Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Ashirin Da Takwas

0
(0)

<< Previous

Cikin baccin da baisan lokacin da ya ɗauke shi ba ya ji wayar shi na ruri, idanuwan shi a rufe ya lalubota, har kiran ya yanke, numfashi ya sauke yana ɗora wayar a ƙirjin shi tare da gyara kwanciya. Wani rurin ya ji wayar ta sake ɗauka, da ƙyar ya buɗe idanuwan shi yana ganin Nuriyya ce, ɗagawa ya yi ya kara a kunne ba tare da ya ce komai ba.

“Masoyi”

Ta kira ta ɗayan ɓangaren, shirun Abdulƙadir ya sake yi, sosai ta ɓata mishi rai, Waheedah ce a tunanin shi da komai shi yasa bai yi lokacinta ba har yanzun.

“Hello”

Ta sake faɗi, muryar shi can ƙasan maƙoshi cike da bacci ya ce,

“Ina jin ki.”

Ya lumshe idanuwan shi da suke mishi yaji saboda bacci.

“Na ga baka dawo ba har yanzun… Don Allah ka yi haƙuri…”

Ta ƙarasa maganar muryar ta na karyewa.

“Ina gida ni tun ɗazun.”

Cewar Abdulƙadir ɗin yana ganin rashin hankalin Nuriyya da zata yi tunanin don ta ɓata mishi rai zai tafi wani wajen, a lokaci ɗaya kuma yana ganin yadda har yanzun bata san wa take aure ba, jin ta yi shiru yasa shi faɗin,

“Kiyi bacci, sai da safe.”

Kafin ta ce wani abu ya kashe wayar shi. Bai taɓa zaton akwai ranar da matar shi zata ɓata mishi rai har ya raba shimfiɗa da ita ba, duk faɗan da zai yi da Waheedah in dai suna gida ɗaya a jikin shi take bacci, ko baya mata magana kuwa. Numfashi ya ja yana sauke shi, ƙirjin shi zafi yake sosai, tunanin Waheedah ɗin yanzun ya ƙara taso mishi da wata irin kewarta. Wayar shi ya duba yana ganin ƙarfe sha ɗaya na dare, ƙaramin tsaki ya ja, dare ma bai yi ba sosai, ga baccin gaba ɗaya ya bar idanuwan shi.

Lambar Waheedah ya kira a kashe.

“Don Allah ki kunna wayarki, ba sai kin ɗaga ba Wahee, ko ringing ɗin na ji a kunne na zan ɗan samu nutsuwa.”

Abdulƙadir ya faɗi yana sake gwada kiran wayar, a kashen dai ya sake ji, tashi zaune ya yi ya jingina bayan shi da jikin gadon. Ɗayan pillow ɗin ya ɗauka yana dora shi kan cinyar shi. Buɗe wajen text ya yi yana rasa abinda zai ce mata, ko da can kalaman shi taƙaitattu ne, balle yanzun kuma. Fasa tura mata yayi yana scrolling can sama, tsofin saƙunanta ya dinga karantawa, duk yawan da suke da shi sai ya ga sun ƙare mishi da wuri, WhatsApp ya koma yana jin daɗin yadda baya goge chat, don lokutta da dama ita take goge mishi in ta ɗauki wayar, sai ta ce yana cika waje.

Don ma ya hanata goge mishi nasu, tunda idan yana wajen da babu network su ɗin yake karantawa suna rage mishi kewarta. Lokacin da ya bi duk wani text ɗin su ya gama karantawa ƙarfe biyu saura. Duniyar yake ji ta mishi wani irin faɗi, ga kaɗaici na ban mamaki da ya lulluɓeshi, da yana jin nutsuwa sallah zai yi har gari ya waye, amma ba shi da wannan nutsuwar. Saukowa ya yi daga kan gadon ya fita daga ɗakin zuwa ɓangaren Nuriyya. Bacci ya samu tana yi hankalinta a kwance, shi yace ta yi bacci da kan shi, baisan me yasa baccin ya ɓata mishi rai ba.

‘Kin ɓata min rai, bana tare da ke shine kika yi bacci kika barni.’

Abdulƙadir ya faɗi a ran shi yana girgiza kai, banɗaki ya wuce ya watsa ruwa. A rayuwar shi baya haɗa wani da wani, hakan na cikin abinda baya so sam, ko faɗa Hajja take mishi ran shi yana ɓaci ya ji tana kwatanta shi da wani. A wajen shi Allah ya halicci mutane daban-daban mabanbanta halaye da ra’ayoyi, har kamanni ma, wanda Allah ya halitta ‘yan biyu suka zo da kamanni ɗaya, suka kwanta a ciki ɗaya ma sai ka sami halayensu daban.

Sai gashi yanzun daya fito ya tsinci kan shi da haɗa halin Nuriyya da na Waheedah a waje ɗaya yana aunawa, Waheedah ba zata taɓa bacci ta barshi ba, ko da shi ya ɓata mata rai, a yadda zata dinga kallon shi da idanuwanta kawai zaka gane babu nutsuwa a tattare da ita.

‘Na baka haƙuri fa Sadauki, kai min magana don Allah, wallahi a takure nake jina, ni bana son yin faɗa da kai.’

Kalamanta suka dawo mishi.

‘Hamma har yanzu fushi kake min? Babba da haƙuri aka san shi.’

Takan ce, duk idan ta yi amfani da Hamma to ya kwana yana mata fushi, ko tana son tambayar shi unguwa, zata ce shi fa Yayanta ne. Murmushi ya ji ya ƙwace mishi, kafin Kjirjin shi ya sake amsawa kamar zai buɗe, har zazzaɓin rashinta a kusa da shi yake ji. Sai da ya sake komawa ɓangarenta ya sako gajeran wando da singlet tukunna ya dawo ɗakin Nuriyya ɗin, baccin da take zai hana mata, tunda shi ya kasa, kuma bayajin tunanin Waheedah zai barshi ya samu.

*****

Da safe da kuyar Nuriyya ta tashi sallar Asuba, tana ta turo baki saboda baccin da ke idanuwanta, bata kwanta da wuri ba, idan ta ce dan bai dawo bane ƙarya take, kallo take yi a system ɗinta suka ɗauke wuta, bata tuna da shi ba sai da cajin system ɗin ya ƙare, kuɗi ne ta riga ta kashe, faɗa ne zai yi ya gama. Ita ko kaɗan bata ma hango zai mata faɗa akan dubu arba’in ba, yadda take ganin kuɗin shi, ya fi ƙarfin dubu arba’in, idan nashi ran ya ɓaci ita ma natan a ɓace yake.

Da ta kira ma ya ce ta yi bacci tana kashe wayar guntun tsaki ta ja ta ajiye ta kwanta, dama ko baice ba baccinta zata yi. Don tun da harya dawo daga ko ina Major ya kai shi bai mata faɗa ba wani abu ya nutsu a ranta. Bata jin akwai wani babban abu da zata yi mishi kuma da zai kai wannan, iya kacin shi faɗa, duk da faɗan na tsaya mata a rai, in ya yi ya gama shikenan. Ta kula ba shi da riƙo, da wahala ya kwana yana fushi kan abu ɗaya. Tana idar da sallah ta janyo wayarta, chajin ta ga saura goma, don ta manta ta saka sanda aka kawo wuta. Haka kawai tunanin azumi da saura kwana biyu ya diro mata, wayar Abdulƙadir ɗin da take kan drawer ɗin gado ta janyo, ta saka sunan Waheedah a ciki ta ga bai buɗe ba.

Ta san dai duk password ɗin shi baya wuce sunanta, don waccan wayar da ya sake haka password ɗin yake, har wani ɗaci-ɗaci take ji duk idan ta ɗauki wayar shi, shi yasa yanzun ta ji zuciyarta ta yi wani tsalle da tunanin ko sunanta ya saka, jikinta har ɓari yake lokacin da ta saka sunanta, sai ta ga wayar bata buɗe ba, kamar daga sama ta ji sallamar shi yana ɗorawa da,

“Me kike min da waya?”

A ɗan tsorace ta ɗaga kai tana sauke idanuwanta cikin nashi da ya ƙanƙance mata.

“Bakomai, zan duba abu ne, nama kasa buɗewa kuma.”

Gira ɗaya Abdulƙadir ya ɗaga mata don bai ga abinda ta ajiye a wayar shi da zata duba ba, hakan ta kula da shi yasa ta ɗora da faɗin,

“Hotuna zan kalla fa, wayata babu chaji, ban saka ba na manta.”

Ƙarasawa Abdulƙadir ya yi yana hawa gadon.

“Ko gaishe ni baki yi ba kike son cinye min cajin waya.”

Murmushi Nuriyya ta yi mishi tana matsawa sosai ta kama hannun shi.

“Ina kwana”

Ƙanƙance mata idanuwa Abdulƙadir ya yi.

“Waheena”

Ya faɗi yana zare hannun shi daga cikin nata ya ja ƙafafuwan shi ya hau dasu kan gadon, cike da rashin fahimta take kallon shi.

“Password ɗin”

Ya faɗi yana kwanciya ya lumshe idanuwan shi, Nuriyya ta bi shi da kallo yadda yake shirin komawa bacci kamar bai faɗa mata abinda ta ji ɗacin shi ya taso daga ƙasan zuciyarta zuwa maƙoshinta ba. Har wani hucin ɓacin rai take ji kamar kububuwa, Abdulƙadir kuwa baccin shi ya koma, yana barin Nuriyya nan zaune ranta in ya yi dubu a ɓace yake. Don kamar ba zata buɗe wayar ba, kafin ta yanke hukuncin Waheedah ba zata hanata latsa wayar Abdulƙadir ɗin ba, tunda yadda take jin mijinta ne ita ma haka take ji. Kuma tana so ta shiga messages ɗin shi har na whatsapp ta ga ko yaushe Waheedah zata dawo.

Wani malolon takaici ya sake taso mata, ganin sai ta ƙara saka wani password ɗin tukunna zata iya gani, gashi lambobi ne wannan karon, haƙura ta yi tana shiga wajen kira ta ga ko yayi magana da Waheedah.

‘Matar Sadauki’

Sunan farko da ta fara cin karo da shi a jerin wajen kiran wayar Abdulƙadir yaso wanke mata ɓacin ran da take ji, kafin ta kula da kiran fita yayi ba shigowa ba, tana kuma ganin

‘Nuri’

Daga kasa, wannan karon wani irin tsaki ne ya ƙwace mata, fita ta yi tana ƙara kula da wallpaper ɗin AbdulKadir ɗin , hoton Fajr ne da ya sa ta jin son samun nata yaron taso mata yana zuwa mata wuya, ba sosai takan yi tunanin samun ciki ba, amma duk idan ta ga giccin Fajr tana jin kamar ace yaron nata ne. Kulle wayar ta yi zata ajiye taga hoton dake fitowa idan an kulle waya ƙunshi ne, daga yatsun ta gane hannun Waheedah ne. A gefen Abdulƙadir ta ajiye wayar tana addu’ar ya mirgino ya ɗora mata nauyi screen ɗin ya samu matsala ko zai rage mata takaicin da take ciki.

Miƙewa ta yi ta cire hijabinta, kan gadon tahau daga can ƙarshe ta kwanta, banda tafasa babu abinda ranta yake, kafin ta matso tana kwanciya jikin Abdulƙadir ɗin da Waheedah take yi kamar nata ne ita kaɗai, sai dai duk yadda bacci bai wadaceta ba, ta kasa samun shi, data rufe ido hoton hannun Waheedah ke mata yawo da sunanta da take da tabbacin ita ta yi saving ɗin lambarta a haka a wayar Abdulƙadir ɗin, saboda rashin aji, ita ba zata yi haka ba da ta ɗauki wayar Abdulƙadir ɗin tana sake nata sunan zuwa

‘Matar Masoyi’

Da tunani barkatai a ranta, dukkan su suna haɗewa suka yi mata wani irin zafi lokaci yake ta tafiya, wutar da aka kawo yasa ta sakkowa daga kan gadon. Caji ta fara sakawa tukunna ta shiga wanka ta fito, gaban mudubi ta zauna ta tsara kwalliya sosai a fuskarta, bum short ta saka da wata ƙaramar riga, tana samun hula ta saka a kanta. Ta yi kyau ɗas da ita, yunwa ta fara addabarta, kitchen ta wuce ta dafa ruwan zafi a kettle ta haɗa shayi mai kaurin gaske ta duba biscuit ta ɗauko, shi ma ya kusan ƙare mata, gashi babu wasu kuɗi a hannunta, zata yi wa Abdulƙadir maganar kuɗi idan an kwana biyu, ta san ba zai hanata ba. A kitchen ɗin ta tsaya ta fara shan shayin don yunwa take ji sosai.

Takun tafiyar Abdulƙadir ɗin taji, kafin ya rungumeta ta baya.

“Yunwa nake ji Nuriyya.”

Yatsine fuska ta yi don ta san baya ganinta, muryarta ciki-ciki ta ce,

“Me zan baka Masoyi? Ni ma yunwar ce ta tashe ni… In haɗa maka shayi?”

Sake matseta Abdulƙadir ya yi yana sauke numfashi.

“Shayi da me?”

Ya tambaya.

“Da biscuit.”

Nuriyya ta amsa, tana sa Abdulƙadir ɗin sakinta ya kama hannunta yana juyo da ita, ta mishi wani irin kyau mai ban mamaki.

“Ni zaki ba shayi da biscuit Nuriyya? Na miki kama da Fajr ne?”

Shagwaɓe fuska ta yi.

“Bansan me zan baka ba wallahi, me kake son ci?”

Kafaɗu Abdulƙadir ya ɗan ɗaga mata, shi ma bai sani ba, Waheedah bata tambayar shi abinda zai ci, bashi kawai take yi.

“Ni dai ba zan ci biscuit ba, bari in yi wanka. Ki min koma menene.”

Ya ƙarasa maganar yana juyawa ya fice daga kitchen ɗin, kamar hakan Nuriyya take jira ta yi wani irin juyi tana buga ƙafarta a ƙasa, ko kaɗan wannan wahalar ce ba zata iya ba sam, a gidansu ma ba girki take ba, can da babu kuɗi, gidan Anas ma sai ranar da ta yi ra’ayi tunda in bai bata kuɗi ba, in ya ajiye ɗauka take, duk bala’in da za su yi, ko kuɗin waye. Daya daina ajiyewa kayan abincin shi take ɗiba ta siyar, akwai gidajen da ake abincin siyarwa kala-kala a unguwar, wani lokacin ma ɗanyen take kai musu, sai a dinga aiko mata dafaffe har kuɗin ta ya ƙare. Ranta a bala’in ɓace ta ƙarasa shanye shayin nata, kitchen ɗin Waheedah ta wuce tana ɗauko duka kwalin indomie ɗin da ko rabi ba’ayi amfani da shi ba.

Bata san abinda zata dafa mishi ba banda indomie ɗin, in zai ci ya ci, in ba zai ci ba kam bata san ya zata yi da shi ba ita. Wannan wahalar ko kaɗan jikinta ba zai ɗauka ba, ta san Waheedah zata dawo babu daɗewa, tunda mayyar Abdulƙadir ɗin ce bata iya nisa da shi. Tana ta kwashema Waheedah albarka a ranta tana ɗora indomie ɗin, ta duba, albasa ma bata da ita sai da ta sake komawa kitchen ɗin Waheedah ta ɗauko ta dawo. Lokacin da Abdulƙadir ya fito har ta ƙarasa ta kashe gas ɗin, ta samu plate ta juye mishi ta saka cokali mai ‘yan yatsu a ciki. Ta ɗauka zai yi magana, bai ce komai ba ya saka cokalin ya fara ci, kitchen ta koma don tayi wanke-wanke, a ƙasan ranta take jin yadda har ta fara gajiya da zaman gidan.

*****

Mami da kanta ta ce mata ta koma gidan Yassar ta huta abinta, babu wanda zai dame ta a can ɗin, don tunda ‘yan gidan suka ga tana nan sai hirar ta dawo ɓangaren Mamin. Ita kanta Waheedah ɗin tana buƙatar shirun, ta san in tana nan gidan ba zata same shi ba, duk da sosai ta ji nauyin da ƙirjinta ya yi ya mata sauƙi, musamman da aka haɗu ana ta hira, sun rage mata kaɗaicin da ta jima tana fama da shi. Sun kuma rage mata zafin zuciyar da take tare da shi, sai gab da Magriba Yassar ya zo ya ɗauke ta da ya dawo daga wajen aiki ya biyo.

Fajr ma bata ganshi ba, bata kuma bi ta kanshi ba, tunda ba baƙon waje yake ba, ballantana yana wajen Hajja inda babu wanda ya isa ko murya ya ɗaga mishi ai ba zai nemeta ba. Da suka koma ta ɗan samu ta ci abinci ɗakinta ta koma, tana sallar isha’i ta haye gado ta ci gaba da kallon fim ɗin da ya rage mata tunani ba kaɗan ba. Har sai da ta ji da ƙyar take buɗe idanuwanta sannan ta haƙura ta kwanta. Ba don ta ji kiran sallah ba, kawai sabo da tashin Asuba ɗin ne yasa tun kafin lokacinta ya ƙarasa har ta tashi. Tana gabatar da sallah Ikram ta ɗauka ta bata ta sha suka yi kwanciyarsu suna komawa bacci.

Sanda ta tashi goma ta yi, wanka ta shiga, ta fito ta ɗauki Ikram don ta yi mata itama, da kuka aka gama wankan, dama in dai kana son jin kukanta to wanka ko yunwa, kafin wani lokaci har ta shirya kanta cikin riga da zani na atamfa da ɗinkin ya zauna mata sosai, kwalliya ta yi tana saka jambaki a laɓɓanta, Ikram ta shirya tsaf tana kallon yadda kamanninta da Abdulƙadir suke ƙara fitowa.

“Ikram ki rufa min asiri mana, don Allah banda idanuwan.”

Waheedah ta faɗi tana gyara wa Ikram ɗin riga da ta ɗauka wasa take mata ta washe mata baki tana dariya, ita ma dariyar ta tsinci kanta da yi.

“Dariya kike ko? Da gaske banda idanuwan…”

Waheedah take faɗi tana jijjiga Ikram da ke dariya sosai.

“Kuma karki yi irin rigimar shi, macece ke wahala za ki sha.”

Abdulƙadir da tun daga bakin ƙofa yake jin dariyar su, hakan yasa shi murza hannun kofar yana shigowa ya tsaya yana ƙare musu kallo da murmushin da ya manta rabon da ya yi shi a fuskar shi ya ce,

“Ki daina hure wa yarinyata kunne…Fajr da ya biyo rigimarki me nace?”

Juyawa Waheedah ta yi fuskarta ɗauke da mamakin ganin Abdulƙadir ɗin, duk da ya saba shigowa waje bata ji shi ba sai dai ta ganshi, ƙare mishi kallo ta yi ya saka gajeran wando iya gwiwarshi na sojoji sai farar riga a jikin shi, ƙamshin turarukanta yake yi. Fuskar shi har lokacin da kumburi, ƙare mishi kallo ta yi kafin ta ɗauke idanuwanta daga kan shi tana janye Ikram ta matsar da ita tsakiyar gadon ita tana zama a bakin gadon, ta ɗora hannuwan ta daga gefe da gefe. A hankali Abdulƙadir yake takawa zuwa inda take, tsintar kan shi ya yi da tsugunnawa saboda Waheedah ta sunkuyar da kanta.

Hannun shi ya kai yana ɗago da haɓarta, agogon da ke ɗaure da hannun shi ta bi da kallo, shi ne kyauta ta farko da ta shiga tsakaninta da shi, duk tarin agogunan shi, wannan ɗin shi ya fi ɗaurawa fiye da ko yaushe, lokuta da yawa wanka da alwala duk da shi yakeyi, fatar duk ta ƙoƙe, in ta yi mishi magana sai ya ce agogon na da muhimmanci a wajen shi, har wani ta siya mishi, amma dai ya fi son wannan ɗin. Bama aiki yake ba, bata san me yasa yake yawo da shi ba. Abdulƙadir idanuwanta yake son gani, so yake ya ga ko da giccin tarin soyayyar da take mishi ne.

“Wahee…”

Ya kira yana wani irin sauke murya cikin yanayin da bai san zuciyar shi zata taɓa iya jin shi ba balle ta fito da shi, idanuwan nata kuwa ta saka cikin na shi, maganganun Mami na dawo mata suna saka wani abu da bata san yana kulle a ƙirjinta ba buɗewa. Komai take ji yana dawo mata kamar a lokacin yake faruwa, tana jin wasu irin hawaye da suke fitowa daga wani waje a zuciyarta da ya jima yana ciwo kafin su fara zuba kamar an buɗe su, ɗumin su ya fara ji a jikin hannun shi da yake kan haɓarta kafin ta sake sunkuyar da kanta. Da sauri Abdulƙadir ya tashi ya zauna gefenta yana kama hannunta ya juyo da ita ta fuskance shi.

“Waheedah…”

Ya kira yana jin yadda kukanta ya ƙarasa birkita mishi tunani, wani irin dana sani yana saukar mishi kamar ruwan sama, ba ita ba, yana jin zai jima a rayuwar shi bai ɗaga wa wani hannu ba a yanayin da yake jin shi. Hannu yasa yana kamo fuskarta ta ture shi tana saka nata hannun ta goge hawayen da sun ƙi daina zubowa, hannu Abdulƙadir ya sake kaiwa, kafin ya taɓa fuskarta ta sake ture shi.

“Ka ƙyale ni….ka bar ni.”

Ta faɗi cike da kashedin da Abdulƙadir bai taɓa tunanin tana da zuciyar fito da shi ba, don sanyin halinta ya yi yawa, wani kuka na sake ƙwace mata. Gyara zaman shi yayi yana ƙoƙarin saka hannuwan shi duka biyun wannan karon, ture su ta sake yi da dukkan ƙarfinta tana miƙewa, wani irin kallo take mishi da yasa shi jin kamar an watsa mishi ruwan ƙanƙara.

“Ka ƙyale ni, ka je ka taɓa fuskar Nuriyya.”

Da mamaki Abdulƙadir yake kallonta, kafin shi ma ya miƙe yana son haɗe space ɗin da ke tsakanin su, bai san abinda ya kamata ya ce mata ba, kuma lallashinta yake son yi, ta ƙi bari ya taɓa ta, gaba ɗaya komai ya cunkushe mishi.

“Don Allah ki yi haƙuri Waheedah…”

Ya faɗi yana jin shi ma gab yake da nemo kuka duk inda yake, ƙila in ya ta ga hawaye a fuskar shi sai ta gane abin da nata hawayen yake mishi, takawa ya sake yi, ta ɗago hannuwanta tana ƙoƙarin ture shi, kama hannuwan nata ya yi ya sa ƙarfi ya riƙe su.

“Karyewa kike son yi shisa za ki ture ni ko?”

Kiciniyar ƙwacewa take yi zuciyarta na wata irin tafarfasa

“Na ce ki yi haƙuri…Don Allah ki yi haƙuri, ba zan ƙara ba wallahi.”

Abdulƙadir ya ƙarasa maganar muryar shi na karyewa, har lokacin yana riƙe da hannuwan Waheedah da take kallon shi kamar tana shirin rufe shi da duka, ga hawayen da baya so sun ƙi daina zubar mata.

“I’m sorry”

Ya faɗi da harshen Turanci yana ɗorawa da faɗi cikin harshen Larabci,

“Ana Asif…”

Sosai yake kallonta, tunda yake bai san yadda haƙuri yake fitowa daga zuciya ba sai yanzun da yake a gabanta, hannunta ɗaya ya ɗago ya dora shi a kan ƙirjin shi in da zuciyar shi ke dokawa kamar zata fito waje saboda tashin hankali.

“Su kaɗai ne yarukan da nake ganewa, idan akwai wani kalar haƙurin ki faɗa min ….na ce bazan ƙara ba, idan akwai abinda na yi miki banda mari ki faɗa min duk sai in haɗa in baki haƙuri.”

Abdulƙadir yake faɗi yana jin a wannan gaɓar ko me take so shi ɗin zai yi in dai zata haƙura ba zata ƙara furta mishi kalmar ya sauƙaƙe mata auren shi ba, hannuwanta take kiciniyar ƙwacewa, sakar mata ya yi, yana kallo tasa ka bayan hannu ta goge fuskarta da har ta ƙara ja saboda kukan da take yi.

“Kin ga fuskar ki har ta kumbura, ki yi haƙuri kar kanki yayi ciwo Wahee…”

Kallon shi take, tana jin wani tuƙuƙin kishi na ban mamaki yana taso mata.

“Baka yi tunanin kaina zai yi ciwo ba ka ƙara aure ban sani ba?”

Maganar ta dirar mishi cikin kunnuwa tana ɗaukar wasu daƙiƙua kafin ta ƙarasa cikin kan shi tana rarrabuwa zuwa inda zai fahimta.

“Da kayi auren ka ban sani ba kamar na isa in hanaka, sai ka zaɓi ka ɗauki wata daya kafin ka gaya min ta text…Text!”

Waheedah ta maimaita maganar cikin gunjin kukan da ya ji ya samu wajen zama a zuciyar shi yana daskarar da shi tsaye a wajen, wannan karon ita ta taka tana haɗe space ɗin da ke tsakanin su, cikin fuska take kallon shi.

“Baka yi tunanin abin da zan ji ba ko Sadauki? Banda darajar da zan san ka yanke hukuncin da ba rayuwarka kawai zai canja ba har da tawa…. Bai isheka ba sai da ka sake nuna min duk abin da zan ji a kai ba matsalarka bane, ka faɗa min ka ƙara aure ta text!”

Wannan karon da hargowa ta ƙarasa maganar tana ture Abdulƙadir ɗin duk da ko motsi ya kasa yi, tsaye yake kamar bishiyar da ta samu dashe mai kyau, kalamanta yake ji na saukar mishi da wani irin yanayi da ba shi da kalaman ɗora su, kuka Waheedah take yi mai sauti, zuciyarta na ciwo kamar zata rabu da ƙirjinta, numfashi take ja tana fitar da shi a wahalce, sai dai kalaman take ji na tunkuɗeɗeniya da juna wajen fito mata, ta gaji da rikee su, ta gaji da riƙe komai.

“Da ka faɗa min ta text, ko kaɗan hankalin ka bai baka ka faɗa min ƙawata ka aura ba ko? Saboda kai ne, Abdulƙadir da babu wanda ya isa, darajar kowa a ƙasan taka take shi yasa baka faɗa min ba sai da ka ɗauko ta ka kawo min ita cikin gida na….ƙawata Sadauki… Ƙawata ka aura, idan ka so ka kasheni za ka iya…”

Waheedah take faɗi numfashin ta har barazanar tsayawa yake saboda kukan da take tana kuma magana a lokaci ɗaya, amma ta kasa shiru, Abdulƙadir ɗin take turewa ko motsi ya kasa yi.

“Baka yi tunanin ya zan ji ba ko? Shi yasa duk matan Kano….matan duk da suke Kano. Me yasa sai ita? Me yasa zaka sa in raba komai naka da ita?”

Ta ƙarasa maganar wannan karon kamar wadda ta sami taɓin hankali, jikinta ko ina ɓari yake da kukan da take, hannun Abdulƙadir ɗin guda ɗaya ta kamo da duka nata biyun tana ɗorawa akan ƙirjinta.

“Ka ji?”

Ta tambayeshi wasu sabbin hawayen na wanke mata fuska tana sake ware hannun shi akan ƙirjinta in da zuciyarta ke mata ciwo kamar zata faɗo, wannan karon muryarta da rauni ta fito tana kuma sauka can ƙasa.

“Tun ban san menene so ba zuciyata take doka maka, baka bani dalili ba, ban taɓa buƙatar wani dalili na son ka ba, saboda ƙaunar ka bata bani wannan zaɓin ba, don ban taɓa faɗa maka ba shi yasa baka yi tunanin ina kishin ka ba?”

Waheedah ta faɗi tana sauke hannun shi daga ƙirjinta tana saka yatsunta cikin nashi ta dumtsa.

“Duk yadda zuciyata take faɗa min yadda take son ka kasance nawa ni kaɗai, kullum sai na faɗa mata kai ba nawa bane ni kaɗai, addini bai ce ka zama nawa ni kaɗai ba, na sani Sadauki…don Allah me yasa ka haɗa ni kishi da ita? Me yasa ita? Ƙawata ce Sadauki? Ka manta kamar Amatu nake jin Nuriyya?”

Hannun shi Abdulƙadir ya zame daga cikin nata yana matsawa da baya taku biyu, kafin ya juya ya sake wani taku biyun, tsugunnawa ya yi yana neman iskar da yake ji ta mishi kaɗan kamar mai asthma haka numfashin shi yake barazana, miƙewa ya yi har lokacin iska yake nema tukunna ya tantance asalin abinda yake ji, abinda kalamanta suke mishi, bin shi Waheedah ta yi tana sake kamo hannun shi, tana jin ɗumin hawayenta wani na tunkuɗo wani kafin ta ce mishi,

“Ina za ka je?”

Kai Abdulƙadir ya girgiza mata yana son samun wadatacciyar iskar da zai iya fito da sauti kowanne iri ne, zuciyar shi yake ji kamar an sa hannu a ƙirjin shi an matse ta ana rabata da duk wani jini da yake jikinta.

“Baka duba cewar na ɗauki ido na ƙyale ka ba, sai ka dinga zuwa min da ita kamar kana son nuna min ƙawata ce ka aura, saboda ka isa, babu kuma yadda zan yi da hakan.”

Waheedah ta faɗi da wani irin nisantaccen yanayi a fuskar ta, kai Abdulƙadir ya sake girgiza mata yana so ta yi shiru ko numfashin shi zai dai-daita kan shi ya rage zafin da ya ɗauka, nata kan take girgiza mishi idanuwanta har wani yaji-yaji suke mata, tana haɗawa da jijjigawa kamar yana bacci tana so ta tashe shi.

“A gabana kake riƙe ta, tana kwanciya a jikin ka….kana so ka kashe ni tana tayaka… Zuciyata na min ciwo… Sosai zuciyata take min ciwo… Bazan iya zama da kai ba, za ka kashe ni…”

Cewar Waheedah, kafin a gajiye ta ƙarasa da,

“Ba soyayyar ka bace farko na, ba zata zamo ƙarshe na ba!”

Hannun shi ɗaya Abdulƙadir ya ɗago yana kama na Waheedah ya cire daga jikin ɗayan nashi yana dafe fuskar shi da tafukan shi, tare da jan wani irin numfashi a wahalce, ba zai tuna ranar ƙarshe da wani abu ya same shi yasa shi jin yana son ya ruga wajen Hajja ba sai yanzun. So yake ya ruga wajen ta kamar yaro ɗan shekara uku da aka ƙwacewa abin wasan shi, wata ƙila idan ya ruga Hajja ta saka hannu ta tarbe shi in zata iya ta ɗaga shi ta riƙe shi a jikinta hawaye su zubar mishi ya samu sauƙin abin da yake ji. A filin duniya, a shekarun shi da Allah ya bashi aron su daga ranar farko zuwa yanzun da yake tsaye bai yi tunanin akwai tashin hankali kalar wanda yake ciki ba.

Tun kafin ya auri Waheedah duk idan ya kalleta akwai raunin da yake tare da ita da yake saka shi jin son yi mata rumfa ya kareta daga duk wani abu da yake a ƙarƙashin ikon iyawar shi, lokacin da igiyar aure ta ɗaure su ƙarƙashin inuwa ɗaya, bai fito daga masallacin da hakan ta faru ba sai da alƙawurra masu tarin yawa, cikin su har da ƙoƙarin ganin wani abu bai cutar da ita ba, in har yana da ikon hakan. Sai dai a tsawon zaman su duk yadda ya so kareta daga hakan, bai yi tunanin kareta daga kan shi ba, bai yi tunanin shi zai iya cutar da ita fiye da kowa ba. Da za’a tambaye shi mutane uku da za su yi komai saboda shi, mutane uku da zasu sadaukar da komai don farin cikin shi, Waheedah zata zamo ta ukku bayan Hajja da Abba.

Da gaske ne ba zai ce ya buɗe zuciyar shi da soyayyarta ba, kafin ranar da Yassar ya yi mishi zancen ta, bai taɓa ko a mafarki hango aurenta ba. Amma tun kafin hakan ita ɗin ɓangare ce ta rayuwar shi, ko da bai aureta ba yana da tabbacin labarin rayuwar shi ba zai cika ba tare da ta fito a shafuka da yawa ba. Daga ranar daya aure ta ya san cewa ba ita ya fara so ba, amma ita ɗin ce duk wani abu da yake buƙata. Baya tunani mai tsayi a kan kowanne ɓangare na rayuwar shi, shi yasa bai taɓa tunanin hukuncin da ya ɗauka shi kaɗai ya shafa, shi kaɗai zai taɓa har da ita ba, kuskuren farko da ya ji ya yi a rayuwar shi. Yake kuma jin shi har cikin ƙasusuwan shi shi ne manta duniyar shi gauraye take da tata, manta cewar duk wani mataki da zai taka to ya taka shi tare da Waheedah ne, abinda duk ya taɓa shi zai taɓa ta itama, kamar yadda yake jin duk abinda ya taɓa ta shi ya taɓa. Shi yasa yanzun ciwon da take ji ya lulluɓe shi ruf.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×