Da wani irin sanyin gwiwa ta ƙarasa ɓangarenta, watakila har yanzun Waheedah bata jin daɗi ne, in baka da lafiya dama komai fita ranka yake shi yasa. Ko kuma ta ji haushi ne din bata yu mata ya jiki ba, ita kuma sai lokacin tunanin ya zo mata. A haka ta ƙarasa ɓangarenta, ta samu Abdulƙadir kan doguwar kujera a zaune. Ƙarasawa ta yi ta zauna a gefen shi, yana jin shigowarta, ran shi a ɓace yake, ga yunwa da yake ji kuma. Bai san me yasa sai yanzun yake jin haushinta ba, da na kuɗin shi da ta kashe, da kuma na yau da ko kaɗan bata neme shi ba ballantana ta san ba shi da lafiya har ya yini a asibiti.
Har yanzun ya ga alama bata san waye shi ba, ko don rashin Waheedah a kusa da shi ne yasa yake ganin komai ma ba shi da muhimmanci, yanzun da yasan ba zata barshi ba, ya samu natsuwar da zai fuskanci sauran matsalolin shi. Baya son kashe kuɗin da ba shi da dalili, komai nashi a kan tsari yake, sosai yakan yi tunanin abinda take yi da kuɗi, kuma ba a ɗan zaman sun nan ya kula da idan ya ajiye kuɗi a wallet tana kwashewa ba, ko ya zo yin kwana biyu, in dai zai mata nata kwana ɗayan sai ta ɗibar mishi kudi.
Idanuwa ya ɗauka ya saka mata ya ga gudun ruwanta, yanzun ne ta gama kawo mishi wuya.
“Mu me za mu ci?”
Nuriyya ta buƙata muryarta a sanyaye, don sosai ta saka ranta a abinda Waheedah ɗin ta girka. Sai take jin da wahala ta iya cin taliyar da ta dafa.
“Ke ba mace bace? Baki dafa naki ba ne?”
Abdulƙadir ɗin ya buƙata yana tsareta da idanuwa, duk da maganganun shi sun mata zafi, murmushi ta ɗan yi.
“Na dafa mana taliya.”
Bai ce mata komai ba, ganin hakan yasa ta miƙewa ta samu plate ta zubo musu taliyar, har miyar ta haɗe. Tare suka ci, Abdulƙadir na rasa ranshi da yake a ɓace ne, ko taliya ce da bai cika so ba, ko kuma girkin ne ba shi da gabas, don ko gishiri-gishiri na miyar ma bai ji ba, sai wani ɗaci-ɗaci. Turawa kawai ya yi, ita kanta Nuriyya da tana da wani zaɓi sam ba zata ci taliyar nan ba, sa wa ranta cin girkin Waheedah da ta yi yasa taliyar ƙara fitar mata daga rai. Tana kai kwanon kitchen ɗakin baccinta ta wuce, ta ɗauki wayar ta. Tallar littafin Hauwa A Usman Jiddarh ta gani ‘Na Saki Reshe, tana tunanin Sarƙaƙiyar da take ciki na yadda za’a yi jarumin ya kasance gagarumin ɗan fashi.
Ba’a kai da fara shi ba, hakan yasa ta jan dan ƙaramin tsaki, dama jiya littafin Faɗime na Ɓingel ta maimaita don sosai take jin daɗin littafin, soyayyar da aka shimfiɗa ciki na tuna mata dalilin da yasa ta auri Abdulƙadir tun da farko, amma yanzun ta fara gajiya don taci karo da abinda ba shi take tsammani ba. Ganin babu abinda zata karanta yasa ta ɗauko system ɗinta, dama tana lallaɓa fina-finan da take da su ne, tana buɗewa sai ga Abdulƙadir ya shigo ɗakin, ƙarasawa ya yi kan gadon ya hau ya saka hannu ya ja system ɗin.
“Masoyi…”
Ta faɗi tana kallon shi, bai mata magana ba yasa hannu yana kashe system ɗin ya kuma ɗauke ta daga kan gadon gaba ɗaya ya ɗora kan drawer ɗin da take gefen shi ya juyo yana tsura mata ƙananun idanuwan shi da suka sa ta yin shiru.
“Ki kashe mana wuta.”
Ya fadi, don makunnin ba’a yi shi a kusa da gado ba, miƙewa Nuriyya ta yi tana zuwa ta kashe wutar ta dawo ta kwanta ita ma, sai dai ga mamakinta, juya mata baya Abdulƙadir ya yi da alamun bacci zai yi. Wani abu ta ji ya yi mata tsaye a maƙoshi, bata son ya sauke mata faɗan shi, shi yasa ta haƙura bata ɗauki system ɗin ba, wayarta ta ci gaba da dannawa, tana ganin yadda status ɗin kowa ya gauraye da maganar ganin wata.
“An ga wata.”
Ta faɗi, Abdulƙadir ya ji ta, surutun ne ba zai yi da ita ba yau, asalima niyyar azumi ya ɗaura a zuciyar shi, sake gyara kwanciya ya yi yana fuskantrta, wayar da take hannunta ya fisge yana sakata a key ya ajiye a tsakiyarsu tare da faɗin,
“Ki kwanta Nuriyya.”
Muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce,
“Bana jin bacci wallahi, baka san baccin da na sha ba yau da ka fita.”
Shi yasa bata neme shi ba, baccinta ya fi jin inda yake muhimmanci. Abdulƙadir ya faɗi a ran shi, zuciyar shi na ƙara jagulewa.
“Bazan sake magana ba…”
Cewar Abdulƙadir ɗin cikin iko da gadarar shi da take ɓata mata rai. Gyara kwanciya ta yi, ranta in yayi dubu a bace yake, batasan iya lokacin da ta ɗauka a haka ba har bacci ya ɗauketa itama. Su dukkan su baccin suke, shi Abdulƙadir baccin da ya kwana biyu bai yi ba ne ba, ita kuma Nuriyya baccin da bata yi da wuri bane, ko ma da wurin ta kwanta shi yake tashinta sallar asuba, in ba haka ba sai dai ta makara, don in baya gari makara take yi. Hakan yasa ko kiran sallar farko basu ji ba, suna ta bacci har ƙarfe shida saura.
Haske Abdulƙadir ya gani cikin idanuwan shi, kasancewar window ɗin ɗakin baccin Nuriyya ɗin daga waje yake, duk da wanda yake waje ba zai iya hango su ba, su da suke ciki za su iya hango shi, haka gilashin window ɗin yake. Amma bai hana hasken da yake nuna alamar gari ya waye shigowa ba. Murza idanuwanshi ya yi da hannu yana ƙara runtsa su, kafin ya buɗe su cikin tashin hankali yana miƙewa zaune babu shiri, hasken da ya gani cikin ɗakin bai saka shi ya yarda ba, sai da ya ɗauki wayar Nuriyya da take gefen shi ya danna, yana ganin shida saura minti goma.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”
Abdulƙadir ya furta yana kai hannu ya jijjiga Nuriyya.
“Ki tashi mun makara.”
Ya faɗi yana hasaso kalar yunwar da zai ji a yinin yau, don shi azumi bai yi Sahur ba rayuwar shi na cikin tashin hankali.
“Nuriyya…”
Abdulƙadir ya kira yana bubbugata, idanuwanta ta buɗe da ƙyar tana yin miƙa.
“Dalla ki tashi ƙarfe shida fa.”
Wata irin miƙewa Nuriyya ta yi tana kallon shi.
“Ƙarfe shida? Shida fa? Ba mu yi Sahur ba, baka tashe ni ba.”
Wani irin kallo Abdulƙadir ya watsa mata yana jan tsaki.
“Ban tashe ki ba? Ba ke ya kamata ki tashi ba, ki dafa mana abinda za mu ci, nine zan tashe ki?”
Shagwaɓe fuska ta yi, tanajin idanuwanta na cika da hawayen baƙin ciki, duk yadda suka yi zaman rashin mutunci da Anas yana tashinta lokacin azumi, tunda ya ga ranar da bata yi Sahoor ba ta zama abin tausayi, a kwance ta wuni shame-shame. Shi ne Abdulƙadir zai sauke mata faɗa kamar akwai inda aka rubuta cewar ita ya kamata ta tashe shi dole dole.
“Kaima idan ka tashe ni ai ba wani abu bane Masoyi.”
Ta faɗi wani abu na tokare mata wuya, ƙanƙance idanuwan shi Abdulƙadir ya yi.
“Magana za ki faɗa min?”
Ya buƙata cike da neman ta furta wani abu ya sauke mata faɗan shi, kai ta girgiza a hankali, hawayenta na ƙara taruwa, ƙwafa ya yi yana sauka daga kan gadon ya wuce banɗaki, abin na haɗe mishi waje ɗaya, ga baƙin cikin rashin Sahur ga Asuba daya rasa, ga Nuriyya da zata yi mishi kukan rashin dalili. Sai da ya ɗan watsa ruwa a gaggauce tukunna yayi alwala ya fito, ba ma shida kaya a ɗakin nata, dole sai ya je ɓangaren Waheedah. Nuriyya ya kalla da bata ko nuna alamar tashi ba.
“Ke ba za ki yi sallah ba?”
Ƙafafuwanta ta sauko daga kan gadon.
“Ba za ki yi wanki ba kuma? Banɗakin ki baya shigar miki ido, me yasa bakya wankewa ne? Da ƙyar na yi wanka a ciki.”
Abdulƙadir ya ƙarasa yana wucewa ta fice daga ɗakin. Wannan karon hawayenta ta ji sun zubo. Wani malolon baƙin ciki na tokare mata ƙirji, a haka ta ɗauro alwala ta dawo ta gabatar da sallar asuba. Tana idarwa ta koma banɗakin, ta sa tsintsiyar da take a ciki ta wanke shi sama-sama, ko omo bata saka ba. Ba zata fara ƙarar da karfinta a banɗaki tun yanzun ba, don wani sharri ma, cikinta har ya fara murɗawa da alamar yunwa. Wani zaninta ta ɗauka ta haɗa duka kayan wankin da suke cikin bandakin ta kulle su, ta dawo ta cire zanin gadonta don ya yi dauɗa sosai shi ma ta kai banɗaki ta ajiye akan wancan kayan wankin, zata fitar da su tunda Waheedah ta dawo.
*****
Abdulƙadir kuwa ɗakin Waheedah ya wuce yana turawa wani ƙamshi ya cika mishi hanci, ɗakin a gyare yake tsaf. Ta sake zanin gado, ko ina tsaf tsaf, tana zaune kan gado ta miƙe ƙafafuwanta, ta goya Ikram ta gaba tana kwance akan ƙirjinta, hannunta ɗaya rike da Qur’ani. Ba zai ce ga kalar ɗinkin jikinta ta yadda take zaune ba, amma atamfa ce, ta ɗaura daankwalin atamfar, fuskarta fayau babu kwalliya. Amma ta mishi kyau har zuciyar shi dokawa take. Sai da ta idar da ayar da take kan karantawa, tukunna ta ɗago idanuwa ta sauke su kan Abdulƙadir ɗin.
“Ina kwana.”
Ta furta cikin sanyin muryarta tana ɗan mishi murmushin da ya ji zuciyar shi ta ɗan nutsu.
“Wahee… Ya kuka tashi?”
Ɗan langaɓar da kai ta yi.
“Alhamdulillah…”
Idanuwan shi Abdulƙadir ya ƙanƙance mata.
“Shi ne baki tashe mu ba? Mun makara, yanzun fa muka tashi, ko sallah ban yi ba.”
Ware mishi idanuwa Waheedah ta yi, ita ba Sahur take yi ba, sai dai in ta tashi ta yi brush ta sha ruwa, in tana da kankana ta ɗan sha don samun ladan Sahur ɗin, ko ta ci dabino wasu lokuttan, yau ɗin ma hakan ta yi. Zata yi ƙarya idan ta ce bata yi tunanin duba ko Abdulƙadir ɗin ya tashi ba, tunda ta san yadda yake wahala idan bai yi sahur ba, kawai dai ta tsinci kanta da share koma meye yake son yin tasiri a kanta.
“Na ɗauka kun tashi, kasan ni ba Sahur nake ba.”
Kai kawai Abdulƙadir ɗin ya iya jinjina mata, ba sai ta faɗa mishi ba, ya san fushin da take yi da shi ne, ko ya tashi Waheedah zata ƙara kiran wayar shi ta tabbatar da hakan, wahala take son ya sha, kuma zai shata ɗin yau ya sani. Kaya ya wuce ya ɗauka, yana ganin yadda Waheedah bata ce ya bari ta ɗauko mishi ba.
“Ka ɗauki na kwana biyu ka wuce da su Sadauki, in ka ɗauki kaya ka je da su ɓangarenta ka cire a can ka bar mata acan, karka dawo min da su nan don Allah.”
Ta ƙarashe maganar da roƙon shi kamar yana da wani zaɓi.
“Ki zo ki dauko min to.”
Abdulƙadir ya ce kamar ƙaramin yaro, Qur’anin ta ajiye tana tallabe Ikram ta sauko daga kan gado, kaya ta ɗauko mishi, riguna da gajerun wanduna, har da na ciki kala bibbiyu, tunda shi ba manyan kaya yake sakawa ba, yana da su, in ta yi magana kan ya saka bakinta ne zai yi tsini, ba zai sa ba, baya son manyan kaya. Hannun shi ta ɗago tana saka kayan a ciki, ta yi mishi murmushi har haƙoranta suka fito, idanuwa Abdulƙadir ya ƙanƙance mata.
“Ko turare baki fesa min ba.”
Kallon shi ta yi.
“Bafa kayi sallah ba, lokaci na wucewa kuma.”
Wani irin shagwabe mata fuska ya yi, ta wuce ta koma ta yi zamanta, ta sake ɗaukar Qur’ani ta ci gaba da karantawa a bayyane da muryar da ta tsaya dai-dai kunnuwanta. Da kanshi yaje wajen mudubinta yana ɗaukar turaruka ya feshe kayan dashi, ko inda yake ma Waheedah bata kalla ba, balle ya yi tunanin zata yi mishi magana. Har ya gama ya fice daga ɗakin, ta sauke numfashi tana cigaba da karatunta. Ko da ta idar, bata fita ba sai wajen ƙarfe goma, da Ikram ta fita kar ta ajiyeta ta farka taita kuka dn wanki zata yi kafin su ɗauke wutar su.
Sai da ta fara share ɗakin wankin tukunna ta koma ɗakinta ta ɗauko jakar da suka dawo da ita da. Tana cikin firfito da kayyakin wankin sai ganin Nuriyya ta yi kamar mikiya, ta diro ɗakin wankin, da ƙaton zanin gado da alamar kayan wanki ne a ciki.
“Lafiya?”
Waheedah ta tambaya tana tsare Nuriyya da idanuwa cikin yanayin da yasa Nuriyyar jin duk ta daburce, Waheedah ɗin na mata wani irin kwarjini na ban mamaki, don ko babu fara’a a fuskarta bata haɗe girar sama da ta ƙasa haka.
“Ina kwana”
Nuriyya ta faɗi saboda ta rasa abinda zata ce kafin ta yi saurin ɗorawa da,
“Ya jiki?”
Sai da Waheedah ta kalleta na wasu daƙiƙa, tana sata jin duk ta tsargu, kafin ta amsa da,
“Lafiya.”
Ta ci gaba da hidimarta, tsaye Nuriyya ta yi mamaki duk ya gama cikata. Kayan wankin ta ajiye tana juyawa ta fice daga ɗakin. Wankinta Waheedah ta yi don ba shi da yawa, ta kwashe ta zuba a wata babbar roba, Ikram ta zo ta kwantar akan doguwar kujera tana saka pillow ɗin ta tareta, don yarinyar ta cika juye-juye, karta faɗo. Tukunna ta koma ta ɗauki robar ta fita bayan gidan inda igiyoyin shanya suke, ta shanya kayan ta dawo. Wanda Nuriyya ta ajiye ta kwashe tanajin nauyin shi, ɓangaren Nuriyyan da tunda ta shigo gidan zata ƙirga lokacin da ƙafafuwanta suka taka ta nufa, a tsakiyar falo ta ajiye mata kayan tana juyawa, ɗakin wankinta ta janyo ta saka mukulli ta rufe ta ɗauki Ikram suka shige ciki.
Nuriyya kuwa fitowa ta yi don ta kawo wanu hijab da ta gani da datti, ta ci karo da jibgin kaya ajiye a falo. Tsaye ta yi turus tana kallon kayan cike da mamaki, ba rashin lafiya bace take damun Waheedah, wani hali na banza ne ta ɗauka da ba nata ba, don bata santa da shi ba. Ranta a bala’in ɓace ta ɗibi kayan wankin tana komawa da su ciki ta ajiye a tsakiyar banɗakin, itama tana da injin wankin ai, bawai bata da shi bane ba, kitchen ta koma ta ɗauko ledar omo ta dawo tana kallon Abdulƙadir da yake a kwance yana danna waya.
“Masoyi…”
Ta kira shi muryarta na fitowa a karye, hakan yasa shi ɗago idanuwanshi ya kalle ta.
“Ya ake amfanin da abin nan?”
Daƙuna mata fuskar shi ya yi.
“Wanne abu?”
Ya tambaya, yana sa kunya ta rufeta, don ta tsani ace duk irin wannan abubuwan na gayu ita bata iya ba, muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce,
“Na wanki.”
Miƙewa zaune Abdulƙadir ya yi yana kallonta cike da rashin fahimta, hakan ya sa ta sake faɗin,
“Injin wankin, ya ake amfani da shi?”
Har lokacin kallon ta Abdulƙadir yake yi.
“Da ina kika je da kayan? Ba na ga kin fita da su ba.”
Maganar shi yasa ranta ƙara ɓaci.
“Ɓangaren Waheedah…”
Ta amsa a taƙaice tana ƙin mishi bayani, wannan karon fuskar shi ce ɗauke da tsantsar mamaki.
“Me kike nufi da ɓangaren Waheedah?”
Kanta ta saddar ƙasa ganin irin kallon da Abdulƙadir ɗin yake mata.
“Ita kika kai ta yi miki wankin saboda baki da hankali?”
Abdulƙadir yake faɗi yana jin ranshi na ƙara bacie fiye da yadda yake a ɓace, don bai taɓa ganin irin wannan rashin hankalin ba, shi yasa ya siya mata nata injin wankin itama, yadda ma ba sai ta je ɓangaren Waheedah dine ba gaba ɗaya akan maganar wanki. Yana ɗaukar abubuwa da yawa a rayuwar shi amma baya son raini.
“Ajiyeta kika yi da za ki kai mata wanki Nuriyya?”
Kanta ta ƙara saddarwa, hawaye na tarar mata cikin idanuwa a karo na biyu daga wayewar garin yau, ko kaɗan bata saba a sakata a gaba ana mata faɗa ba, ko a gida dama Baba ne yake mata faɗa in ta yi wani abin, to sai ta yi abu goma, Mama bata faɗa mishi ba. Ranta ɓaci yake yi duk idan akai mata faɗa, balle kuma yanzun da take jin ta yi girman da duk wannan abubuwan bai kamata ana mata su ba, ranta a ɓace ta ce,
“Karka ce haka…”
Tunda shi ba zama yake gidan ba, kuma Waheedah ɗin na wanke mata da, bai sani bane ba.
“Dama can nake kaiwa, yau ne kawai ta dawo da shi.”
Sosai Abdulƙadir yake kallonta.
“Wankin kike ɗauka daga nan, sai ki kai ɓangarenta, sai ta wanke miki?”
Yayi tambayar yana saka Nuriyya jin kamar ta yi wani laifi ne, wata ‘yar dariya Abdulƙadir ya yi da ko kaɗan bata da alaƙa da nishaɗi kafin ya sauko daga kan gado yana ficewa daga ɗakin ya doko ƙofar kamar zai karyata. Ɓangaren Waheedah ya nufa ko sallama bai yi ba yadda ya tura ɗakin yasa ta buɗe idanuwanta daga baccin daya soma fisgarta.
“Wanki kike ma Nuriyya? Akan wanne dalili?”
Ya buƙata yana jin yadda ranshi ya kai ƙololuwa wajen ɓaci.
“Baka taɓa kula ba sai yanzun?”
Waheedah ta buƙata a sanyaye, don yana gidan Nuriyya take kwaso wankin ta kawo mata bangarenta, shi yasa ta ɗauka ya sani.
“Karki amsa min tambaya da tambaya, karki ƙara bata min rai Wallahi.”
Yadda ya yi maganar da yanayin fuskar shi yasa ta sauke idanuwanta daga cikin nashi, akwai yanayin da ta san ba zata fara gwada haƙurin shi a cikin su ba, yanzun na ɗaya daga cikin su.
“Ko ban siya mata engine wanki ba, akan wanne dalili za ki yi mata wanki? Ajiyeki ta yi?”
Numfashi Waheedah ta sauke.
“Ina azumi ni kam”
Ƙanƙance mata idanuwa ya yi.
“Ni na ce miki bana azumin ne?”
Kai ta girgiza mishi a hankali, tana jin murmushin da yake shirin ƙwace mata, tayie kewar rikicin shi.
“Allah ya baka haƙuri Sadauki, yanzun ai zata wanke abinta ka ga, kuma menene dan na haɗa na wanke?”
Kallon da ya yi mata yasa ta yin murmushi.
“Yi haƙuri”
Tsaki kawai Abdulƙadir ya ja yana ficewa daga ɗakin, su duka biyun haukata shi suke son yi ya ga alama. Akwai halayen Nuriyya da yawa da yake kula da su yanzun da baya ganin su da, ɗakin ya koma yana samunta inda ya barta, banɗakin ya wuce ranshi a ɓace har lokacin, tsayen da Nuriyya ta ga ya yi ne yasa ta bin shi, nuna mata yadda zata yi amfani da injin wankin ya yi, ba ma komai ta gane ba saboda a masife yake nuna mata komai, yana gamawa ya fice daga ɗakin, falo ya koma ya kwanta kan doguwar kujera yana huci shi kaɗai. Ga hanjin shi da ya tattaru ya ƙulle waje ɗaya. Bacci yake son yi, rana na ƙarawa kuma, yana so ya ɗan shiga kasuwa, don ba zai ba Nuriyya kuɗin shi ba. Komawa ɗakin ya yi ya ɗauko wallet da mukullin mota sai wayar shi ya fita daga gidan.
*****
Da ƙyar ya dawo gida, har wani haske-haske yake gani yana gilmawa ta cikin idanuwan shi saboda yunwa. Ga maƙoshin shi kamar sahara, a bushe da ƙishi, a hanya ya tsaya ya yi Azahar, kayan ma da ƙyar ya fito da su daga mota, daga dankali sai doya da cefane ya siyo, sai kuma ƙwai da da ƙyar ya samo shi. Ga kasuwar a shaƙare, darajar watan azumi shi yasa duk wanda ya take mishi ƙafa in ya bashi haƙuri ko amsa baya samu, amma da mutanen da zai mara Allah kaɗai ya san yawansu, duk da haka sai da ya watsa ma wani me Napep zagi, bai ko juyo ba illa ƙara gudun Napep ɗin ganin wandon sojoji a jikin Abdulƙadir ɗin.
Yana shiga ya wuce ɓangaren Nuriyya ya ajiye kayayyakin a ɓangarenta, tukunna ya koma mota ya ɗauko apple ɗin da ya gani yana shiga ɗakin Nuriyya, a falo ya sameta zaune, ta kwantar da Ikram a kujera tana mata wasa, sallamar shi ta sa ta amsa tana ɗago da kanta, fuskar shi ta kalla ta ga gajiyar da take tattare da shi, ledar ya miƙa mata ta sa hannu tana faɗin,
“Sannu da gajiya…”
Kai Abdulƙadir ya jinjina mata, yana kallonta, jira yake ta ce mishi zata haɗa mishi ruwan wanka ya watsa ruwa, ko bata ce haka ba, ta faɗa mishi wani abin, ta nuna mishi damuwarta kamar yadda ta saba, amma ta ajiye ledar apple ɗin tana mayar da hankalinta kan Ikram.
“Wahee na gaji sosai, kuma yau ana rana.”
Hancinta ta haɗa da na Ikram ɗin da take wangale bakinta da babu haƙora, suna saka zuciyar shi cika fam da ƙaunar su, hankalinta na kan Ikram ɗin ta ce,
“Sannu, akwai rana kam, ni da nake cikin gida ma ina jin zafi.”
Kallonta ya yi, muryar shi da wani irin sanyi ya ce,
“Na san na yi laifi, na sani Wahee, ki horani ta kowanne fanni zan ɗauka. Amma wannan rashin kulawar banda ita, zuciyata ba zata ɗauka ba Wallahi.”
Yadda ya ƙarasa maganar yasa ta yin shiru bata ce komai ba, tana jin shi ya juya ya fice daga ɗakin. Numfashi ta sauke me nauyi, sai ta ji wani irin kaɗaici ya danneta, kewar Fajr take ji, da yana nan da ya dameta da surutun shi, addu’a take a ƙasan ranta, Allah yasa AbdulKadir ɗin ya je ya taho da shi, tunda ita ba zata iya kira ta ce a dawo da shi ba. Tana nan zaune aka kira sallah, ta tashi ta ɗauki Ikram suka koma ɗaki.
Abdulƙadir yana shiga ɗakin Nuriyya a kwance ya sameta kamar gawa, har sai da ta tsorata shi ganin ko motsin kirki bata yi.
“Nuriyya…”
Ya kira, tana ɗago kanta da ƙyar ta kalle shi, dariya ya ji ta kubce mishi.
“Duk azumin ne?”
Ya tambaya yana zama gefen gadon, ta matsa mishi can, duniyar take ji ta haɗe mata waje ɗaya, ga baƙar yunwa da take addabarta, ga wankin da ta yi akwai kayan da suke zuba, duk ta haɗe su da masu haske. Hatta zanin gadonta ya yi kampala-kampala, zaman gidan take jin ya gundureta, ga kuma faɗan Abdulƙadir ɗin. Zama ta yi tana tunanin rayuwar da ta tsara wa kanta kafin shigowa gidan shi, da wannan da take yi yanzun. Ga kuma Waheedah ta ƙara sawa komai ya kwance mata, mamaki take yi tana ƙarawa, babu kalar tunanin da bata yi ba, ko wasu ƙawaye Waheedah ta yi masu mugun hali da suka bata shawarar canza mata haka.
“Wallahi ba ka ji cikina ba, kamar an min sata.”
Murmushi Abdulƙadir ya yi, zuciyar shi yake ji ta yi nauyi a ƙirjin shi. Kan gadon sosai ya hau ya kwanta, idanuwan shi ya rufe yana jin gajiya sosai. Bacci ya yi har la’asar don sai da Nuriyya ta tashe shi tukunna ya yi alwala ya fita masallaci. Sa’adda ya dawo sun kawo wuta, ya yi zaman shi a falo yana kallon namun daji a tashar discovery. Har wajen biyar kafin ya ga Nuriyya ya fito daga ɗakin tana bin bango, shi ma yunwar yake ji. Kitchen ta shiga tana rasa abinda zata fara yi, bata ma san abinda zata dafa ba, tunda bata ga alamar Waheedah zata yi girki da su ba. Ita yau ma ba zata je ɓangarenta ba, alƙawari ta yi wa kanta.
Zama tayi ta yanki doya ta fere tana samu ta ɗora, tunda ta ga kwai, gara ta soya musu doya da ƙwai kawai. Buɗe fridge ta yi tagae babu lemu ko ɗaya sai ruwa, falo tazo tana samun Abdulƙadir ɗin ta ce,
“Masoyi bamu da abin sha fa a ɗakin nan, ko fanta ka siyo mana.”
Yana riƙe da remote, hankalin shi na kan TV ya amsa ta da,
“Banda kuɗi.”
Yana cigaba da kallon shi, abinda ya zame mishi dole ya yi shi zai yi, tunda ta yi mishi ɓarnar kuɗi zata gane kuskurenta. Tsaye ta yi tana kallon shi cike da mamakin faɗin ba shi da kuɗin da ya yi, ranta a jagule take jin shi.
“Me za mu yi buɗa baki da shi to?”
Har lokacin bai kalli inda take ba ya amsa da,
“Nima ban sani ba.”
Yana ci gaba da kallon shi. Kitchen Nuriyya ta koma, ta cika kamar zata fashe, don ta kashe dubu arba’in shi yasa yake mata wannan wulaƙancin, wayarta ta ɗauka tana duba account ɗinta ta ga babu abin arziƙi a ciki. Kuɗin hannunta kuma bai wuce dubu huɗu ba, shi yasa take ƙara jin kamar bata da lafiya, don ta tsani ta ji babu kuɗin kirki a jikinta, in ba zai bata ba ta san zai ajiye, zata kuma ɗiba idan ya ajiye. Don tana buƙatar abubuwa na ciye-ciye. Doyar ta sauke da tafasa ɗaya ta yi ta tace ta. Ko gishiri ta manta ana zubawa balle ɗan sikari tunda sabuwar doya ce, ko ba sabuwa ba ma taste ɗin na yin daɗi na daban in ka ɗan saka sikari.
Ruwa ta maka mata, ta ɗauki cefanen ta juye wajen wanke wanke ta gyara shi, jiri ma take ji saboda yunwa. Markaɗawa ta yi duka ta juye shi a tukunya. Tana da ɗanyar kaza a fridge ta ɗaukota, ba zata iya wata wahala ba, itama ruwa ta saka mata ta wanketa, da ƙanƙara a jiki har lokacin ta ɗauketa tana zundumawa cikin kayan miyar tunda a yayyanke take, ƙanƙara ce ta yi, zata narke in ta ji wuta, ta zuba ruwa kofi biyu, duk su hadu su tafaso tare sai ta yi miyar da yawa ta saka a fridge, ɗiba kawai zata dinga yi. Mai ta ɗauko ta bulbula a kai, ta ɓare maggi ta zuba ta rufe tana komawa ɗaki ta kwanta.
Mintina talatin ta ba miyar ta fito tana ganin ruwan ya tsane, jujjuyawa tayi ta sauketa tana kashe gas ɗin. Doyar ta yayyanka ganin yamma ta yi sosai, ta kaɗa kwai ta zuba maggi, ta ɗora mai. ‘Yar albasa ta ɗauka ta yanka cikin ƙwan tana tuna cewar bata zuba a cikin miya bama. Ƙaramin tsaki ta ja tana ƙara ɗauko wata albasar ta yayyanka a plate ta budee miyar ta zuba a ciki ta mayar ta rufe, tukunna ta zuba doyar cikin ƙwan ta cakuɗa ta juye ta gaba ɗaya a cikin mai tana komawa gefe ta tsaya. Aikam ya fara tasowa yana zuba har ƙasa, gabanta ya yi wani irin mummunab faɗuwa, zuwa ta yi ta kashe gas ɗin mai ya zubo mata ta saki ihun da yasa Abdulƙadir shiga kitchen ɗin da gudu.
Hannu yakai yana kashe gas ɗin ya kama na Nuriyya zuwa wajen famfo ya sakar mata ruwa.
“Mahaukaciya ce ke? Me kike yi haka?”
Hannunta ta cire daga cikin ruwan tana yarfewa saboda azaba. Turo baki ta yi kawai don tana yin magana fashewa zata yi da kuka, bata san me yasa komai yake jagule mata ba haka. Shi kanshi Abdulƙadir ɗin ranshi ya ji ya ƙara ɓaci, ƙananun faɗa haka ba halayyar shi bane ba, amma a kwanakin nan jinshi yake komai ma na faɗa ne, ganin idan ya tsaya a kitchen ɗin fada zai mata yasa shi fita kawai ya koma ya zauna inda ya tashi. Nuriyya doyar ta samu wani waje ta rage, tana rage man ma, ta sake kunna gas ɗin, ta soya ta ciki da kwan jiki duk ya naɗi mai, ta kwashe ta saka wadda ta rage ɗin itama ta soyata, doyar nayin wajenta kwan ma yanayin wajen shi. Zuwa lokacin shida har da kwata.
Don Abdulƙadir ya wuce ɗaki don ya ɗaura alwala, yana so ana kiran sallah ya fara saka wani abu a cikin shi tukunna ya fita masallaci ko zai samu natsuwar yin sallah. Nuriyya kettle ta ɗauka da nufin ɗora ruwan zafi su sha shayi, shaf ta manta da man da ya zube a kitchen ɗin, ga kuma ruwan da ta zubar don ta cika kettle ɗin, ta kuma taka shi tana nufar inda socket zai yi, ta taka man tana wata irin zamewa, sai da ta yi sama, kettle ɗin ma ta yi sama tukunna su duka suka sauka kusan a tare, kettle ɗin a gefe da ruwan ciki da ya mungule gaba ɗayan shi, ita kuma akan mazaunanta ta yi warwas a ƙasa. Ta ɗauki wasu daƙiƙai tana sauke numfashin wahala kafin ta ja ƙafafuwanta ta miƙe.
Jikinta take kakkaɓewa duk ta naɗe ruwan a doguwar rigar da ke jikinta, kettle ɗin ta ɗauka ta tari wani ruwan, tana ƙoƙarin mayar da hawayen da suka cika mata idanuwa taf. Gaba ɗaya duniyar ta hautsine mata a cikin ƙanƙanin lokaci. Kettle ɗin ta jona tana kunnawa. Sannan ta sa abin goge-goge na tsaye ta fara aikin goge kitchen ɗin, tanajin kiris take jira ta fashe da kuka. Tana gama gogewa ta sake mayar da miyar kan wuta ta bata mintina biyar tukunna ta kashe, ko tayi ko bata yi ba a haka zata ci.
Tana nan tsaye ruwan ya tafasa, kettle ɗin ta kashe kanta, ta ɗauko flask tana juyewa ta ji kiran sallah. Ta ƙarasa ta rufe, ruwa ta ɗauko a fridge sai ga Abdulƙadir ya shigo kitchen ɗin, ya karɓe robar daga hannunta yana budewa ya yi Bismillah ya kafa bakin shi, Nuriyya na bin shi da kallo har ya sauke robar tare da wani irin numfashi, ruwan ya miƙa mata ta karɓa itama ta sha, yana dirar mata ciki da wani yanayi mai sanyi.
“Ki bani wani abu in ci in fita masallaci.”
AbdulKadir ya faɗi yunwa yake ji har kanshi na mishi ciwo. Kular doyar ta buɗe mishi, a tsaye ya saka hannu yana ɗauka ya saka a bakin shi duk da ta mishi zafi, yanajin ta kamar babu gishiri, kuma ƙwan bai kama ba, Waheedah harda tattasai take saka musu in zata soya. Bai yi magana ba, saboda yau ɗaya ga azumi, ba zai ɗora alhakin faɗansu akan shaiɗan ba, asalin halayen su ne za su bayyana. Ficewa ya yi daga kitchen ɗin zuwa masallaci, jikinshi har kyarma yake sa’adda aka idar ya taho gida. Ɓangaren Waheedah ya wuce yana jin ƙamshin da ya haɗe waje ɗaya bai san ko na menene ba, amma ya ƙara mishi yunwa. Kan darduma ya sameta a ɗaki, tana Azkar ne da alama.
“Sannu da shan ruwa.”
Ya faɗi yana kallon yadda fuskarta ta yi wani sanyi. Murmushi ta yi mishi tana idar da addu’ar ta.
“Sannun mu.”
Ta amsa shi tana miƙewa ta ninke dardumar da take kai. Kallonta Abdulƙadir yake ta yi yana kallo ta fita daga ɗakin, tana dawowa da apple a hannunta ta gutsura tana taunawa, Ikram ta ɗauka a gefen shi tana samun waje ta zauna, yarinyar ta gyara wa zama ita ma a jikinta don ta bata ta sha, ta ci gaba da cin apple ɗinta, cikin shi da ya ji ya yi wata irin murɗawa yasa shi miƙewa, don da alama Waheedah ba zata bashi abinci ba, ta daina son shi yanzun.