatar mishi da a sume yake. Duk wata allura da akai mishi da ruwan da suka ɗaura mishi a kan idon Yassar aka yi shi. Da suka gama ma, bai bi ta kan su ba, likitan ma da ya yi mishi magana ya ga alamar hankalin shi ba a kan su yake ba, shi yasa ya fita ya samu su Hajja da ke tsaye a bakin ƙofar, ko takalma babu a Kjafarta, Hijab ɗin jikinta ma sallar Azahar zata yi da a haka zata fito, ita sukai wa tambayoyin da suke buƙata wajen buɗe wa Abdulƙadir ɗin kati, lokacin Dr. Isah ya fito wajen, Dr. Aminu na kallon shi da faɗin,
“Mahaifiyar Yassar ce abokin ka, sun kawo marar lafiya ne.”
Gaishe da Hajja, Dr. Isah ya yi yana mata kallon sani dama tunda ya zo wajen, amma shi yasan ba Mama bace ba, sai dai ko cikin matan Baban Yassar ɗin. Mai jiki yake tambayarta, yana cewa ta je kawai zai ƙarasa sauran, har kuɗin buɗe katin shi ya biya. Tukunna ya Kjarasa ɗakin da Abdulƙadir ɗin yake suna gaisawa da Yassar da ya ɗora da,
“Me ya same shi ne?”
Don sai lokacin ya ji ya samu natsuwar buƙatar hakan, Hajja likitan ya ɗan kalla da take zaune kan farar kujerar roba, tana share ƙwallar da ta ji ta tarar mata a gefen idanuwanta.
“Ka yi min magana Isah, dole zata sani tunda Maman shi ce.”
Kai Dr. Isah ya jinjina don ya yi magana da Dr. Aminu shi yasa ya ce,
“Jinin shine ya hau sosai, Allah ya rufa asiri da ya samu matsala, don Allah a guje ma ɗaga mishi hankali. Idan ya ƙara faɗuwa haka zai iya samun matsala sosai…”
Wani abu Yassar ya ji ya Kjulle a cikin shi.
“Hawan jini?”
Ya maimaita cike da shakku a muryar shi, yana ganin kai da Dr. Isah ya ɗaga mishi.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…oh Allahna.”
Cewar Yassar da yake jin wata sabuwar damuwa ta lulluɓe shi, ganin halin da ya shiga yasa Dr. Isah yi mishi sallama tare da yi wa Abdulƙadir ɗin fatan samun sauƙi. Yassar ɗin idanuwan shi ya tsayar kan Abdulƙadir da sai lokacin ya motsa yana saka Hajja faɗin,
“Abdulƙadir…”
Fuskar shi ya daƙuna ba tare da ya buɗe ido ba ya ce,
“Wahee…”
Kunne daga Hajja har Yassar ɗin suka kasa, can ƙasan maƙoshi Abdulƙadir yake ci gaba da sambatun da bai san yana yi ba ma.
“Waheedah ki yi haƙuri… Ba zan iya ba, Wallahi ba zan iya ba.”
Numfashi Hajja ta ja tana fitar da shi, idanuwanta na cikowa da hawayen tausayin ɗan nata, sosai maza suke tunanin suna da iko akan mace, saboda Musulunci da al’ada sun saka matan a ƙarƙashin su, sai dai da yawa cikin mazan sun ma abin juyayyar fahimta, Musulunci bai saka mace a ƙasan namiji saboda ta kasance mai rauni ba kawai, sai don wani ƙarfin zuciya da Allah ya dasa mata da ba kowa ne yake fahimta ba, mace na da juriyar ɗaukar laulayin ciki da ya fi kowanne yanayi wuyar sha’ani, tana da juriyar naƙuda da duk wani ƙashi da yake bayanta sai ya motsa, a lokaci ɗaya kuma tana da juriyar ɗaukar haƙuri da ƙaddarar wahalar ɗa namiji.
Mace za ta iya haƙurin shekaru da baƙin cikin ɗw namiji ba lallai ko a fuskarta a fahimci hakan ba, amma rana ɗaya da zata ware ta kwatanta rama kaɗan cikin wulaƙancin, hankalin ɗa namiji sai ya yi tashin da duk wani makusancin shi zai fahimci yana cikin yanayin damuwa, ƙarshe sai ya ba mutane tausayi saboda ya kasa jurewa har a juyar da al’amarin ana ganin ita macen ta yi haƙuri, cikin masu mata rashin adalcin har da ‘yan uwanta mata, su da ya kamata su fahimci halin da take ciki fiye da kowa. Shi yasa Hajja take ganin a duniya babu babban munafuncin da mata suke yaudarar kan su da shi sai faɗin,
‘Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne’
Don yanzun da take zaune a gaban Abdulƙadir take ƙara ƙaryata zancen, ba don bata ji zafin abinda ya yi wa Waheedah ba, ta kwatanta kanta da Waheedah ta kuma san ko kusa ba zata ɗauki abinda Waheedah ta ɗauka ba, idan bata mutu ba, auren nata zai mutu. Har ƙasan ranta kuma take jin da Waheedah ɗin Zahra ce da wahalar gaske idan bata je ta ɗauko ‘yarta ba. Amma ba Zahra bace, Waheedah ce, kuma a wannan gaɓar ɗanta take ji fiye da ita, ciwon ‘ya mace kan zama na ‘ya mace ne kawai idan akwai samun riba a cikin al’amarin, shi yasa munafunci ne kawai a faɗin hakan.
Waheedah take so ta yi haƙuri ta yafe ma Abdulƙadir, don kuwa ba zata jure ganin ɗanta a cikin wannan halin ba, hakan yasa ta faɗin,
“Yassar zaka ɗan zauna da shi in je in dawo?”
Kai Yassar ya jinjina mata, ya sanar a wajen aikin shi, babu inda zai iya zuwa in ba gani ya yi Abdulƙadir ɗin ya ji sauƙi ba. Tun farko abinda yake mishi gudu kenan, amma Abdulƙadir baya jin magana, taurin kan shi sai Allah, abinda zuciyar shi ta gaya mishi dai-dai ne shi yake aikatawa, bai taɓa zaton zai kwatanta ba Waheedah haƙuri ba sai yanzun, yana kuma jin son kai da rashin son gaskiyar da yake cikin hakan, bai damu bane kawai.
“Kabani mukullin motar ka.”
Babu musu Yassar ya ɗauka ya miƙa mata, karɓa Hajja ta yi tana miƙewa. Yassar ya bi ta da kallo ganin babu takalma a ƙafarta, bai ce komai ba, ya koma inda ta tashi ya zauna ya saka idanuwan shi a kan Abdulƙadir da duk motsin da zai yi sunan Waheedah ne a bakin shi, Yassar na jinjina wa ƙaddarar su, ya ɗauka ya san zafin so a kan Hauwa, yanzun Abdulƙadir da Waheedah ke nuna mishi bakomai suka sani ba a soyayya, don tasu kalarta daban ce.
*****
Rabonta da gidan Yassar tun lokacin da matar shi ta yi ɓari, da yake yarinyar ta sha wahala sosai. Bata kuma zata zata zo gidan ba tare da wani dalili da zai kasance ya shafi Yassar ɗin ko Hauwa ba, bata taɓa tunanin dalilin Abdulƙadir zai sa ta zo gidan Yassar ɗin ba, a ƙofar gida ta yi parking ɗin motar, tunda ta san in ta gama abinda take yi sake fita zata yi, bata ga wahalar sai ta shigo da motar ba. Tsakuwoyin da ta taka na tuna mata cewar babu takalma a kafarta, haka ta shiga cikin gidan, maigadin kan shi kallon ta yake don yana da tabbacin ba lafiya ba.
Har cikin gidan ta shiga, ta ci karo da Waheedah da take fita daga kitchen ɗin, ita ma Ikram zata wanke ma jiki ta sake mata pampers ta ji ruwan da sanyi, tausayi yarinyar ta bata shi yasa ta dafa, tana sake mata kuma bacci ta koma, shi ne ta fito ta kawo kettle ɗin ta ci karo da Hajja, sai da zuciyarta ta doka, musamman yanayin Hajja ɗin.
“Hajja…”
Waheedah ta kira cike da shakku da alamar tambaya, inda take Hajja ta ƙarasa.
“Alfarma na zo roƙa Waheedah.”
Hawaye Waheedah ta ji sun cika mata idanuwan da suke a kumbure suna zubowa a hankali.
“Nasan za ki ce na so kaina, za ki ce na duba buƙatar ɗana sama da taki, amma banda wani zaɓi… Wallahi yanzun ma yana asibiti, faɗuwa ya yi Waheedah.”
Hajja ta ƙarasa maganar muryarta na karyewa, wasu hawayen Waheedah ta ji sun ƙara zubo mata, muryarta a sarƙe cike da kuka ta ce,
“Hajja nima in naje asibitin gado za su bani.”
Kai Hajja ta jinjina mata.
“Na sani, ki yi haƙuri, don Allah ki yi haƙuri, ki duba yadda ya koma cikin sati ɗaya… Kina tunanin zai iya rabuwa da ke? Bakomai yake raunana Abdulƙadir ba, ban ma taɓa ganin abinda ya saka shi shiga yanayi haka ba… Shi yasa na zo in baki haƙuri, koma menene ya yi miki don Allah ki yi haƙuri.”
Hannu Waheedah tasa tana goge fuskarta, amma wasu hawayen ke zuba, ita kam haƙurin ne bata so su bata, saboda zuciyarta har ta fara karyewa, musamman da Hajja ta dafa kafaɗarta fuskarta cike da roƙo tana faɗin,
“Ki yafe mishi dan girman Allah, ki duba roƙo na Waheedah…”
Kuka Waheedah take yi, hakan yasa Hajja ta riƙe ta a jikinta, ƙaddarar yaran na tsaya mata, ita kanta Waheedah ɗin a idanuwanta zaka ga rauni, Abdulƙadir ɗin ne ya taɓata sosai, amma rabuwa da shi ne ƙarshen abinda take buƙata. Cikin kuka ta ce,
“Hajja bansan ya zanyi ba… Ban sani ba ni kam.”
Riƙeta Hajja ta yi sosai.
“Haƙuri za ki yi, ki yi haƙuri… In ya yi abinda ya nuna miki ke ɗin baki da muhimmanci halin da ya shiga yanzun ya isa ya karya shi… Ke ɗin ce rayuwar shi Wallahi…”
Kai Waheedah ta girgiza tana ƙin yarda da kalaman Hajja, wani kishi na ban mamaki na turnuƙe zuciyarta, da ita ce rayuwar shi da bai haɗa ta kishi da Nuriyya ba, da ita ce rayuwar shi da bai ci mutuncinta ya auri aminiyarta ba. Ɗagowa ta yi daga jikin Hajja tana saka hannuwanta duka ta share hawayenta.
“Waheedah…”
Hajja ta faɗi tana rasa da kalaman da zata yi amfani da su don rikici take gani shimfiɗe a idanuwan Waheedah ɗin, da gaskiyar mutane ka guji ɓacin ran mai haƙuri.
“Jinin shi ya hau.”
Hajja ta ce tana saka Waheedah rausayar da kai, cikin sanyin murya ta ce,
“Nima hawan jinin nake fama da shi Hajja.”
Hawaye na zubar mata, duk idan ta yi zaton hawayenta sun ƙare sai wani abin ya sake faruwa da za su ci gaba da zuba kamar an buɗe fanfo, numfashi Hajja ta ja tana fitar da shi kafin ta ce,
“Shikenan Waheedah, Allah ya zaɓa muku abin da ya fi alkhairi.”
Ta juya tana ficewa daga gidan. Ɗaki Waheedah ta koma ta ɗauki wayarta, kuka take har bata ganin abinda ke rubuce a screen ɗin wayar sosai, sai da ta goge fuskarta tukunna ta lalubo lambar Abba ta kira, bugun farko ya ɗaga da faɗin,
“Waheedah.”
Wani irin kuka ta rushe da shi da yasa Abba cewa,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… Waheedah me ya faru? Menene? Me akai miki?”
Ta ɗayan ɓangaren, kana jin tashin hankalin da ke cikin muryar shi, numfashi take fitarwa kamar zata shiɗe saboda kukan da take yi.
“Ab….Abba…”
Ta iya faɗi da ƙyar tana ɗorawa da,
“Kowa na ta bani haƙuri… Abba har Hajja haƙuri take bani, zuciyata ciwo take min Wallahi… Da na tuna zuciyata ciwo take min… Ab…Abba ban san ya zanyi ba.”
Tanajin ya sauke numfashi, cikin taushin murya mai cike da lallashi ya ce,
“Kiyi duk abinda zuciyarki zata nutsu da shi, karki bari haƙurin da suke baki ya sa ki yin zaɓin da za ki cutu, kar kuma ki bari fushinki yasa kiyi zaɓin da ba za ki yi da na sani.”
Kai Waheedah take jinjinawa tana goge fuskarta da bayan hannunta.
“Kina ji na?”
Abba ya faɗi yana sa ta sake jinjina mishi kai.
“Zan zo in duba ki anjima, ki samu ruwa ki sha, ki daina kuka kin ji Waheedah? Komai zai yi dai-dai.”
Kai ta jinjina tana ƙara goge fuskarta, bata ce komai ba ta sauke wayar daga kunnenta, bata samu damar sanin mahaifinta ba, amma Abba ya bata ƙauna da kusancin da ko mahaifinta jinin shi dake yawo a jikinta ne kawai zai nunawa Abba. Abu biyu ta sani, zuciyarta na mata ciwo na gaske na biyun a fili ta faɗe shi.
“Kin yi kaɗan in bar miki mijina Nuriyya… Na bar miki abubuwa da yawa a rayuwata, ban da shi, ban da Sadaukina…”
Ta goge hawayen da suka zubo daga zuciyarta tana jin wani irin ƙarfin gwiwa da bata taɓa jin irin shi ba.