Tun da ya shiga gida ɓangaren Waheedah ya wuce, ɗakin baccin su ya shiga, ya zauna a gefen gadon. Kan shi sarawa yake tunda ya fito daga asibitin, bai san ta inda zai fara tarar matsalar da Waheedah take son janyowa rayuwar su ba, don bai san me ya shiga kanta ba, ƙafafuwan shi ya janyo da nufin ɗora su akan gadon ya ga takalman shi da bai kwance ba.
"Ba zan cire ba!"
Ya faɗa a fili, da Waheedah yake, don ita ce ba ta so yana shigo mata da takalma har ɗaki, abinda take so shi take. . .