Zaune take gaban mudubi ba don za ta yi kwalliya ba, tunda ta fito daga wanka ta saka wa jikinta riga da wando na Pakistan, ta ɗauko hula ta ajiye kan mudubin, anan ta shafa mai ta zauna ba tare da ta san asalin abinda take tunani ba. A hankali ta ɗauki farar hular ta saka a saman kanta, tana gyara zamanta, hasken hular na saka nata hasken ƙara fitowa. A hankali cikin sanyin yanayinta ta yi baya da kujerar da take kai ta miƙe tsaye. Madai-daicin tsayin da take da shi bai hana sirantakarta fitowa ba, duk. . .
Allah yakara basira da zakin hannu