Idan akwai abinda yake yi a nutse a rayuwar shi bai wuce tuƙi ba, ko Yassar da ya koya mishi tuƙin idan za su je wani waje yakan ce mishi,
'Abdulkadir kana taka mota kamar za ta cije ka. Don Allah ka ƙara gudu.'
Shi kam bai ga saurin da yake ba. Yanzun ma a nutse yake tuƙinshi, kamar yana da duka lokacin da yake buƙata. Waheedah kuwa ta nutsu a gefe tana wasa da wallet ɗinshi da take hannunta, zuciyarta na doka mata a ƙirjinta kamar za ta fito waje. Ga shirun da yake cikin. . .