Bayan Wata Shida
Ba zata ce ga lokacin da ta taɓa jin daɗin rayuwarta irin watanni ukun nan ba, tana gama iddarta ta fara shiga gari yadda take so, satinta ɗaya bayan rabuwarsu da Abdulƙadir ta samu ta fita da rana ita da Asma suka je gidan suka kwashe kayan kitchen ɗinta, bata samu Abdulƙadir a gidan ba, sai Waheedah da sallamar su kawai ta amsa. Har da kayan abincin da suke kitchen ɗin kaf ta kwashe tana tafiya da su gida. Haka ta ce wa Mama cikin kuɗin kayan kitchen ɗinta ne da ta siyar. Da su ta siyi atamfofi da leshi, ta rage sauran da a kayan ƙwalam da maƙulashe ta ƙarar da su.
Kwalliya take yi ta kece raini, samari ne suke mata layi kala-kala suna mata hadarin kuɗi, sai yanzun ta san rabuwa da Abdulƙadir ɗin alkhairinta ne, saka yau take jinta, a watanta na biyu bayan ta gama idda ne ta haɗu da Saminu. Matashin saurayin da bazai shige shekara talatin da biyu ba, daga yanayin shi tasan bai taɓa aure ba kafin ya tabbatar mata da hakan, da wuri ta sanar da shi cewar ita aurenta biyu, nuna mata yayi duk wannan ba matsala bane ba. Dogone sosai mai ƙirar ƙarfi, kusan da kaɗan zai fi Abdulƙadir, sai dai nesa ba kusa ba, ba za ka haɗa kyawun Saminu da Abdulƙadir ba. Saminu ya tsere mishi tun daga hasken fata da dogon hanci, wayewa kawai Abdulƙadir zai nuna mishi. Da alamu Saminu bai yi karatun boko ba, don turancin shi irin wanda akan tsinta a hanya ne. Ya ce mata dai shi ɗan kasuwa ne.
Yana siyar da atamfofi da leshi da suke kawowa daga Legas zuwa nan garin Kano. Rashin wayewar shi bai dami Nuriyya ba, saboda yana sakar mata kuɗi kamar baisan ciwon su ba, ga siyayya yana mata kaca-kaca. Mafarkinta ne yake shirin cika, don a sati Saminu na iya zuwa da mota kala biyu, watan su ɗaya cif da haɗuwa ta nuna tana so ya fito, ya ce mata babu wata matsalar komai. Wannan karon Baba da kanshi ya faɗa wa wakilan Saminu cewar Nuriyya ta taɓa aure har sau biyu. Sukace duk Saminu ya sanar da su. Ko sadaki dubu hamsin suka bayar.
Kallo ɗaya zaka yi wa Nuriyya kaga tsantsar farin cikin da ke fuskarta, ga sabuwar waya ƙirar infinix dal a kwali Saminu ya kawo mata. ‘Yar walima ta yi a gidansu Asma ta tara ƙawayenta aka ralle, tunda dubu ɗari Saminu ya bata don yin hakan. Da kan shi ya yi mata maganar tarewa ta nuna mishi ita bata da wani kayan ɗaki ba kuma ta da kuɗin yi. Zuwa yayi da mota ya ɗauke su ita da Asma suka je wani tsantsareren gida ɗakuna shida, da komai da komai a ciki, ya ce ta duba idan ya yi mata. Ranar da suka dawo har Mama sai da ta kula da rawar ƙafar da Nuriyyar take yi.
“Ki dai bi komai a hankali Nuriyya…”
Cewar Mama, farin cikin da Nuriyya take ciki yasa ta faɗin,
“In shaa Allah. Na gode.”
Ta wuce ɗaki. A kwana biyun sosai ta matsa wa Saminu kan maganar tarewa, ya ce karta damu zai zo har gida ya ɗauketa ranar wata alhamis da ta yi juyin waina gardamammiya da rayuwarta. Har gida Saminu ya shiga suka gaisa da su Mama, ya yi musu siyayya sosai ta kayan ciye-ciye, ya kuma ƙara yi musu godiya tukunna ya fita waje yana jiran Nuriyya. Ta ɗauki jakarta da mayafinta a kafaɗa Mama ta shigo ɗakin.
“Nuriyya kinga kin samu mijin da alamu suka nuna yana sonki, don Allah ki bi rayuwar nan a hankali, ki yi haƙuri da duk yadda zata zo miki…”
Kai Nuriyya take jinjina wa duk wata nasiha da Mama ta yi mata ba don ta ji ta ba, don hankalinta na kan alƙawurran da Saminu ya yi mata, na cewar hajjin shekarar da ita za’a yi ta. A satin za su je su yi hoto, a fara maganar biyan kuɗi. Tun a mota take faɗin,
“Kasan a jirgi kawai nake hango ni?”
Don ta gama faɗa wa su Asma da duk wasu ƙawayenta maganar zuwan su Hajji, group ɗinsu ma yanzun Hajiya Nuri suke kiranta, sunan da yake ƙara sawa kanta ya kumbura. Tunda suka hau titin unguwar su take kula da cikin kurna yake nausawa maimakon Rijiyar zaki inda gidan da ya kaisu ita da Asma yake. Ganin suna barin cikin kurna suna nufar Ɗan Dinshe, unguwar da tafi tsana duk a cikin ƙaramar hukumar dala yasa ta faɗin,
“Naga muna yin Ɗan Dinshe.”
Kai Saminu ya jinjina mata, don shi ɗin ba mai yawan magana bane ta kula.
“Zan amshi saƙo ne.”
Ya amsa ta a taƙaice, numfashi ta sauke mai nauyin gaske tana sake gyara zama cikin motar. Haka har suka ƙarasa cikin Ɗan Dinshe, kusan ƙarshen unguwar don gidan da ya yi parking ne ƙarshe a unguwar sai wani gidan bulo daga gefe, unguwar shiru kamar an yi sata. Ta so ta zauna a cikin motar ya ce mata ta fito su shiga tare, bata son duk wani abu da zai ɓata mishi rai a daren su na farko yau, shi yasa ta fito, ta dai cika da mamaki ganin ya zaro mukulli a aljihun shi yana buɗe gidan, bin bayan shi ta yi. ƙaramin gida ne ɗan ƙarami, da ɗakuna guda biyu, banɗaki sai ɗan kitchen da ko ƙofa babu, sai ƙaramin risho a ciki da ‘yar tukunya daya tabbatar mata da cewar kitchen ne.
“Gidan fa babu kowa… Wanne irin saƙo za ka karɓa?”
Nuriyya ta faɗi tana kallon shi, ko kulata bai yi ba ya tura ɗakin da yake a share tas, da katifa matsakaiciya an gyarata itama, sai ƙamshin kafur yake da alamar yanayin damuna yasa aka saka saboda warin raɓa. Zuciyarta ta ji ta kasa natsuwa da ta shiga ɗakin.
“Ni dai ka ɗauki saƙon da za ka ɗauka mu wuce.”
Wani irin kallo Saminu ya yi mata da yasa hantar cikinta kaɗawa.
“Babu saƙon da zan ɗauka.”
Ya ƙarasa maganar yana samun waje gefen katifar ya zauna.
“Ki shigo malama kar sauro ya cika mana ɗaki.”
Cike da rashin fahimta Nuriyya take kallon shi.
“Ki shigo sai in miki bayani.”
Zuwa lokacin ƙafafuwanta har rawa suke, shiga ɗakin ta yi tana kasa zama, don zuciyarta dokawa take ta yi da wani irin ƙarfin da yake saka jikinta ɓari.
“Wata huɗu da suka wuce na shiga unguwarku wajen wani abokina muna zaune majalissa wajen mai rake kika zo kika wuce. Kina gifta mu na ji kin kwantamun har ƙasan raina, lokacin na furta hakan. Ban bar majalissar ba sai da na ji kaf labarinki, aurenki da Anas da kuma mijin Kawarki da kika aure. Cikin ƙasa da awanni biyu suka faɗa min labarin da nasan kin fi ƙarfina, saboda ba ni da kuɗin da za ki gani ki saurareni.”
Saminu ya ƙarasa maganar yana mata wani murmushi da yasa ta jin kamar an watsa mata ruwan ƙanƙara.
“Sunana Saminu da gaske, kuma kamar yadda na faɗa miki ɗan asalin ƙauyen Ɗan Busai da ke nan jahar Kano ne ni. Abinda ba ki sani ba shine ni bani da wasu kuɗi, mahaifinki ya san sana’ata ni direban babban mota ne, kuɗin duk da nayi miki hidima da su, kuɗin da kikai tunanin ina da su tsintar su na yi. Sai bayan na tsince su ne tunanin in zo miki a matsayin attajirin me kuɗi ya zo min saboda kin manne min a zuciya. Ko kaɗan bakiyi wahalar siyewa ba saboda abin duniya ne a gabanki, nan ɗin ne gidan da na samu na gina a cikin sana’ar da nake… Kar kuma kiyi tunanin akwai wani tashin hankali da za ki yi da zai sa in sakeki saboda wallahi na sha banban da duk wasu maza da kika aura a baya, babu kalar tashancin da ban ci karo dashi ba, ban je wajenki ba sai da na yi shirin zama da ke a duk yadda kika so mu zauna.”
Mayafinta Nuriyya ta sauke daga kafaɗa tana wulwula shi cikin son fifita fuskarta da iska ta daina kai mata, bata taɓa sanin menene tashin hankali ba sai yau. Tunda Saminu ya fara magana take jin wasu notika na kwancewa a jikinta, cigaba ya yi da faɗin,
“Duk motocin da kika ga ina zuwa wajenki da su cikin ragowar kuɗin da suka rage min nake arowa, gidan dana kaiku na ubangidan wani abokin wasana ne da yake gadi na roƙe shi alfarma na je da ku kika gani, na so in ji babu daɗi na yaudararki da na yi, sai na ga mu dukkan mu ba don Allah muka gina dangantakar ba, ni don son mallakarki, ke kuma don son abinda nake da shi, za ki iya taimaka min mu gyara zaman mu daga yau mu nemi yafiyar Allah.”
Wannan karon dariya Nuriyya ta yi da bata da alaƙa da nishaɗi, tana son wani ya zo ya tasheta daga wannan mugun mafarki, don a mugun mafarki ne kawai zata auri direba, direban ma na babbar mota.
“Da gaske ina kasuwanci, tunda idan na kai timatiri legas ina ɗauko gawayi in dawo da shi nan in siyar.”
Da kuka dariyar ta ƙwace mata, kafin ta sa hannu tana goge hawayen ta ajiye mayafinta a ƙasa ta kalli Saminu tana faɗin,
“Wallahi ƙaryar iskanci kake yi, ni za ka yaudara? Saminu ni zaka yaudara? Sakina za ka yi yanzun nan don bazan taɓa zama da kai ba. Ka ga na maka kalar matar da zata zauna a wannan akurkin kajin?”
Dariya Saminu ya yi.
“Saki? Ai wallahi gara ki fara sakawa a zuciyarki mutuwa ce abinda zata gifta ta raba ni da auren ki.”
Mayafinta Nuriyya ta tsugunna ta ɗauka tana jin yadda duniyar take jujjuya mata, shirin fita take yi daga ɗakin, cikin zafin nama Saminu ya taso ya riƙo hannunta, juyowa ta yi ta ɗaga ɗayan da niyyar sharara mishi marin da zai sa ya saketa a daren nan ta koma inda ta fito ya riƙe hannun yana haɗawa da ɗayan ya yi mata rikon da take ji kamar zai karyata tukunna yasa ɗayan hannun nashi ya sharara mata wani irin mari da yasa ta jin wani gishiri-gishiri a cikin bakinta.
“Na gaya miki duk kalar zaman da kike so mu yi da ke shi za mu yi, idan mutunci kike so za mu lallaɓa rayuwar mu, idan rashin mutunci kike so zan zauna da ke da shi.”
Kiciniyar ƙwacewa take tana auna mishi kalar zagin da in sun kwana a tasha yakan ji karuwai na yi wa masu neman su. Shi ya sha alwashin kuɗin goron da akewa direbobi na bin mata ba zai zamana cikin su ba, ko ba don komai ba yana tsoron lahirar shi, duk tangaririya da wahalar rayuwar daya sha da saken da ya samu sanadin mutuwar iyaye bai saka shi ya lalace ba. Iskanci zaɓi ne a kowanne yanayi duk da yakan zo da ƙaddara, amma akwai zaɓi a cikin al’amuran rayuwa. Wani marin ya sake ɗauke ta da shi yana wurgi da ita kan katifar ɗakin ya fita ya kulle ɗakin daga waje, yanajin yadda take dukan ƙofar tana cigaba da auna mishi zagin da ko a jikin shi.
Mota ya je ya fito da kayayyakin Nuriyyar da suke ciki ya shigo da su tsakar gidan, sai da ya dawo ƙofar gidan ya tsaya abokin shi da ya roƙa alfarma ya zo ya ɗauki motar mutane ya mayar musu ya iso, ya ba shi mukullin tukunna ya koma gidan ya kulle. Ya shiga ciki ya buɗe dakin Nuriyyar da ta fito, ya nuna mata ƙarfi yana ɗaukarta ya mayar da ita cikin ɗakin, bala’i ne take gani irin wanda take jin labarin shi, don Saminu bai jira ya saka abin duka ba, da hannun shi ya ci gaba da mata wani irin duka da ko lokacin da Abdulƙadir yake tashen zane su a Islamiyya bai taɓa mata irin shi ba. Tun tana samun bakin zagin shi tana kai mishi yaƙushi har ta galaɓaita, nishin kuka ma bata iya fitarwa, a haka Saminu ya bi ta yana raya daren.
Zuwa safiya kallo ɗaya za ka yi mata kasan ta gama fita daga hayyacinta, a gida ya yi sallar asuba. Ko kazar daya siyo sai da safen ya ce mata ta zo su ci, kai kawai ta iya girgiza mishi don da ƙyar ta iya samu ta yi wanka ta yi sallah saboda ciwon da ko’ina na jikinta yake mata, shi ne kawai abin daya tabbar mata da cewar ba mafarkin auren Saminu take yi ba, da gaske ne auren shi ta yi.
“Kalar duk zaman da kika zaɓar mana shi za mu yi Nuriyya.”
Ya ƙara tabbatar mata lokacin da ya fice daga ɗakin, kanta kawai ta haɗe da gwiwa wasu irin hawaye masu zafi na silalo mata, Hausawa sun ce babu inda son zuciya baya kai mutum, ko da wasa bata taɓa hango nata zai kawota cikin wannan bala’in ba, ko kadan idan sama da ƙasa za su haɗe ba zata yi zaman aure da Saminu ba.
Epilogue
Hannun hijab take gyara wa Ikram, ta kasa ranƙwafawa saboda tsohon cikin da ke jikinta. Abdulƙadir sai kiranta yake, ya ce shi ba zai shiga cikin gida ba, sai da ta fito harabar gidan ma ta ga ko motar bai shigo da ita ba, ƙofar gidan ta fito ita da Ikram tana tsammanin ganin motar shi. Amma ko alamarta babu, don bai ma ƙaraso ba duk ya bi ya ɗaga mata hankali kamar wani wajen ta zo ba gida ba.
A shekaru uku zata ce babu abinda ya canza musu banda samuwar ƙarin cikin da yake jikinta, rayuwa suke a nutse da ba zata ce a kullum cike take da farin ciki ba, suna samun matsalolin da basu fi ƙarfin yin sulhu tsakanin su ita da Abdulƙadir ba. Sai dai zuwa yanzun ta fahimci rayuwar haka take tafiya a ko’ina, ta koyar da ita babu wani abu wai shi dawamammen farin ciki, sai dai akwai farin cikin da kake samu ko yayane a cikin kowacce rana tunda za ka tashi da tarin dalilan da za ka godewa Allah domin su.
“Waheedah…”
Ta ji muryar Nuriyya ta dirar mata cikin kunnuwa, daga ranar da ta kwashe kayanta rabon da ta sakata a idanuwanta, duk da lokuta da dama takan yi tunanin ko tana wacce duniyar, juyawa ta yi tana kallon Nuriyyar da rayuwa ta sa ta yi wani irin sanyi. Da hijab dogo a jikin ta, duk da ba wata shigar a zo a gani bace a jikinta, ba’a wulaƙance take ba, don har ƙasan ran Waheedah ɗin ta ji daɗin ganinta a nutse. Haka zuciyarta take, wanda suke nufinta da sharri ma da fatan alkhairi take binsu, don a wajenta duka duniyar bata da wani yawa. Mu duka kuma ‘yan cirani ne da muke haɗuwa da mutane mabanbanta a hanyar mu, burin kowa shi ne samun ribar da zai yi alfahari da ita idan lokacin shi ya cika. Shi yasa bata ga dalilin da zai sa ta ɓata lokacinta akan abubuwan da ba za su amfaneta ba.
Sosai Nuriyya ta ji daɗin ganin Waheedah ɗin, tun tana ganin auren Saminu kamar abu na wasa, kamar abinda ba zata taɓa yarda da shi ba, tun tana mishi rashin mutunci yana jibgarta har ta fara saduda da lamurran duniya, don ta je gida Baba ya rantse wannan karon idan har ta kaso auren Saminu ba zata zauna mishi a gida ba, Mama kuma ta ce ba zata ba shi haƙuri ba. Haka ta haƙura ta koma, kullum rana sai Mama ta kirata a waya ta yi mata nasihar da sai da ya ɗauke ta shekaru biyu bata ji ta ba, shi ma shekarun satar fita ta yi batare da ta faɗa wa Saminu ba, akai mummunan hatsari a gaban idanuwanta mota ta take mace da goyonta ko numfasawa ba su yi ba.
Motar kuma ta kama da wuta haka direban ya fito yana ihu yana ci da wuta mutane na ƙoƙarin kawo mishi ɗauki, bata tunanin ta taɓa tsorata kamar yadda ta tsorata a wannan yanayin ba don a gigice ta ƙarasa gidansu da ƙafafuwanta kamar zararriya, tana shiga gida jikin Mama ta faɗa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, gaba ɗaya duniyar bakomai bace ba, kana aikin banza kake cinye kwanakinka, sosai hatsarin ya tuna mata da kwanciyar kabarin da ke jiranta, tarin tashin hankalin da yake cikin kwananta na farko ita kaɗai ba tare da taimakon kowa ba.
Ranar a gida ta kwana, duk da washegari Saminu zai dawo daga Legas. Samun shi ta yi ta bashi haƙuri kan irin zaman da suke yi, sosai kuma suka fahimci juna suka kuma nemi juna gafara. Da ta nutsu sai ta samu farin ciki a zama da direban da ta raina, direban da take ganin ta fi ƙarfin ta yi rayuwar aure da shi a duniyar da bakomai bace, data nemi tana son ta gwada neman aiki da takardun NCE ɗinta bai musa mata ba, cewa ya yi ma akwai wani ubangidan shi zai mishi magana ya ji. Cikin ikon Allah aka samo mata aikin koyarwa a wata Primary ta mata da ke nan Ɗan Ɗinshen. Dai-dai ƙarfin shi Saminu yake mata hidima.
Duk da matsala ɗaya ce take fama da ita yanzun, ita ce rashin haihuwa, banda wannan rayuwa take da ta sa ta gane farin ciki ba koyaushe yake zuwa da kuɗi ba, farin ciki kan zo idan ka samu wadatar zuciya da iya inda Allah ya zaunar da kai. Ta yi nasarar ganin Anas sau ɗaya tun bayan rabuwar su, ta kuma roƙi da ya yafe mata, duk da har yanzun takan yi juyi da amsar da ya bata.
‘Na jima da yafe miki Nuriyya saboda bana son wani abu ya sake haɗa ni da ke, ciki kuwa har da tsayuwa gaban Ubangiji a filin tashin ƙiyama, wallahi na jima da yafe miki karki damu.’
Sosai takan yi tunani akan kalar rayuwar da ta yi a baya, da mutane biyun da suka nuna mata ƙauna fiye da kowa a rayuwarta da yadda ta yi amfani da wannan ƙaunar ta cutar da su.
“Nuriyya.”
Waheedah ta faɗi tana katse mata tunanin da take yi.
“Ki yafe min don Allah, na cutar da ke da yawa, wanda kika sani da wanda baki sani ba, ki yafe min. Waheedah…”
Numfashi Waheedah ta sauke.
“Babu komai, Allah ya yafe mana.”
Wannan karon ajiyar zuciya Nuriyya ta sauke tana ɗorawa da,
“Ki roƙar min Abdulƙadir da ya yafe min shima.”
Kai Waheedah ta ɗaga mata tana hango motar Abdulƙadir ɗin.
“Sai anjima…”
Ta ce wa Nuriyyar tana kama hannun Ikram ɗin.
“Ina Fajr?”
Nuriyya ta tsinci kanta da tambaya tana saka Waheedah juyowa ta kalleta cikin idanuwanta
“Na yafe miki Nuriyya, tun kafin ki tambaya, amma hakan baya nufin ina son sake kasancewa da ke a rayuwata, babu wani abu da zai sake haɗa ni ƙawance da ke.”
Kai Nuriyya ta jinjina ma Waheedah ɗin, bata ko ji zafin maganganunta ba, ko ita ce a matsayinta abinda zata yi kenan.
“Na gode.”
Nuriyya ta faɗi da wani irin yanayi a fuskarta.
“Ina miki fatan alkhairi a duk inda rayuwa zata kai ki.”
Waheedah ta faɗi tana jan Ikram suka tsallaka inda Abdulƙadir ya yi parking ɗin motar, Nuriyya kuma ta shiga gida. Bayan motar ta buɗe wa Ikram ta sakata a ciki, tukunna ta buɗe gaban ta shiga.
“Kinsan sarai gobe zan tafi, shi ne za ki zo ki barni ni kaɗai.”
Murmushi kawai ta yi.
“Nuriyya nagani yanzun ta shiga gida, ta ce in ce ka yafe mata.”
Shiru Abdulƙadir ɗin ya yi ba don bai ji me ta ce ba, sai don a shekaru uku yaune rana ta farko da maganar Nuriyya ta gifta a tsakanin su. Motar shi ya tayar yana wucewa da su gida, ba shi da abin cewa yanzun ma, shi yasa ya zaɓi yin shiru, wanda duk zai ji labarin shi da Nuriyya zai san ƙaddarar zaman aure ce kawai ta gifta a tsakanin su, yanzun ta zama bayan shi, bayan da baya dubawa idan har ya wuce, ya gama yafe mata duk wani kuskure da ta yi mishi a ɗan gajeran zaman da suka yi. Shi ma fatan shi idan ya kuskure mata ya zamana ta yafe mishi.
Dan da Abbba ya kira shi ya sake mishi nasiha kan abinda ya faru ɗin daya kira mishi ko da gaba zai yi tunanin ƙara aure sai da hanjin cikin shi ya murɗa, yana addu’ar Allah yasa ƙaddarar shi ta zama da mata biyu ta ƙare daga kan Nuriyya, Waheedah ta ishe shi rayuwar duniya yana kuma fatan ta zama matar farko da zai nema idan ya tsallake duk wani mataki yayi nasarar shiga aljanna.
Suna ƙarasawa gida an kawo wuta, Ikram na ta tsalle ganin TV a kunne da tashar cartoon network da suka saka Shun the Sheep. Nan falon suka barta suna shigewa daki. Waheedah na cire hijabin da ke jikinta, Abdulƙadir ya taka ya haɗe space ɗin dake tsakanin su, sai nishi take kamar ta yi wani aikin ƙarfin.
Hannun shi ɗaya ya ɗora kan cikinta kamar abinda yake ciki hakan yake jira yayi motsin da ta ji har bayanta ya amsa tana runtse idanuwanta ta buɗe su akan Abdulƙadir da yake mata dariya.
“Ke kam kamar ba matar soja ba.”
Hararar shi ta yi.
“Da zan iya dana cire cikin nan ka ɗauke shi ko na kwana biyu ne.”
Tsinin cikin bazai barshi ya rungumeta yanda yake so ba, hakan ya saka shi sakin hannunta ya zagaya yana rungumeta ta baya tare da raɗa mata maganganun da sirrine a tsakanin su, hannu ta sa tana ɗan ture shi tare da yin dariya kafin ta ɗora hannunta saman nashi da yake kan cikinta tana lumshe idanuwanta.
Abdulƙadir ɗinta, sojan ta, Sadaukin ta. Bata same shi da sauƙi ba, ƙaddarar zaman su bai kawo su inda suke da sauƙi ba, bata da wani tabbaci akan yadda rayuwa zata ƙare musu, amma tana da yaƙinin in dai suna tare da juna ko ya rayuwa zata hankaɗe su ko da sun faɗi ɗayansu zai ɗaga ɗaya.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki.
Littafin Nan yayi ma’ana sosai Allah ya Kara basira Lubnah
Littafin yayi ma’ana sooosai da sosai, sai kin ga yadda na ke jin Abdulkadir a rai na kaman da gaske in samo shi in masa shegen duka wallahi amma Alhamdulillah everything fell in place. Allah ya kara basira. Mun gode