Tunda ta gama baccin safenta ta gyara ɓangarenta tsaf, sannan ta yi wanka ta shiga kitchen. Ɗan wanke-wanken da take da shi ta yi. Ikram na kwance cikin kekenta tana bacci. Fridge ɗin ta duba ta ga tana da naman rago, kawai sai marmarin tuwon semo da miyar ɗanyar kuɓewa ya kamata. Fito da shi ta yi don ya huce, ya yi ƙanƙara, ta ɗauki Ikram suka fito ta kulle kitchen ɗinta. Ɗaki ta koma ta kira Naziru a waya ta ce ya je ya siyo mata ɗanyar kuɓewa ya kawo mata in ya zo sai. . .