Shopping Cart

Close

No products in the cart.

Abdulkadir by Lubna Sufayan

Abdulkadir | Babi Na Ashirin Da Uku

<< Previous

Yakan ji mutane na faɗin gwiwoyin su sun yi sanyi, akwai lokuta da yawa da zai ce ya taɓa jin irin yanayin, bai san asalin yadda yake ba sai yanzun da yake a bakin ƙofar gidan shi amma ya kasa shiga.

“Oh Allah na.”

Ya tsinci kan shi da faɗi ganin da gaske shi ne a tsaye bakin ƙofar gidan shi ya kasa shiga. Lumshe idanuwan shi ya yi yana buɗe su tare da sauke numfashi, duk wani sauran ƙarfi da yake jin ya rage mishi ya tattaro ya murɗa hannun ƙofar da shi. Ƙafafuwan shi da yake ji kamar itace saboda nauyin da sukai mishi ya ja yana shiga cikin gidan da yin sallamar da ta tsaya cikin maƙoshin shi. Gyaran murya ya yi yana sake yin sallama, amma duk da haka a hankali ya ji muryar shi ta fito.

Da ƙyar ya ja ƙafafuwan shi zuwa bedroom ɗin su, ko sallama sai bayan ya tura ya shiga ya yi ta. Amsawa Waheedah ta yi, tana jera kaya a wardrobe ɗin ɗakin da ke jikin bango.

“Takalma Sadauki… Saboda kai bana sallah a tsakar ɗaki sai na saka darduma, ko ina shigar min kake da takalma…”

Nan inda yake ya tsaya ya kwance igiyar takalman da suke ƙafarshi yana zame su tukunna ya ƙarasa cikin ɗakin ya zauna kan gado.

“Sannu da aiki…”

Ya furta da wani irin sanyin murya da yasa ta barin abinda take yi ta juyo tana kallon shi.

“Sadauki?”

Waheedah ta kira cike da alamun tambaya, don yanayin shi gaba ɗaya ya bata tsoro, ganin bai ɗago ba, asalima sake sukunyar da kan shi ya yi, yasa ta rufe wardrobe ɗin tana ƙarasawa ta zauna kusa da shi. Kafaɗar shi ta dafa tana faɗin,

“Lafiya? Me ya faru? Mene ne? Wani ba shi da lafiya ne a gida?”

Kai Abdulƙadir yake girgizawa da duk tambayarta, amma ya kasa ɗagowa ya sauke idanuwan shi cikin nata. A karo na farko da yake tir da gaggawa kan al’amura ba tare da tunani ba. Saboda bai taɓa tunanin zai ji abinda yake ji ɗin ba yanzun, ya rasa ƙarfin gwiwar fuskantar Waheedah ya faɗa mata ya yi aure, an ɗaura mishi aure, matsalar shi ba gaya mata da wa aka ɗaura mishi auren bace a yanzun, ta in da ma zai fara mata maganar auren. Kan shi ya ɗora a kafaɗarta yana sauke wani irin numfashi. “Waheedah….”

Ya faɗi cikin wani irin yanayi, hannunta ya kamo ya riƙe yana rasa kalaman da zai yi amfani da su. Da Hajja bata mishi fushi sai ya kirata ta zo ta taimaka mishi ta faɗa wa Waheedah ɗin, ko Yassar ma, wani dai ya fara faɗa mata don shi kam har wani zazzaɓin tashin hankali yake ji ya fara rufar mishi.

“Kana bani tsoro Sadauki… Na kasa yarda komai lafiya.”

Waheedah ta ce tana dumtsa hannun shi da yake cikin nata. Idanuwan shi ya lumshe da maganganunta yana jin komai ya yi mishi tsaye cik. Waheedah ce, Waheedahr shi. Ta ina zai fara faɗa mata ya ƙara aure ba tare da saninta ba, sai yanzun tunanin ita ya kamata ta fara sani kafin kowa ya zo mishi. Ɗagowa ya yi daga jikinta ya ja ƙafafuwan shi kan gadon yana lanƙwashe su. Numfashi ta sauke, tunda ya shigo gidan sai yanzun ya haɗa idanuwa da ita, duk da akwai wani abu da take gani tattare da yanayin fuskar shi da yasa zuciyarta yin rawa.

Fuskarta ya tallafa cikin hannuwan shi yana faɗin,

“Karki barni Waheedah, ki tabbatar min da ba za ki barni ba.” Nata hannuwan ta ɗora kan nashi da ke fuskarta.

“Don Allah ka gaya min me yake faruwa.”

Ta ƙarasa maganar idanuwanta na cikowa da hawaye don gaba ɗaya ya tsoratata.

“Wani waje mai hatsari za su sake tura min kai ko? Ka faɗa min don Allah…”

Cewar Waheedah muryarta na karyewa. Wannan na cikin ɓangaren da ta fi tsana a aikin shi, in duk aka turasu wajen da ake hatsaniya, tare da kwanciyar hankalinta yake tafiya, wayar duk da za ta ji sai gabanta ya yi wani irin faɗuwa, idan ta yi sati ɗaya bata ji shi ba, ko baccin kirki bata yi. Tana da tabbacin matan sojoji tare suke raba duk wani tashin hankali dake cikin aikin mazajen su. Mata da yawa na son auren Sojoji, ita Abdulƙadir take so, in da tana da yadda za ta yi da bai zo mata a Soja ba. Tashin hankalin da ke cikin aikin shi yana da yawa.

Kai ya girgiza mata, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Babu inda aka turani, kawai ina son jin ba za ki barni ba.”

Murmushin ƙarfin hali ta yi ba don zuciyarta ta nutsu ba, amma shi ɗin ma bata ganin nutsuwa a tattare da shi, bata so ya koma wajen aiki a haka.

“Ka taɓa ganin mata ta bar mijinta? Ina zan je nikam…ina tare da kai daga yanzun har sauran kwanakin da Allah ya ara min.”

Numfashi Abdulƙadir ya sauke yana barin kalamanta na samun wajen zama a ƙasan zuciyarshi. Ya kai mintina biyu tukunna ya saki fuskarta yana miƙewa, banɗaki ya shiga ya watsa ruwa, amma ko kaɗan bai ji wani sauƙi ba, hankalin shi yake ji ya ƙi kwanciya, ga wani ɓangare na zuciyarshi da yake azalzalar shi ya faɗa wa Waheedah ɗin kawai ya huta, amma ya kasa samun ƙarfin gwiwar faɗa mata, bai san ta in da zai fara ba.

Kwanciya suka yi, Waheedah na jikin shi, ko kaɗan bacci ya ƙaurace wa idanuwan shi, ya rasa abinda yake mishi daɗi a duniya, ƙarfe huɗu ya miƙe ya ƙara yin wanka, shi ya haɗa kayanshi, ya rasa ƙarfin zuciyar tashin Waheedah ɗin, kai kawon da yake yi da motsin shi da ya yi yawa shi ya tasheta. Fuskarta kawai ta wanke ta yi brush ta wuce kitchen tana fara fere dankalin turawa, iya wanda Abdulƙadir ɗin zai ci ta soya. Kafin biyar har ta gama komai ya ci, tana kula da yadda yake komai da wani irin sanyi da yake taɓa mata zuciya.

Kafin asuba yake fita dama, Yassar ne yake zuwa ya sauke shi a tasha. Amma yau kwata-kwata Abdulƙadir ɗin bai tsammaci zai zo ba, har sai da ya ji ƙarar shigowar mota tukunna. Jakar shi ya rataya Waheedah ra raka shi har bakin ƙofa, ta kasa sabawa har yanzun, duk ranar da zai tafi sai ta yi kuka. Yanzun ma idanuwan ta cike suke da hawaye, muryarta na rawa ta ce,

“Allah ya tsare min kai a duk inda za ka shiga. Ka kula da kanka don Allah…”
Kai Abdulƙadir ɗin ya ɗaga mata yana rungumeta a jikin shi, saman kanta ya sumbata da gefen fuskarta, tukunna ya ɗago ta daga jikin shi.

“Zan yi ƙoƙari in dawo wata na gaba in shaa Allah. Ki kula mon da kanku…”

Sake rungumeshi ta yi tana jin kamar kar ya tafi. Da ƙyar ta iya raba jikinta da nashi, ta sa hannunta ta share ƙwallar da ta taru mata. Shi kanshi yana jin barin nata, da son samun shi ne duk inda zai je da ita zai tafi. Amma ya fahimce ta da ta faɗa mishi Fajr na buƙatar samun ilimin addini mai inganci, zaman Lagos ba nata bane da yara, ta fi so ta natsu waje ɗaya. Shi yasa ma ya dawo da ita Kanon, tun da shi ma wani lokaci aiki na ɗauke shi na watanni, duk in da ya kai ta in hakan ya faru ita kaɗai za ta zauna. Gara a gida in da ya san tana zagaye da ‘yan uwa.

Sai da ya sake sumbatarta tukunna ya fice daga gidan yana jin yau ba wani ɓangaren shi ya bari ba, har da wani irin nauyi mai girman gaske da rashin gaya mata maganar auren shi, tunda ta tashi yake motsa bakin shi, kalamai ne suka ƙi fitowa. Abba ya kamata ya tambaya ta inda zai fara tunda shi ya yi hakan har sau uku. Zai fi kowa sanin kalaman da ya dace ya yi amfani da su, amma Abba fushi yake mishi, tun da bai kira shi yau ya mishi Allah ya tsare ba.

Wajen motar Yassar ɗin ya ƙarasa ya buɗe ya shiga yana faɗin,

“Hamma ina kwana…”

In da yake Yassar bai kalla ba ya ja motar yana fita daga gidan. Numfashi Abdulƙadir ya sauke.

“Kai ma fushin kake yi kenan har yau… Ni ban yi fushi ba Hamma kai ne kake yi… Ok.”

Abdulƙadir ya ƙarasa maganar yana sauke wani numfashin.

“Da Kawu Ali muka je jiya… An ɗaura auren tun jiya… Ban faɗa wa Waheedah ba, Hamma na kasa faɗa mata, tunanin bai zo min ba sam sai bayan an ɗaura auren. Ya kamata in faɗa mata…”

Katse shi Yassar ya yi da cewa,

“Wallahi, Wallahi idan ka ci gaba da magana zan saukeka ka nemi abinda zai kaika tasha ko ka taka da ƙafa bai dame ni ba. Allah kaɗai ya san yadda na kai zuciyata nesa na fito… Ka yi abinda kake so, wannan matsalarka ce, tun jiya ka riga da ka nuna min banda matsala da aurenka. Kabar shi a haka kawai, bana son jin duk wani abu da ya shafi tsakanin ka da Nuriyya, yanzun, anjima, gobe, kai har iya zaman rayuwar aurenku idan kana son zaman lafiya da ni ba za ka kawo min zancen ta ba.”

Muryar Yassar ɗin ta tabbatar wa da Abdulƙadir yana nufin dukkan kalaman da ya faɗa, daga zuciyarshi ya yi maganar. A karo na farko da ya ji baya son ƙure haƙurin Yassar ɗin. Shiru ya yi, yana ƙara jin komai ya haɗe mishi waje ɗaya. Wayarshi ya laluba yana ganin text din Nuriyya. Mayar da ita ya yi ya ajiye, ita ma bai san me zai ce mata ɗin ba, bai san me zai ce wa kowa ba. A bakin tashar unguwa uku Yassar ya sauke Abdulƙadir ɗin yana faɗin,

“Allah ya tsare…”

Ya ja motar shi ya wuce, da gaske fushi Yassar yake mishi, don yakan samu waje ya yi parking, baya tafiya sai ya ga Abdulƙadir din ya shiga mota suna shirin tashi tukunna. Wani irin numfashi Abdulƙadir ya ja yana fitar da shi a wahalce, zai yi ƙarya idan ya ce ranshi bai sosu ba, amma Waheedah ta danne duk wani abu da yake ji yau. Zai bi takan sauran al’amura idan ya samu hanyar faɗa mata ya ƙara aure.

*****

In da Baba ya fita ya barta, nan ya dawo ya sameta, ba don bata so ta tashin ba, sai don tanajin tsoron tashi ta farka daga mafarkin da take yi na cewar Abdulƙadir ya zo neman aurenta wajen Baba. Magana ce da take jin ta kamar almara. Sallamar da Baba ya yi yana kiran Mama ya katse mata tunanin da take yi, duk da hakan bai sa ta daina jinta kamar a mafarki ba. Mama ta fito tana kallon Baba da farin cikin da ke fuskar shi.

“Auren Nuriyya aka ɗaura yanzun a masallaci.”

Cike da mamaki Mama take kallon Baba, ta san kullum zancen shi baya wuce na Nuriyyar duk sa’adda za su keɓe, amma bai mata zancen ya samo mata miji ko kuma akwai wanda ya same shi da maganar aurenta ba.

“Ban fahimta ba, aure fa ka ce Baban Nuriyya…”

Kai Baba ya jinjina mata.

“Fitar da na yi ðazun da maganar suka zo, to a shirye suke ashe.”

Har lokacin da mamaki a fuskar Mama ta ce,

“Duk da a shirye suke, kuma ba auren farko bane abin da mamaki, ba don baya faruwa ba har a auren budurwar, amma gaggawa na daga shaiɗan fa, wanene yaron? A musulunce ya kamata a yi bincike kafin a ɗaura.”

Murmushi Baba ya yi.

“Na sani, nima na yi tunanin, amma ganin ɗan gidan Alhaji Ahmad ne shi yasa ma ban ƙi ba.”

Da wani sabon mamakin ƙarara a fuskar Mama take kallon Baba.

“Ɗan gidan Alhaji Ahmad kuma? Wanne daga ciki?”

Gyaran murya Baba ya yi tukunna ya ce,

“Abdulƙadir.”

Wannan karon da tashin hankali bayyananne Mama take kallon shi, cike da yanayin da yasa yajie gabanshi ya faɗi.

“Lafiya kuwa? Me ya faru?”

Kai Mama take girgizawa

“Abdulƙadir na ji ka ce,

Abdulƙadir ɗan gidan Alhaji Ahmad.”

Da sauri Baba yake jinjina mata kai.

“Eh shi na ce.”

Bango Mama ta laluba tana samun kujera ta katako ta zauna akai tana wani irin mayar da numfashi tare da faɗin,

“Nuriyya me kika yi? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…”

Sosai Baba yake kallon Mama.

“Ki min bayani yadda zan gane… Me yake faruwa wai.”

Kai Mama ta ɗaga tana kallon Baba da idanuwan da suke cike da hawaye, ko da faɗa mishi ta yi ba lallai bane ya fahimta, abu ne da ‘ya mace kawai za ta fahimci ciwon shi, don ita zuciyarta wani irin zugi take mata, bata jin za ta ɗauki abinda akai ma Waheedah ɗin, bata san hawayen ta sun zubo ba sai da ta ji su kan kuncinta, muryarta na sarƙewa ta ce,

“Abdulƙadir ɗin ne baka sani ba? Baban Nuriyya Abdulƙadir ɗin ne baka gane ba kafin ka biyewa son zuciyar ‘yarka ka wakilci ɗaurin auren nan ko me?”

Ƙafafuwan shi Baba ya ji sun yi sanyi, tsugunnawa ya yi, yasan matarshi farin sani, a tsawon zamansu, abinda zai sa ta zubar ƙwalla babba ne.

“Maryama na kasa fahimtar ki, ki min magana yadda zan gane, kaina ya ɗaure.”

Wani irin kallo Mama take mishi da duk ya ƙara dagula mishi lissafi.

“Ka san yana da aure ko?”

Kai Baba ya jinjina yana kallonta cikin ƙaguwa da jin sauran zancen.

“Kana so ka ce min baka san wacece matar shi ba?”

Kai Baba yake girgiza mata, zai iya tuna lokacin da akai auren Abdulƙadir ɗin, su uku ne ko fiye da haka aka ɗaura wa aure ranar in zai tuna, don a makare ya je, ko cikin masallacin bai samu shiga ba saboda cikowar mutane, ya tsaya ne har Alhaji Ahmad ya fito ya yi mishi Allah yasa alkhairi ya wuce. Wani irin ɗaci Mama take ji har ƙasan zuciyarta, bata shiga harkar Nuriyya ne saboda bata son rainin yarinyar, shi yasa a lokuta da dama take binta da ido, ta san tana da halaye marasa kyau, amma bata taɓa zaton ko za ta nunawa kowa zai faɗa kan Waheedah ba.

“Amma kasan Waheedah ai.”

Kan dai Baba ya sake ɗaga mata.

“Ya za ki ce na san Waheedah… Waheedah fa.”

Baba ya maimaita, yarinyar da aminiyar ‘yar shi ce, ƙaunar da ke tsakaninta da Nuriyyar ta ƙara ƙarfin zumuncin shi da Alhaji Ahmad ɗin har yake samun alkhairai da dama daga shi har ‘yar tashi. Hankali da nutsuwar yarinyar yasa duk shekarun shi yana ganin girmanta ba kaɗan ba. Kuma ko da Nuriyya ta yi aure duk idan Waheedah ta zo gida sai ta biyo ta gaishe da su ko baya nan, yakan dawo ya samu saƙon abin alkhairin da ta kawo musu.

“Hmm…”

Mama ta faɗi zuciyarta kamar za ta baro ƙirjinta, sai da ta haɗiye wani abu da ya yi mata tsaye a maƙoshi tukunna ta ce,

“Mijinta ne ka aura wa ‘yarka.”

Cikin tashin hankali Baba yake kallon Mama, yana son ta ce mishi abin da ya ji ba gaskiya bane ba. Ya san Waheedah ɗaya daga cikin yaran Alhaji Ahmad ta aura, amma har ga Allah ba zai ce wanne bane a cikinsu, kuma bai taɓa kawo wa ranshi Abdulƙadir ɗin bane ba, tunda da kan shi ya zo neman auren Nuriyyar, kuma ita ma Nuriyyar ta sani, ko a mugun mafarki kuma bai hango cewar za su haɗu su biyun suyie wannan cin amanar da addini bai haramta ba, amma kunya da kara ta haramtashi ta kowacce fuska.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”

Baba yake faɗi yana maimaitawa, idan hankalin shi ya yi dubu gaba ɗaya ya gama tashi. Ya rasa abinda zai ce, miƙewa Mama ta yi tana ƙara share ƙwalla kafin ta ce,

“Bansan abin da kikayie ba Nuriyya, ban san da idon da za ki kalli Waheedah a matsayin kishiya bayan duk halaccin da ta yi miki da zumuncin da ke tsakanin ku ba, wallahi ban sani ba. Ni kam na san ba zan iya kallon idanuwan yarinyar nan ba…. Duk da ina son ta san ba da sa hannuna kikai mata wannan cin amanar ba.”

Mama ta ƙarashe maganar tana barin wajen, Baba kuwa har lokacin ya kasa magana, hannu yasa cikin aljihunshi ya zaro sadakin Nuriyya da tunda aka fara maganar kanta yake a ƙasa, hawaye kawai suke zubar mata ba don za ta iya cewa ga asalin dalilin zubar tasu ba. Duk da ta daina jin duk wata magana da ta biyo bayan an ɗaura aurenta da Abdulƙadir, sai yanzun da ta bi kuɗin da Baba ya ajiye mata da kallo.

“Wallahi da na san mijin Waheedah ne sai dai ku nemi wanda zai ɗaura muku auren nan Nuriyya… Ban san me kika yi ba, daga ke har shi, ban kuma san dalilinku na yin abinda kuka yi ba. Amma in kun yi da son zuciya amana ba za ta taɓa barinku ba.”

Baba ya faɗi yana tashi shi ma. Ɗakin shi ya wuce yana jinjina al’amarin da kuma ɗaukar da Waheedah za ta yi musu ta mutanen da basu san darajar zaman tare da girman alkhairi ba, kuma ba zai ga laifinta ba. Da gaske ne gaggawa a komai daga shaiɗan take, yadda ya ƙagu ya rabu da Nuriyya yasa shi amincewa auren ba tare da tunanin komai ba. A karo na farko da ya bi son zuciyarshi gashi tun ba a je ko ina ba ya fara da na sani. Nuriyya kuwa kuɗin ta ɗauka tana komawa ɗaki ta kwanta, har lokacin bata daina jinta kamar a mafarki ba.

Wayarta ta ɗauko, duk da tana shakkar ta kiran Abdulƙadir ɗin, text ta tura mishi.

‘Na gode Masoyi, duk da na kasa yarda na zama matarka, wallahi ina jina kamar a mafarki.’

Sai da ta ga saƙon ya shiga tukunna ta sauke wayar kan ƙirjinta tana jin wani irin nishaɗi da bata taɓa ji ba a rayuwarta yana lulluɓeta, kafin bacci ya kwasheta cike da mafarkin rayuwar da za ta yi a matsayin matar Abdulƙadir.

*****

Komai bai sake haɗe mishi waje ɗaya ba sai bayan komawar shi Lagos. Duk wani wanda yake sama da shi a gidansu sai da ya kira ya yi mishi tas kan maganar auren, gaba ɗaya babu wanda ko Allah yasa alkhairi ya yi mishi, ya manta rabon da ya yi kwanaki da ɓacin rai haka. Har ƙannen nashi ma Zahra sai da ta yi mishi text.

‘Hamma baka kyauta mana ba, za ka zage ni na sani, amman bai dame ni ba wallahi. Abinda ka yi baka kyauta ba.’

Ya kuwa kira ɗin ya sauke mata masifa kamar zai cinyeta, kukan ta da ya ishe shi ne yasa shi kashe wayar shi, dama wanda zai huce akan shi yake nema. Gaba ɗaya ya rasa yadda zai yi ko in da zai saka ranshi ya ji sanyi, ga Waheedah duk waya ko video call ɗin da za su yi sai ya ga ta ƙara mishi wani irin kwarjini da ko maganar kirki sai ya yi da gaske yake iya haɗa ta balle har ya yi mata zancen auren. Nuriyya ma kullum suna waya a gajarce, a satika biyun da yayi a Lagos doguwar waya ɗaya suka yi, shi ma bayan ya kira Anty Talatu da tunda yake a rayuwarshi bai taɓa tunanin akwai ranar da zai buƙaci wani abu daga wajenta ba.

Amma babu yadda zai yi, babu wanda zai tambaya tun da duka ‘yan gidansu ba sa magana da shi don ya ƙara aure, ita ce ta fara zuwa kan shi. Ko ita ɗin ma mamaki ne bayyane a muryarta da ta ɗaga wayar, suka gaisa tana ɗorawa da,

“Lafiya dai ko AbdulKadi? Kowa lafiyar shi ƙalau?”

Kai ya ɗaga kamar tana ganin shi.

“Lafiya ƙalau Anty, zan tambayeki ne dama.”

Yana jin sauke numfashin da ta yi kafin ya ɗora da,

“Idan ka auri bazawara za ka yi akwatuna duka ko?”

Dariya Anty ta yi daga ɗayan ɓangaren.

“In kana da halin hakan, ai kyautatawa ce, amma ba kowa yake yi ba gaskiya. Za ka iya magana da ita ka ji, wasu sunfi son a basu kuɗin ma akan a sai musu kayan, kai ma kuma zai fi maka sauƙi.”

Jinjina kai Abdulƙadir ya yi, don bai fahimci maganar Kawu Ali kan lefen ba, ita kuma Nuriyya bata yi mishi zancen ba. Shi yasa ya kira Antyn don ya ji in sai yayi ne sai ya san yadda zai yi.

“Kamar nawa zai isa?”

Ya tambaya.

“Gaskiya ba zan ce ba, daga dubu ɗari in kana da hali har ɗari biyu ma, ko ƙasa da hakan. Iya aljihunka iya abin da za ka yi.”

Shiru Abdulƙadir ya yi.

“Idan na ce banda dubu ɗari biyu na yi ƙarya, amma akwai hidindimu a gabana ni kam, matata na da ciki.”

‘Yar dariya Anty ta yi.

“Baka yi tunanin akwai wata hidima a gabanka ba kake shirin ƙara aure, na ɗauka halin naku na maza ne ya motsa ai, aljihunka ka ji a cike da kuɗin da baka san yadda za ka yi da shi ba sai ƙarin aure…”

Ɗan murmushi Abdulƙadir ya yi.

“Na san ba za mu gama wayar nan lafiya ba Anty… Dole sai kin faɗa min maganar da zan ji dama ban kira ba.”

Dariya Anty ta yi sosai.

“Allah ya shirya mana halinka Abdulƙadir…”

Sallama ya yi mata tare da godiya kafin ya kashe wayar. Da gaske yake da yace mata hidima ce a gaban shi, akwai kuɗaɗen da yake ajiye da sai dole ce take sawa ya taɓa su, yana ajiyewa ne saboda tsaron lalura. Don sai da aka haifi Fajr tukunna yasan kula da yara ba abu bane me sauƙi. Sai ma da ya fara haƙora, ga ƙyanda. Shi yasa baya wasa da ajiye kuɗi don irin lalura haka. Yanzun kuma Waheedah na da wani cikin, yana son ta samu duk kulawar da take buƙata, asibiti me kyau da bai fi ƙarfin shi ba. Sannan ga kayan babies da ita ma kayan da zai mata da sauran hidindimu. Amma auren ma shi ya yanke hukuncin yin shi. Dole ne ya yi abinda ya dace.

Akan maganar kuɗin kayan ne suka yi doguwar waya da Nuriyya. Ya karɓi account number ɗinta ya tura mata, ta mishi maganar tarewa ya ce mata sai ya koma nan da sati biyu sai su yi maganar. Ba don ba shi da wajen da zai ajiyeta ba, sai don har zuwa lokacin bai faɗa wa Waheedah ba. Duk wayar da za su yi sai ya ji zuciyarshi ta doka, hankalin shi baya kwanciya sai ya ji tana mishi hira, gani yake kamar wani daga cikin ‘yan gidansu zai sameta ya faɗa mata. Duk da zai so hakan, za su hutar da shi, amma kuma dukkan zuciyarshi na faɗa mishi zai kyautu ya faɗa mata da kan shi. In da zai samu ƙwarin gwiwar yin hakan.

Idan ya ce ga yadda watan ya wuce mishi da sauri haka ya yi ƙarya. Bai taɓa ganin gudun kwanaki ba sai da ya ganshi yana haɗa abinda yake buƙata a ‘yar jakar shi da yammacin juma’a, don ranar zai bi motar dare ya isa Kano da safiyar asabar. Ya san yau ɗin ne ranar ƙarshe da yake da ita da zai faɗa wa Waheedah ya ƙara aure, idan bata sani yau ba sai ya je gida gobe tukunna, ba kuma ya jin zai iya kallon idanuwanta ya faɗa mata. Bashi da wannan ƙarfin halin, yanzun kuma yake sanin hakan.

Gefen gadon ɗakin yake zaune, ya miƙa hannu ya ɗauko wayar shi. Lambar Waheedah ya lalubo, basu daɗe da gama magana ba, ita tasa shi ya tashi ya haɗa kayan shi, ta ce karya taho da yunwa, ya ci wani abu. Amma abinci ne ƙarshen abin da yake ranshi. Sake kira ya yi, ta ɗaga da faɗin,

“Sadauki… Har ka shirya kayan?”

Kai ya ɗaga mata ba tare da ya ce komai ba, don a rayuwarshi ita kaɗai ce take fahimtar shirun shi, da ya yi magana da bai yi ba Waheedah takan fahimta, abin ya daina bashi mamaki.

“Menene? Shirun nan naka yana mun yawa kwana biyu. Wani abu yana damunka amman ka ƙi faɗa min ko?”

Numfashi ya tsinci kanshi da saukewa da bai san yana riƙe da shi ba. Muryarshi na rawa ya ce.

“Magana nake so in faɗa miki, ba tun yau ba, tun ana gobe zan taho, ban san ta ina zan fara bane Wahee…a karo na farko da bansan ya zan miki magana ba, ina nufin ke ce, komai faɗa miki nake ba tare da tunani ba, na kasa yanzun…. Ina so in faɗa miki har raina amma na kasa.”

Ya ƙarashe yana jin wani irin tashin hankali da bai taɓa tunani ba

“Ni ce kamar yadda kace… Akwai wani abu da za ka ɓoye min? Ka faɗa min don Allah… Mene ne?”

Kai Abdulƙadir yake girgizawa, yanayin muryarta ya ƙara sa ya ji komai ya kwance mishi.

“Ban san ya zan fara ba.”

Shiru ta ɗan yi na wasu daƙiƙu kafin ta ce,

“Sadauki kana tsoratani, ciki ne a jikina ko ka manta? Ka faɗa min don Allah.”

Wannan karon hannu yasa yana dafe kan shi, bugun zuciyarshi na ƙaruwa, sauke wayar ya yi daga kunnen shi yana kashewa. Kafin ya rasa ƙwarin gwiwar da yake ji ya buɗe shafin tura saƙo ya fara rubutu.

‘Aure na yi ana gobe zan dawo Waheedah, ban san ya zan faɗa miki ba.’

Ya tura yana jin kamar ya bi shi ya kamo, sai dai kamar auren shi ne, ya riga da ya faru, babu damar komawa baya ya canza komai, saƙon ya riga ya shiga don ya nuna mishi alama Waheedah ta samu, zufa yake ji a duk wata kafa ta jikin shi yana jiran ganin saƙonta. Da hasken wayar ya ɗauke sai ya sake taɓawa, bai san ya ɗauki mintina talatin yana jiran saƙonta ba sai da ya duba lokaci.

‘Don Allah kice wani abu Waheedah, ki ce wani abu.’

Nan ma sai da ya ƙara mintina goma yana zufar da duk iskar fankar da ke ɗakin bata kai mishi kafin ya ga wayar shi ta kawo haske. Jikin shi babu in da baya rawa ya ɗaga yana dubawa.

‘Ran daren da za ka tafi? Wata ɗaya da ya wuce kenan ko?’

Da sauri ya fara bata amsa

‘Da gaske Wahee, ki yarda dani tun ranar na so in faɗa miki, tun ranar.’

Wannan karon bata ɗauki lokaci ba ta turo mishi.

‘Karka damu. Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, bari in yi alwala na ji an fara kiran Magriba.’

Wata irin ajiyar zuciya Abdulƙadir ɗin ya sauke, kafin ya sake ganin text ɗinta.

‘Allah ya tsare ya kawo mana kai lafiya, ka dai ci abinci karka manta. Zan sa chargy an kawo wuta, saura 2%.’

Da murmushi a fuskarshi ya ce,

‘Na gode, Na gode sosai. In shaa Allah. Ki kula min da ku. Zan kira ki da na shiga mota.’

Ya sa ran amsa ko ya take, da ya ga bata turo komai ba ya miƙe yana haƙura. Wanka ya shiga ya yi ya fito ya sake kayan jikin shi tukunna ya fita masallaci. Sai da ya biya ya siya abinci ya ci, hankalin shi yake ji ya kwanta sosai. Yasan dama idan kowa bai fahimce shi ba, Waheedah za ta fahimce shi, shi yasa take da matsayin da babu wanda yake da shi a rayuwar shi. Yana dawowa jakar shi ya ɗauka ya yi addu’a a bakin ƙofa kafin ya fita ya kulle gidan yana takawa zuwa gate da zai samu ya je inda zai hau mashin zuwa tasha.

Next >>

1 thought on “Abdulkadir | Babi Na Ashirin Da Uku

Leave a Reply

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.