Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Ashirin Da Shida

1
(1)

<< Previous

Tun da ya tunkari ƙofar yake jin ƙauri ya cika mishi hanci, yana buɗe ƙofar ya saka ƙafafuwan shi cikin falon Waheedah yake jin ƙaurin na ƙaruwa, ɓangaren Nuriyya ya ƙarasa yana ganin hayaƙin da yake fitowa daga kitchen ɗin ya turnuƙe falon, gaban shi ya ji ya yi wani irin mummunan faɗuwa, da gudu ya shiga kitchen ɗin, hayaƙin na shaƙe mishi kafofin shige da ficen iska, ya soma tari, ta inda ƙaurin yake fitowa Abdulƙadir ke nema. Kafin idanuwan shi sukai kan tukunyar da ta yi wani irin baƙi. Hannu ya kai ya kashe gas ɗin ya fito daga kitchen din yana takawa zuwa ɗakin baccin Nuriyya.

Tunda Abdulƙadir ɗin ya fita, ta tashi ta ɗora ruwa ta zuba shinkafa a ciki don ita ba tsayawa za ta yi sai ruwan ya yi zafi ba. Dawowa ta yi ta ɗauki wayarta tana ganin text, dubawa ta yi ta ga dubu arba’in, murmushi ta yi hankalinta da yake a tashe ta ji ya kwanta. Dama ko da Abdulƙadir din bai dawo ba ita ba tunanin abinda ya same shi ko abinda ake mishi ne a gabanta ba, tunanin abinda zai mata idan ya dawo shi ne matsalarta, tunda kuma ya tura mata kuɗi kamar yadda yakan yi duk wata, hakan na nuna alamar babu abinda zai faru. Ko faɗa ma bai mata ba, shi ya sa ta wuce ɗakin baccin.

Akwai wasu takalma da aka turo a group ɗinsu na mata da ƙawarta Safara’u ta saka ta ciki, takalman sun mata kyau, har ta private Safara’u tai mata magana ko zata siya, sai dai ta kashe kuɗin hannunta tas, ta yi niyyar ta nuna wa Abdulƙadir ɗin dama in ya kwana biyu ya huta, sai ga Waheedah ta zo tana asibiti ita kuma. Bata san cutar da har yanzun take damunta da bata warke ba ma, takalmin ta ce tana so dubu bakwai da ɗari biyar, ta tura kuɗin, sai ta tura wa Safara’u balance dine atamfofin da ta ɗauka wancan watan dubu goma, ta kuma tura wa mai ɗinkinta shi ma dubu goma. Kafin wani lokaci dubu huɗu ce ta rage mata a banki.

Kwanciya ta yi kan gadon da yake a hargitse tana manta cewar ta ɗora wani girki tunda ba sabawa ta yi ba. Hankalinta ya nutsu kan littafin Ɗan Adam na Rufaida Omar da take karantawa, don littafin sai ka nutsu zakae fahimce shi yadda ya kamata. Ranta ƙal take jin shi, ko kadane bata ji shigowar Abdulƙadir da ya nutsar da hankalin shi kanta ba, ya ɗauka ma wani abin ne ya sameta har ta ɗora girki ya yi wannan kamun ko ƙaurin shi bata ji ba.

“Nuriyya…”

Abdulƙadir ya kira ranshi a matuƙar ɓace, da alama bata ma jishi ba, don ta yi rufda ciki ne da waya riƙe a hannunta.

“Nuriyya!”

Ya sake kira da ƙarfi wannan karon yana saka ta juyowa a tsorace, ganin shinee yasa ta tashi zaune tana ajiye wayar tare da faɗin,

“Sannu da zuwa.”

Da idanuwa Abdulƙadir ya kafe ta.

“Baki da hankali ko? Baki da hankali za ki dora girki ki dawo ɗaki ki zauna kina danna waya. Gobara kike son ki haɗa min a gida Nuriyya?”

Gabanta ne ya yi wata irin mummunar faɗuwa tana miƙewa tsaye.

“Ina za ki je?”

Abdulƙadir ya buƙata.

“Wallahi na manta ne!”

Ta amsa tana wani irin sauke murya da ya ƙara ɓata mishi rai.

“Saboda girkin ba shi bane a gabanki, ya za ki ɗora girki har ya yi wannan ƙonewar kina faɗa min kin manta?”

Idanuwanta Nuriyya tajio sun ciko da hawaye, ta manta ranar ƙarshe da aka tusata gaba ana mata faɗa haka, dama shi ne in yana nan baya rasa abinda zata yi da zai mata faɗa.

“Masoyi mantuwa ce, kowa na yi kuma.”

Idanuwan shi Abdulƙadir ya ƙanƙance a kanta, yana jin yadda ranshi yake ƙara ɓaci, ba zai ɗauki wata rashin kunyar bayan wadda Waheedah ta gama sauke mishi ba. Ƙarasawa ya yi ya kama hannunta ya fara janta zuwa hanyar da zata fita dasu daga ɗakin, binshi kawai Nuriyya take har kitchen ɗin tana ganin hayaƙin da har lokacin bai gama fita ba.

“Meye a hancinki? Danna waya ya fi miki muhimmanci, ki kalli kitchen ɗinki, yaushe rabonki da shara Nuriyya? Wanke-wanke fa?”

Hannunta da ya damƙa take murzawa da ɗayan, tana jin wani hawaye mai ɗumi ya zubo mata.

“Karki min kukan banza da ba shi da dalili wallahi…”

Abdulƙadir ɗin ya faɗa, dan bayason kukan banza. Raɓa ta ya yi ya wuce yana fita daga kitchen ɗin, ɗaki ya koma ya shiga banɗaki, yana ganin yadda farin tiles ɗin ya yi duƙun-duƙun, bangon har wani dallakin dauɗar da baisan ko tun ta yaushe bace ba, ga kayan wanki kaca-kaca. Tsintar kanshi yayi da kasa amfani da banɗakin, ya fito yana ganin bedroom ɗin ma a hargitse. Kai kawai ya girgiza yana tunanin kalar Nuriyya, in da zaman kallo ne ko danna waya babu wanda zai nuna mata.

Ɓangaren Waheedah ya wuce ya shiga banɗakin ya gama abinda zai yi ya fito. Ɓangaren Nuriyyan ya koma ya zauna a falo yana ɗora ƙafafuwan shi kan kujera don jin ƙasar da yake takawa kan kafet ɗin. Yana jin kacafniyar kwanoninta a kitchen ɗin. Da alama wanke-wanke take, aikam abin da take yi kenan, ranta a ɓace yake, bata san yadda zata sake mishi maganar ‘yar aiki ba, idan azumi ya zo mata Waheedah bata dawo ba ta gama yawo ta sani. Ƙugunta ta ji ya gaji lokacin da ta gama tana share kitchen ɗin, fitowa ta yi ta samu Abdulƙadir ɗin a zaune.

“Yunwa nake ji ni kam.”

Ya faɗi yana kallonta, don zaman da ya yi waje ɗaya ya sa yunwar taso mishi. Nuriyya kamar za ta yi kuka ta ce,

“Nikam me zan baka? Ka ga abincin ne na ɗora ya kama, ko za ka yo mana takeaway?”

Kai ya girgiza mata, yadda yake ji bazai iya fita ba.

“Ko indomie ki dafa min, bazan iya fita ba Nuriyya.”

Robobin lemukan ta ƙarasa tsincewa da na ruwa tana komawa kitchen ɗin, ranta in ya yi dubu ya gama ɓaci. Ita har ranta bata yi niyyar cin indomie ba, bata ma tunanin tana da indomie ɗin, dubawa ta yi, sauran data rage mata ce ta dafa jiya. Fitowa ta yi tana kallon Abdulƙadir ɗin, muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce,

“Babu indomie.”

Juyawa ya yi yana kallonta da mamaki.

“Baki siya ba ne wancan watan?”

Kai Nuriyya ta girgiza mishi, ita wancan watan kuɗin da ya bata ne gaba ɗaya ta tattara ta siyi zoben gwal ƙarami, dubu biyu kawai ta cika. Babu abinda ta siya, ta ɗauka ma shi zai siyo musu.

“Ki duba kitchen ɗin Waheedah.”

Abdulƙadir ɗin ya faɗi da alamar gajiya a muryarshi. Wucewa ta yi ta ɗibo indomie ɗin guda huɗu ta dawo.

“Masoyi.”

Ta kira tana ɗorawa da,

“Yaushe Waheedah zata dawo? Jikinne har yanzun?”

Kai Abdulƙadir ya jinjina mata.

“Zata dawo, tana gida… da ta ƙara warwarewa.”

Wucewa Nuriyya ta yi ba tare da ta ce mishi komai ba. Ranta ya ƙara ɓaci ba kaɗan ba, ashe gida Waheedah ta wuce abinta saboda baƙin hali. Nan da nan ta dafa indomie ɗin, don zata ce duk a abinci ita kaɗai take dafawa babu wata matsala, a plate ta zubo musu ta saka cokula tana fitowa da ita ta ajiye, cokalin Abdulƙadir ya ɗauka, duk yunwar da yake ji bata hanashi faɗin,

“Baki dafa mana ƙwai ba? Haka za mu ci?”

Ba tare da Nuriyya ta kalle shi ba ta ce,

“Banda ƙwai ni.”

Da alamar ƙosawa a muryarta, ta kula ba a iya ma Abdulƙadir ɗin, ta samu waje ta zauna.

“In za ki yi mana siyayyar azumi ki siyo mana, ina so ni fa.”

Cewar Abdulƙadir ɗin yana fara ɗibo indomie ɗin da ta yi mishi zafi yana jira ta huce, kallon shi Nuriyya take cike da rashin fahimta.

“Ba kai za ka siyo ba?”

Kai Abdulƙadir ya girgiza mata.

“Me yasa zan tura miki kuɗin idan ni zan siyo.”

Hanjin cikinta Nuriyya ta ji sun tattaru sun kulle waje ɗaya.

“Wanne kuɗin?”

Ta tambaya cikin bayyanannen tashin hankali, indomie ɗin da ya ɗibo ya kai bakin shi ya tauna yana haɗiye tukunna ya kalli Nuriyya.

“Na tura miki dubu arba’in ɗazun, baki gani ba ne?”

Kai Nuriyya ta ɗaga don da ƙyar ta haɗiye indomie ɗin da ke bakinta.

“Na siyayya ne dama?”

Cikin rashin fahimta Abdulƙadir yake kallonta kafin ya ce,

“Nuriyya…”

Saboda yanayinta da ya gani duk ta daburce, ya kirata ne yana tambayar ko lafiyarta, amma ita bata fahimce shi ba, ta ɗauka ko ya gane bata da gaskiya ne.

“Wallahi bansan na siyayyar azumi bane Masoyi, na san kana bani kyautar kuɗi.”

Kallon nata Abdulƙadir yake yi, yana son fahimtar in da kalamanta suka dosa, kallon ne take jin yana ƙara rikita ta.

“Na siyi takalma a ciki, dama wancan watan akwai atamfofin da na ɗauka, shi ne na cika kuɗin…. Sai na biya kuɗin ɗinki kuma.”

Cokalin Abdulƙadir ya ajiye cikin abincin yana kallon Nuriyya.

“Ban gane me kike ce min ba, kuɗin da na tura miki ɗazun ɗin ne kika siyi su takalma da atamfofi?”

Kai Nuriyya ta ɗaga mishi, cikin tashin hankali take faɗin,

“Don Allah ka yi haƙuri, wallahi bansan na siyayya ba ne.”

Kallonta Abdulƙadir yake yana rasa abinda ya kamata ya yi, ranshi da yake ƙoƙarin kwantarwa ne Nuriyya take ta ɓatawa tunda ya shigo. Tsaye yake akan gidan shi, in dai kayan sawa ne duk bayan wata biyu ko uku yake ba Waheedah kuɗi ko zata siya, ita ma Nuriyyar ya fara bayan watanta biyu da zuwa, to tana yawan tambayar shi kuɗi, ko zata yi ankon suna ƙona bikin ƙawayenta, ko zata siyi wani abin, shi ya sa ya daina bata. Akwai kuɗin da ya ware na siyayyar kayan sallar su dama.

“Kuɗin kayan abincinne kika siyi takalma da su Nuriyya? Abinda duk nake miki bai isheki ba sai kin taɓa min wannan kuɗin?”

Kai Nuriyya ta girgiza mishi.

“Baki da takalma? Baki da kayan sawa? Kin tambaye ni kuɗin takalma na hanaki ne?”

Abdulƙadir yake tambaya yana kallonta, kai kawai take girgiza mishi, miƙewa Abdulƙadir ya yi abincin gaba ɗaya ya fita daga ranshi, ita ma Nuriyyar miƙewa ta yi tana da na sanin faɗa mishi, hannun shi zata kama ya ce,

“In kika taɓa ni sai na mareki Nuriyya…”

Tsaye ta yi tana zare idanuwanta da suke cike da rashin gaskiya.

“Yau ya zama ranar ƙarshe da zaki min amfani da kuɗin hidimar gida kan wani abu daban, wallahi ranki zai mugun ɓaci tunda na ga alama ke baki da hankali.”

Abdulƙadir ya ƙarasa maganar ranshi a ɓace.

“Don Allah ka yi haƙuri.”

Nuriyya ta faɗi, wani irin kallo Abdulƙadir ɗin ya watsa mata, haƙurin da take bashi ne yake jin yana ƙara ɓata mishi rai, wucewa ya yi yana komawa ɓangaren Waheedah, don idan yana ganin Nuriyya komai zai iya faruwa. Kan kujera ya kwanta yana lumshe idanuwan shi. Da Waheedah na nan ma ko yaya ne zuciyarshi zata yi sanyi, amma ta yi tafiyarta saboda ta daina damuwa da shi, abinda ya fi tsana fiye da komai ya tsinci kanshi tsundum a ciki, tunanin safiyar ranar da sukayi faɗa da ita.

Kwanan shi biyu da zuwa, yana kula da yanayinta tunda ya zo. Shirunta ya mishi yawa, bai dai tambaya ba sai safiyar ranar tana kitchen tana soya musu fanke ya shiga yai tsaye yana jingina bayan shi da kantar kitchen ɗin.

“Wahee me yake damun ki?”

Ya tambaya, da wani nisantaccen yanayi a fuskarta ta girgiza mishi kai.

“Lafiya ta ƙalau.”

Ta faɗi tana cigaba da aikinta, da idanuwa Abdulƙadir ɗin yake binta har ta gama ta ɗauki kulolin tana wucewa falo. Har suka karya idanuwan shi na kanta, shirun nata ta ba shi yake har ƙasan zuciyarshi, ranar ta karɓi girki, tunda hutu zai yi kwanan shi biyu a wajen Nuriyya. Sake binta kitchen ya yi ya samu tana wanke-wanke.

“Shirun ki ya min yawa.”

Ba tare da ta kalle shi ba ta amsa a taƙaice.

“Babu komai.”

Kasa fita ya yi daga kitchen ɗin har ta gama wanke-wanke tana goge kitchen ɗin, ta ɗauki ƙaramin towel na goge-goge ta sake fitowa falo, Abdulƙadir ɗin na binta. Tana jin shi, bata da abinda zata ce mishi, bata kuma jin yin surutun, yana tsaye Nuriyya ta fito tana faɗin,

“Masoyi…”

Goge-gogenta Waheedah ta cigaba da yi duk da zuciyarta da take jin kamar zata buɗe ƙirjinta ta fito, ta gefen idanuwanta ta ga Nuriyyar ta ƙaraso ta kama hannun Abdulƙadir ɗin tana saka wani irin tuƙuƙin kishi taso mata. Bata san me suke cewa ba saboda zafin da ƙirjinta yake yi ya ɗauke mata hankali daga kan su. Bayau ta fara gani ba, wani lokaci suna zaune a kujera Nuriyyar zata fito daga ɓangarenta ta zo ta zauna gefen Abdulƙadir ɗin, ko ta kwantar da kanta a jikin shi, ko ta riƙe hannun shi, duk wani abu da jikinsu zai haɗu a gaban Waheedah ɗin ta kula shi take yi.

Bata taɓa ɗaga kai ta kalle su ba, ballantana ta yi magana, ta san idan aka tsaya tambayarta kalar soyayyar da take yi wa Abdulƙadir ba zata iya misaltata ba. Sai dai ko da wasa bata yi tunanin tana da zafin kishi ba sai da ta ga Nuriyya a kusa da shi. Bata ƙara sanin zafin kishinta ya girmama ba sai lokacin da Abdulƙadir ɗin ya fara mata hirar Nuriyya da bata son ji, baya kuma kula da bata tanka mishi duk idan yanayi. Ko fim take kallo in sun kalla da Nuriyya sai ya fara bata labari har abinda Nuriyya ɗin ta faɗa kan fim ɗin.

Babu abinda ta gaji da shi sai yadda ran girkinta ko ba ranar girkinta ba sai dai ta gansu a ɓangarenta zaune suna jira ta gama girki su ci, idan girkin Nuriyya ɗin ne ma in ta zuba musu tare suke ci mata abinci a falo. Bata taɓa jin ta gaji da su biyun ba irin wannan karon, daga Nuriyyar har shi Abdulƙadir ɗin da ya kwaso mata ita ya ajiye mata a gida ta gaji da su, ko ganin su bata son yi. Ji take idan bata ɗan fita ta sha iska ko yaya ba komai zai iya faruwa.

Tana jin kamar daga ranar da Nuriyya ta shigo gidan wani abu mai kama da bomb ya kunnu a cikin jikinta, abinda ganin Nuriyyar da Abdulƙadir ke ƙara wa gudun lokacin fashewa, yanzun tana jin yana gab da tarwatsewa kuma ba zai yi kyau ba. Muryar Abdulƙadir ɗin ta ji yana faɗin,

“Wai zata fita ne da, kuma ta fasa.”

Ɗagowa Waheedah ta yi tana kallon shi, kafin ta ji Fajr ya riƙo mata hannu.

“Omma banga socks ba, nasa uniform ɗin.”

Kai ta jinjina mishi.

“Zan duba idan na shiga ɗakin Fajr.”

Sakin hannunta yaron ya yi yana komawa kan kujera in da ta kwantar da Ikram.

“Karka tasar min yarinya ban gama aikina ba.”

Ta ce mishi, hakan yasa shi matsawa gefe ya zauna. Hankalinta ta mayar kan Abdulƙadir.

“Zan je gida anjima…”

Tana kallon yadda yake girgiza mata kai tun kafin ta ƙarasa maganar.

“Za ki bar ni ni kaɗai… A’a kam, ba yau ba Wahee.”

Cikin idanuwa ta kalle shi wannan karon.

“Ni ina so in je, don Allah ka barni.”

Ta ƙarasa maganar wani abu na mata tsaye a maƙoshi, kai Abdulƙadir ya ƙara girgiza mata.

“Kar ma mu fara jan maganar nan, ba za ki je ba.”

Hawaye ta ji sun cika mata idanuwa da take da tabbacin basu da alaƙa da hanata fita da ya yi, kawai ta gaji ne har cikin ƙasusuwan jikin ta.

“Gaskiya Sadauki sai na je… Ina so in je gida ni kam.”

Da bayanannen mamaki a fuskar shi Abdulƙadir yake kallon ta, bata taɓa mishi magana da wannan yanayin ba, baya kuma son ta fara.

“Ba za ki je ba to.”

Ya faɗi yana ƙanƙance mata idanuwanshi, sai dai rikicin da yake cikin nata ya fi nashi.

“Za mu gani.”

Ta faɗi tana juyawa da nufin komawa kitchen ta wanke towel ɗin da yake hannunta.

“Me kika ce?”

Abdulƙadir ɗin ya tambaya ranshi a ɓace, juyowa ta yi tana saka idanuwanta cikin nashi.

“Ka jini ai, cewa na yi za mu gani.”

Murmushi Abdulƙadir ya yi me sauti.

“Za mu ga me?”

Ya tambaya, wuce shi Waheedah ta yi ta ajiye towel ɗin tana fitowa, bata so ko me take ji ya tarwatse mata cikin gidan. Ta gaban Abdulƙadir ɗin ta zo wucewa.

“Ba fa in da za ki je Waheedah…kin ji ni ai.”

Ikram ta gyara wa kwanciya, ganin kamar zata faɗo tana cewa,

“Sai kai ta yi kuma.”

Sosai Abdulƙadir yake kallonta.

“Rashin kunya za ki min Waheedah?”

Ya tambaya yana jin kanshi har ɗumi yake ɗauka saboda ɓacin rai, ɗagowa ta yi tana matsowa kusa da shi.

“Idan rashin kunya na yi maka me zai faru?”

Mamakin da yake ji ne yake ƙoƙarin danne yadda ranshi yake tafasa, da za’a tambayeshi zai ce babu rana ɗaya da Waheedah zata iya ɗaga mishi murya balle har ta kalli cikin idanuwan shi tana fada mishi magana. Murmushin takaici ya sake ƙwace mishi, juyawa ya yi da nufin ya bar mata ɗakin, don komai zai iya faruwa ya ji ta ce,

“Na ɗauka wani abin za ka yi ai…”

Baisan me ya shiga kanta haka ba, har tambayarta ya yi da ya ga kamar wani abin yana damunta ta ce mishi bakomai.

“Waheedah ki kiyaye ni, Allah ki kiyaye ni, karki ce zaki fara min rashin kunya. Gida ne ba za ki je ba, duk kwanan nan ma babu inda za ki je, ba gida kawai ba ko ina ne ma.”

Dariya Waheedah ta yi da take nuna mishi shi ɗin bai isa ba, tana ƙara ɓata mishi rai.

“Lallai…”

Ta faɗi tana sake yin wata dariyar, runtse idanuwan shi ya yi yana buɗe su a kanta, ranshi in ya yi dubu a ɓace yake, ya manta ranar ƙarshe da wani abu ya ɓata mishi rai irin hakan, baya jin ma a duniyar shi gaba ɗaya akwai wanda ya isa ya ɓata mishi rai har haka, sai dai ita ɗin.

“Ban isa ba kenan ko me kike son ce min?”

Ganin kallon da take mishi ya tabbatar mishi da abinda take nufi kenan.

“Waheedah…”

Ya faɗi cike da kashedi.

“Meye Sadauki? Ni fa sai na fita, ka ji na faɗa maka ma.”

Juyawa ya yi yana soma tafiya, gidan zai bar mata gaba ɗaya, idan ya daina jin ba zai ɗauke ta da mari ba sai ya dawo ya ji ta inda rashin kunyar nan da ba halinta bane take fitowa. Bin shi Waheedah ta yi tana riƙo hannun shi, in bata fita ta shaƙi wata iska daban da ta gidan ba tana jin matsala zata samu, ƙirjinta zafi yake.

“Ka ce min in je ni dai, ka ji… Don Allah.”

Hannun shi ya zame daga cikin nata.

“Ki sakeni kafin in mareki.”

Wannan karon mamaki ne ƙarara a fuskar ta.

“Saboda zan fita shi ne zaka mare ni? To ka mare ni don Allah… Ka mare ni ka ga in zai hanani fita.”

Hannun shi Abdulƙadir ya zame yana ci gaba da tafiya, sake riƙo shi ta yi, ko kaɗan baisan ya akai hannun shi ya sauka kan fuskarta ba yana haɗawa da tureta, ya manta yadda ko kaɗan bata da kuwarin kirki, kafin ya riƙota ta kai ƙasa kanta na buguwa da tebur ɗin da yake ajiye a wajen, lokacin da yai ƙasa yana rikotai har jini ya fara taruwa inda da alama ta fasa kanta ne. A rikice yake girgiza ta.

“Waheedah…Waheedah…”

Tunda yake a duniya bai yi tunanin zai ga tashin hankali kalar wanda yake gani yanzun da take riƙe a hannun shi kamar bata numfashi ba. Bai yi tunanin akwai abinda zai gigita shi kamar wannan gigitar ba, sai yanzun da yakejin duniyar ta haɗe mishi waje ɗaya.

*****

Gyara kwanciya ya yi yana sauke wani irin numfashi, kuskure ne ya yi da bai san ta in da zai fara gyarashi ba, na lokacin ya manta yadda Waheedah matarshi ba Ƙanwarshi ba, da tana ƙanwar shi har lokacin zai ɗauketa ya kaita asibiti, in ta ji sauƙi suka dawo gida zai sa cable ya zane rashin kunyar da tai mishi, ya kuma zane wadda take jin zata yi mishi a gaba. Amma matarshi ce, baisan da wanne ido zai kalli Abba idan ta faɗa mishi ya mare ta ba, don a gaban shi Abba kan faɗi duk namijin da ya ɗaga wa yarinyar shi hannu ya sani sai dai ƙaddara amma ya daki auren shi.

Sai dai ya bata haƙuri, ya kamata ta haƙura, ta sake bashi wata damar, ko me zata ce mishi, duk rashin kunyar da zata yi mishi ba zai ma kulata ba ballantana ya ɗaga mata hannu. Tashi zaune Abdulƙadir ya yi yana dafe kan shi da hannuwan shi biyun, komai yake ji ya haɗe mishi waje ɗaya, baisan da me zai ji ba, ranshi da yake ɓace da Nuriyya da ko kaɗan bata kula hankalin shi ba’a kwance yake ba ta ƙara ɓata mishi rai, ko da Waheedah da ta hargitsa duk wani kwanciyar hankalin shi.

Yasan da bai yi rashin kunya lokacin da aka bashi damar yin bayanin ƙarar shi da Major ya kai ba, da wahala ma ya kwana, tunda bayani kawai zai yi su ce mishi ya ja wa matar shi kunne, sai ya ba Major haƙuri, amman ba zai iya wannan ba. Rashin kunya ya tsula har Major ɗin ya sa mishi hannu, da suka yi detaining ɗin shi kuma ya sake jibgar wani a cikin cell ɗin. Shi ya sa yai kwanakin da ya yi, gashi sai yanzun yake jin ciwon da jikin shi yake mishi.

Waheedah ko wannan bata duba ba take ƙara kallon idanuwan shi tana cewa ya rabu da ita, shi kam ba shi da wannan zuciyar, haƙuri zata yi ta yafe mishi ta dawo su yi zaman su. Don shi ba zai taɓa iya rabuwa da ita ba. Yanzun ma ji yake yadda ranshi yake a ɓace in bai ganta ba akwai matsala, wata irin kewarta yake ji tana danne shi kamar bai ganta awanni kaɗan da suka wuce ba, a gigice yake jin rayuwar shi da wata irin rashin nutsuwa da kusancin Waheedah kawai yake samar mishi. Tashi yayi yana laluba aljihun shi ya ji mukullan motar shi suna ciki. Ficewa ya yi daga gidan ya shiga mota, wajen Abba za shi, in Waheedah bata dawo gidan shi ya ji ta a kusa da shi ba yau bai san yanda zai yi da tunani ba.

*****

Tsintar kan shi yayi da kasa nufar ɓangaren Abba kai tsaye, don haka ya wuce wajen Hajja, a falo ya sameta zaune da remote a hannunta, Zainab da ita ce autarta kuma tana aji ɗaya a jami’a a yanzun tana zaune gefen Hajja ɗin.

“Hamma ina wuni.”

Ta faɗi bayan Hajja ta amsa sallamar Abdulƙadir ɗin, kai kawai ya ɗan ɗaga wa Zainab ɗin da ta miƙe ta bar musu falon. In da ta tashi Abdulƙadir ya koma ya zauna, yana dafe kan shi cikin hannuwan shi don ya rasa abinda zai ce. Kallon shi Hajja ta yi, tunda ya shigo tagan shi a firgice, kamar ba Abdulƙadir ɗin ta ba, kamar ba sojan gidanta ba, cikin kwanaki bakwai gaba ɗaya ya fita hayyacin shi. Ba zata ce auren soyayya sukai da Alhaji Ahmad ba, asalima baifi sau biyu tagan shi kafin a tsayar da maganar auren su ba.

Ba kuma kasafai take fahimtar soyayya irin ta yaran yanzun ba, amma akan Abdulƙadir da Waheedah ta san cewa ƙaddarar data haɗa su mai girma ce, don ko ita sosai ta jinjina al’amarin sanin yadda Waheedah take da sanyin hali, shekarun da taga suna wucewa ba tare da matsala ko ɗaya daga gidan Abdulƙadir ɗin ba ya nutsar da hankalinta, ta sake jinjina ƙaddarar zamansu lokacin da ta ji ya auri Nuriyya, duk idan ta ga Waheedah a gidan sai tai ta kallonta tana mamakin yadda ta shanye wannan cin amanar.

Don ita kam ta san ba zata iya ba, da saninta ma a auren Alhaji Ahmad sai da ta kai zuciya nesa, har gobe kishin sauran matan shi kan motsa mata ba kaɗan ba, shi ya sa bata son wani abu ya sami auren ɗan nata da Waheedah, babu macen da zata iya zama da shi tana da wannan tabbacin, Nuriyyar ma ba baki tai musu ba, babu inda auren zai je ko ba na cin amana bane, saboda ta kula da yarinyar tana da ji da kai da son abin duniya.

“Abdulƙadir…”

Hajja ta kira tana ganin ya ɗago fuska yana sauke mata ƙananun idanuwan shi.

“Ka ci abinci?”

Kai ya girgiza mata, yunwar ma ya neme ta ya rasa. Miƙewa Hajja ta yi, da sauri Abdulƙadir ɗin ya ce,

“Hajja na rasa yadda zan yi…na bata haƙuri Hajja… Bansan ya zan yi ba kuma. Wallahi bazan iya rabuwa da ita ba.”

Numfashi Hajja ta sauke, tausayin shi na cika mata zuciya. Kitchen ta wuce ta zuba mishi shinkafa da miya da lettuce. Ta dawo ta miƙa mishi, karɓar plate ɗin ya yi ya ajiye akan kafet.

“Ba abinci ba Hajja… Matata…”

Numfashin Hajja ta sake saukewa

“Ka ci abincin Abdulƙadir… Zan roƙi Abbanku sai a bata haƙuri ka ji…”

Kallon Hajja yake yi.

“Za’a bata haƙuri da gaske? Abba ya ce ba zai saka baki ba fa… Hajja haka yace ya daina saka baki a lamurrana, don Allah shi ma ki ba shi haƙuri… Nikam rayuwata na cikin wani yanayi.”

Yadda ya ƙarasa maganar take ji har cikin ranta, bata taɓa ganin ɗan nata yayi laushi haka ba, da bakin shi yake kiran a ba wa Abba haƙuri yau, tura ta kai bango. Shi ya sa take jinjina wa ƙoƙarin maza, za su ɗauki shekaru suna musgunawa mace, ko a fuskarta da wahala a gane, amma rana ɗaya idan ta ware ta rama sai ka gani a fuskar shi namijin. Sai ka ji an fara bata rashin gaskiya saboda halittarta da juriya aka santa. Yanzun wanda duk zai ga Abdulƙadir ɗin sai ya tausaya mishi, da yawama za su manta cewa koma me yake faruwa da shi yanzun laifin shi ne, wasu ma za su ce me yasa Waheedah ba zata haƙura ba tun da har ya buɗe baki ya bata haƙuri.

Amma yarinyar kawai ta san abin da ta haɗiya tunda har take neman ya sauƙaƙe mata.

“Ka ci abinci Abdulƙadir, zan ma Abban naka magana.”

Kai Abdulƙadir ya jinjina mata, shi abincin ma yau ba damun shi ya yi ba. Sai da Hajja ta sake ɗauko plate ɗin ta miƙa mishi a hannun shi, cakuɗawa ya yi gaba ɗayan shi ya fara ci, taunawa yake yana haɗiyewa da wani irin nisantaccen yanayi shimfiɗe a fuskar shi.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

1 thought on “Abdulkadir | Babi Na Ashirin Da Shida”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×