Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Ashirin

0
(0)

<< Previous

Mafari

Rigima ce ta saka shi biyo mota daga Lagos zuwa garin Kano, don tashi motar in ba hutun ƙarshen shekara zai zo ba, baya tahowa da ita, babu yadda Waheedah bata yi da shi akan ya biyo jirgi ba, ya ce mata ba shi da kuɗi, wata ya yi nisa, ga hidimar gida da sauran hidindimun da ke gaban shi. Sai da ta ce mishi ya biya kawai, akwai kuɗi a hannun ta, Abba ya bata kyautar kuɗi, bata yi amfani da su ba, akwai kuma kuɗin da shi ma yake bata, duk bata siyi komai ba, amma ya ƙi. Jikin shi babu inda baya ciwo, ga rashin wadataccen bacci tunda motar dare ya biyo, da safe ya iso garin Kano.

Tunda Waheedah ta haɗa mishi ruwan wanka ta yi tafiyarta kitchen ta ci gaba da aikin kifin da ta fito da shi don ya huce tun da asuba, tun da ya yi ƙanƙara a fridge. Sanda ya fito daga wanka, ta ɗauko mishi riga da wando marasa nauyi, sakawa ya yi yana binta kitchen ɗin. Buɗe-buɗen kulolin duk da ya gani yake yi, ko kallon shi Waheedah bata yi ba, kifinta take gyarawa, tana jinshi ya ƙaraso inda take, ya ɗora kanshi a kafaɗarta, ta baya. Ture shi ta yi.

“Sai na saka maka ƙarnin kifi ko?”

Ƙanƙance mata idanuwanshi ya yi.

“Ni kike ta sharewa ko Wahee? Yunwa nake ji, ki bani abinci, tun jiya ban ci komai ba.”

Kwandon da ta zuba kifin a ciki ta ɗauka ta ɗora cikin wani kwano, ta saka omo ta wanke hannuwanta da sink ɗin wanke-wanken ma, tana son kifi, amma sosai ƙarnin shi yake damunta, shi yasa duk abinda zata yi amfani da shi bata iya ajiyewa, sai ta wanke. Ƙaramin towel ta ɗauka ta goge hannuwanta, sai lokacin ta kalli Abdulƙadir sosai, da ya biye mata, tun jiya da suna tare, yanzun idan ya tafi tana iya wata uku ko fiye da haka bata saka shi a idanuwanta ba, don ma manhajar Imo da ta shigo, suna video call sosai, amma ba kamar dai yana kusa da ita ba.

“Duk lokacin da na samu na ganinka yana da muhimmanci a wajena, ka min asarar kwana ɗaya saboda baka jin maganata.”

Ta ƙarasa tana hararar shi, murmushi ya yi yana faɗin,

“Kin san wa kika aura Wahee, kin sanni.”

Kai ta jinjina mishi, ita kuwa ta san shi fiye da kowa da yake da kusanci da shi, wucewa ta yi ta gaban shi tana fita daga kitchen ɗin.

“Da gaske yunwa nake ji, Allah banci komai ba.”

Wannan karon ita ta yi dariya, har mamakin yadda yake rayuwa a matsayin Soja take yi, da wajajen da ya shiga, da wanda ta san zai shiga a nan gaba. In yana bata wasu labaran, takan tambaye shi ya yake yi da abinci. Ɗan ɗaga mata kafaɗu yakan yi.

‘Tunanin ko zan sake ganinku, ko zan sake samun damar riƙe ki a jikina baya barina yin wani tunanin, Hajja kan zo mun a rai, amma tana da wasu yaran, rashina zai mata sauƙi duk idan ta kalle su, bana son barinki, tunanin yadda za ki yi yana sani jure komai, ciki har da rashin abinci ko na tsayin kwanaki nawa.’

Ranar farko da ya faɗa mata hakan, kasa magana ta yi, sake shigewa jikin shi ta yi, tana ƙoƙarin mayar da hawayen da suke cike da idanuwanta, ban da nemawa kanta sauƙin mutuwa da kariya daga azabar kabari, ta manta ranar ƙarshe da ta yi wa kanta wata addu’a, dukkan sujjadarta cike take da neman Allah ya tsare mata mijinta. Matan sojoji ne kawai za su iya fahimtar wannan fargabar da take ciki a duk ranar da baya kusa da ita, ko bata ji muryar shi ba, ko ta nemi wayarshi bata shiga ba. Zuwa yanzun za ta iya cewa sai zazzaɓi ya yi da gaske yake kwantar da ita, don sun yi wani irin sabo na ban mamaki.

Wajen cin abincin ta, sai dai ta janye kujerun ta goge, ta kakkaɓe su, in ba ranar da ta yi baƙi ba. Abdulƙadir ba so yake ta kai mishi abinci can ba, ya fi so ya zauna a kan kafet, har ya saba mata ita ma, ko baya nan kan kafet take zama ta ci abincin ta. Yanzun ma ta riga ta fito da kulolin da flask ɗin shayi. Sai da ya zauna tukunna ya ce mata,

“Ina yaro na?”

Numfashi ta sauke, tana zama ita ma.

“Hamma Yassar ya ɗauke shi tun jiya.”

Daƙuna mata fuska Abdulƙadir ya yi.

“Kin san zan zo…. Me yasa za ki bar shi ya tafi da shi? Ni zan je in ɗauko yarona.”

Bata ce mishi komai ba, dankalin da ta soya ta zuba mishi a plate, ta samu ɗan kwano da ta fito da shi ta zuba farfesun naman da ɗumamawa ta yi da safen, don tun jiya da rana ta yi ta saka a fridge. Bata san yadda Abdulƙadir yake so ta fara cewa Yassar kar ya tafi da Fajr ba. Wannan aikin sai shi, don akwai dawowar da ya yi ya je har gaban Hajja ya ɗauko yaron shi. Wani abin idan ya yi sai dai ita ta ji kunya, shi kam ko a jikin shi. Hira suke ɗan yi sama-sama har ya gama cin abincin ya miƙe, tayata kwashe kwanonin ya yi ya wanko hannun shi a kitchen ɗin, ya fito yana faɗin,

“Zanje mu gaisa da Hajja… Sai in biya in ɗauko Fajr…ko za ki raka ni?”

Kai Waheedah ta girgiza mishi.

“Aiki zan yi wallahi, don Allah karkai mun rigima Sadauki, ka ga kifi na gyara, aiki zan yi… Ka je ka dawo.”

Waheedah ta ƙarasa tana shagwaɓe mishi fuska, don ya fara ƙanƙance mata idanuwanshi cike da rigima, zai iya cewa ta ajiye kifin su je su dawo.

“Shikenan tun da ba za ki raka ni ba.”

Langaɓe kai ta yi.

“Ba ƙin rakaka na yi ba, aiki zanyi. Anjima kaɗan za ka fara kira min yunwa.”

Murmushi ya yi, ɗakinta ta wuce ta ɗauko wallet ɗin shi da wayar shi da suke ajiye kan gadonta, buɗe wallet ɗin ta yi ta ga da kuɗi a ciki, ta fito tana kawo mishi. Numfashi ya sauke, zai iya rantsewa da ya gan shi a kusa da ita yake manta yadda zai yi abubuwa da yawa. Da bata ɗauko mishi ba, ya manta wallet ɗin da wayar basa jikin shi. Har bakin ƙofa ta raka shi, tukunna ta dawo ta shiga kitchen.

*****

Da Mami kawai ya gaisa, don bai samu Hajja ba, yarinyar ƙanwarta ta haihu, tunda safe ta tafi Aminu Kano. Tunanin ya kira wayarta bai zo mishi ba, da bai sha wahala ya fito ba, ya yi kwanciyar shi yai bacci. In ya tashi sai ya zo ya ɗauki Fajr ɗin. Fitowa ya yi daga gida, yana sako ƙafarshi bakin ƙofa yana cin karo da ita, wani irin tsalle zuciyar shi ta yi daga ƙirjin shi, kafin ta koma mazauninta tana ci gaba da wani irin dokawa da yake ji har cikin kunnuwan shi.

A duk tsawon shekarun nan, bai taɓa barin kan shi ya yi tunaninta ba, saboda yasan matsayin hakan a addinin shi, ya kuma san darajar kan shi, faɗin garin Kano zai musu kaɗan da duk namijin da ya san yana mishi tunanin Waheedah. Kuma ko ba komai, shi mutum ne da baya tunani akan abin da ya wuce. Nuriyya na ɗaya daga cikin su, ganin ƙarshe da ya yi mata yana NDA ne, kuma daga lokacin sai labarin aurenta ya samu. Bai sake saka ta a idanuwan shi ba, tunaninta kuma bai sake faɗo mishi ba. Sai yanzun, duk shekarun nan kusan, ba su nuna a jikinta ba, tana nan yadda ya san ta, sai dai wata irin wayewa da ta shige ta, da sauri ya sauke idanuwan shi yana neman yafiyar Allah a cikin zuciyar shi na tsayawa da ƙare mata kallo da ya yi.

“Hamma… Ina kwana.”

Ta faɗi, muryarta na sauka kunnuwan shi da wani irin yanayi da bai taɓa tunani ba. Idanuwan shi har lokacin suna ƙasa ya amsa ta.

“Lafiya…”

A taƙaice, kamar yadda yakan yi tun da can, ita kanta Nuriyya bata yi tunanin ganin shi ba, watan aurenta shida kenan da mutuwa, ta je gidan Waheedah sosai a tsakanin, don tunda ta gama iddarta take yawo sosai da sosai. Ba za ta yi ƙarya ba, ganin kwanciyar hankalin da Waheedah take ciki a duk lokacin da takan je gidanta yana tsaya mata a rai, shi yasa ma ta kusan wata ɗaya yanzun bata taka gidan ba. Yadda Waheedah ta samu duk wani abu da take mafarkin samu na tsaya mata. Miji mai kuɗi, ga gidanta da ita kanta ɗinta, ga yaronta da take ji kamar ta sace saboda yadda yake mata kyau. Duk da bai kai hasken fatar Waheedah ɗin ba, yaron ya fi su dukkansu kyau.

Ko a wayar Waheedah ta so ganin Abdulƙadir ɗin, ta ga yadda ya koma. Haka kawai ta tsinci kanta da son sani, amma bata samu damar hakan ba, Waheedah kuma ko da wasa bata yi mata zancen shi ba, bata ga fuskar da za ta sako mata da zancen ba ita kuma. Don sosai Waheedah ta canza, ba wai ita Nuriyyar ta canza wa ba, ita ɗin ce gaba ɗaya ta canza. Don duk wani sirrin aurenta da taso ji ta kasa, tana mata kyauta kamar da, su sha labarin duniya dai, amma hirar halin da aurenta yake ciki, ko wani sirrinta sam bata ji ko ɗaya ba. Abin kuma ya tsaya mata.

Abdulƙadir ɗin take kallo, ya ƙara girma, don sai ta ganta ‘yar ƙarama a gaban shi, ya aske gashin kan shi ƙasa sosai, sai ta ga idanuwan shi kamar sun ƙara ƙanƙancewa, akwai tabbai ƙanana a fuskar shi, sai wani babban tabo da alamun ɗinki ne daga gefen haɓarshi zuwa wuyan shi, zuwa wani waje cikin rigar shi da take son ganin iya inda tabon ya tsaya. Shi kam bata ga alamar ya canza ba, don yadda ya amsa mata gaisuwa, hakan yake amsa mata tun da can, a taƙaice, cike da rashin kulawar da yake ɓata mata rai.

Gani ta yi yana shirin wucewa, da sauri ta tsinci kanta da faɗin,

“Hamma…”

Juyowa Abdulƙadir ya yi yana ƙoƙarin kar su haɗa idanuwa, zuciyarta ta ji tana dokawa.

“Aure na ya mutu, wata shida da suka wuce, aurena ya mutu…”

Ta ƙarashe tana kallon yadda a hankali ya sauke idanuwan shi cikin nata. Wannan karon kallonta yake, kallonta yake yi da canjin da kalamanta suka haifar mishi, kallonta yake yi yana jin yadda babu shamakin igiyar auren da yake tunanin ta haramta mishi hakan. Ba zai ce ga abin da ya faru ba, yana jin wani hijabi da yake tsakanin su ya yaye, yana jin abinda yake tunanin ya binne a NDA na warwarewa.

“Me yasa?”

Ya buƙata, cike da rashin fahimta Nuriyya ta ce,

“Me yasa me?”

Sai da Abdulƙadir ya haɗiye wani abu da ya tsaya mishi a wuya, tukunna ya amsa ta. “Me yasa kika faɗa min?”

Wannan karon tata zuciyar ta ji ta doka, ita kanta ba za ta ce ga asalin dalilin da yasa ta faɗa mishi ba, kawai ta ji tana so ya sani ne, ba da tunanin komai ba.

“Ina so ka sani ne kawai.”

Kai ya girgiza mata, ya raɓa ta ya wuce yana jin yadda take bin shi da idanuwa, yana kuma jin yadda da duk takun da zai yi da canjin da kalamanta suka yi mishi. Mashin ya tare zuwa gidan Yassar ɗin. Har cikin gida ya shiga, ya samu Yassar ya fita shi da Fajr ɗin, hakan yasa shi juyawa, ko zama bai yi ba, duk yadda Hauwa ta tabbatar mishi da cewar ba nisa Yassar ɗin ya yi ba. Gida kawai yake son ya tafi, wajen Waheedah ko zai daina jin abin da yake ji.

Bayan Kwana Biyu

Baccin da bata samu a kwanaki biyun da Abdulƙadir ya zo bane take ramawa, don da ƙyar ta kai Fajr makaranta, bata tashi ba sai da Azahar, masallaci ma suna raka’ar ƙarshe, a daddafe ta yo alwala ta gabatar da sallah, jin yadda jikinta ya yi nauyi har lokacin yasa ta sake watsa ruwa, Atamfa ta saka, riga da zani ta ɗaura ɗankwalin a kanta, ko mai bata shafa ba, tun da Abdulƙadir ɗin baya nan, bata ga wahalar da kanta da zata yi ba. Falo ta fito ta kunna kayan kallon ta ganin da wuta. Tunanin Abdulƙadir ɗin zai iya kiranta kowanne lokaci yasa ta tashi ta ɗauko wayarta daga ɗaki.

Text ta tura mishi.

‘Ya hanya? Allah ya tsare ya sauke ku lafiya.’

Ta ajiye wayar, duk da kallon da take yi bai hanata tunanin wanke-wanken da yake jiranta a kitchen ba. Ƙwanƙwasa kofa taji anayi.

“Shigo…”

Ta faɗi, tana tuna cewar ta rufe ƙofar da mukulli, tashi ta yi ta ƙarasa ta buɗe, murmushi na ƙwace mata ganin Nuriyya.

“Sannu da rashin kirki.”

Waheedah ta faɗi tana mayar da ƙofar ta rufe, dariya Nuriyya ta yi suna ƙarasawa suka zauna.

“Ina ta so in zo Allah…. Ban samu lokaci bane.”

Harararta Waheedah ta yi.

“Haka za ki ce dama, kin ga ma sai ki min kitso, kan ya ishe ni wallahi.”

Kai Nuriyya ta jinjina mata, suna gaisawa sosai, Nuriyyar ta ɗora da faɗin,

“Fajr ana makaranta?”

“Wallahi kam, tunda na kaishi na dawo na kwanta. Babu abinda nayi a gidan nan. Bari in yi wanke-wanke dai, me za ki ci? Akwai shayi, ko in tafasa mana taliya tunda ina da miya?”

Ɗan jim Nuriyya ta yi kafin ta ce,

“Taliyar dai, ba ma yunwa nake ji ba, ki gama aikin ki a nutse…”

Kitchen Waheedah ta wuce ta bar Nuriyya a falon. Kwanciya ta yi ta ɗauki remote ta canza tashar zuwa Arewa24, wani fim ɗin Hausa suke yi ‘Bakin Alƙalami’. Shi ta nutsar da hankalinta tana kallo, kafin ta ji wayar Waheedah ɗin na ruri kan kujerar, daga kitchen ɗin Waheedah ta ce,

“Nuriyya don Allah taimaka min da wayata, Sadauki ne ina jin…”

Miƙewa Nuriyya ta yi daga kujerar tana ɗaukar wayar, aikam shi ɗin ne, ga sunan nan a rubuce, haka kawai sai ta ji zuciyarta tana wata irin dokawa, lambar ta nutsar da hankalinta akai, komai na Abdulƙadir daban ne, lambar kanta ba mai wahala bace ba, hanyar kitchen ɗin ta nufa da wayar, ta miƙa wa Waheedah, da sauri ta dawo ta ɗauki tata wayar, gabanta ke wata irin faɗuwa lokacin da ta saka lambar Abdulƙadir ɗin a wayarta ta yi saving da ‘Hamma Abdulƙadir’.  Ta mayar da wayar cikin jakarta ta ajiye. Ta koma ta kwanta, amma yadda gabanta yake faɗuwa yasa kwata-kwata ta daina fahimtar fim ɗin.

Ko da Waheedah ta fito daga kitchen ɗin ma sai take ganin kamar za ta gane abinda ta yi, har wata zufa take ji ta daban, duk da fankar ɗakin, da ƙyar ta iya yi wa Waheedah kitson, suka ci abinci, tana yin sallar la’asar ta ce wucewa za ta yi. Tana kai Magriba ma wasu lokuttan, musamman in ta zo Fajr na makaranta tunda wuni yake, haɗe makarantar tasu take da Islamiyya. Sai ta ce sai ta gan shi za ta wuce, amma yau ɗin ba a nutse take ba. Biscuit kala-kala da cake ɗin da matar Yassar ta kawo mata lodi guda ta ɗibarwa Nuriyyan, ta bata dubu biyu, don ta san za ta kwana biyu bata dawo ba.

Yanayin ƙaddarar Nuriyyan na tsaya mata a rai, duk da bata tambayeta me ya faru ba, ta san da laifin Nuriyyar a mutuwar aurenta, amma Waheedah na cikin mutanen da basa yanke wa kowa hukunci ba tare da sanin asalin abinda ya faru ba. Tana mata fatan alkhairi a ko da yaushe, don har yanzun bata da wata ƙawar da ta fi ta, sai dai ‘yan uwanta. Sukan kwana biyu basu haɗu ba yanzun kuma, Amatu ma aure ya kai ta Gombe. Dukkan su aure ya yi nisa da su, sai wani abin ya faru akan haɗu gaba ɗaya. Sai dai waya ko da yaushe da sukan yi.

A nan falon ta yi zamanta, tana jiran lokacin ɗauko Fajr daga makaranta ya yi ta je ta taho da shi. Wani indiyan fim ta nutsu tana kallo.

Lagos

Wanka ya yi, ya kwanta, daga shi sai singlet da gajeran wando, ya ja bargo ya rufe jikin shi, saboda ruwan da ake yi, garin ya yi sanyi, kuma yana jin ƙiwar tashi ya kashe fanka, lokaci irin wannan yakan yi kewar Waheedah kamar ba jiya suka rabu ba, da tana nan za ta kashe mishi fanka, har bargon ma ita za ta rufa mishi, ko bacci yake za ta lulluɓe shi, yadda ake take gane yana jin sanyi na ba shi mamaki, amma Waheedah ce, takan gane yana buƙatar abubuwa da yawa a lokutan da shi kan shi bai gane yana buƙatar ba.

Hoton shi ya ɗauka yana rufe da bargon ya tura mata a whatsapp, yana shiga tana hawa ta buɗe, ita ma nata ta turo mishi da Fajr da ke bacci a kusa da ita, tare da rubuta,

“Muna ta kewarka.”

Daga ƙasan hoton, hira suke yi sosai, don in yana hira da ita baya ma fita daga kan chat ɗin ballantana ya duba ko wani ya mishi magana, Waheedah ma ta koya mishi chatting, kuma da ita kaɗai yakan yi hira mai tsayi. Sai ƙannen shi in sun gaishe da shi yakan amsa, suma ba kullum ba. Message na iya kwana biyu bai ko buɗe ba. Ba don ya gaji da hira da Waheedah ɗin ba, tun da kullum bata rasa labarin da za ta ba shi, ya ce mata ta kwanta, don yasan za ta tashi da sassafe ta shirya Fajr makaranta. Sai da ya ga ta sauka, tukunna, bai kai da kashe datar ba kiranta ya shigo. Da murmushi ya ɗaga ya kara wayar a kunnen shi.

“Bakya jin magana ko? Bance ki ajiye wayar ki kwanta ba.”

Yana jin dariyarta ta ɗayan ɓangaren.

“Zan ji muryarka ne fa, yanzun zan kwanta.”

Har lokacin da murmushi a fuskar shi.

“Ke kaɗai nake sawa abu, sai kin ga dama Waheedah, in faɗa miki magana ki yi kamar baki jini ba…”

Dariyar ta sake yi.

“Yanzun zan kwanta Allah. Sai da safe. Allah ya tsare mana kai.”

Amsawa ya yi da,

“Amin. Ki kula da ku.”

Tukunna ya kashe wayar, ya sauketa daga kunnen shi, yana duba lokaci, karfe sha ɗaya har da rabi, saƙo ya gani a saman na Waheedah da shi ne ƙarshe.

‘Hamma…’

Dubawa yayi da mamakin ko waye, ba zai wuce Zahra ba, don ita ce sarkin sake lamba, kullum cikin yarda waya take. Buɗewa ya yi yana ganin tana online, da sauri ya amsa.

‘Na’am…”

Fara typing yayi da shirin tambayarta ko lafiya? In ya ji lafiya ne sai ya sauke mata faɗa da tambayar abinda take yi online da daren nan. Hannuwan shi ya ji sun daina rubutun da yake yi ganin saƙon da ya shigo.

‘Nuriyya ce.’

Daƙuna fuska ya yi, sannan ya ƙanƙance idanuwan shi, ba don bai gane ta ba, sai don mamakin dalilin da yasa take mishi magana da tsakiyar dare haka. Tun ranar da ya ganta tana manne da ranshi kamar yadda takan yi tun lokacin da take budurwa, lokacin farko da zuciyar shi ta fara doka mata, ba baƙon yanayi bane a wajen shi, shi yasa bai dame shi ba balle ya hana shi hidindimun shi.

‘Ok.’

Ya rubuta mata, ya ja data ɗin shi ya kashe, ya ajiye wayar a gefe ya gyara kwanciyar shi, addu’ar bacci ya yi ya lumshe idanuwan shi, Nuriyya manne da zuciyar shi, bai san me zai ce mata ba shi yasa ya kashe data ɗin shi, bai ma san ko yana so ya yi hira da ita ɗin ba. In ya riga ya gama waya da Waheedah baya son jin muryar kowa kuma, ko yin magana da wani. Don ko Yassar ya kira shi yakan ɗaga da faɗin,

‘Na fa yiwa Matata sallama Hamma, kana kirana kuma, na gama jin muryarta yanzun ina jin taka.’

Yassar yakan amsa shi da,

‘Wallahi da bani da aure, kai zaka sa dole in fara nema, sai kace kai kaɗai ne me mata a duniya.’

Dariya kawai Abdulƙadir zai yi, amma har ranshi baya so kowa ya yi mishi magana in ya yi sallama da Waheedah. Bai ƙi ta zamo farko da ƙarshen wadda zai wa magana a duk ranakun shi ba. Da wannan tunanin a ran shi bacci mai nutsuwa ya ɗauke shi.

*****

Wayarta take kallo, ta tsammaci ya tambayeta in da ta samu lambar shi, tun jiya ta kasa samun sukuni, so take yi ta kirashi, amma ta kasa samun ƙarfin gwiwar yin hakan. Har ranta tana shakkar shi, kwarjinin da yake mata da, ganin shi da ta yi ya ninku. Bata san me take tsammanin zai faru ba. Amma tana son mishi magana ɗin, sai yanzun da ta kasa bacci, da tunanin shi fal ranta tukunna ta yanke hukuncin ta duba shi a whatsapp.

Hoton dake kan display picture ɗin shi ya fara saka zuciyarta ɗaukar wani irin zafi, hoton shi ne, sai hannun Waheedah da yake riƙe cikin nashi, yatsunsu lanƙwashe cikin na juna, Abdulƙadir ɗin ya ɗago hannuwan ya sumbata. Wani irin abu take ji, in da tana da ƙarfin ikon sake hoton, ta cire hannun Waheedah ta saka nata a ciki, za ta yi hakan, tun ranar farko da ta je gidan Waheedah take jin son samun abinda duk take dashi. Dp ɗin Abdulƙadir ya saka shi cikin lissafin abinda take son samu iri ɗaya da Waheedah.

‘Ok.’

Ɗin shi take ta kallo ta kasa yarda da cewar bai ma damu da ita ɗin bace, balle har ya tambayi inda ta samu lambarshi.

“Zan sa ka damu da ni Hamma Abdulƙadir… Wallahi na fi ƙarfin wulaƙancin ka…”

Ta fadi a fili, kalaman na zauna mata, tanajin yadda take a shirye da ta yi komai in dai za ta same shi, kwanciyar hankalin da Waheedah take ciki, shigar alfarmar da take yi da komai nata, take son samun irin shi. Kwanciya ta yi tana lumshe idanuwanta, muryar Anas na dawo mata.

‘Saki kike so ko Nuriyya? Tunda na aureki hankalina bai kwanta ba, ke kanki ba ki bari naki ya kwanta ba, balle ki bari nawa ya kwanta, saboda kina hangen abin duniya. Ba baki na miki ba, amma wallahi ba za ki taɓa samun kwanciyar hankali ba, alhakina ba zai barki ki samun wannan nutsuwar ba. Ba wai zan sake ki don kin isa bane, zan sake ki saboda ina buƙatar samun kwanciyar hankali…’

Tashi zaune ta yi tana girgiza kanta cike da son ɓatar da tunanin Anas daga ranta, ƙarya yake ya ce alhakin shi zai kamata. Ta yarda farkon auren su ta bashi wahala, bala’in yau daban na gobe daban, in da take so tafiya take ko ya barta ko bai barta ba, abinci kuwa sai dai inya dawo ya dafa, har gyaran gidan shi yake yi. Amma ta ƙarfi da yaji Anas ya karɓi mutuncinta, a cewar shi abin nata bana ƙare bane ba. Daga lokacin kuma tashin hankalinta ya fara ita ma, don Anas daina raga mata ya yi, sai ya daina kawo abinci, duk idan ta fita ba tare da ya barta ba, sai ta kwana ta yini da baƙar yunwa, komin zagin da za ta yi mishi.

Haƙƙin shi in ya tashi karɓa baya tausaya mata, ƙarfi yake nuna mata. A haka ta samu shigar cikin farko, a shekarar auren su, lokacin ya fara nuna mata wani irin gata da soyayya, kome tace tana so sai ya yi mata, amma ba wannan bane a gabanta, da rana ɗaya bata taɓa jin soyayyar Anas ba, kullum tsanar shi kuma gaba take yi a zuciyarta. Kuɗin da ta dinga karɓa a wajen shi sanadin cikin, da su ta yi amfani aka cire mata shi. Don ba za ta haɗa jini da Anas ba, balle yara su sa ta zama da shi.

Idan ance mata za ta yi shekara huɗu da Anas za ta ƙaryata, ko shekara bata hango ba, ciki biyar ta zubar a gidan shi, na ƙarshen ne ya gane, kuma shi ne ya yi sanadin sakin da ya yi mata. Har gida yazo ya samu Baba ya bashi haƙuri, ya kuma yi mishi bayanin duk abin da ya faru. Ta ga tashin hankalin da bata taɓa tunani ba, don Baba cewa ya yi sai ta koma ko ya tsine mata, kafin ya ji saki Uku Anas ɗin ya yi i mata. Ko kaɗan Baba bai ji daɗin zancen ba, Hausawa kan ce ka haifi yaro ba ka haifi halin shi ba. Haka Nuriyya ta zame mishi.

Ba don yana duba abubuwa da yawa da korar Nuriyya daga gidan zai haifar mata da shi ba, da babu dalilin da zai sa ta ci gaba da zamar mishi a gida. Amma duniya ta nuna mishi ta zaɓa fiye da darajtasu da mijin aurenta, idanuwa su Baba ya ɗauka ya saka ma Nuriyya, ya barta da duniyar da yake da tabbaci za ta gyara mata zama. Mama dama ba darajar kirki take da shi a idanuwan Nuriyyar ba tun da can, balle yanzun da take ganinta dai-dai da kowa. Ganin babu mai mata faɗa yasa take duk abinda taga dama. Kullum yawon gidajen ƙawayenta tun na FCE da yawancin su ‘yan duniya ne na asali.

Maza kuwa kala-kala take tarawa a ƙofar gidan su. Yanzun ne take jin lokaci ya yi da za ta tsayar da hankalinta kan ƙudirinta. Don duk a cikin masu zuwa mata da maganar aure bayan ta ƙare iddarta, talakawa ne, masu kuɗin da maganar banza sukan zo mata. Ita kuwa duk fitsararta bata kai nan ba, aure take son yi, soyayya bata gabanta, in da za ta huta ta yi abinda take so ne muradinta. Ta kuma hango hakan akan Abdulƙadir. Komawa ta yi ta kwanta, ta ɗauki wayar, duk da zuciyarta da take dokawa bai hana ta tura mishi text ba.

‘Na ga ka sauka, har ka yi bacci? Sai da safe Hamma. Allah ya tsare mana kai.’

Ta saka wayar a caji ko da za su kawo wuta cikin dare tukunna ta kwanta. Juye-juye take, bacci ya ƙaurace mata, tunani ne a ranta kala-kala.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×